Sashe 88
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina kwance ina kallonsa ya gyara babyn duk ya sasu a towel ya ajiye su saman bed! ya tsuguna gabana tare da fadin"Sannu." kaina na daga masa, yace."Bari na sa miki ruwa kiyi wanka ko."? shuru nai ya mike yana fadin"Sumayya ke 'yar baiwa ce shiyasa Ubangiji ya baki nakuda mai sauki wannan abin alfahari ne a garemu." toilet din ya nufa, na mike a hankali na tattare towel din dake jikina, hannu nasa na dauko daya na duba naga namiji ne ajiyar zuciya na sauke nace"Allah ya albarkace ka." a hankali na dauko dayan na duba shima namiji ne tamkar an tsaga kara da dan uwansa, dukkaninsu sun dauko kammanin mahaifinsu, addua nai masa ina jin wani irin farin ciki a cikin raina, haka ya fito ya sameni ya murmushi yace"Jarumata kinga kyautar da Allah yay mana ko.''? murmushi nayi nace"Wallahi nagani kuma nagode masa daya bani kyautar 'ya'ya biyu a lokaci guda.''' Yace.'' Ina mutukar alfahari dake Sumayya ke kikayi namijin kokari har na samu wad'annan yaran."
Murmushi kawai nai na fara kokarin mikewa, ya taimaka min muka nufi toilet, komai na wanka ya hada min yace ki fara shiga ruwan dumi tukkuna sai ki gasa jikinki idan ba zaki iya ba nayi miki."?
Nace"Ka bari kawai zanyi.'' yace."Kin tabbata."? kaina na daga masa yace."Okey bari kafin ki fito na sanar da Mamma." Da sauri ya fita daga toilet din na girgiza kaina a nutse na shiga cikin ruwan zafin daya had'a min.
*Na kudi ne*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar biyan kudin littafin ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal group #300 account.... 0542382124....Binta umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊ðŸ?)
107
Jin sheshshe'kar kukanta ya cika masa kunne yasa ya juyo da fuska a murtuke yana kallonta, a sanyaye tace" Dan Allah kayi hakuri ka janye sakin nan da kayi min nasan ban kyauta ba dana fadawa mahaifiyarka amma idan za'a bi gaskiyar magana kowa yasan kaine mai laifi bai kamata ka yanke irin wannan hukuncin akaina ba kayi hakuri ka janye sannan na roke ka da Allah da annabi ka daina amfani dani da condem nima inaso na haihu na samu sanyin idaniya a duniya kada ka cutar dani ka lalata min mahaifa."
Tausayi ta bashi ganin yanda take kuka gabad'aya tayi sanyi dan tun ranar daya saketa ta rasa nutsuwa kullum cikin bashi hakuri take tabbas kamar yanda Sumayya ta fada masa yanxu babban laifi shike dashi dan Lawisa ta gaji ta nemawa kanta mafita ba laifi bane tunda shi kansa yasan yana cutar da ita saboda yasan illar kwayoyin daya dinga dibga mata idan kuwa hakane yana da kyau yayi mata afuwa akan abinda tayi masa ya yafe mata ya mayar da ita dakinta kodan ya samu sassauci daga gurin mahaifiyarsa.......Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta da alamun sassauci a fuskarsa yace." Lawisa zan mayar dake dakin ki saboda matata Sumayya ta wuce komai a gurina kina ji dai da kunnanki yanda take kuka akan hukuncin da nayi miki inaso ki dauketa a matsayin 'yar uwa ba kishiyasa ba duk wasu mugwayen halayen ki ki sanja su zama masu kyau mutukar kika cutar da Sumayya wallahi bazan barki ba, ina fatan ki gane."
A sanyaye tace"Nagane na kuma gode da naci albarkacin Sumayya domin ta cancanta ta kowane fanni wallahi tuntuni na dauketa a matsayin 'yar uwa a shirye nake dana zauna lafiya da ita babu cuta babu cutarwa kaima inaso ka kamanta adalci a tsakanina da ita tunda azahiri ka nuna kafin sonta dani."
Girgixa kansa yayi yace."Ba wai nafi sonta akanki bane Lawisa Sumayya ta cancanta a sota saboda kyawawan halayenta yarinyar ta bada gudumawa mai yawa a rayuwata wannan dalilin yasa nake nuna mata kulawa wanda har kike ganin kamar nafi kaunarta dake kema ina kaunarki inaso kisa a ranki cewa ni dan uwanki ba zan kara cutar dake ba saboda yanzu nagane gaskiya insha Allahu kuma na daina amfani dake da condem kuma ki kwantar da hankali da ikon Allah kema zaki haifa min 'ya'ya masu albarka."
Murmushin farin ciki tayi tace"Nagode sosai ina rokon Allah ya dawwamar mana da zaman lafiya ya kuma bamu zuria mai albarka." amsawa yayi yana murmushi yace."Tunda kin zama amarya ki shirya muje musha iska daga nan sai ki rakani store nayi wa baby siyayya."
Cikin farin ciki ta mike da fadin"To shikkenan bari nayi wanka na fito." toilet na nufa ya bita da kallo yana girgiza kansa.
Akwati uku suka ciko da kayan baby komai biyu ya dinga dauka, Lawisa ta dinga mamaki da dai ta gaji tai magana kai tsaye yace."Jikinsa na bashi twins zai haifa sabida haka kawai ta kyaleshi aikuwa ido ta zuba masa yayi ta labtar kaya, itama Sumayya ya siya mata 'kananun kaya masu yawa.......mota cike da kaya suka dawo gida.
Can masarauta kuwa tana cikin alhini da damuwa sakamakon rasuwar mai girma Ciroma dab da magariba Allah ya kar'bi rayuwarsa bayan yasha fama da jinyya.......Mutuwar maigirma Ciroma ta girgiza jama'a da yawa suka tsorata mussaman Uwargida da 'Ya'yanta, duk sun rud'e sai koke koke suke a gidan.....Hajiya Karima duk da bata hayyacinta sai da taji a jikinta, da kyar Wali ya sheda mata mutuwar mijin nata faduwa tayi a gurin ta suma ko bayan data farfad'o ma kasa gane kanta akayi ta dinga surutai tana kuka, Wali da kansa ya dauko Dr Sadiya tayi mata allurar bacci.
Tunda suka wayi gari suka rasa abinda ke damunsu da kyar suka karya kummalo suka shirya jikinsu suna jiran abokanan tafiyar tasu su fito domin su hadu su tafi airport...... Kira ya shigo Wayarsa dake saman drowar....Ita ta dauka ta mi'ka masa ya karba yana dubawa ganin Number Shatima yasa ya sauke ajiyar zuciya ya daga da sallama a bakinsa, gaisawa sukayi Shatima nata tunanin ta yanda za'ayi ya fada masa mutuwar.....Yace."Shatima yanzu nan zamu hadu mu tafi airport insha Allah karfe daya na rana mun sauka a gida.'' a sanyaye yace."To masha Allah ina rokon Allah ya kawo ku lafiya." yana gama maganar sai ya kashe wayar cikin zuciyarsa yace bari kawai ya bari tunda dawowa zasuyi, shi kuwa magajin sarki jikinsa ne ya bashi akwai matsala, sai ya kara kiran wayar shatiman ya dauka, yace."Ka fada min abinda yake faruwa dan jikina ya bani akwai abinda kake 'boye min kodai wani abu ya samu Sumayya ne."?
Shatima ya sauke ajiyar zuciya yace."Magajin sarki masarauta tayi babban rashi." gabansa ne ya fad'i! yace."Waye ya rasu."? jin maganar mutuwa yasa da sauri ta dawo kusa dashi. Shatima yace."Allah yayi wa Baba Ciroma rasuwa jiya da daddare yanzu haka har mun kaishi mun dawo."!
"Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! kalmar daya fada kenan jiki a sanyaye ya kashe wayar ya juyo suka had'a ido Lawisa baki na rawa tace" Da gaske baba ya rasu."? kansa ya daga mata sai kawai ta zube kasan dakin ta hada kai da gwiwa ta dinga rusa kuka tana jan innalillahi wa'ina ilahi raji'un.! zama yayi kusa da ita ya rungumeta a jikinsa ya dinga rarrashinta cikin kalamai masu sanyi da tausasawa.
Lawisa tashin hankali mai tsanani ta shiga a lokacin da taga halin da mahaifiyarta take ciki.......cikin 'kunar zuciya ta rungume d'an uwanta Wali dake tsaye akan mahaifiyar tasu, tana kuka tace"Wali Baba ya mutu ga Hajiya ta had'a da lalura mai wahalar magani ga aunt Lauratu tayi mutuwa irin wacce ba'aso ta mutu ba tare data tuba ga Allah ba, kafin muyi tafiyar nan sai da na zauna dasu na hanasu aikata abinda suka kud'urta saboda nasan dole Ubangiji ya tona musu asiri tunda ita wacce suka nufa da sharrin bata da hakki akansu amma da yake shaid'an ya riga ya gama shiga jikinsu sukaqi saurarata sabida naqi basu hadin kai hakan yasa ko sallamar arziki bamuyi dasu ba na tafi cikin damuwa da tunanin abinda zai biyo baya akan abinda zasu aikata hakika nayi nadamar kasancewar hajiya a matsayin u........Katseta yayi yana girgiza mata kansa ido jawur yace."Kada kice haka Lawisa duk lalacewar uwa uwace gabad'ayanmu mun san mahaifiyarmu bata da nagarta abinda yafi kamata muyi mata a yanzu shine addua domin ita kadai tafi bukata Lawisa a yanzu ina mai tabbatar miki da cewa Hajiya tayi nadama dan tsabar tension (damuwa) ne ya sanya mata shiga cikin wannan yanayi kullum yini take tana kuka da sambatu sai anyi mata allurar bacci ake samun lafiyarta saboda haka kada ki sake kamanta wata mummunar magana akanta insha Allahu Allah ya ganar da ita gaskiya, shi kuma baba addua zamu bishi da ita dan yayi mutuwa irin wacce ake bukata alhamdulillhi ya mutu da kalmar shahada a bakinsa wannan shine babban abin alfaharinmu."
Lawisa zama tayi kasan kafet tana kuka tana kiran innalillahi Khalisat kanwarta tazo ta rugunmeta suka cigaba da zubar da hawaye, Hajiya Karima kukansu ne ya tasheta daga bacci ta mike a firgice! ganin Lawisa yasa ta sauko daga gado ta zauna a gabansu kawai sai itama ta fashe da kuka tana girgiza kanta.
Muniru yace."Shikkenan kun tasheta yanzu idan ba Allah ne ya takaita ba zata fara surutai." kallonsa tayi tana girgiza kanta tace"Munniru kun mayar dani mahaukaciya ko. "? girgiza kansa yayi yana kallonta! ashar! ta d'ura masa tana wata irin zabura! tace" Nayi maka karya kenan."? ganin tana kokarin mikewa tsaye yasa Wali yace da Munniru maza ya fita, sai kawai ta dawo kan Wali din ta dinga cusa masa ashar yana rirriketa.....Lawisa ta taimaka masa suka zaunar da ita akan gado, sai kawai ta fashe da kuka tace"Lawisa Babanku ya mutu Lauratu kanwata data rage min itama ta mutu wuta ta cinyeta ni yanzu meye amfanin zamana a duniya wayyo Allah na shiga uku na lalace."!!!! da karfin gaske take maganar tana buge buge hade da d'ora hannu akanta.....Wali hankalinsa ya tashi da sauri ya fita daga dakin Lawisa da Khalisat suna kuka suka rirriketa tana fizgewa.