← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 90

Sashe 27

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Na kudi ne..!*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar biyan kudin karatu ga yanda abin yake.....Vip gruop#600 normal group #300 account... 0542382124...Binta umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084563262*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
53&54
Wai shin da wane ma'auni zan auna irin wulakancin da guy nan yake min? me nayi masa kullum yake wulakanta ni yake cin zarafina yana tozartani! a ganina ban cancanci haka daga gurinsa ba, ina ruwansa da alaqata da Haruna da har zai dauki zafi! ya kiramu fasikai wannan kalma daya kiran mu da ita tafi damuna akan watsa min fruit salad din da yayi.
Hannu nasa na share hawayen daya kasa daina zuba, na mike jikina a sanyaye na shiga gyara gurin ina jin wani irin zafi a zuciyata tsaf na gyara gurin na nufi kofa da niyar fita, kicibus mukayi da Haruna kallona ya shiga yi yana nazari, nayi saurin sunkuyar da kaina ina kokarin magana yace."Sumayya me ya 'bata miki jikinki."? Ji nayi zuciyata ta karye hawaye suka zubo min, murya na rawa nace"Haruna muje kada ya sauko ya same mu a tsaye."

A sanyaye ya bude min kofa na fita ya biyo bayana, sai da mukayi nisa sosai na sheda masa abinda ya faru Haruna shuru yay yana girgiza kansa yace."Sumayya ni dai banga abinda mukayi wanda ya kaucewa sharia ba amma zan kiyaye shige miki idan kina gurin kada wata maganar ta sake biyo baya.

Nace"Nima haka na gani amma wannan shawarar daka yanke itace tafi amfani idan kana so muyi hira ka bari idan na gama abinda nakeyi na fito sai muyi hirar." Yace."Babu damuwa anjima zan sanar da mahaifina maganar auramu sai ya samu baba Lawi su tattauna." Murmushi nayi nace"To shikkenan hakan yayi.'

Haruna har sashenmu ya rakani na sanjo kaya na fito ya rakani sashen Ciroma domin amsa kiran da Gimbiya Lawisa keyi min.

Samun ta nayi a hakimce bayin ta sun kewaye ta sai fadanci sukeyi durkusawa nayi ina gaisheta, a wulakance ta amsa, ta dubesu tare da basu umarnin tashi. da sauri suka bar gurin.

Minti biyar a tsakani naji muryarta." Sai yanzu ki kaga damar zuwa."? cikin nutsuwa nace"Afuwa ranki ya dade aiki nake a lokacin da kika aika kirana ki gafarce ni."

Shuru tayi tana watsa min kallon banza tace"Sumayya anya kuwa kina aikata aikin da nake sanya ki kuwa nifa bana ganin canjin komai a gurin Yarima kullum iskanci yake min ya'ki ya dinga nuna min so da kulawa.

Nace"Haba ranki ya dade ba zan ci amanarki ba ina aikata aikin ki akan tsari kin san komai sai a hankali insha Allah zaki shawo kansa zai soki ya kaunaceki tamkar ransa.

Murmushi tayi tace"Sumayya shiyasa nake sonki domin kina kwantar min da hankalina amma al'amarin Yarima Ali ya soma bani tsoro wallahi.'"

Murmushi nayi nace"Ranki ya dade ki yawaita addua kina rokon Allah ya janyo miki hankalinsa kanki gefe guda kuma kina 'yan daburu irin namu na mata.

Gyara zamanta tayi tace"Sumayya duk dabaru na sun kare wallahi kullum na kai masa ziyara da fada muke rabuwa gabadaya ma ni gani nake kamar tunaninsa na wani guri bana gabansa.

Shuru nayi ina nazarin abinda zance mata naji tace"Ko kina ganin na bashi kaina ne."? na kalleta da sauri inayi mata kallon mara hankali .....Tace"To Sumayya duk wasu dabaru nayi ya'ki karkato da hankalinsa kaina.

Nace"Ranki ya dade idan kika bashi kanki ya sanki a matsayin mace ai kin cutar da kanki ko kunyi aure ba zakiyi daraja ba kuma wulakancin da zaiyi miki sai yafi nada, kada kiyi wannan gangancin ki cigaba da dayin 'yan dabaru insha Allah za'a dace."

Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke tace"Shikkenan Sumayya zan cigaba da bin shawararki." Nace"Yawwa ranki ya dade......Akushin dake gabanta tace"Ki dauka wannan ki kai masa farfesun kifi ne nayi masa ki tabbatar yasha farfesun dan na zuba sinadarai a ciki kuma ina saka ran zanci galaba."

Nace"Angama ranki ya dade yanzu kuwa zanje na aikata aikin ki." Akushin na dauka na rike hannu biyu nai mata sallama na bar gurun......Lantana dake la'be tana ganin fitowar Sumayya a hankali tabi bayanta

Ina isa inda nake zubar da kayan asirin na waiwaya ko'ina sai dana na tabbatar da babu kowa a gurin na watsar da farfesun da sauri na rufe akushin na bar gurin ina jin takaicin abinda ke faruwa.

Ko zaman minti goma banyi ba sakon kiran Lawisa ya iskeni, Cike da mamaki nake kallon 'Yar aiken, inaso nayi magana Babana ya katseni da fadin na tashi naje....jikina ya bani akwai wani abu mikewa nayi nasa takalmana nabi bayan 'Yar aiken.

Tsaye muka sameta tana kaiwa da kawowa a gurin, fuskarta kawai ta isa ta nuna min akwai matsala "Ranki ya dade gan......Kafin na karasa ta wanka min mari! tana huci tace" Sumayya ashe dama munafurta kikeyi ? ashe duk abinda nake baki zuwa kike kina zubarwa.''

Gabana ya yanke ya fadi baki na rawa nace"Ranki ya dade waye ya fada miki haka? wallahi karya ne ina bin umarninki.'' Wani marin ta sake kawo min nayi saurin kaucewa ina binsu Lantana da kallo sai 'kus-'kus sukeyi tabbas a cikinsu wata ta kawo gulmar.

"Bazan yarda da rantsuwarki ba Sumayya sai kin tabbatar min da gaskiyar magana daga bakin ki kana kuma ki nuna min inda kike zubar min da kaya.''

Shuru nayi zufa na keto min.

" Ke nake saurare 'yar iska munafuka kawai."

Naji ciwon zagin da tayi min amma sabida nasan nice bani da gaskiya yasa na cije nace"Ranki ya dade dik wacce ta kawo miki gulma gaskiya ne duk wani kayan asiri da zaki bani nasawa Yarima abinci da ruwan sha zubarwa nake a wani kebantacen guri idan baki manta ba ko dazu sai dana sake tunasar dake cewa asiri ba zai janyo miki kauna da so ba nace miki ki dage da addua sannan kuma ki canza salo, wannan dalilin yasa nake zubarwa saboda ba zan jefa kaina a halaka ba."

Huci! ta dinga yi tana kallona tace"Shin kin san irin mak'udan kudin da ake fitarwa kafin a 'karbo maganin nan kuwa."? shuru nayi mata tace"Lallai Sumayya baki da mutunci kuma wallahi sai na dauki tsatstsauran mataki a kanki ki shige muje ki nuna min inda kike watsar min da kaya."

Nace"Ranki ya dade ki gafarce ni banyi hakan dan na bata miki rai ba ina guje miki fushin Alla....Hannu tasa ta gwabe min baki! rufe min baki munafuka kawai wallahi sai naci mutuncinki a gidan nan." shuru nayi ina kallonta tasa takalmanta tayi gaba suka rufa mata baya, sai da sukayi nisa kana nabi bayansu..

a gurin na same su Lantana tana nuna mata ramin da nake zubawa. juyowa tayi tana kallona na sunkuyar da kaina kasa, rai a bace ta juya suka rufa mata baya.....wata rumfar bukka na samesu sai zurga zurga take tana magana dasu.

Ina karasowa gurin tace nasa gwiwata a kasa, nayi yanda tace kallonsu tayi tace su biyo layi kowacce ta mare ni hagu da dama.

Mikewa nayi ina kallonta nace"Ranki ya dade ke nayi wa laifi dan haka ke zaki hukunta ni basu ba.''

"Sumayya so nake ki 'kask'anta yanda kika sa raina baci kema naki sai ya 'baci."!

" Ranki ya dade ki gafarce ni ba zan zauna wanda muke matsayi daya dasu su mare ni ba gaskiyar magana kenan."

Tana huci! tace"Ni kikewa gardama ko."? kasa nai da kaina babu yanda xa'ayi na zauna su Lantana su mareni duk abinda za tayi sai da tayi.

"Lantana je ki kirawo min Buba kice yazo da bulalarsa." Lantana da sauri ta tafi....hannu ta goya a baya ta shiga zagaye gurin
cikin zuciyata nace wahalalliyar banza da wofi kawai.

Buba da Haruna na tare suna hira Lantana ta isa gurin ta shedawa buba kiran da ake masa, Buba yace kije ganinan zuwa...

Haruna jikinsa ne yay sanyi yace"Buba dan Allah kada ka doki Sumayya akan gaskiyarta."Buba yace."Idan tana tsaye a gurin dole nabi umarninta idan ta bar gurun zan kyaleta amma dai duk da haka zan dinga dubarar dukan kasa a madadin ita nake duka."

Yana kare maganarsa yay saurin barin gurin, Haruna jikinsa dik yayi sanyi kwata kwata baya so a ta'ba lafiyar Masoyiyarsa. yana kokarin mikewa Buba ya karaso gurin hannunsa nannade da murtukekiyar bulala mai baki biyu, ko sauraransa beyi ba yay gaba.
Haruna da sauri ya nufi sashen Yarima domin ya sheda masa abinda ke faruwa.

Sai da gabana ya fadi ganin katuwar bulalar dake hannun Buba, gumi ya dinga tsiyaya a jikina dana sani na yarda su Lantana sun mareni da tuni an wuce gurin.

"Ranki ya dade gani." Buba ya fada yana me kaskantar da kansa....

jajayen idanunta ta watsa masa tace"Buba so nake ka zane jikin Sumayya har sai rigarta ta yage wallahi idan ka sassauta mata sai ka fuskanci hukunci daga gurina."

Murmishi yayi irin na mugunta yace."Angama ranki ya dade." Bulalar ya daga da karfi gaske ya labta min a gadon bayana, kara na saki na rintse idona ina jin radadin zafi a inda ya doke ni....Gimbiya Lawisa murmushi tayi suma su Lantana suka soma dariya, ido jawur nake kallonsu....Buba na dariyar shakiyanci ya sake daga bulalar zai labta min "Kai kar ka daketa." da sauri na bude idona! yana tsaye a gurin haruna na gefansa gani nayi kowa ya shiga hankalinsa har ita Lawisan ta sunkuyar da kanta.

Hannu nasa na sharce gumin goshina ina godewa Allah da zuwansa gurin........'"Kai buba me tayi maka kake mata irin wannan dukan."? yana watsa masa harara yake maganar. Buba yace"Ranka ya dade umarnim gimbiya lawisa ne amma ni Sumayya ba tayi min komai ba."

Yace."To duk ku bar gurin nan." Buba dasu Lantana suka bar gurin...yunkurawa nayi zan tafi yace."Ke! ku sameni a gurina domin naji ta bakin kowa dan na fahimci akwai rashin jituwa a tsakaninku.'' gurin ya bari haruna yabi bayansa.
Kawai sai na tsinci kaina da watsa mata kallon banza a fusace na bar gurin....Gimbiya lawisa a sanyaye ta nufi sashen Yarima saboda tana tsoron abinda zai biyo baya tana tsoron ya tozarta irin na kwanakin baya
Chapter 27 · 0% Book details