← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 90

Sashe 53

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acp ya bashi hannu yana kokarin mikewa yace."Haba abokina ai babu komai ka daina godiya dan Allah kafi karfin ayi maka komai kuma kada ka manta binkice da kare rayukan al'umma a kanmu yake kaga kuwa dole ne mu tsaya maka a cikin al'amuranka har sai munga komai ya daidaita." Murmushi yayi ya mika masa hannu sukayi musabaha, hannunsu a hade suka fita daga falon.

Bayan fitar su na jima a zaune a falon ina nazari mikewa nayi da sauri na kama hanyar fita, sai nayi karo dashi, fuskarsa kawai na kalla naji jikina ya mutu, kana ganinsa da yanayinsa zaka gane yana cikin tsananin damuwa kawai dan dai yana da kokari ne, tausayinsa ne ya rufe na koma falon ina kallo ya zauna kasan kafet, a sanyaye nace"Na kawo maka kayan karin."?Girgiza kansa yayi yace."Sumayya bana tsammanin zan iya cin wani abu yanzu cikina ya cunkushe da damuwa."

A sanyaye nace"Ka barwa Allah komai da sannu zai kawo maka sauki kada kayi wa kanka horon yunwa." Girgiza kansa yayi bece min komai ba ya cigaba da kallon guri guda.

Nace"Na kawo maka ko."? kansa ya daga alamun "Eh." da sauri na dauko tire din dana shirya kalacin......a gabansa na ajiye, yace."Hada min tea." da sauri na had'a masa, hannu yasa ya dauka yana kur'ba yana kallona, soyayyan dankali da kwai na zuba mishi a plate nace"Ka dinga hadawa da dankalin." Shuru yayi min ya cigaba da kurbar tea din ba tare da ya dauki dankalin ba......a sanyaye na mike da fadin."Ni zan tafi." Ban jira ya amsa ba na kama hanyar fita...."Sumayya." sunana ya kira na juyo ina kallonsa.
"Kizo ki karya kema." girgiza kaina nayi nace"Nace"Na karya a gurinmu." Bata rai yayi yace."Wannan uban dankalin da kika zuba waye zai ci miki." ? kai tsaye nace"Kaine zaka cinye abinka." Girgiza kansa yayi yace."Idan kina so naci to zo ki zauna ki taya ni ci bana so ki tafi ki barni cikin kad'aici.'' Kallan mamaki nayi masa, ya dage min gira yana lumshe idonsa gabadaya ji nayi gwiwata tayi sanyi a duk lokacin da zaiyi min irin wannan kallon nakan shiga cikin wani irin yanayi.

"My love." a firgice! na kalleshi, yayi murmushi da fadin"Meye na furgita dan na kira ki da wannan suna. Nace"Dan Allah ka daina kirana da suna nan."
"Saboda me."? nace" Kawai dai bai dace ba." Yar dariya yayi yace."Sumayya kenan to zan daina amma ba yanzu ba." Nace"To nagode." Juyawa nayi zan bar gurin, Yace."Kada ki fita." Dafe goshina nayi cikin yanayi na damuwa na juyo ina kallonsa.
Yace.'"Na dame ki ko."? shuru nayi, "Ki dawo ki cinye dankalin ki." Saboda ya barni na tafi yasa na koma na zauna, kusa dashi.

Plate din dankalin ya turo min yace."Oya had'a tea mai kauri ki hada da dankalin ba zan barki ki fita ba sai na tabbatar da cewa cikin ki ya cika......ba tare da nayi masa musu ba na tsiyaya tea din daidai misali, ido ya tsira min da cup din tea a hannunsa ya bar kur'ba kawai yana kallona.

Nace"Wannan kallon da kake min yayi yawa za kasa na k'ware dan Allah ka dauke idonka." Ba tare da yace uffan ba ya dauke kansa cigaba yayi da kur'bar tea dinsa, a nutse nake kur'bar tea din ina had'awa da dankalin, ina kallonsa yana kallona ta gefan ido cikin zuciyata nace"Wannan idan maye ne ya kama mutum sai ya kasheshi na rasa abinda yake kallo a jikina.
cikin damuwa na ajiye cup din tea d'in! kawai naga ya ajiye nasa ya dauki nawa, daidai saitin bakina yasa a bakinsa ya sumbuta kafin ya fara kur'ba! ya wani tsatstsare ni da ido, jikina ne yayi sanyi na dinga jin shigar bakon yanayi sunkuyar da kaina kasa nayi kwata-kwata bana san kallonsa saboda yanayin yanda yake sarrafa idonsa a kaina yasa naji bani da kuzari....Cup din tea din ya ajiye a gabana yana nuna min inda bakinsa yake wai na dauka nasha!! kawai na tsinci kaina da bin umarninsa, ina kokarin daidaita bakina a inda yasa nasa Lawisa ta shigo falon, cikin shigar alfarma 'kamshin turaranta duk ya game gurin, 'Kwarewa nayi nayi saurin ajiye cup din ina kallonta a yayin da take kokarin karasowa gurin da muke, sunkuyar da kaina nayi naganin yanda taci kunu! mikewa nayi da sauri, yace."Sumayya koma ki k'arasa.''! girgiza kaina nayi nace."Ranka ya dade na'koshi.'' ido ya tsira min yana so ya tabbatar da maganarsa, Gurin na bari ina fargabar kallon da Lawisa takeyi min..

Kallonta yayi sama da kasa babu laifi tayi kuma za'a huta da ita Lawisa nada kyawun jiki gata fara tas jikinta dam sai dai bata da tsayi sosai, kusa dashi ya nuna mata wai ta zauna, zama tayi tana wani cin magani tace......

*Na kudi ne!*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya, keda kika futa da littafin keda Allah idan kina so ki biya ga yanda abin yake....Vip gruop#600...normal#300 account... 0543282124....Binta umar gtnank....idan kati zaki turo#400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:27 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
84
"Wai dan Allah me yake tsakanin ka da wannan yarinyar ne? a gaskiya kusancin da nake gani a tsakaninku yana d'aga min hankali wallahi! nasan dai kafi karfin kace kana sonta tunda a karkshinka take to me zai sanya ta dinga zama kusa da kai tana cin abinci da kai."? Cikin yanayi na bacin rai ta karashe maganar,

Shuru yayi yana kallon guri guda bai ce mata uffan ba, Lawisa ta sake sha'ka! murya na rawa tace" Da kaifa nake magana kana jina kayi shuru shin kasan irin son da nake maka kuwa."?

A nutse ya dago kansa yana kallonta, yace." Babu abinda yake tsakanina da ita sai mutunci kada ki manta wannan yarinya itace amintaciyyar baiwa ta yanda na amince da ita ko ke ban amince dake ba saboda haka ki daina damuwa idan kin ganta a kusa dani idan da yiwuwar na aureta zan aureta babu ruwana da 'kas'kancinta."

Lawisa wasu zafafan hawaye suka shigo zubo mata a kumatu tace"Yanzu kai dan Allah sai ka auri yarinyar nan shin me ka gani a tare da ita wanda ya burgeka dan Allah kada kayi min haka kada ka had'ani kishi da wannan ma'kaskanciyar idan aure kake so ka auri 'yar mulki irina amma ni nafi karfin nayi kishi da wannan yarinyar."

Gyara zamansa yayi yana kallonta fuskarsa a 'bace! yace." Ni baki isa ki tsara min ga yanda zanyi ba, Sumayya baiwa tace kuma ta cancanci na aureta na 'yantata daga baiwa ta dawo mai 'yanci! Sumayya ta nayi min abinda ke bakiyi min ba, sannan naji kina fadin cewa mai na gani a tartare da ita nagarta da kyawawan halaye nagani har yasa nayi sha'awar auranta nasan kin san hakan ba haramun bane ko? zan aureku ku biyu a rana daya daga yau kisa a ranki mijinki mijin mace hudu ne bayan na aureku zan iya kara biyu sannan inyi kwarkwara idan ina da ra'ayi saboda haka kada ki kara zama a kusa dani kice zaki tsara min yanda zan tafi da rayuwata."

Lawisa hawaye kawai take sharewa tana kallonsa tsabar bakin ciki da takaici ya hanata cewa komai, da shashshekar kukanta ya dameshi mikewa yayi ya haye sama ya barta zaune a gurin tana kuka na rashin madafa.

"Lallai wannan yaro bashi da kirki wato ta inda ya 'bullo kenan? ya rasa yarinyar da zai aura sai baiwa makaskanciya wacce take karkashinki da ita zai hada ki kishi lallai kuwa zanje na samu mahaifiyarsa akan maganar." Hajiya Karima mahaifiyar Lawisa ce ke wannan bambamin.

Lawisa na kuka tace."Wallahi Hajiya ni kaina nayi mamakin al'amarin kuma abin ya tsoratar dani mutuka dan banyi tsammanin zai iya auranta ba saboda nasan kin san yanda yarinyar take da muni gata 'baka wai har cewa yake zai aureta saboda kyawawan halayenta sannan harda cewa tafi ni a gurinsa sau dubu."

Hajiya karima na girgiza kafa tace"Ki daina kuka kina damunki insha Allah idan 'kura ta lafa zan samu mahaifiyarsa da maganar dole ya za'ba ke ko baiwa dan kinfi karfin kiyi kishi da baiwar gidanku."

Kai tsaye dana fita daga bangaran Yarima gurinsu Haruna na nufa, nan na samu gurun da jama'a sun kewaye mahafiyarsa suna tausarta, ganin yanda idanun jamaa yayi caaa a kaina yasa nayi niyyar juyawa, wata mata dake bakin kofa tace"Aa sumayya ya zaki koma kuma ki shiga mana."

Simi-simi na shige gabana na faduwa na zauna a gabanta ina gaisheta, da kyar ta amsa min tana harara jamaar dake kusa da ita suna taya ta, shuru nayi na minti uku kafin nace"Ubangiji Allah ya jikan Haruna da dukkanin musulmin daya rigamu gidan gaskiya." Tsiraru ne suka amsa adduata, na cigaba da cewa"Lami akwai wata igiya da take daure a hannun Haruna dan Allah ita nake so ki bani domin za'ayi binkice akai."

Hannu ta daga min tace."Sumayya wane binkice kuma bayan bukatarki ta biya kin kasheshi domin ki samu nasarar auran Yarima to bari kiji duk halin da kike ciki keda iyayenki mun sani Yarima ya bukaci ya aureki a lokacin da baikon Haruna akanki koda Maimartaba ya samu labari yace ba za'ayi haka ba dole ki auri Haruna Shi Yarima ya hakura, da kuka ga haka sai kuka shirya kashe Haruna saboda biyan bukatarku ko ba haka bane."?

Ina kuka nace"Hakane maganarki amma inaso ki sani wallahi bamu muka kashe Haruna ba kwanansa ne ya 'kare kuma ni ko kusa ko alama bana kaunar na auri Yarima saboda wani dalili nawa, wallahi nafi bukatar na auri Haruna domin shi nake so muna san junanmu aka shiga tsakaninmu dan Allah kada ki sake wannan maganar Bamu kashe Haruna ba."

Tsaki taja tace"Ni dan Allah ki tashi ki bani guri bani da wata magana dake a yanzu." Hannunta na rike ina kuka nace"dan Allah kiyi hakuri ki dauko min igiyar nan wallahi binkice za'ayi a kanta." Wacce take kusa da ita tace"Ke munafuka tashi ki futa ko kuma yanzu muyi miki duka wallahi wane irin binkice za'ayi bayan mun san gaskiyar lamari zaki zo ki nayi mana kukan munafurci."
Chapter 53 · 0% Book details