Sashe 64
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na dinga kallonsa ina mamakin maganarsa "Tara 'ya'ya shine bai da alfanu."? 'kwarai kuwa mutukar gurin daukar cikinsu da haihuwarsu na barazana da rayuwarki to gwara ki hakura.'' cikin takaici nace" Mace koda haihuwa ko babu haihuwa sai ta mutu! kuma inaso kasani duk macan data mutu gurin haihuwa tayi shahada saboda haka ka daina wannan maganar dik wata wahala mai shigewa ce iyayenmu da kakannin mu a haka duk suka tara 'ya'yansu dan haka dan Allah ka daina wannan maganar sam bata dace ba su 'ya'ya rahama ne sannan kuma a ranar lahira Annabi Muhammad (SAW) zaiyi alfahiri da jama'arsa.........
*Na kudi ne.*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya ni! Keda da kika futa da littafin keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal gruop#300....account... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊ðŸ?)
91
Har yanzu fuskarsa babu sassauci yace."Nasan da haka ba sai kinyi min wa'azi ba a tsarina ni bana son tarin 'ya'ya da yawa bayan haka kuma ita haihuwar wahala gareta mutanan da dana yanzu ba daya bane nada sunfi kwari da karko na yanzu kuwa haihuwa daya biyu sun lalace shiyasa bana son ki haihu da yawa." Murmushin takaici nayi nace"Ni kam wannan magana ta isheni wallahi duk yanda nake so na fahimtar dake yanda al'amarin yake ba zaka fahinta ba saboda haka mu bar maganar iya adadin 'ya'yan da zan haifa a duniya Allah ne kadai yasan yawan su."
Shuru yayi yana kallona, babu alamun nadama a fuskarsa na dinga mamakin halinsa bashi da rufi ko kadan duk abinda yake zuciyarsa fada yake yi kansa tsaye in banda abinsa waye yake gudun rahama ai 'ya'ya rahama ne amma shi tun kafin ma yayi auran ya yankewa kansa hukunci Allah dai yasa kada zama da turawa yasa ya dauki munanan dabi'unsa dan gashi alamu nan."
Kaina na sunkuyar ganin yana kure ni da kallo nace"Ka tafi gurinka dan Allah ko da akwai abinda kake bukata."
Ajiyar zuciya ya sauke yace."Ina bukatar abubuwa guda uku amma nasan da wuya na samu duka.
Kallonsa nayi ya daga min kai da fadin"farko dai ina bukatar naji ki a jikina na biyu ina bukatar abinci na uku kuma nayi wanka."
'Bata fuska nayi nace"Tashi muje falo na baka abincin." girgiza kansa yayi yace."Kije ki kawo min nan ni babu wani falo da zanje." na jima ina kallonsa kafin nayi yun'kurin mikewa sai na tuna da kayan dake jikina da sauri na koma na zauna gabana na faduwa.
Bargon dake jikina yake kokarin janyewa na rike da kyau ina girgiza masa kaina nace"Dan Allah dauko min hijabina gashi can akan kujera.
Cike da mamaki yace."Lallai kin raina ni zaki aika."? girgiza kaina nayi yace."Dallah tashi ni ki kawo min abinci me zaki boye min bayan komai nawa ne."
Idona ne ya kawo ruwa nace"Ni dai dan Allah ka miko min hijabin wallahi kayan masu fitar da tsaraici ne." kallona ya shigayi yana girgiza kai yace."Tsaraici.''? kaina na sunkuyar ina sake rufe jikina da bargon, mikewa tsaye yayi kawai yasa hannu da karfi ya fizge bargon daga jikina, tsigar jikina ta mike da sauri na takure jikina guri guda ina watsa masa harara!
Wani irin kallo yake bina dashi tun ba kirjina ba nasa hannu ina karewa, ajiyar zuciya ya sauke a hard'e yace."Tashi." 'kin tashi nayi na takure jikina hawayen bakin ciki na nema ya kufce min......"Kin san Allah idan baki tashi ba zan aikata miki abinda bakya so yanzu." jin abinda yace yasa da sauri na kalleshi, gani nayi idanunsa ya sauya, gabana na faduwa na mike, ya bini da wani irin kallo da hannu ya nuna min k'ofar fita, ina takure jikina na kama hanyar fita a jikina naji kallona yake shiyasa da saurin gaske na bude kofa na fita.......a gurguje nake hada masa abincin kawai naji motsinsa a bayana, da sauri na juyo kirjina da nasa ya had'u hannuwansa duka ya d'ora akan mazaunaina! ya wani matseni a kirjinsa yana matsa min mazaunai! kirjinsa na doka da karfi! tsaki naja da sauri na janye jikina, bina yake da kallo kamar maye, nayi gaggawar daukar tire din dana shirya masa abincin na barshi a tsaye a gurin.
Ina ajiye tire din na dauki dogon hijabina nasa na zauna kan kujera gabadaya raina ya 'baci da irin abinda yake min.
Koda ya shigo dakin be kalli inda nake ba, yaje ya zauna gaban abincin a nutse ya zuba abinsa ya fara ci, sai da ya kammala tsaf ya tashi ya nufi toilet........jin shuru bai fito ba yasa na shiga tunanin abinda yake a ciki, motsinsa naji nayi saurin kallon kofar toilet din daga shi sai gajeran wando da vest jikinsa ya nuna alamun ruwa wanka yayi, kallonsa nake har ya isa kan gadona ya kwanta hankalinsa kwance ya rufe jikinsa da bargona.......Nace"Bangane ba." shuru yayi min.......nace"kasan bai dace ba ko dan Allah ka tashi ka tafi gurina hakan bai dace ba."
"Sumayya bazan tafi ba yau anan nayi niyyar kwanciya idan kuma kina da karfi kizo ki fitar dani." nace"Wacece ni ranka ya dade Allah ya baka hakuri." mikewa nayi na kama hanyar fita gwara na bar masa dakin akan mu kwana tare nasan halinsa zai iya haike min.
Kawai na ganshi a gabana ido jawur na kalleshi! bai tanka min ba ya murza key a jikin kofar ya zare keyi din ya barni a tsaye!
Hawayen takaici suka zubo min, a gaskiya lamarinsa akwai wuyar sha'ani! juyawa nayi naga ya koma ya kwanta tare da lullube jikinsa da bargo.
Jiki a sanyaye naje na kwanta kan sofa ina kudindine jikina da hijabina, miryarsa naji ciki ciki yace."Ki zo ki kwanta ba zanyi miki wani abuba."
Share shi nayi ina jin wani irin haushinsa a raina, magana yake min nayi masa banza daya gaji sai yayi shuru can kuma na dinga jin saukar numfashinsa a hankali nan na gane bacci ya daukeshi, a hankali na gyara kwanciyata ina addua a cikin zuciyata.
Da asubah kusan a tare muka tashi dan ina jin motsin shigarsa toilet na bude ido, zaune na mike ina salati can naji kira ya shigo wayarsa, a nutse na mike na iske inda wayar take, lokacin kiran ya katse wani ya shigo, ina kokarin daukar wayar ya fito daga toilet din jikinsa sanye da kayansa na jiya daya cire da alwala a tare dashi, a nutse na mika masa wayar na nufi toilet domin daura alwala, koda na fito samunsa nayi zaune a gefan gado ya rufe fuskarsa da tafukan hannayensa, gabana ya fadi! da sauri na karasa kusa dashi tare da fadin"Lafiya."?
Fuskarsa ya bude yana kallona da jajeyen idanunsa yace."Sumayya daya daga cikin matan da nayi wa operation ce ta mutu misalin uku da rabi na dare.
Kafafuna suka shiga kyarma zama nayi kusa dashi ina kiran innalilihi wa'ina ilahi raji'un."!!!! dakin yayi shuru na minti uku kafin ya sauke zazzafar ajiyar zuciya ya kalleni, hawaye na share nace"Ubangiji Allah ya jikanta Allah yasa aljanna makomarta."
Ya amsa da "ameeen ya rabbi Jiya fa lafiya lau aka fito da jaririn kafin na fito daga hospital din sai da na tabbatar da komai yayi normal sannan! ashe bayan tafiya da minti arba'in jini ya tsinke mata kafin ayi wani yunkiri ta mutu ta bar jaririnta." murya na rawa ya karasa maganar......Nace"ikon Allah kenan! kaga ita waccar matar yaron ne ya mutu ita tana raye! wannan kuma gashi ta mutu ta bar yaron Allah babu yanda baya tsara lamarinsa, dama haka rayuwar duniya take Allah Ubangiji yasa mu cika da imani." Babu kuzari a tare dashi ya amsa da ameeen ya rabbi! mikewa yayi da fadin"Bari naje masjid." A sanyaye na bishi da kallo har ya fita daga dakin.
Ina kokarin nad'e daddumar da nayi sallah ya shigo dakin, kallo na bishi dashi ina mamakin abinda ya shigo dashi, na dauka ai ba zai dawo ba, yanayin fuskarsa ya nuna cewar lallai akwai magana a tare dashi.
Zama yayi kan gado da fadin"Zo Sumayya." a nutse naje na zauna gefansa, ya jima yana kallona kafin yace." Bana so ni dake muyi aure a bebai yana da kyau tun kafin zaman aure ya had'amu ki san abinda nake so da wanda bana so a tsarina mace d'aya ta isheni sai dai nasan hakan ba zai yuwu ba sannan bani da ra'ayin tara 'ya'ya koda matan aurena zasu kasance hud'u to na riga na tsara rayuwata bance kowace mace dole sai ta haihu dani ba! yara biyu zuwa uku sun isheni rayuwar duniya Sumayya ina da tausayi mutuka wanda shine dalilin daya sa kwata-kwata naji haihuwa bata burgeni saboda irin wahalar da mata kesha kafin suyi bana so duk haihuwa ya kasance sai kinsha wuya kin galabaita saboda haka na zaunar dake na fada miki tsarina itama Lawisa zan zauna da ita a yau na fad'a mata ra'ayina ina fata zakiyi wa maganata kyakkyawar fahimta.
Cikin wani irin yanayi na alhini da damuwa nake kallonsa, tsabar mamakin maganarsa ma ya hanani cewa komai baya son haihuwa ya riga ya tsarawa kansa rayuwa wannan wane irin bayahudan mutum Allah ya had'ani dashi, dauke kaina nayi kawai ina girgiza kaina!
Ya juyo da fuskata muna fuskantar juna yace."Banji kice wani abuba." Murmushin takaici nayi nace"Ai ni maganar taka ce tayi min nauyi shiyasa kawai nayi shiru ina auna maganar."
Yace."Wane irin kina auna maganar okey to ina sauraranki naji a wane ma'auni kika ajiyeta." yakarasa maganar tare da tsare ni da ido.
Kallonsa nayi babu wasa a tare dani nace"Ni dai nasan musulma ce gaba da baya kuma nasan addini daidai gwargwado to a matsayina na musulma wacce ta kadaita Allah shi kad'ai ban isa na tsarawa kaina rayuwar da nake so ba koda zan haifi 'ya'ya dubu a duniya to ba zan ta'ba butulcewa Allah ba.'''