Sashe 44
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kanshi a kasa yana rubuce rubuce jikin wata takarda ya amsa sallamar Haruna, haruna yaja gefe ya tsaya hannunsa rike da kwandon abincin, sai bayan kusan minti goma ya dago kansa, Haruna da sauri ya mika gaisuwarsa, babu yabo babu fallasa ya amsa, Haruna yace.''Ranka ya dade Sumayya ta aikoni da kayan karin kummalon ka." Yayi shuru yana kallon takardar dake gabansa, dagowa yay a nutse yace."Haruna kaje da abincin nan ba zan iya cin komai ba yanzu idan kuma kana bukata kaje ka samu wasu su taya ka ci''
A sanyaye yace."To godiya muke ranka ya dad'e Allah ya taimaka maka a cikin dukkunanin al'amuranka." Ya amsa da amin ya Allah. hanya ya nuna masa da hannu da fadin"Kana iya tafiya." Haruna da sauri ya bude kofa ya fita bayan yayi masa fatan tashi lafiya.
Haruna yana fita direba ya samu yace ya fito su samu wani guri suci abincin dan wanda aka kawowa baya bukata, Direba da sauri ya kulle mota suka samu wani 'ke'bantaccan guri a cikin asibitin suka zauna a nutse suka fito da kayan abincin.........Funkaso ne shar dashi yana ta kamshi, suka bud'e fulas din miya yawun bakinsu duk ya tsinke, cikin plate suka zuba funkason da yawa suka lafta miya da uban nama, suka shiga ci suna hira, bayan sun gama ci da minti biyar gabad'ayansu suka fice daga hayyacinsu suka dinga mur'kususu a gurin suna matagugu! da ri'ke cikinsu!! salati suka shigayi idanuwansu suka kafe suna kallon sararin samaniyya, babu shakka gubar da'aka zuba cikin abincin mai karfi ce dan anan take Haruna ya fadi a gurin rai yayi halinsa, minti goma a tsakani direban shima ya fad'i yana kiran sunan Allah....
*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi baki biya ba, keda kika futa da littafin keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake....Vip group #600 normal group #300....account... 0542382124..Binta umar gtbabk...idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKAWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊ðŸ?)
75&76
Koda na fito samun Haruna nayi shi kadai a zaune ya zabga uban tagumi! kai tsaye inda yake na nufa a sanyaye na zauna a gefansa kallonsa nayi a nutse na kira sunansa Ya dago yana kallona da jajayen idanunsa, tausayi ya bani saboda nasan irin kaunar da yake min, nace"Haruna kada ka tayar da hankalinka akan wannan maganar Yarima bai isa ya raba tsakaninmu ba.'"
Cike da mamaki yake kallona kafin yace."Sumayya kin san bani da kwanjin da zanyi gogayya da Yarima a gurun neman auranki dole na hakura dake na bar masa."
Nace"Haba Haruna kada ka bani kunya mana me yasa zaka karaya da wuri ashe dama duk so da kaunar da kake min suna ya tara ba zaka iya tsayawa a fafata da kai ba."
Girgiza kansa yayi yace."Sumayya kenan ba zaki gane abinda nake nufi ba, ki sani ni bawa ne wanda yake karkashin masarauta dole ne nabi umarni koda kuwa hakan na barazana da rayuwata tilas na janye maganar auranki kamar yanda ya bukata cewa na sanar da mahaifina halin da ake ciki to dole na fada masa ya samu mahaifinki ya sheda masa halin da ake ciki."
A sanyaye nace"Amma ban ta'ba tsammanin haka daga gurunka ba wallahi na raina kaunar da kake min daga magana guda har ka karaya ka janye na yarda kaima ba sona kake ba sha'awata kake.'' rai a bace na mike zan bar gurin da sauri yace."Sumayya duk me ya janyo wannan maganar dan Allah ki tsaya ki saurare ni wallahi karfina akafi akan soyayyarki amma ina me tabbatar miki da cewa da wani ne ba Yarima ba to da sai inda karfina ya 'kare.''
Saboda yanda nake jin zafi a zuciyata yasa ko tsayawa banyi ba bare na saurari maganarsa, gurinmu na shiga raina a 'bace."
Kai tsaye k'uryar daki na shiga na kwanta hawaye ba zuba a kuncina Yarima zai gwada iko da mulki ya aureni domin ya biya bukatarsa daga baya ya sake ni anya kuwa zan iya amincewa da wannan al'amarin.
"Sumayya." Muryar Tambaya naji tana kirana, da sauri na goge fuskata na amsa da "Na'am." Tace."Yawwa ashe kin shigo kinga ni ina zaune zaman jiran shigowarki bacci ya dauke ni babanki ma bai shigo ba ko."?
Nace"Eh bai shigo ba ai lokacin dana shigo kina bacci shiyasa." Tace"Eh yanzu ma motsinki naji na farka akwai kwad'on zogale a kicin na ajiye miki." Nace"To kafin na kwanta zan dauka naci.''
Shuru tayi ba sake magana ba da alama bacci ne a kanta, sai da aka jima tukkuna na mike a hankali na fita na dauko kwadon zogalen a tsakar gidan na zauna nasa kwanon zogalen a gabana na garara ci gabad'aya hankalina ya dauke gurin tunani naji muryar Babana a kaina....da sauri na dago kaina ina kokarin kawar da damuwa ta nace"Baba ka shigo." a sanyaye yace."Eh tun dazu nake tsaye a kanki ina magana baki ji ba." Shuru nayi ba wai dan bani da abin fada ba."
Yace.''Ki dauko kwanon abincin ki shigo ciki akwai maganar da zamuyi.'' naji gabana ya fadi jin abinda yace binsa nayi da kallo har ya shiga dakin.......Mikewa nayi ba tare dana dauki kwanon zogalen ba nabi bayansa dakin.
Zaune na same shi a kan shimfid'arsa kallon guda nayi masa na gane yana cikin damuwa, a sanyaye na zauna ina fuskantarsa
Kallona yayi a nutse yace."Sumayya wani babban al'amari ne yake so ya faru dake damu baki daya." Nayi shuru ina sauraransa nasan dai mahaifin haruna ya sameshi da maganar data dame ni.
Ya cigaba da cewa"Yanzu kafin na shigo mahaifin Haruna yaron nan da aka tsayar da maganar auranku yazo min da wata magana wacce ta sani farin ciki ta kuma sani fargaba." shuru yay yana kallona na lura kamar yana jin nauyin fada min maganar nace"Baba na riga nasan maganar dakake so ka fad'a min." kallona yayi yana so yayi magana Tambaya ta mike zaune da alamun bacci a tare da ita tace"Allah yasa dai lafiya naji sai magana kuke 'kasa-'kasa ga alhini a tare daku.''
A sanyaye yace."Tambaya yanzun nan mahaifin Haruna yake sheda min cewar yaronsa ya janye maganar auransa da Sumayya saboda ba zai iya had'a takara da magajin Sarki ba."
Tambaya cike da tsoro tace."Malam kayi min bayani yanda zan fahimta bangane ba zai iya had'a takara da magajin sarki ba, me ya sako Yarima cikin al'amarin auran Haruna da Sumayya."
Murmushi yayi yace."Tambaya Magajin Sarki da kansa ya umarci Haruna ya janye maganar auransa da Sumayya saboda yana so ya aureta."
Tambaya gud'a ta ragwad'a cike da farin ciki da annushuwa tace"Malam da gaske kake wannan magana ko mafarki nake yi." Murmushi yayi yace."Ba mafarki kikeyi ba gaskiya ne wannan maganar." Tambaya kamo ni tayi ta rungume a jikinta ta dinga rangwad'a min gud'a akaina tana zabga min addua." har sai da babana ya dakatar da ita sannan ta sake ni kana ganinta kasan tana cikin walwala da farin ciki.
Ni kam kallonsu kawai nake ina mamakin murnar da sukeyi tabbas da sun san da munufar da Yarima zai aureni da basuyi murna ba, ganin yanda suke ta farin ciki yasa na danne damuwata kawai na dinga binsu da kallo.....Babana sunkuyar da kansa yayi yana girgiza kansa, Tambaya tace."Malam ya kuma naga ka shiga halin damuwa." Ajiyar zuciya ya sauke yace."Tambaya ina tunanin abinda zai biyo baya idan Allah ya kaddara al'amarin babu shakka mutane zasu nuna mana bakin ciki ina tsoran kada wani ya cutar damu ta dalilin wannan al'amarin." A sanyaye tace."Malam ka kwantar da hankalinka babu abinda zai same mu da izinin ubangiji duk wanda ya nufe mu da sharri sai ya koma kansa da yardar Allah kuma wannan aure sai anyi shi tunda maganar ta fito daga bakin Yarima ai magana ta kare sai da muyi kyakkyawar addua."" Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleni a nutse yace."Sumayya kinyi shuru baki ce komai ba ina fata kinyi na'am da wannan al'amari."
A sanyaye nace" A gaskiya Baba ni wannan al'amari sam be kwanta min a rai ba wannan dalilin ne yasa kukaji nayi shuru da bakina." Tambaya hannuna ta rike a sanyaye tace"Haba Sumayya kiyi wa kanki kyakkyawan addua mana ki roki Allah yasa haka shine alkairi a rayuwarki mu dai mun amince da wannan sauyin da Allah yayi miki a matsayinmu na iyayenki muna miki fatan alkairi kuma muna umartarki da ki kar'bi al'amarin da zuciya daya insha Allahu Allah zai sa albarka a ciki." ajiyar zuciya na sauke a sanyaye nace Allah yasa albarka a cikin al'amarin." Gabadaya suka amsa da "ameeen ya Allah."
Washe gari da safe sukuku! na tashi inata tunanin yanda al'amura zasu kasance a gaba iyayena sun kar'bi al'amarin hannu biyu sai murna da farin ciki suke wannan dalilin yasa gabadaya gwiwata tayi sanyi kawai na zubawa sarautar Allah ido ina tunanin yanda al'amura zasu kasance............Sallama mukaji daga waje, da sauri babana yasa takalminsa ya fita, minti biyar ya dawo yana murmushi yace."Tambaya al'amarin nan fa da gaske ne dan yanzu Magajin sarki ya aiko naje na sameshi a gurinsa.
Cikin murna tace"To shikkenan Ubangiji Allah yasa muji alkairi." Yana kokarin fita ya amsa da ameeen ya Allah."
Cikin hijabi na fito daga daki kafadata rataye da jakar litattafai na, nace"Tambaya ni zan shiga gurun karatu'' Tace."To yau ba zakije sashen Yariman ba." Ajiyar zuciya na sauke a hankali nace"Zanje idan na taso." Girgiza kanta tayi tace"To Allah ya bada sa'a sai kin dawo." amsawa nayi da ameen nasa takalmana na fita.
"Ranka ya dad'e babu wani abu da zaka nema a gurina na kasa mallaka maka mutukar ina da iko ni ne mahaifin Sumayya kuma na baka ita ina rokon Allah ya sanya alkairi a cikin auranku'''
Magajin sarki fad'ad'a fuskarsa yayi da murmushi cikin jin dadi yace." Nagode sosai da wannan kyauta da kayi min insha Allahu zan samu Maimartaba na sheda masa maganar da duk yanda mukayi nagode kwarai da gaske kana iya tashi ka tafi.'''
Lawi godiya yayi sosai kafin yay masa sallama ya fito fuskarsa cike da annushuwa! kai tsaye bangaran dawakai ya nufa yana tafiya yana addua akan Allah yasa alkairi a cikin al'amarin.