← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 90

Sashe 28

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Na kudi ne...*
Allah ya isa kika karanta baki biya ba idan kina so ki biya ga yanda abin yake......Vip group #600 normal #300 account.. 0542382124...Binta umar gtbank....idan kati zaki turo kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa Dashan Allah✊�)
51&52
Shara na samu Tambaya nayo shigowata yasa ta dakata ta tsaya tana kallona. kasa cewa nayi da ita komai nayi saurin shigewa daki, Tambaya kasa nutsuwa tayi ta ajiye tsintsiyar hannunta a sanyaye tabi bayanta, samuna tayi a zaune na zabga tagumi, shigowarta tasa nayi gaggawar cire tagumin ina kallonta xama tayi gefena a nutse tace"Sumayya lafiya na ganki kin shigo jikin ki a sanyaye ina fatan ba wata matsala bace."? shuru nayi ina kallon kasan gurin, shawarwari nake da zuciyata yana da kyau na sanar da mahaifiyata abubuwan da suke faruwa saboda ina jin tsoron wani mummunan abu ya faru nasan nida iyayena zamu shiga uku, ni sam ban san me yasa baya so mahaifiyarsa tasan abinda yake faruwa ba, kuma idan akace za'a cigaba da tafiya a haka to babu shakka ni dashi rayuwarmu na cikin matsala domun 'yan uwansa basa kaunarsa zasuyi amfani da yardar da yake musu su cutar dashi babban burinsu suga baya motsi a duniya inda shi kuma ya kasa ganewa kullum gani yake ba zasu ta'ba cutar dashi ba.....A sanyaye na warware mata abunda ke faruwa babu abinda na rage mata, yanda na lura itama jikinta yayi sanyi amma domin ta kwantar min da hankali yasa ta dafa kafad'ata tace"Sumayya ki nutsu kinji ko ki daina sa wasiwahsi a cikin zuciyarki insha Allah ba zasuyi tasiri a kansa ba duk sharrin da suke shiryawa zai koma kansu, kamar yanda yace baya bukatar mahaifiyarsa tasan abinda ke faruwa to kiyi shuru kada ki sheda mata, shawarar da zan baki shine ki tsananta gurin kula da shige da ficen masu shiga sashensa, sannan ki kula da duk wani abu naci da zasu kawo masa insha Allah duk sharrinsu sai ya koma kansu, ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru sai ikon Allah."

Ajiyar zuciya na sauke ina kallonta hakika naji sanyi a zuciyata sakamakon kwantar min da hankali da tayi nace"Insha Allahu zan kula kuma ba zan fada Mamma Fulani maganar ba, zan cigaba da kula dashi ina addua kema a matsayinki na mahaifiyata ina rokon ki ki taya ni addua Allah ya kareni daga fad'awa cikin mugun hali."

Tambaya tace"Kada ki damu Sumayya kullum cikin yi miki addua muke insha Allahu kuma adduarmu ba zata fad'i kasa ba.

Nace"Nagode sosai ina fatan kin bude akwatin kin duba kyautukan dake ciki. Da murmushi a fuskarta tace"Ban bude ba kada ki manta da zaki fita cewa kikayi sai kin dawo sai mu bude."

Mikewa nayi ina yar dariya nace"Da kin sani kin bude kin rigani gani ai kina da iko akan duk abinda ya dangance ni." Tambaya mirmushi tayi ba tace komai ba tabi ta da kallon kauna da tausayi.

Cikin nutsuwa na bude akwati nasa hannu ina fito da kayan ciki. Manya manyan lifayu ne guda uku sunyi kyau sosai sun kuma birgeni mutuka sai na dinga hango kaina a ciki nasan zasuyi min kyau kasancewa ta doguwa....sauran kayan na cigaba da dubawa, d'inkakkun atampa guda biyu supar da ingila anyi musu dinkin mutanan Nijar rigunan har gwiwa anyi musu ado da bakin leshi mai tsada... mayafai da takalma biyu sai turare biyu sai set din mayukan shafawa, Tambaya bakinta kasa rufuwa yayi ta kasa daina duba kayan sai farin ciki take tana godiya, ina mirmushi na dauki 'yar karamar akwatin da zoben gold din ke ciki na bude a nutse na fito da zoben ina duba shi sai kyalkyali yake yanda nake jin nauyinsa a hannuna nasan zaiyi kudi sosai Tambaya tace"Kai amma wannnan zoben yana da kyau sosai duba sai kyalli yake."

Nace"Tambaya gold ne Mamma ta bani wai nasa a hannuna nayi ado dashi." Tambaya ta kar'bi zoben tana dubawa, kawai sai hawaye ya shiga zobowa a fuskarta, da sauri na kalleta ina mamakin kukan da take.

Girgixa kanta tayi tace"Sumayya dole nayi kuka nayi mamaki! yanzu kece zaki saka zoben gold a hannunki tinda nake a masarautar nan ban ta'ba ganin baiwar da tayi ado da gold ba sai *murjani* amma cikin ikon Allah ke anyi miki kyautar zoben gold mai dauke da tambarin masarauta babu shakka Sumayya kin kafa tarihi a cikin bayi.

Mirmushi nayi na girgiza kaina ina kara duba zoben ni kaina ina mamakin al'amarin dan sai da ta fada ma sannan na duba zoben sosai naga tambarin masarautar jiki, ajiyar zuciya nayi na zura zoben a ya tsana na tsakiya, sosai yay min kyau na mika mata hannuna, rikewa tayi ta goge fuskarta da fad'in "Yanda kika sa shi bana fatan duk rintsi ki cireshi inaso ya dawwama a hannunki har ranar mutuwarki."

Hannu nasa na goge mata fuska da fad'in "Ki daina hawaye rabona ne ya rantse har Mamma tayi min wannan kyautar abinda kawai nake bukata a gurin ki shine addua ki cigaba dayi min akan Allah ya cigaba da bani ikon rik'e amanarta.

Hannuna dake fuskata ta rike ta sumbata cikin kauna tace" Sumayya insha Allahu kina tare da nasara a rayuwarki ke kadai muka haifa ke muke gani muji dadi in Allah ya yarda adduarmu sai tayi tasiri a kanki." Murmushi nayi cikin jin dadi mayar da kayan cikin akwati hannu tasa tana taya ni.

Babana ma da shigo yaga abin arzikin dana samu yay ta murna yana farin ciki, yace idan anyi sallar isha'i sai na jagorance su suje suyi godiya, haka kuwa akayi muna idar da sallar muka tafi.....

Tare muka sameta da yaron nata yana kishingide a gefanta ita kuma tana zaune tana fuskantarsa da alama magana mai muhimanci sukeyi.....a nutse muka gaisa dasu, na kalleta da murmushi a tare dani nace"Ranki shi dade mahaifana sunyi farin ciki sosai da kyautar bajintar da kikayi min dalilin daya sa ma suke ce lallai sai na kawo su sunyi miki godiya bisa alkairin da kikayi min.

A nutse ta juya tana kallonsu fuskarta a sake tace"Haba Tambaya ai yarinyarku ta cancanci abinda yafi haka menena na zuwa godiya, ni wallahi Sumayya ta gama min komai data tsaya take kula da Babana babu abinda ba zan iya yi mata ba, saboda haka kada ku damu kanku akan duk wata kyauta da zanyiwa 'yarku domin ta cancani abinda yafi haka.

Cike da farin ciki sukayi kasa da kansu suna sake jaddada godiyarsu babana yace."Ranki ya dade kasa hakuri nayi nace lallai ta kawo mu mu mika godiyarmu a gurinki babu abinda zamu ce miki sai dai fatan gamawa da duniya lafiya, muna rokon ubangiji Allah ya tsare gabanki da bayanki Yarima Ali Allah ya kareshi daga sharrin abin'ki.'' Mamma Fulani cikin kulawa take amsawa, kafin ta bamu umarnin tafiya, kallon gefan da yake nayi, tun lokacin da muka shiga ya sunkuyar da kansa gashi har mun 'kare abinda ya kaimu mun mike bai dago kansa ba, hakika wannan 'bakin halin nasa na 'bata min rai! Babana ya durkusa kusa dashi da fadin"Ranka ya dade a tashi lafiya." Dukkaninmu bamuyi zaton zai amsa ba ballantana ya dago kansa, dalilin daya sa ma kenan lokacin daya dago nayi saurin sunkuyar da kaina ina mamaki! "A sauka lafiya nagode." Abinda yace kenan ya mayar da kansa kasa, Sai da mahaifana sukayi gaba sosai kana nabi bayansu, gaskiya naji dadi sosai dana ganshi rad'au dashi! sai na saki raina ina addua akan Allah ya kiyaye gaba.

****
Bayan sati biyu al'amura na tafiya sannu a hankali, yanzu ya daina ta'ba min jiki sai dai kullum cikin yi min masifa yake abu kadan idan na kuskure sai yayi min wulakancin da zanji tamkar na dora hannuwana a ka, haka dai nake ta daurewa ina kulawa dashi tare da saka idona akan dukkanin abinda zai cutarshi.....Moddibo yay tafiya shiyasa na dan samu nutsuwa, sai dai Gimbiya Lawisa dake yawan aikowa kirana idan naje zata bani lemo ko farfesu da girke girke tace lallai na bashi yaci jiki na rawa nake kar'ba kafin na fita sai na tabbatar mata da cewar zan cika aikinta, ina fitowa nake samun inda babu idanun mutane na haka rami na zuba a ciki.....haka mukeyi da ita kullum kuwa cikin kallon shashasha nake mata cikin zuciyata ina fadin dama ta daina wahalar da kanta domin na lura koda da asiri a kansa ba zai tank'waru! kamar yanda take so ba, kanyi dariya da mamaki a duk lokacin da zata kawo masa ziyara kullum basa abin arziki ko sun fara hira cikin mutunci ta koma fad'a ya ci mata mutuci tas amma saboda bata da zuciya bata sati zata sake zuwa nayi ta mamakin al'amarin tunda ni dai tunda nake dashi ban ta'ba gani yaje gurinta domin suyi hira ba, a zahirin gaskiya Son da take masa bai kai wanda yake mata ba kamar dai yanda take fad'a kullum shine har yanzu ba ta gane inda ya dosa ba, dariya na kanyi a duk lokacin da tayi wannan maganar a zahiri yana nuna mata bata gabansa amma sai kace dabba ta kasa ganewa.

Ina tsaka da aiki ta aiko kirana, nace aje ace mata gani nan zuwa." da sauri na gama had'a fruit salad samun sa nayi a kishingid'e a gurin da yake hutawa, aikin da ya saba yake yi latsa waya, tire din hannuna na ajiye kusa dashi a nutse nace"Ranka ya dade ga fruit salad din na had'a."

Wannan karon be k'yale ni ba, naga ya ajiye wayar tare da mi'kewa zaune, gani nayi ya zuba min ido yanayi min kallon da ya jima beyi min irinsa ba, sai jikina yay sanyi na tabbata akwai matsala tunda ya tsareni da ido.

"Meye tsakanin ki da Haruna ne? naga yana yawan bin ki kicin idan kina aiki.'' Shuru nayi ina nazarin abinda zance masa.

"Bakya ji ne."? a dakile yay maganar yana sake tsareni da ido.

Ajiyar zuciya na sauke na dago a nutse nace" Akwai kyakykyawar fahintar juna a tsakanina da Haruna bayan wannan babu wani abunda yake tsakanina dashi.
Chapter 28 · 0% Book details