← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 90

Sashe 56

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaina na dauke jin wani irin abu dangane dashi, ya miko min brush da fad'in" Maza ki wanke bakin ki idan kuma ba zaki iya ba nayi miki ko."? saurin kar'ba nayi na nufi inda famfo yake, a nutse na wanke bakina cikin dubara nai alwalar, ya karaso gurin hannuna ya rike muka fita daga toilet din.
Farin hijabi irin na ma'aikatansa ya samin a wuyana ya gyara min dadduma na tayar da sallah.

Zama yayi kan kujera da wayarsa number Acp ya kira, suka gaisa cikin mutumci yayi masa bayanin dukkanin abinda ke faruwa, Acp yace."Tabbas biri yayi kama da mutum ranka ya dade a binkicenmu na baya sai da naso na fuskanci wani habu daga gurinsa to alhamdulillahi dama barinmu mu kama wanda yake da hannu acikin al'amarin sabida haka ka kwantar da hankalinka insha Allahu yau din nan zamu dam'keshi dole ne yayi mana bayanin yanda al'amuran suke faruwa." Yace."Okey to babu damuwa amma bana so ku shiga masarautar da niyyar kamashi kuje gurin aikinsa ku tozartashi acan sannan ku daureshi ku tafi dashi, bayan kun dam'keshi ka kira ni a waya inaso dik wani bayani da zaiyi ya kasance ina gurin." Acp yace."Babu damuwa insha Allah zan kira ka idan komai ya kammala." Sallama sukayi ya kashe wayar, ido muka had'a! naga fuskarsa ta rikice da zallar 'bacin rai! a gaskiya ban ta'ba tsammanin ina da kima a gurinsa ba.
A marairaice nace"Don Allah ka bar maganar nan wallahi idan nice na yafe."
Wani irin kallo yayi min kafin yace."Kada ki sake wannan maganar idan kina so mu zauna lafiya dake kiyi shuru da bakin ki Muddibo kashe ki yayi niyyar yayi kina tsammanin idan kin bar duniya zanyi rayuwa mai dadi? dole ne nabi kadin jinin daya zubar miki."

Kallonsa na dinga yi ina mamakin maganarsa nace"Mutuwa dole ce a gurin ko wane musulmi koda Muddibo ya kasheni nayi shahada kuma na rataya a wuyansa sabida haka dan Allah ka daina wannan maganar.

Ya jima yana kallona kafin yace."Ke! Sumayya bari nayi miki maganar k'arshe daga yau na 'yan taki kin zama mai 'yanci kuma insha Allahu a cikin satin nan za'a daura min aure dake! inaso ki zauna a k'arkashina cikin tsaro! dan na fahimci cewa ma'kiya zasu huce fushin su a kanki to zan aureki ki zauna a karkashina mu cigaba da rayuwa cikin inuwa daya.

Cikin tsabar kad'uwa da firgici nake kallonsa, ya daga min hannu tare da fadin"Bana bukatar naji komai daga bakin ki na gama yanke hukunci." Mikewa yayi tare da fad'in "Tashi muje gida." Na mike jikina a mace! gaba yayi nabi bayansa ina mamaki abinda yake shirin faruwa da rayuwata, Yarima zai aure ni sabida ya ceci rayuwata! ko kuma dai zai aureni ne saboda ya biya bukatarsa a kaina kamar yanda ya kud'urta a can baya, wannan tunane tunane ne ya dameni a fakaice na dinga kallonsa ina so na karanci abinda ke cikin zuciyarsa.

*Na kudi ne..*
Kada ki karanta mun littafi idan baki biya ba, idan kina bukatar ki biya ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal gruop#300 account.. 0542382124.....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta whsap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:27 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
86
Duk yanda naso na karancin abinda ke cikin zuciyarsa kasawa nayi dan gabad'aya tunda muka shiga mota ya sanja fuskarsa ta rikid'e sosai tamkar wanda bai ta'ba dariya ba, na dinga satar kallonsa ina mamakin sauyawarsa, har muka shiga masarautar wata magana ta fatar baki bata had'ani dashi ba......"Mika'il Ka wuce damu can sashen Mahaifiyata." Da sauri na kalleshi, hankalinsa nakan direba yana bashi umarnin inda zai ajiyemu, Mika'i da sauri ya juya mota ya hau hanyar da zata sadamu da sashen mahaifiyar tashi......Alhamdullilahi naji yace kafin yasa hannu ya bude kofar motar, yana fitowa nima na fito kaf ma'aikatan dake gurin suka bar abinda sukeyi suka zo suna mika gaisuwarsu gurinsa, nayi mamaki sosai da ganin ya tsaya yana amsa musu, gaba yayi da sauri nabi bayansa, jama'ar gurin suka bi bayanmu da kallo domin dayawa daga cikinsu sun dauka ba zata dawo da rai da kafafunta ba saboda yanda aka fita da ita jina-jina da jini.

Tana zaune kan kilishi da carbi a hannunta muka shiga falo tare da sallama a bakin mu. zamanta ta gyara ta amsa sallamar tare da tsira mana ido fuskarta kadai ta isa ta nuna mana cewar taji dadin ganinmu, cikin sanyi jiki nake tafiya kaina a kasa, dan shi har ya karasa kusa da ita ya zauna suna gaisawa, gurfana nayi a gabanta kawai naji ta janyoni ta rungume kam a jikinta sai saukar hawayenta naji a bayana, kawai naji nima zuciyata ta karye hawaye ya dinga kokarin kwace min.

Cikin rarrashi yace."Mamma dan Allah ki daina kuka ai gatanan da ranta bata mutu ba kamar yanda Muddobu yayi niyyar kasheta." buka Da sauri ta kalleshi tana mamakin furucinsa. kansa ya daga mata yana so ya tabbatar mata da gaskiyar maganarsa,

A sanyaye ta dago ni tana kallon fuskata, cikin alhini ta dora hannunta saman raunin dake goshi na murya na rawa tace"Sannu kinji ko."? kaina na daga mata cikin kokarin danne damuwata nace"Mamma ki kwantar da hankalin ki insha Allahu babu wani abu da zai sake faruwa dani dukkanin mai nufin mu da sharri zai koma kansa."

Ajiyar zuciya ta sauke tace"Sumayya jiya da kyar na iya bacci saboda wannan tashin hankalin daya faru, shin wai su waye sukayi kokarin halakar dake ne."? Shuru nayi tare da sunkuyar da kaina kasa

Ta daga kai tana kallonsa domin karin bayani, yace."Mamma kamar yanda na fada miki da farko hakane Muddobo shi kadai ya nemi ya halakar da ita kawai saboda taki bin umarninsa.

Cike da mamaki mai tsanani tace"Ni kuwa wannan al'amarin ya bani mamaki mutuka sumayya me muddibo yake so kiyi masa kika gaza har ya kai matakin daukar dutsen wuta ya buga miki.

Murya na rawa na shiga fada mata dukkanin abinda ya faru......Mamma kuka take sosai tana girgiza kanta, gabad'ayan mu hankalinmu ya tashi muka dinga rarrashinta, da kyar tayi shuru ta rike hannuna kam! "Sumayya ke 'yar halak ce kuma kin cancanci komai a gurina hakika kina d'aya daga cikin mutane da ba zan ta'ba mantawa dasu ba a tarihin rayuwata, kina da gaskiya da amana kin rike amanar dana baki duk rintsi kina kokarin kare lafiyar gudan jinina ni kuwa me zanyi miki a duniya wanda zai birgeki." ta karasa maganar tana rintse hannuna da nata.....mirmushi nayi a sanyaye nace"Ranki ya dade wallahi banyi wannan aikin domin ki biyani ba, duk abinda nakeyi akan Yarima inayi ne saboda Allah da manzon sa, Mamma wallahi bana bukatar komai a gurinki..........Mirmushi tayi tana kallona tace"Sumayya babu macan data dace da Babana sai ke ina rokon alfarma a gurinki dan Allah ki aureshi domin ki cigaba da kula dashi." Kaina na sunkuyar gabana na faduwa naji yace."Mamma ki kwantar da hankalinki dama nima hukuncin dana yanke kenan zan aureta saboda kyawun halinta da kuma tsayayyarta akaina sannan kuma zan aureta ne domin ganin ta k'ubuta daga gurin masu farautar ta, tunda duk iya kokari sunyi domun suga bayana Allah be nufa ba wannan dalilin yasa suka dawo kanta tunda itace garkuwata to idan suka kasheta suna ganin bukatarsu zata biya a kaina." ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa" Mamma na riga na yanke hukunci akan Muddibo sai dai duk abinda zai faru ya faru na shedawa Acp dukkanin abinda ke faruwa kuma ya tabbatar min da cewa zasuje su kamashi a gurin aikinsa, dole sai tabbatar mana da gaskiyar lamari."

Fulani shuru tayi tana nisawa kafin tace"Babana ba zan hanaka ka dauki mataki akan wannan lamari ba, idan ya kasance da saka hannu Muddibo cikin faruwar wannan al'amari to duk matakin da hukuma zata dauka a kansa daidai ne saboda haka yanzu zan sa aje fada a sanar da mahaifinka cewa yazo shida 'yan uwan nasa a zauna ayi magana." girgiza kansa yayi yace."Hakan yayi yana da kyau kowa ya sheda cewa Muddibo shine wake d'aya a cikinmu ke Sumayya ki nutsu sosai duk wani abu da kika san ya faru to kiyi bayani yanda kowa zai fahimta, kaina na daga gabana na wani irin faduwa.

Fulani wayarta ta dauka ta kira jakadiyarta tace maza taje fada ta sanar da Maimartaba tana da magana dashi da 'yan uwansa su Waziri.'' Jakadiya da sauri ta amsa ta mike ta fita.

Ya kalli mahaifiyar tasa a nutse yace."Mamma inaso Yarinyar nan ta zauna a gurinki bana bukatar ta sake koma sashen su har abada ta bar gurin sai dai taje da niyyar gaishe da iyayenta.

Murmushi tayi tace"Babana babu damuwa Sumayya zata zauna a gurina har zuwa lokacin da za'a daura muku aure.''' Yace."To nagode kwarai da gaske Mammana." Falon ne yayi shuru kowa na sa'ke-sa'ke a zuciyarsa, ni dai gabad'aya hankalina a tashe yake ina tsoron abinda zai faru idan jama'a suka sheda cewa Muddibo shine yake farautar d'an uwansa shin idan kowa ya yarda da maganata iyayensa zasu yarda kuwa? wace irin fahinta zasuyi min......shigowarsu falon yasa hankalina ya dawo daidai lokaci guda na shiga nutsuwata kaina a kasa, na gaishesu, Maimartaba ya dinga kallona yana girgiza kansa, a nutse ya kalli yaron nasa da fadin"Ina fatan yarinyar nan bata hadu da wata matsala ba."?

Yace."Ranka ya dade Allah ya kiyaye bata samu rauni mai muni ba amma hakika wanda ya aikata mata wannan mugun abu ranta yaso ya d'auka.'' Waziri yace."Subahannallahi! wai shin ke Sumayya ya akayi al'amarin nan ya faru dake muna so kiyi mana bayanin komai."

Mamma tace"Eh shine ai yasa na tura nace kuzo dukkaninku dan mu tuntuni tayi mana bayani kuma mun gamsu mun yarda da cewar yarinyar nan ba zata 'kir'kiri karya domin ta d'orawa wani sharri ba, a gaskiya idan kukaji wanda ya aikata mata wannan mugun abu sai kunyi mamaki amma inaso kafin ta fara bayani maimartaba ya bada umarnin kiran iyalan 'yan uwansa."
Chapter 56 · 0% Book details