← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 90

Sashe 65

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bangane inda maganar ki ta dosa ba." fuska a murtuke yayi maganar, Nace"Ina nufin ban yarda da wannan tsarin naka ba ban sani ba ko ita Lawisan.......Mik'ewa tsaye yayi a zafafe! ya nuna ni da hannu yace."Ke ki shiga nutsuwarki fa ko dan kinga ina bibbiyar lamarinki kada ki manta da manufar da zan aureki kawai hallacin ki a kaina yasa na janye mummunan kudirina akanki! yanzu nazo ina fad'a miki ra'ayi kina wata magana kin san dai ke baki isa ki ruguza min tsari ba ko."?

Kallonsa nayi naga sai wani huci! yake nace"Allah ya huci! zuciyarka ni bana munafurci shiyasa tun kafin tafiya tayi nisa na fad'a maka nawa tsarin saboda haka kaine zaka zauna ka nemawa kanka mafita."

Ya jima yana kallona kafin yaja tsaki mai karfi ya kama hanyar fita daga dakin, kallo na bishi dashi ya bude kofar dakin a fusace! ya fita.

Ajiyar zuciya na sauke na tallafe ha'bata gabana na faduwa da wannan gagarimar matsalar da take kokarin kunno mana Magajin sarki baya son haihuwa saboda wasu banzayen hojjojinsa marasa tushe da maka wanda ni kuma nake ganin duk abinda za'ayi sai dai ayi amma ba zan bi hanyar da yake kokarin d'ora ni a kai ba wallahi bazan 'kayyadewa kaina haihuwa ba sai na haifi iya adadin 'ya'yan da Allah ya hukunta."

A nutse na fito falo cikin kwalliya kamar koda yaushe kuma ko alama ban bar wani 'bacin rai a fuskata ba wanda zai sa ta fahimci wani abu, muka gaisa cikin mutunci da kulawa kafin ma fara karyawa kamar yanda muka saba............Falon ya shigo tsaf dashi cikin shirin fita, kamshin turaransa duk ya cika mana hanci, amma fuskarsa kawai ta isa ta nuna maka cewa yana cikin 'bacin rai! dauke kaina nayi har ya karaso inda muke ya zauna gaban mahaifiyarsa yana gaisheta.

Ta amsa cikin kulawa da fadin"Babana jiya ai gajiya mukayi da jiranka muka kwanta ina fata dai anyi aiki cikin nasara." ?

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Mamma sai hakuri wallahi jiya ban shigo ba sai can dare koda na shigo kai tsaye sashena na nufa saboda nasan kunyi bacci." kallonsa nayi ina mamakin 'karyar dayayi, ya cigaba da cewa."Alhamdulillahi lafiya lau muka gudanar da aikin mu sai dai bayan dawowata gida d'aya ta amsa kiran ubangiji ta mutu ta bar yaron ita kuma dayar yaron ne ya rasu amma yanzu haka tana cikin koshin lafiya."

Girgiza kanta ta shiga yi cikin alhini da damuwa tace"Ya Allah kaji k'an musulmi Ai tayi shahada babana duk matar data mutu gurin haihuwa Allah yace."Aljanna ce makomarta sai dai muyi fatan samun baiwa irin tata." Kallonta yayi yana girgiza kansa yace."Hakane Mamma Allah kasa mu cika da imani." Ta amsa da ''ameeen ya rabbi."' Kallonsa nayi a nutse nace"Barka da asubah."

"Barka dai." ya amsa a takaice! Kokarin mi'kewa yake tace"A'a ba zaka tsaya kayo break fast ba."? girgiza kansa yayi yana duba agogon hannunsa yace."Mamma gabad'aya bani da kuzari wallahi cikina ya cushe bana sha'awar komai a yanzu mybe idan naje ofis na samu Coffee nasha ya isa." Tace"Babana bana so kana zama da yunwa kada fa ka manta kune kuke hanamu zama da yunwa to me yasa kuma kake karya doka."?

'Yar dariya yayi yace."Mamma kada ki damu insha Allah idan naje ofis zan samu wani abu naci yanzu babu lokaci dana zauna nayi break din.".

Tace."A ina zaka samu abu kaci kawai dai ka fad'a ne! bari kawai Sumayya ta had'a maka snaks ka tafi dashi." yace."To Mamma." Tace."Sumayya ki duba dakina akwai snakas cikin firji sai kisa masa a leda yanda zai isheshi." nace."To ranki ya dade." A nutse na mike na nufi dakin nata...........Suna hira na fito na same su, na mika masa ledar kar'ba yayi ba tare daya kalleni ba, na koma inda nake ina kallonsa da mamakin abinda yake min.....sallama naji sunayi da sauri nace"Ranka ya dade Allah ya tsare ya kiyaye gabanka da bayanka." a dakile ya amsa min." hakan besa ta gane akwai matsala a tsakanina dashi ba tunda sau tari haka yake amsa min magana a ciki shiyasa bata fahimci komai ba, nima nayi saurin korar 'bacin raina na fuskanceta sosai muka cigaba da hira cikin mutunci da mutunta juna.

Haka muka kasance da juna tsakanina dashi babu yabo babu fallasa dan duk wannan shige min da yake ya daina watarana ma idan ya dawo daga asibiti baya nema na nice nake fitowa nayi masa barka da zuwa! ko kadan ban damu da wulakancin da yake min ba saboda na riga nasan ni nake da gaskiya a duk inda zamuje shiyasa fushinsa sam be daga min hankali ba...............Yau saura kwana biyu daurin aure gabadaya masarautar ta hargitse sai abubuwa akeyi irin na al'ada Mamma ta mayar da hankalinta sosai gurin gyarani da ingantattun magungunan matan da take sawa a kawo mata, kullum sai bani wani turere na tsuguna akai haya'kin na ratsa a jikina, ni da kaina na tabbatar ingancin turaran dan ba headquarter na kawai ke kamshi ba gabadaya jikina ne ke kamshi duk inda na gifta kamshi na mussaman ne ke tashi............Jakadiya ce ta zauna tayi min 'kananun kitso irin na bare bari da yake ina da tsayin gashi yasa tufkar kitson ta kwanta gefe da gefen fuskata, ana ya gobe daurin aure da sassafe ta shigo dakina da kayan lalle(kunshi) haka na zauna tasa min salatif a kafafuna da hannayena kana tasa lalle akai tasa leda ta d'aure! ta gyara gurin, zama tayi kusa dani tana d'ebe min kewa, sai da mukayi zaman awa hudu da rabi tukkuna ta cire min lallan, na dinga bin kafafuna da kallo ina murmushin farin ciki tunda nake banta'ba adon lallai irin wannan ba Lallai jakadiya tana da zane sosai yanda ta fitar da zanan kunshi ragadau ya dinga burge ni gashi yayi wani irin jajawur, hannuwana na kalla nace"Jakadiya kinga kamar na hannun ya fi fitowa." tace"Eh ai da yake shi aka fara cirewa shiyasa yasha iska ne." murmushi nayi ina kallonta ta shiga turare min kafafuna da wani turere data zuba a cikin wani dan madaidaicin kaskon wuta.

'Bangaran Lawisa ma shiri suke sosai ita da mahaifiyarta Hajiya Karima ta tashi a tsaye tasa Lawisa sai bankar magunguna take lallai sai tafi Sumayya ni'ima a gurin miji! duk wani gyara da ake bukatar amare suyi a lokacin auransu kowacce tayi nata daidai gwargwado yayinda shi kuma angon nasu yayi musu bajintar kayan lefe kowacce akwati goma sha biyu cike da kayan amfani sannan kuma yasa an gyarawa kowacce sashen da zata zauna a gidan, dan bashi da ra'ayi had'asu a guri guda, duk abinda kowacce zata bukata tana dashi a sashenta.

*RANAR DAURIN AURE*
Masarautar ta cika da jama'a manyan mutane attajirai masu mulki malamai da sauran jama'ar gari kowa ya samu halatar daurin auran *Yarima Ali Abdul-aziz* inda wakilai suka sheda daurin auran kowacce akan sadaki dubu dari - dari bayan kammaluwar daurin auren sai masarautar ta hargitse da bushe-bushe gami da wassanin al'ada Ango yayi shirin hawa kilasa domin nuna murnarsa da Allah ya nuna masa zuwan wannan rana mai albarka.......Har dare ana abu d'aya a masarautar wassani iri-iri aka dinga gudanarwa, Sai da Ango ya shiga gida tukkuna kowa ya watse wa'inda suke masarautar suka nufi gurinsa wa'inda kuma suka shigo domin taya murya suka dinga fita jama'a kamar ranar idi! babu shakka jama'ar gari sunyiwa masarauta kara sun nunawa Sarki Abdul-Aziz Abdullahi kauna shima yaji dadi sosai dan kafin taro ya watse sai da ya mika godiyarsa zuwa gare su..

*Na kudi ne...*
Kada ki karanta min littafi idan baki biya ba! keda kika fita da littafin keda Allah! idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake...Vip gruop#600 normal gruop#300....account... 0542382124....Binta umar gtbank.....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannam number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
92
Tare suka shiga sashensa da Shatima, suka kimtsa jikinsu cikin kayan sarauta komai iri daya sukayi sosai sukayi kyau kana ganinsu kaga angwaye, da yake tare da Shatima aka daura auran shima amaryarsa 'Yar sarkin kazaure ce sun jima suna soyayya sai kawai iyaye suka zauna suka tattauna al'amarin lokaci guda akayi komai aka gama sai bayan da'aka daurawa Yarima aure da mata biyu tukkuna shi aka daura masa aure da tashi amaryar mai suna Mansura......koda suka fito kai tsaye sashen Waziri suka nufa sukaje suka gaisa dashi da iyalinsa sukayi musu bangajiya Waziri ya jima yana musu addua da fatan alkairi kafin su fito su nufi sashen Galadima shima iyalinsa duk suna nan sai hidima sukeyi, suka gaisa a tsanake Galadima yaji dadin ganinsu ya dinga farin ciki yana yi musu fatan alkairi, koda suka fito sai suka nufi sashen Ciroma yana zaune a kan kujera Hajiya Karima na kusa dashi sannan 'ya'yansa gabadaya sun kewaye shi suna magana, shigowarsu tasa dukkaninsu suka kalli bakin kofa......Ganinsu su biyu cikin kayan sarauta yasa wani bakin ciki ya lullu'besu da tuni harda Muddibo acikinsu Sunyi sanadiyar mutuwarsa sun kwantar da hankalinsu suna rayuwar jin dadi. Hajiya Karima ce ke wannan maganar cikin ranta, Ciroma kuwa b'acin ransa ya danne ya dinga murmushi yana amsa gaiswarsu tare dayi musu fatan alkairi Hajiya Karima kuwa lokacin da suke gaisheta kawar da kanta tayi sai da Wali yayi mata magana tukkuna ta amsa a ciki. gabadayansu basu ji dadin abinda mahaifiyarsu tayi ba har yanzu ta kasa 'boye 'bacin ranta gaban kowa nunawa take, suna fita Lawisa ta mike tabi bayansu, da sauri tace."Dan Allah ku tsaya." Magajin sarki da Shatima suka tsaya suna kallonta kamar wata mutuniyar arziki ta nufe su, Ya dinga kallonta yana mamakin kyawun da tayi tai ado sosai tayi kyau tamkar wata balarabiya lumshe idonsa yayi yana tunanin irin ni'imar da zai samu a tare da ita, ta tsaya kusa dashi kamshin turaranta ya bugi hancinsa bude idonsa yayi sosai yana kallonta, tace"Dan Allah kuyi hakuri da abinda hajiya tayi muku wallahi dukkaninmu bamu ji dadi ba."
Chapter 65 · 0% Book details