← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 90

Sashe 40

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Magajin Sarki ya turke Suwaiba ita dashi ya tsoratar da ita mutuka Suwaiba na kuka gami da nadamar abinda tayi ta sheda masa yanda al'amarin ya faru, wato Muddibo ne ya tursasata kan lallai sai tabi umarninsa tayi amfani da wani igur'bataccan ruwa mai wari daya kawo mata cikin wata jarka yace lallai tayi dahuwar abinci da ruwan kuma ta tabbatar Abinda ta dafa Yarima yaci, babu yanda ta iya haka ta dinga mu'ku-mu'ku da ruwan guban har dai ta yanke shawarar dafa doya dashi, bayan ta tsame doyar ne tana tsaka da soyawa a ranar da al'amarin zai faru ya shigo kicin din ya sallameta daga aiki ita kuma Sumayya ta dauka ta kaiwa su Haruna suka ciki.

Magajin Sarki beyi mamaki ba dan yaji ta ambaci sunan Muddibo dama tuntuni yake zargin akwai sa hannunsa a cikin faruwar al'marin, nasiha mai ratsa jiki yayi mata ya tsoratar da ita sannan ya nuna mata illar abinda ta aikata wato ta amince an hada baki da ita anyi kisan kai. Suwaiba kuka kawai take tana neman gafararsa, yace."Bani zaki nema gafara ba Allahn daya hallice ki shi zaki nema gafara ki tuba ki nemi gafararsa sai ya yafe miki."
Tace."Insha Allah na tuba nabi Allah da manzon Allah ba zan sake yarda wani ya tursasani ga aikata sa'bon Allah ba.'' Magajin sarki yaji dadi sosai da tuban ta, sallamarta yayi ta tafi tana addua akan Allah yasa kada ya fad'awa mahaifinsa harda saka hannunta a cikin faruwar al'amarin, bangaran Yarima kuwa baya tsammanin zai fad'awa kowa maganar domin fitar da ita yana nufin abubuwa da yawa barin ta shine yafi kwanciyar hankali.

******

Yau asabar duk ranakun weakened baya fita da wuri yana gida yana hutawa wani sa'in har na gama abinda nake na fita yana sama yana bacci abunsa abin mamaki yau dana shiga samun sa nayi a falo a zaune yana kallon kwallon kafa. gaishe shi nayi babu yabo babu fallasa ya amsa, kicin na nufa ya kira sunana

Tsayawa nayi ina kallonsa, kusa dashi ya nuna min. "Zo ki zauna yau ranar taki ce zamu tattauna maganar dana jima ina fada miki."

Gabana ne ya fadi ni sam na manta da wata magana, cike da rashin tsoro nace"Yallabai wace irin magana zamu tattauna wacce har sai nazo na zauna kusa da kai."

remot din hannunsa ya ajiye yace."Magana ce ta mussaman wacce take bukatar sirri."

Ajiyar zuciya na sauke nace"Ni da kaine kadai a dakin nan ina ganin ba sai na zauna kusa da kai ba babu wanda zaiji ko ya gani kawai ka fadi maganarka ."

'Kure ni yayi da ido yana kallona, nima nawa idon nasa masa dan gabadaya yanzu na daina jin tsoransa, "Kinga ni ba wani abu zanyi miki ba naga kina min kallon rashin yarda maganar da zanyi miki nafi bukatar na ganki a kusa dani shine dalilin daya sa nace kizo ki zauna?"

Shuru nayi ina naxarin maganarsa a sanyaye yace."Ki yarda dani da maganata ba zanyi miki komai ba." kallonsa nayi naga yana marairaicewa, ajiyar zuciya na sauke naje na zauna kusa dashi.

Ya kai minti biyar yana kallon k'asan gurin kafin ya dago kansa ya kalleni, kauda kaina nayi gefe, hannuwana ya ri'ke nayi saurin kallonsa! a sanyaye yace."Sorry.'' ajiyar zuciya na sauke nace"Ka sakar min hannuwa ka kuma fadi maganar dake bakinka."

Murmushi yayi yace."Yarinyar nan watarana idan kina bani umarni har mamaki kike bani gaskiya kina da karfin hali kina kuma burgeni wani lokacin kuma kina 'kuntata min"

Zum'bura bakina nayi na kauda kaina gefe hannuwana na cire daga nasa.
Hannu yasa ya juyo da fuskata naga yana min wani irin kallo wanda ya sani faduwar gaba, da sauri nace"Wai baka zaka fadi maganarka ba." Ba zato naji saukar hannunsa a le'bena yana shafawa.'' doke hannun nayi ido jawur nace"Ai dama nasan sai ka gwada halin ka." mikewa nayi da sauri yay gaggawar mayar dani na zauna
Fuska a hade yace."Ni kike dokewa hannu.'' hanci na hura ina ji tamkar na doki bakinsa dan haushi fitinannan mutum ne shi mai 'ketare iyakokin ubangiji.

Ajiyar zuciyarsa naji na kalleshi naga ya shiga hankalinsa sosai, kasa nayi da kaina ina jiran naji ta bakinsa

"Kin san abinda yasa nace kizo kusa dani muttauna." ? girgiza kaina nayi nace"Sai ka fada." Yace."Na dauki d'amarar auranki kamar yanda kika kwad'aita min zan aureki insha Allahu ina bukatar amincerki."

Kai tsaye nace"Yallabai ai ka makara me yasa tun lokacin da nayi maka maganar baka amsa ba a yanzu iyaye sun riga sun shiga cikin lamarina da Haruna an tsayar da maganar auranmu wata hudu masu zuwa maganar auranmu ma maimartaba ya san da ita

Wani irin shan kunu yayi yana kallona yace."Karya kikeyi kizo min da wannan maganar baku isa ba keda Harunan naki aure ni zan aureki shi yaje can ya nemi daidai dashi.'"

Cike da mamaki nake kallonsa nace"Haruna nice daidai dashi kamar yanda yake daidai dani kaine zakaje ka nemi daidai da kai tunda ka fada cewa ni ba tsaran auranka bace.''

Shuru yayi gumi na yanko masa. nace"Idan ka gama maganarka ni zanje nayi aikina." Ido jajawur ya dago yana kallona yace."Na fada miki fa baku isa ba wallahi sai an warware maganar auranki da Haruna ko kuma naga bayansa."

Gabana ya fad'i jin abinda yace nace."Ranka ya dad'e kana musulmi kake fad'ar wannan maganar zaka ga bayan Haruna me zakayi masa to."?
Ido yasa yana kallona nace"Ashe kaima zuciyarka irin ta 'yan uwanka ce gashinan kana mummunan lafazi akan wanda be maka komai ba."

Ajiyar zuciya ya sauke ya kama hannuwana duk biyun ya rike a raunane yace."Kada kiyi min wata fassara ta daban raina ne ya 'baci na fad'i wannan maganar Please Sumayya muyi maganar da zata amfane mu ni dake a yanda nake jin ki a zuciyata bana tsammanin zan iya bari Haruna ya aure ki."

Nace"Ranka ya dad'e Haruna shike sona tsakani da Allah kai kuma sha'awata kake zaka aureni domin ka kawar da sha'awarka shikkenan idan bukatarka ta biya sai ka sake ni, Haruna kuma zai aureni saboda yana sona tsakani da Allah badan wani abu na jikina ba kai kanka ka zauna kayi nazari da tunani akan al'amarin nan Yallabai kasowa kanka abinda zakasowa d'an uwanka yanzu babu wata sauran magana a tsakanina da kai tunda maganar aurena da Haruna ta shiga tsakani."

"Kin san dai Haruna bai isa ya had'a neman aure dani ba ko."? kallonsa nayi inaso nayi magana ya katseni a harzuqe yace.''Kije ki kira min Harunan naji ta bakinsa."

Cikin fad'uwar gaba nace"Bangane kaji ta bakinsa ba." Hannu ya d'aga min fuska a had'e yace."Kada ki sake harzuqani kije ki kira min shi nace."

Jikina ne yayi sanyi nace"Dan Allah ka bar wannan maganar ka fuskancin abinda ke gabanka ka auri daidai da kai nima na auri daidai dani."

"Sumayya." ya kira sunana kallonsa nayi, yace."Ba zan hakura dake ba ki rubuta wannan ki ajiye idan kin auri Haruna kin barni sai na hana ku jin dadin rayuwa gwara ku magance matsalarku keda shi Nafi karfin na nemi abu wanda yake kark'ashina ya had'a takara dani dole Haruna ya janye maganar auranki."

Nace"Ranka ya dad'e lafazan ka na nuna min cewar babu kyakkyawan nufi a cikin zuciyarka kada ka cutar da Haruna dan beyi maka laifin komai ba kuma ka daina gwada iko da mulki a kaina Allah ba'a nuna masa gadara idan Allah ya kaddara ni d'in ba matarka bace ya zakayi."?

Jajayen idanunsa ya zuba min yace."Bakya shakka kallon tsabar idona ki fada min magana ko." ? sunkuyar da kaina kasa nayi nace"Gaskiya d'aci gareta shiyasa kake gani kamar naci maka fuska."

Kwafa yayi yace."Dallah tashi ki bani guri kafin na da'uke fuskarki da mari."!! ganin yanda yake zabura yana huci! yasa nayi gaggawar tashi ina mamakin al'amarin.......kicin na nufa ba tare da naje aiken da yayi min ba.

Mikewa yay ya bude kofa ya fita, suna ganinsa suka taso daga inda suke zubewa sukayi a gabansa suna tambayarsa, babu walwala a tare dashi ya kalli Haruna da fadin"Ka shigo ina neman ka." Haruna yace."To ranka ya dade." Juyawa yayi ya koma ciki Haruna yabi bayansa.

Yana tsaye a tsakankanin kujeru Haruna ya same shi, Cike da ladabi yace."Ranka ya dade ina fata banyi laifi ba. wani irin kallo yayi masa kai kana ganin kallon kasan na kishi ne......Yace."Meye tsakaninka da yarinyar nan Sumayya."? Haruna yasha jinin jikinsa a sanyaye yace."Ranka ya dade itace matar da zan aura.'''

''Yaushe aka tsayar da ranar auran naku bani da labari."? Haruna ya sake kaskantar da kansa yace."Ranka ya dade ayi min afuwa wallahi na sha'afa shiyasa ban fada maka halin da ake ciki ba."

Ajiyar zuciya ya sauke ya zauna kan kujera yana kallonsa da wata iriyar murya yace."Inaso ka janye maganar auranka da Sumayya."!

Haruna gabansa ya buga da sauri ya dago kanshi yana kallonsa bakinsa sai rawa yake ''Ranka ya dade ban.......! Hannu ya daga masa ya hanashi karasa maganarsa, Haruna 'kasa yayi da kansa Gumi na tsiyayo masa.

"Kasan a 'karkashina kake ba zai yuwu ina neman abu kana nema ba dole ka janye maganar auranka da yarinyar nan." Wannan maganar da yayi yasa Haruna ya gane inda ya dosa.

Shuru yayi ya kasa magana yayin da gumi ya jikashi jagab ta yaya zai janye maganar auransa da Sumayya bayan ansa rana iyaye da abokanan arziki duk sun san halin da ake ciki, ta yaya zai iya cire tsananin so da kaunar da yake wa Sumayya a cikin ransa? babu shakka wannan babban al'amari ne a gare shi.

"Haruna kana jina ko."? da sauri yace." Eh Yallabai naji maganar ka nasan kai ba sa'ana bane ta kowane fanni! insha Allahu zanbi umarninka."

"Okey nagode sosai inaso ka shedawa iyayenka umarnina." Jiki a mace yace."Idan Allah ya yarda zan sheda musu." "okey kana iya tafiya." Yafada yana nuna masa hanya da hannu.
Chapter 40 · 0% Book details