← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 90

Sashe 57

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Maimartaba yace."Fulani maganarki tayi ma'ana yana da kyau Huwaila na gurin nan yana da kyau Hajiya Karima na gurin nan yana kuma da kyau ace Hajia Kubra da Falmata na gurin nan domin kowa yaji bayanin da wannan yarinya za tayi."

Gabad'ayansu suka amince da maganarta, da sauri ta kira Jakadiyarta tace maza taje ko wane sashe tace maimartaba nada bukatar ganinsu domin tattauna muhimiyyar magana." Jakadiya da sauri ta tafi cika umarni.

Shuru falon yayi bayan kowa ya hallara, Maimartaba ya kalleni a nutse yace."Sumayya dukkaninmu ke muke saurare muna bukatar muji komai daga gurinki."

Ajiyar zuciya na sauke a hankali na dago kaina sai naga dukkaninsu sun zuba min ido yanayinsu ya nuna min cewa ni suke saurare.

Kaina na sunkuyar cikin nutsuwa na fara magana.......................'Karya kike munafuka."!! Hajiya Karima ce ta katseni tana wani irin huci! ta mike tsaye tana nuna ni da hannu 'Karya kike algumguma! kice Muddibo shine wake d'aya 'bata gari! a masarauta me Magajin sarki yayi wa Muddibo da zai kasheshi."!?? Maimartaba ya buga mata tsawa! Mijinta Ciroma shine ya zaunar da ita gumi! sai karyo masa yake, Hajiya Karima ta koma ta zauna tana muzurai idanunta sunyi jajawur saboda tsananin tashin hankali.

Sai da kowa ya samu nutsuwa tukkuna maimartaba ya umarceni dana cigaba da maganata, Na cigaba da cewa"Ranka ya dad'e na rantse da wanda raina yake a hannunsa wannan maganar dana fad'a ba karya bace Muddibo shine ya tareni cikin dare bayan fitowa ta daga sashen Yarima, ya umarceni dana kar'bi magani lallai yana so na zubawa Yarima a lemo ya kuma tabbatar min da cewa mutukar na sake lalata musu aikinsu akan Yarima to sai ya kasheni, koda na kar'bi maganin a hannunsa sai na kwance na watsa masa shi a fuskarsa, na tabbatar masa da cewa ni ba za'a hada baki dani akashe mai rai ba! kafin nayi wani yunkuri ya dauki wani dutsen wuta dake gurin ya tad'e kafafuna na fadi a gurin kawai ya dinga buga min a kaina ina karewa , sawun mutane yasa ya jefar da dutsen ya bar gurin......to tun daga sannan ban san inda kaina yake ba."

Maimartaba yayi shuru yana girgiza kansa gabadaya yanayin fuskarsa ta sauya da zallan 'bacin rai! Ya kalleni a nutse yace."Sumayya koda ba kiyi rantsuwa da Allah da mazon sa ba, na tabbatar da cewa ba zaki zauna ki shirya wannan maganar ba, Tabbas ni na amince da maganarki Muddibo zai iya aikata wannan abu saboda wata manufa tashi." Ya kalli su Waziri da duk fuskokinsu suka nuna alamun alhini da tashin hankali mussaman Ciroma da duk ya muzanta a gurin sai gumi yake idanunsa sun kada sunyi jajawur saboda tashin hankali!

Maimartaba yace."Inaso gabad'ayan ku ku amince da maganar yarinyar kada wanda ya saka kokwanto a cikinta yarinyar nan Sumayya ni na amince da cewa ba za tayi wa muddibo k'arya ba sannan kuma inaso dukkaninnku ku kauda kanku akan irin hukuncin da zan yanke a kansa mutukar hukuma ta tabbatar mana da gaskiyar magana a kansa."

Hajiya Karima ta fashe da kuka mai tsanani! tace"Ranka ya dad'e ka tsaya ka nisa tukkuna kayi binkice akan wannan al'amari wallahi na tabbatar Muddibo ba zai aikata wannan mummunan akin ba a duniya me magajin sarki yayi masa da zai kashe shi, ranka ya dad'e ka duba maganata."

Maimartaba yace."Karima ki kwantar da hankalinki kamar yanda Magajin sarki ya sheda mana cewa yanzu haka Muddibo na hannun hukuma to ba zamu yanke hukunci ba sai mun tabbatar da gaskiya kan maganar saboda haka ki daina kuka kina tashin hankalinki dole Masarauta ta nuna fushinta akan abinda ya aikata.

Da bakin zaninta ta fyace hanci ta kalli Magajin sarki murya na rawa tace"Ali dan Allah kayi hakuri da wannan al'amari kada fa ka manta Muddibo dan uwanka ne tare kuka taso kuna kaunar junanku idan binkice ya tabbatar da gaskiya a kansa to ka yafe masa abinda ya aikata maka.

Yace."Hajiya kiyi hakuri wallahi idan ni Muddobo ya bugawa dutse ya fitar min da jini zan k'yaleshi saboda dangatakar dake tsakanina dashi, amma ki sani ba zan iya hakurin ganin ya zubarwa da wannan baiwar Allah jini na kyaleshi ba haki'kanin gaskiya sai nabi kadin jininta."

Falon yayi shuru kowa yana mamakin maganarsa, ya kalli mahaifinsa a nutse yace."Ranka ya dade wannan yarinya sumayya nayi alkawarin aureta a cikin satin nan nake so a daura min aure da ita inaso gabadayan ku kusa min albarka a cikin aurena da ita." Maimartaba da Waziri fuskarsu ta fad'ad'a da farin ciki suka dinga fatan alkairi a ciki, Ciroma da Galadima kadarah kadahan sukayi magana akai, ita kuwa Hajiya Karima tashin hankali biyu ne ya had'e mata Yarima zai auri baiwa kafin ya auri 'yarta sannan yasa an d'aure mata gudan jininta Muddibo! rai a mugun 'bace! ta mike ta fita, dukkaninsu suka bita da kallo suna girgiza kai......Hajiya Huwaila da yake tana da wayo da siyasa kwata kwata bata nuna wani alamun da zai nuna cewa bakinsu daya da Muddibo ba, cikin nuna farin ciki takeyin fatan alkairi kafin ta tafi........Ciroma kuwa ya jima yana jajanta al'amarin kafin ya mayar da komai ba komai ba a zahiri kenan a bad'ini kuwa shi kad'ai yasan abinda ya kudirta, ya kalli Magajin sarki da fad'in "Inayi maka fatan alkairi a rayuwarka ina kuma baka hakuri a bisa wannan abu da ya faru da kai da dan uwanka sannan kuma inaso na jaddada muku cewa duk wani mataki da hukuma zata dauka akan Muddibo bana bakin ciki da hakan mutukar binkice ya tabbatar mana da gaskiya to ina mutukar farin ciki da umarnin da maimartaba zai yanke a kansa." Maimartaba ya dafa kad'arsa cikin taushin murya yace."Inaso ka kwantar da hankalinka akan wannan abu insha Allahu hukuncin da zamu d'auka akan Muddibo zai zama izina ga masu mugun hali irin nashi.

Muddibo na ofis d'insa sakatarensa ya shiga ya sheda masa cewa yana da baki, kai tsaye yace ya shigo dasu, koda yayi tozali da Acp da sauran jami'ai sai yaji tsoro amma da yake 'kwaro ne sai ya dake! ya nuna musu gurin zama da fadin"Bisimillahi ku zauna." Acp ya girgiza kansa da fadin"Ba zama ne ya kawo mu ba, munzo domin mu tafi dakai." Cike da mamaki yake kallonsa kafin yayi murmushin gadara yace."Akan wane dalili zaku tafi dani Acp me na aikata.''
Acp ya murtuke fuskarsa yace."Muddibo ka aikata mummunan ayyuka ciki kuwa har da yun'kuri kisa."

Muddibo gabansa na bugawa yace."Acp wannan wace irin banzar magana ce? mikewa yayi tsaye cikin hayaniya ce "ku fitar min daga ofis."

Acp ya gyara tsayuwarsa da murmushi a fuskarsa yace."Wannan hargagin da kake da yanayin yanda fuskarka ta nuna ya tabbatar mana da cewa kaine ka aikata abinda muke zarginka dashi."

Muddibo zufa! na keto masa yace."Wai shin Acp wane irin sharri kuke so ku laqaba min ne? wa na kashe da kuke zargina da aikata ta'addanci irin wannan."?

Acp ya kalleshi sosai yace."Kayi yunkurin kashe baiwar gidanku wato sumayya saboda ta'ki kar'bar umarninka."!

Muddubo zabura! yayi yana nunashi da yatsa baki na rawa yace."Acp ka kiyaye harshenka ka daina jifana da wannan munanan kalaman."

Acp ya kalli na kusa dashi cikin bada umarni yace."Ka daure masa hannu muje station idan yaji mazga! zaiyi mana bayani."

Da sauri suka nufeshi, muddibo ya dinga zare ido jikinsa na kyarma gumi! na keto masa, yau shi za'a daurewa hannu!!! yana dan mulki dan sarauta kafin ya ankara yaga sun kamo hannunsa duk biyun ya dinga fizgewa suka rike da kyau suka daura masa ankwa.

Acp yazo ya cire hular dake saman kansa ya ajiye, botiran rigarsa ya cire yace."Ku fita dashi." Muddobo turjewa ya shiga yi bakinsa na rawa yace."Acp ni zaka ciwa mutunci a gurin aikina.''? Acp yace."Kaga Muddibo bani da wata magana da kai muje station kawai dukkanin bayanai suna can.

Muddibo yace."Babu inda zanje wallahi." yafada yana turjewa, Acp wani bahagon mari! ya kwada masa! hancinsa ya fashe ya fara d'igar jini! a harzuke! yace."Muddobo bana san gardama muje station kawai." Muddibo idanunsa sukayi jajawur ya dinga kallon acp din yana mamakin marin daya kwada masa! Acp cikin wata irin tsawa! yace."ba za ka tafi ashe sai na kwance blet kenan."? cikin tsantsar takaici da tashin hankali ya soma tafiya, jami'an suka rirrike kafad'unsa, a haka suka fito daga ofis d'in, cikin tashin hankali jama'ar dake zaune a reception din suka mike tsaye suna kallonsu har suka fita, wasu daga cikinsu har bakin mota suka rakosu, sai da suka ga motar police din ta fita daga ma'aikatar sannan suka koma ciki suna mamakin abinda yake faruwa..........
Chapter 57 · 0% Book details