← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 90

Sashe 70

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya mutsa fuska tayi da kyar tace"To shikkenan." yace."Ina fatan kina shan magungunan dana baki kuma ina fatan gurin ya dena zafi."?

Cikin shagwa'ba tace"Wallahi har yanzu yana zafi da kyar ma nake tafiya ni kam gwara ka kwana a gurinta ko na huta." Dariya ya kyalkyale da ita yana kallonta tana matso hawaye.

Takaicin abinda suke yasa na mike a dake! nace"To ni zan tafi ." da sauri ya kalleni ya wani marairace fuska yace."My love kina jina da Lawisa ko wai ni take kora daga sashenta sabida na ina jin dadi da ita."

kamar na kwad'a masa mari saboda 'bacin rai! na ta'be bakina had'e dayin gaba ba tare dana tanka masa ba."

Da sauri yace."Kada ki fita kizo ki taimaka mata da ruwan zafi! idan yaso itama sai ta ramawa kura aniyarta." Murmushi nayi na juyo ina kallonsu nace"Haba ai kai da ka 'bata kai zaka gyara ni meye nawa wallahi ranki ya dade kada ki yarda ki barshi ya fita sai kin hukuntashi." Dariya ya dinga yi yana kallona ita kam kallon mamaki naga tana yi min, na saki mirmushi duk dan na nuna mata cewa banji haushi ba nace" Sai anjima." juyawa nayi da sauri na fita daga falon da kyar na k'arasa gurina na zauna kan kujera tare da rufe fuskata da hannuwana! innalilihi na dinga ja a zuciyata kafin na samu sassauci cikin sanyin jiki na mike na nufi daki kwanciya nayi ba tare dana warware lifayar jikina ba, tsabar bacin rai da nake ciki ya dinga nema ya sa min ciwon kaina hawaye ne ke kokarin zubowa ina mayar dasu, nasan idan basu zuba ba bazan samu kwanciyar hankali ba, sai kawai na barsu suka dinga zuba a kuncina haka na dinga juye-juye a bed din ina mamakin kaina! kishi ne dani irin mai wahala idan banda abin son zuciya irin nawa menene na damuwa dan yayi auratayya da matarsa.........Zuciyata tace"Duk da haka abinda sukayi miki basu kyauta ba abin kamar da akwai cin fuska a ciki, meye dan sunyi rayuwar aure sai sun fito suna fad'a miki gabad'aya ita dashi basu da addini........Hannu nasa na goge hawayen fuskata na gyara kwanciyata rufin dakin na tsirawa ido ina tunani yanzu yana can yana rarrashinta dan naga sai wani lalla'bata yake kafin na fito, gaskiya halin namiji sai shi, wallahi banta'ba tsammanin zai so Lawisa ba sai gashi lokaci guda yana nuna mata kauna da kulawa a gabana.

Agogon bango na duba har nayi mintina ar'bain da fitowa daga sashen bai shigo ba, na sake jin 'bacin raina ya nunnku! rufe idona nayi na cigaba da nanata kalmar innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! da haka bacci mai nauyi ya dauke ni.

Bacci nayi sosai sai wajejen la'asar na tashi! na dinga mamakin tsayin lokacin dana dauka ina bacci! jikina a mace nai wanka na kimtsa jikina kana na tsaya kan dadduma domin gabatar da sallah! ban tashi daga kan daddumar ba sai dana gabatar da la'asar tukkuna na tashi daddumar na ninke tare da ajiyeta a inda aka tana da kai tsaye falo na nufa ba tare da na cire hijab din jikina ba.

Suna zaune a guri guda ganina yasa duk suka mike tsaye, cike da mamaki! nace "Meye haka daka ganina duk kun razana."

Sunkuyar da kansu sukayi ba suce komai ba, nace"Daga yau dan Allah kada wacce ta sake ganina ta razana kuma bana so kuna sa gwiwarku a kasa gurin gaisheni."

Mariya tace"Ranki ya dade ai dole ne mu girmamaki domin kin cancanta." Nace"Nasan da haka ai ni bana so ku d'aura min izzah ne! duk girman da zaku bani ku bani mustad'a'a kada yayi yawa."

Gabad'ayansu suka amsa da "To ranki ya dade insha Allahu zamu kiyaye." ajiyar zuciya nayi tare da zama kan kujera, Sakina tace"Ranki ya dade ko a kawo miki abinci nan."?

A nutse nace." Me kuka girka." ? "Ranki ya dade damubun shinkafa ne." murmushi nayi nace"Aikuwa kun burgeni wallahi jeki kawo min." da sauri ta mike ta nufi gurin cin bincin, waya ta na cigaba da dubawa har ta gama jera kayan abincin a teble din dake gabana,
Kokarin zuba min take na ajiye wayar da fadin"Kuje kawai zan zuba da kaina." godiya sukayi min da sauri suka fita.

Ina kokarin bud'e fulas naji zubowar abu a pant d'ina, gabana ne ya fad'i! da sauri na mi'ke na shiga toilet domin na tabbatar da zargi! ina tsugunawa shine ya fara zuba! "shikkenan! abinda na fad'a kenan ina girgiza kaina, kai amma wannan abu bai kyauta ba! ruwa nasa na wanke jikina na gyara gurun na fito, na kimtsa jikina, falon na koma na zauna gabadaya jikina ya mutu da ganin al'adata ango naso ya gwangwaje abu yayi masa cikas! ta'be bakina nayi a zahiri nace" Gwara haka sai muga 'karyar kwad'ayi! ko yaya zaiyi idan ya ankara! dariya nayi na girgiza kaina fulas din abincin na bud'e! 'kamshi ya bugi hancina dambun yayi shar-shar dashi yaji gyada da zogale sai kamshin man gyad'a yake, da sauri na zuba wanda zai isheni nayi bisimillah a nutse na fara ci ina gyada kaina tamkar kunnena ya tsinke dan d'adi gaskiya sunyi kokari sosai domin dambun ba 'karamin dadi yayi ba.

To a haka na kasance a sashena ni kad'ai har bayan isha'i bai shigo ba raina ya 'baci mutuka gashi girman kaina ya hanani kiransa a waya babu irin sa'ke-sa'ken da zuciyata ba tayi min ba, daga karshe dai daki na shige nayi shirin kwanciya zama nayi gefan gado da romot a hannuna tashar larabawa na kama naga suna drama irin tasu, kawai sai na shiga bargo na kwanta tare da cigaba da kallon film din kasancewar ina dan jin labaraci yasa na dinga fahimta sosai film din ya dauke min hankali! kawai naji an turo kofar dakin.

Ido muka had'a dashi yana sanye da shadda fara kal! tasha aiki kafarsa sanye da bakin takalmi kansa kuwa hula ce 'baka irin mai tsayi wacce ake d'ora nad'i a kai.

Mi'kewa zaune nayi ina masa barka da zuwa! ya zauna kusa dani yana kallona yace."Kinji shuru ban shigo ba ko."? kaina na daga ina kallonsa, sosai yayi min kyau a ido kayanmu na hausawa nayi masa kyau sai dai bai fiye sakawa ba yafi amfani da 'kananu ......Ya cigaba da cewa"Bayan barin ki gurin Lawisa nida Shatima muka nufi can masarautar kazaure domin gaisuwa da bangajiya dawowar mu kenan yanzu."

Nace"Ayya! sannu gaskiya kunsha hanya dama nima da naji shuru baka shigo ba nace mybe ko kaje asibiti ne ashe tafiya me nisa kukayi.''

'Kure ni da ido yayi yace."Da kikaji shuru ban shigo ba me ya hanaki kiran waya ta." ? shuru nayi dan saboda nasan ban kyauta ba."

Yace."Lawisa tafi ki wayo ke kuwa kin zauna girman kai kin dauki kanki daidai dani kina ganin idan kin kira wayata kin zubar da ajin ki ko.'??

Da sauri nace"Wallahi ba haka bane nima yini nayi ina bacci sai gefin la'asar na tashi sai nasa wayar a chaji dama kuma yanzu nake tunanin kiran ka."

Ta'be bakinsa yayi yace."Kyaji dashi dai.'" a sanyaye nace"Dan Allah kayi hakuri idan hakan ya 'bata maka rai."

Sakin fuskarsa yayi yace."Na yafe miki yanzu dai ina bukatar abinci.'' cikin jin nauyi nace"Sai da nayi maka yanzu." cike da mamaki yake kallona yace."Kada dai kice min baki ci abinci ba har yanzu."

"Naci abincin mana." yace."Karya kikeyi kin zauna da yunwa tun safe." Nace"Wallahi naci abinci na koshi dan kafin na tashi a bacci hadimai sun shirya komai."

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Amma kuma kika ce zaki shiga kicin." ina wasa da yatsun hannuna nace"Ai nafi bukatar na girka maka da hannuna domin na samu lada."

Kallona yake yana murmushi yace."To nagode amma kada kiyi abu mai wuya kiyi min indomee.'" cike da mamaki na kalleshi! girarsa ya daga min girgiza kaina nayi nace"Ranka ya dade indomee ba abincin bace ba zata gamsar da kai ba."

Shuru yayi yana kallona yace.'' Okey to ai bana so ki wahala ne shiyasa nace kiyi min indomee amma tunda kina bukatar ki bani abinci mai gamsarwa babu damuwa nima nafi son haka naci na koshi na samu kwarin jikina." Yana min wani irin kallo ya karashe maganar, murmushi nayi na mike a nutse nace"Bari na shiga kicin din! mikewa yayi da fadin"Okey kafin ki gama bari na shiga gurin 'Yar uwarki muyi sallama." shuru nai masa muka fito tare ni na nufi kicin shi kuma ya kama hanya ya fita.

Fatan doya nayi masa na gama aikina tsaf na shirya masa duk abinda zai bukata tire din abincin na kai dakina na ajiye a gefa agogo na duba ina mamakin dad'ewarsa daga zuwa yin sallama ya share gindi ya zauna awarsa daya da fita, zuciyata tace watakila yana gurun mahaifiyarsa ki dinga yi masa uzuri! ajiyar zuciya na sauke tare da dauke kaina daga kallon agogon dake kafe a dakin............Mikewa nayi na shiga toilet domin sake kimtsa jikina pad na sanja na fito sai na ganshi a zaune gaban kayan abincin yana bud'awa, da sauri na karasa kusa dashi, yace."Kinji shuru ban dawo ba ko."?
"Umm." nace, yace." Ina can gurin Mamma! ga wannan ma tace a kawo miki wai ke kadai zaki ci kada ki bani." akushin dake gabansa na kalla! ya mi'ko min, nasa hannu na kar'ba a nutse na bud'a kaza ce guda anyi mata dahuwar magani sai kamshi take! da sauri na rufe ina kallonsa, hankalinsa nakan abincin gabansa, da sauri na kar'ba ina kokarin zuba masa yace."Mamma ta huttashe dani da kazar amarci."

Kallonsa nayi da mamaki a tare dani! yace."Ai na bud'a na gani ta dafo miki kaza tayi lugub! wai harda cewa ko roma kada na d'and'ana." yanda ya fad'i maganar a sakarce ya bani dariya nace"Ban hanaka ci ba idan kana bukata sai na baka."
Chapter 70 · 0% Book details