← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 90

Sashe 2

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Finkice bulalar yayi daga hannuna ya daga da karfin gaske ya shaud'a min a bayana ban san sanda na k'wallara k'ara ba, wannan 'karar da Sumayya tayi har can gurin taron babu wanda beji ba.
Maimartaba ya tashi fadawa da sauri yace suje su duba cikin gidan..........."Wuce mu koma gurin taro ki fuskanci hukunci ko su waye iyayenki a cikin gidan nan kin janyo musu fushin masarauta.'' Abinda yake fada min kenan tare da inginza ni wai lallai sai mun koma gurin taron, ni kuma tsabar taurin kaina sai turjiyewa na keyi hawaye na zuraro min.
Fadawan da Sarki ya turo suka karaso gurin suna tambayar abinda ke faruwa, a take Sarkin kofa yayi musu bayani, Naga babban cikinsu ya zare min ido hade da buga min razananniyar tsawa! ya bani umarnin shigewa mu tafi. Turjewa nayi ina kallonsa da busassun idanuna a fusace! ya tattare babbar rigarsa ya d'auki ni ya sa'ba a kafad'arsa kai tsaye gurin taron ya nufa dani ina kuka da dukansa da zille zille haka ya dinga ratsa mutane dani bai dure ni a 'ko'ina ba sai gaban maimartaba. gurfana nayi nayi qasa da kaina hawaye na karakaina a fuskata.......Lawi da matarsa hankalinsu ya tashi dan ganin 'yarsu a gaban maimartaba da alama ta janyo musu fushin masarauta sai duk jikinsu yay sanyi cikin kaskantar da kai suka sunkuyar da kansu gabansu na faduwa, Gabad'aya gurin shuru yay kowa na jiran sarki yayi magana.....wanda har lokacin Yarima Ali! na tsaye goye da hannu kamar wani soja! Maimartaba ya kalli bafaden yana bukatar karin bayani.
Da sauri ya sunkuyar da kansa kasa yace."Ranka ya dade wannan yarinyar can cikin gida muka sameta tare da d'aya daga cikin masu tsaron kofar bangaran bayi suna jayayya da juna kan umarnin daka bayar." Mai tsaron kofa yace."Allah ya taimake ka na ganta zata shiga gida sai na dakatar da ita tare da tambayarta wanda ya bata izinin baro gurin taro bayan ba'a tashi ba shine take fadin maganar da bata cancanta ta fito daga bakinta ba a matsayinta na makaskanciya bai kamata ta nuna gazarwata gurin jimirin tsayuwa a cikin rana domin tar'bar Yarima Ali ba, yarinyar tayi min bayani cewar ita ba zata iya tsayuwa a cikin rana ba."
Gurin yay tsit kowa na mamakin furucin da 'yar gidan Lawi bawa! tayi shin da me take taqama dashi ko kuma dame tafi sauran bayin dake masarautar da har take fadar wannan maganar.......Yarima Ali kansa a kasa kamar mai kallon kasan gurin amma yarinyar kawai yake kallo takasan idanunsa bakin gilashin dake idonsa shi ya hana a gane ita din yake kallo, mamaki maigirma yake akan furucin yarinyar ba zata iya tsayuwar a rana ba saboda bata daukeshi da mahimanci a cikin masarautar ba, murtuke fuskarsa yayi ya kauda kansa daga gefan da take gurfane wani irin tsanar yarinyar yaji a cikin zuciyarsa.......Maimartaba yay gyara murya a nutse yace."Yarinya meye sunanki."? Murya na rawa tace"Ranka ya dade sunana Sumayya Lawi mahaifina shine ke kula da 'bangaran dokuna." Sarki yay shuru na minti biyu kafin yace."Sumayya me yasa kika karya dokar masarauta bayan kin san dacewa qa'ida ne idan na kira taro kowa ya hallara kuma masarauta bata bawa kowa damar tafiya ba sai na tashi shin kin san muhimmacin wannan ranar a gurina da masarautar gabad'aya."? Kanta a 'kasa ta girgiza kai da fad'in "A gafarce ni a ranka ya dad'e nima ba'a son raina ba wallahi kaina ne keyi min ciwo." Jin abinda tace yasa Yarima Ali harar gefan da take yaja tsaki 'kasa-'kasa d'auke kansa yay yana sake 'bata rai.

Sarki! yace."Naji uzirin ki Sumayya mai yasa da zaki tafi baki nemi izini a gurin wakilai ba." Shuru tayi tare da kaskantar da kanta kasa....Maimartaba yace."Wannan rana nada mutukar mahimanci a gurina da masarautarmu rana ce wacce ya kamata mu sata a cikin kudin tarihin masarauta, tsayin shekaru goma sha biyar masarauta tayi ba tare da d'an cikinta ba wato Yarima Aliyu mai jiran gado.....Tun yana da shakaru goma sha biyu a duniya ya sauke al'kur'ani maigirma tare da sauran littafan addini sai na turashi can kasar amuruka domin neman ilimin zamani Aliyu ya za'bi karatun likitanci wanda ya tabbatar min dashi ne ra'ayinsa ni kuma na goya masa baya domin ya samu ingantaccan sani ta kowane 'bangare..Alhamdulillahi ya sama dukkanin abinda ake bukatar a samu muna sanya ran dawowarsa gida sai 'kasar ta b'ukaci daya zauna da ita domin ya taimaka musu da abinda Allah yayi masa, ina zaune a fada sa'ko ya isa gareni akan wannan magana, ba'a son raina na amince da zamansa a kasar ba sai dan ganin shi ya nuna yana bukatar ya zauna ya taimaka musu yasa na amince masa, anan yake tabbatar min da cewa shekara bakwai kacal zaiyi dasu ya ajiye aiki ya dawo 'kasar sa domin suci moriyarsa wannan dalilin ya sanya na amince da bukatarsa.....A Yau ne Allah yayi nufin dawo dashi gida gabad'aya kamar yanda yayi min al'kawari, wannan dalilin yasa na bada umarni kan cewa dukkanin wanda yake karkashin masarautar nan ya fito domin ya nuna farin cikinsa akan dawowarsa gida lafiya, sai gashi ke! da baki san shi ba kin kasa tsayuwa ki tantance shi ki kama hanya kin tafi koda yake kema kin kawo uzirinki ciwo ya wuce komai! saboda haka anyi miki afuwa abisa karya doka da kikayi amma kada ki sake kwatanta abinda kikayi a yanzu dai masarauta ta yafe miki laifin da kika kaita."

Kaina a 'kasa nace"Godiya nake ranka ya dad'e ubangiji Allah ya qara maka lafiya da nisan kwana insha Allahu ba zan kara ba." Lawi da Tambaya iyayena sune suka karaso gurin suka gurfana gaban maimartaba suna godiya gami da sake neman afuwa." Maimartaba ya girgiza kansa a nutse yace."Babu damuwa kuna iya tashi." Da sauri muka miqe a tare muka koma muka tsaitsaya cikin 'yan uwanmu bayi.......
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *[email protected]*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
Chapter 2 · 0% Book details