Sashe 43
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai tsaye nace"Wai shin sau nawa zan fada maka wannan maganar ne? na fada maka cewa ba zan ta'ba amincewa da kai akan sa'bon Allah ba ranka ya dad'e ba zan baka kaina ba koda kuwa zaka sa min bakin bindiga a mak'ogwaro na wallahi akan na baka kaina sai dai ka kashe ni."!!!
Ya dinga kallona fuskarsa tana rikicewa da wani 'bacin rai gabad'aya kammaninsa sun sauya! nima idanuna nasa masa ina tabbatar masa da gaskiyar maganata........Motsin bude kofa ne yasa gabad'aya muka kalli bakin kofar, gimbiya Lawisa ce ta shigo cikin shiga ta alfarma da alama kwalliyar ta mussaman ce, ganinmu daf da juna yasa nan take yanayin fuskarta ya sanja da zallan 'bacin rai.
Matsawa nayi daga jikinsa na sunkuyar da kaina gabana na wani irin fad'uwa, Gimbiya Lawisa ta karaso kusa damu shashshekar kukanta naji tana magana........ da sauri na dago kaina ina kallonta ina kuma mamakin abinda take fada, tana wani irin kuka ta cigaba da cewa"Yanzu meye a jikin wannan mummunar yarinyar da har kake rungumeta a jikinka ashe dama ba aikin abinci kawai take maka ba tana biya maka bukatarka idan ta tas........Wani gigitacan mari ya kwada mata ido jajawur yace."Kada ki sake jifan mu da wata mummanar kalma kawai saboda kin shigo kin tarar damu daf da juna sai ki fassara da wata manufa ta daban! wallahi idan kikayi wasa akan wannan dalilin sai na janye maganar auranki dama ba sonki nake ba takura min akeyi.'
Lawisa gumi ya dinga yanko mata kai amma Yarima baida kirki a gaban baiwa ya kwada mata mari yana fadin ba sonta yake ba.sunkuyar da kanta tayi takaicin duniya ya isheta wai shin ya za tayi ta janyo hankalinsa a kanta, tsaki yaja mai karfi ya wuce ya bar mu a tsaye a gurin..
Ganin ya futa yasa nima nayi yunkurin barin gurin, da sauri ta tari gabana na kalleta ta kalleni cikin tashin hankali tace''Sumayya ki fada min abinda ke tsakaninki da Magajin sarki." Cikin jarumta nace"Ke me kika gani a tsakaninmu."? a fusace tace"Wace irin magana kikeyi wannan ki bani amsar tambayata." nace"To babu wani abu dake tsakanina dashi."
"Babu abunda ke tsakaninki dashi na ganku dab da juna." Cikin k'osawa nace"Duba kirjina ki gani'' ta dinga wulkita idanunta tana dubawa. nace"Me kika gani."? ''Naga kamar kin kone." Kai tsaye nace"Shi ya 'kona ni da kunun gyada mai zafi haka kawai banyi masa komai ba, idan kina so ki tabbatar ga sheda nan." na nuna mata kayan dake watse a gurun, a sanyaye ta kalleni tace"To me yasa na ganku dab da juna?" kaina na dafe cikin damuwa nace"Nadama yayi da abinda yayi min shine yake min tofi a gurin 'kunar."
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Allah ya taimake ki kin fada min gaskiya kuma naga sheda a zahiri wallahi da baki fada min gaskiya ba da sai na dauki mataki mai tsauri a kanki''' cikin takaici nace ranki ya dade na baki shawara."? tace"Ina jinki." nace "Ki rage son Yarima domin idan kika bari ya gane zaki sha wahala tunda gashi a gabana yana fadar shi takurashi akayi akan ya aureki.'"
Bina tayi da kallo ta kasa cewa komai, ganin haka yasa na sunkuya na kwashe kayan dake watse a gurin, kicin na kai na fito na sameta a tsaye a inda take, goge gurin daya 'baci nayi tas na mayar da Mopar na fito na sameta a tsaye sai kace gunki sai tunani take tsaki naja a zuciyata na kama hanyar futa ina fadin shashasha mara tunani.
Ban shiga gurin mu ba sai da na samu Haruna na fad'a masa labari mai dadi.
Haruna ya dinga murna yana godewa Allah, a gurin yayi sujjadar godiya ga Ubangiji ya mike yana mana kyakkyawar addua.
Jigum-jigum! na samu iyayena a tsakar gida, gwiwata tayi sanyi d'an farin cikin dana shiga dashi ya dauke, guri na samu na zauna ina tambayarsu..
A sanyaye Tambaya tace"Maimartaba ya aiko mahaifinki yaje koda yaje fada sai yace masa maganar auranki da Haruna tana nan dan haka suje su cigaba da shiri shi bai bada goyan baya Yarima ya aureki ba. Sumayya lokacin da naji wannan maganar sai da na kusa kuka gaskiya naso ki auri magajin sarki."
Murmushi nayi nace"Tambaya ki daina damuwa dan Allah tunda kikaga Allah yayi haka to shine alkairi." babana yace."Nima abinda nake ta so ta gane kenan amma taki fahimta sai damuwa take."
Nace"Hakane baba duk yanda Allah ya tsara haka zamuyi hakuri mu kar'ba nima naso na auri Yarima saboda ganin yanda kuka nuna farin cikin ku amma tunda kukaga Allah ya zartar da wannan hukunci to shine alkairi ni daku sai mu barwa Allah ikonsa'' na fadi hakane domin na kwantar musu da hankali amma ko daya bana fatan auran Yarima saboda nasan da aniyar da zai aureni nafi sha'awar auran Haruna saboda nasan shine daidai dani kuma yana min kaunar da Yarima ba yayi min irinta.
*****
Bayan sati biyu al'amura suka cigaba da gudana yanda ya kamata, maganar aurena da Yarima ta rushe tsakanina kuma da Haruna a kullum 'kauna da sha'kuwa na kara 'karuwa a tsakaninmu yanzu mun kwantar da hankalin mu mun daina fargabar abinda zai faru tunda Maimartaba ya shiga cikin al'amarin mun san dole duk wanda yake adawa da auranmu ya hakura, ta 'bangaran Yarima kuwa kullum babu yabo babu fallasa a tsakaninmu ya zuba mana ido dan tun ranar daya 'kona ni wata magana mai tsayi bata sake shiga tsakaninmu ba, kullum ina shiga nayi aikace aikace na baya ce min kanzil sai magana ta kama sannan zai kulani naji dadi sosai daya janye jikinsa dani ina adduar Allah yasa ya hak'ura ya rabu dani nayi rayuwata hankali kwance..................Cikin shiri ya sauko ya same ni ina goge-goge yace."Sumayya bana tsammanin zan zauna nayi breakfast." kallonsa nayi yana gyara necktie d'in wuyansa nace"Ranka ya dad'e yana da kyau dai ka zauna ka karya kafin ka futa idan ka zauna a ofis baka da lokaci saboda jama'a." Girgiza kansa yayi yana gyara gilishin idonsa yace." Ba zan iya tsayawa ba amma ki bawa Haruna ko Hamza kayan breakfast din ya kawo min ofis." Nace"To shikkenan ranka ya dade Allah ya bada sa'a." Amsawa yayi tare da kama hanyar fita, har ya kai bakin kofa ya tsaya na kalleshi saboda nasan da abinda ya tsayar dashi, yace."Na bar bedroom dina a bude ki gyara min har toilet." nace"To insha Allahu zan gyara."
Fita yayi ni kuma da sauri na hau saman domin gyara masa dakin kamar yanda ya 'bukata.
Koda ya shigo falon yaji shuru kai tsaye kicin ya nufa nan yaga komai a shirye akan tire ajiyar zuciya ya sauke, yaji dadi sosai da samun komai a kammale, hannu yasa ya dauko wani abu a cikin aljihunsa, ya kwance abun dake cikin wata bak'ar takarda, bud'e fulas din yay nan yaga miyar taushe wacce taji gyada da watadaccan nama, sai kamshi take, gabadaya ya zazzage abinda yake cikin takardar a cikin miyar yasa spoon ya juya sosai maganin ya 'bace a cikin miyar, rufewa yayi da sauri ya fita daga kicin din yana addua Allah yasa bukatarsu ta biya.
Tsaf na gyara masa dakin nasa turaran wuta mai kamshi kana na sauko kasa, kicin din na nufa a gurguje na had'a komai a cikin wani kwando na mussaman
Hannuna rike da kwandon dake dauke da abincin na fito na samu Haruna shi kadai a zaune , ina mirmushi nace"Sahibi kana zaune kai kadai ina Hamza ya tafi ya barka cikin kadaici." kallon kauna yayi min yace."Hamza yaje gurun iyayensa domun su gaisa nima abinda ya hanani tafiya ina jira ki fito nayi tozali dake.
Murmushi nayi cikin kauna nace"Haruna kenan to gani na fito ina fata kaji dadi daka ganni." Yace."Naji dadi sosai Sumayya jiya kwana nayi ina mummunan mafarki sai nake ganin kamar na kusa rabuwa dake Sumayya mafarkin jiya ya bani tsoro wallahi."
Ji nayi gwiwata tayi sanyi nace"Haruna dan Allah ka daina irin wannan maganar bana so insha Allahu babu abunda zai rabamu nasan har yanzu kana fargaba akan lamarina da Yarima to ka kwantar da hankalinka tunda Maimartaba yace dole ya hakura ai magana ta kare."
Murmushi yayi yace."To shikkenan Sumayya insha Allahu na daina damuwa sannan kuma ina rokon Allah ya cika mana burinmu." Cikin jin dadi na amsa da ameen ya rabbi."
Nace"Magajin sarki yau ya futa da sauri da alama akwai abinda yasa ya kasa tsayawa ya karya kummalo shine yace idan na kammala komai kai ko Hamza wani ya kai masa ofis."
Yace."To babu damuwa ai tunda Hamza baya nan bari na kar'ba kawai na kai masa."
'Dan 'bata fuska nayi nace" bana so kasha wuya naso Hamza yana nan da shine zai kai masa.
Dariya yayi ya mike tsaye yace." Sumayya kenan kamar yanda bakya so na wahala nima haka wallahi dani mai iko ne da duk wannan wahalar bakiyi ba." murmushi na dinga saki ina kallonsa, ya kar'bi kwandon abincin daga hannuna, tare muka jera har gurin da motoci suke, nayi wa daya daga cikin direbobin bayani a take ya mi'ke had'e da bud'ewa Haruna mota ya shiga, shima ya zauna a mazauninsa, hannu na daga masa da murmushi a fuskata nace"Sai ka dawo." shima da kyakykyawan murmushi a fuskarsa yake daga min hannu, na dinga mamakin yanda fuskarsa ke fitar da annuri murmushin da yake min yayi yawa dan har direba yaja motar bai dauke idonsa daga kaina ba, a sanyaye na nufi gurinmu gabana na faduwa kadan kadan...
Koda ya isa ofis ruwan coffee kawai yasha yaji ya gamsar dashi, kawai sai ya cigaba da aikin dake gabansa, yayin da marasa lafiya keta shige da fice a asibitin...............Haruna a nutse ya fito daga motar bayan direba yayi parking a gurin da aka tanada, kai tsaye cikin asibitin ya nufa, da yake yasan ofis din nasa kai tsaye kofar ya nufa, masu gadin kofar suka dakatar dashi. sai da daya ya shiga ya sheda masa tukkuna ya fito ya bashi umarnin shiga.