← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 90

Sashe 49

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Okey to babu damuwa." Acp ya dauki waya ya kira daya daga cikin ma'aikata, ya shigo sanye da kayan aiki qamewa yayi yana miqa gaisuwarsa, Acp yace."Kuje da Merry gidan Sarki zaku dauko wannan yarinyar Sumayya zamuyi binkice akanta." qamewa yayi da fadin"Okey sir.'' da sauri ya juya ya fita...........

*Na kudi ne!*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya, keda kika futa da littafin keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake....Vip group #600 normal group #300 account... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:27 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
82
"Dan Allah kar kaqara." nafada ina sake janye jikina. Lumshe idonsa yayi ya bude a take na sunkuyar da kaina gabana na wani irin faduwa ganin yanda lokaci guda idanunsa suka jirkice."
"Idan bakya so na ta'ba ki to tashi muje mu kwanta." Hannuwana nasa na rufe kirjina hawaye na zubo min nace"Nifa ba zan yarda na kwanta daki d'aya da kai ba tunda dai kai ba muharrami na bane." Tsira min ido yayi babu yabo babu fallasa yace."Nace dake babu abinda zan miki kin tsaya taurin kai ko tom zaki janyo na kwanta a kanki yanzu."

Kallonsa nayi ina girgiza kaina hawaye na sake zubo min, ni dai ban san da wane nataccan mutum Allah ya had'ani ba."

''Ki daina zubar min hawaye bakya gajiya da kuka Sumayya kina dani bai kamata ki dinga zubar da hawaye ba."

Cikin zuciyata nace "Zubar da hawaye dole ne tunda Allah yasa ka sauka kasar nan nake kuka har yanzu na kasa samun sassauci."

A zahiri kuwa shuru nayi ina kallonsa tare da kare kirjina da hannuwana, murmushi yay ya kawo hannu zai ta'ba ni zabura nayi da sauri na matsa ina girgixa masa kaina.

Dariya yasa yana kallona, na dinga watsa masa harara hawaye na zubo min, matsowa ya sakeyi sai kawai na mike da sauri zan bar gurin.

'kuguna ya ri'ko kawai ya janyo ni na zauna a cinyarsa, kansa ya d'ora a kafadata, naji ya sauke zazzafar ajiyar zuciya, hucin numfashinsa ne yake nema ya kassara ni! kafad'ata na gotar ya sake mayar da kansa yana shanshana wuya na, kafin nayi wani yun'kuri naji yana sumbatar wuyana sai goga fuskarsa yake a gurin, cikin tashin hankali nace"Dan Allah ka bari na yarda zan bika dakin."

Shuru yayi yana cigaba da abinda yake, gabad'aya jikina ya mutu kasala duk ta baibayeni tuntuni hawaye ya daina fita tsoro da fargaba duk sun dabaibaye ni.

Hannuwansa yake kokarin 'dorawa a kirjina na rike katamau! muryana na rawa nace"Ka bari."!!! Girgiza kansa yayi a kasalance yace."Ki bari na ragewa kaina damuwa." cikin takaici nace"Ranka ya dade wani lokacin kaine kake janyowa ina maka abinda be dace ba yanzu dan Allah meye amfanin wannan iskancin da kake min."! a kufule nake maganar.

girgiza kansa yayi saitin kunnena yace."Ni ba d'an iska bane.'' fuzgewa nayi na mike ina kallonsa dik ya koma wata kala nace"To idan ba d'an iska bane menene kawai ka matseni a jikinka kana wani abu."

Hannu ya miko min da fadin "Zo my love ina cikin mayen sonki." Naji kamar na kwad'a masa mari! girgiza kaina nayi nace"Ba sona kake ba dan inda kana sona ba zakayi kokarin yin wani abu dani ba har sai na zama mallakinka." Hannu ya miko zai rike nawa na kauce! ina watsa masa harara, mikewa yayi tsaye, abinda nagani yasa ni saurin kautar da kaina, gabansa ya mi'ke sosai har ya nuna ta gaban rigarsa, gabana na faduwa nayi yun'kurin barin gurin, hannuna ya rike ya juyo da fuskata yana kallona, na dinga kauda kaina dan bana so naga abinda yake firgitani!

"Sumayya." sunana ya kira can cikin ma'koshi!! kasa amsawa nayi gabana sai faduwa yake yace."Kinga abinda kika janyo min ko."? k'in kallonsa nayi kawai naji ya dauki hannuna ya d'ora a gurin, ihu! mai karfi na kurma! na tunkud'eshi ya fadi saman kujera! fita nayi daga tsakanin kujerun na dinga nuna shi da hannu ina girgiza kaina, ganin ya yun'kura zai mike yasa a guje na bude kofar kicin na shiga na kulle ina haki! da kiran sunan Allah!

Yarima a jigace! ya haura sama ya zube kan bed yana jan numfashi, hannu ya dora saman joystick d'inshi tana nan a mike tana harbawa, a raunane yace."Kaico! kaicon ki da kai kanki inda bai dace ba! kaicon ki da sha'awar abinda ke karkashin ki!!! jijjigata yayi yaji kamar ya murd'eta ya huta da takaici! mikewa yayi zaune yasa hannu ya dafe goshinsa zufa ce kawai take keto masa, idanu yasa kan agogon dake kan bedside Uku shaura na dare, mikewa yayi yana rangaji ya shiga toilet ruwan sanyi ya dinga kuzawa kansa yana kiran sunan Allah a zuciyarsa.

Jingina nayi jikin kofar na dinga wani irin kuka abubuwa biyu sun dame ni Mutuwar Haruna ta tsaya min a rai! sai kuma masifar wannan taqadirin da Allah ya jarrabeni dashi hakika da ina da inda zanje bayan masarautar nan to dana gudu na huta da masifar wannan bawan Allah.

Zamewa nayi na zauna kasan ties had'a kaina nayi da gwiwa ina takure jikina sosai nake addua a zuciyata akan Allah ya kawo min mafita.

Tsakanin Magajin sarki da Sumayya babu wanda ya rintsa yanda suka ga rana haka suka dare!

Asubah nayi na bude kicin din na fito, lokacin yana kokarin saukowa ko kallonsa banyi ba na karasa bakin kofa, hannu nasa naji ta a rufe gefe na matsa sakamakon karasowarsa gurin
Daf dani ya tsaya yana sanye da jallabiya ash color sai kamshin turare yake, na dauka zai min magana sai naga shima ya dauke kansa, kofar ya bude ya fita, da sauri nabi bayansa.........Hadimansa na ganin fitowarsa suka karaso gurin ganina yasa sukayi sak!! yace."Sumayya ta kwana a sashena dalili jiya ni da ita bamu shigo da wuri ba sai bayan sha biyu na dare wannan dalilin yasa na hanata tafiya sashensu." yafadi hakane domin kada su zargi wani abu.

Sunkuyar da kansu sukayi suna masa barka da fitowa, gaba yayi ba tare daya amsa musu ba da sauri suka rufa masa baya domin shiga massalaci.

Ina kokarin shiga gurin mu babana ya fito daure da alwala, ganina yasa ya zube a gurin yana godewa Allah! mikewa yayi ya rike hannuna cikin murna yace."Sumayya ina fata ba suyi miki komai ba."? Nace"Ba suyi min komai ba baba amma dai basu gama binkicensu ba." A sanyaye yace."Ni da mahaifiyar ki bamu rintsa ba saboda fargaba kwana mukayi muna addua akan Allah ubangiji ya kubutar dake." Hawaye na share ina jin tausayinsu na ratsa ni nace."Baba insha Allahu Gaskiya tana tare da mai gaskiya in Allah ya yarda Allah zai wanke ni." ya amsa da ameeen da fadin" Ki shiga ciki mahaifiyarki ta ganki ko hankalinta ya kwanta." Da sauri nace"To baba." Lawi sai da yaga shigewarta cikin gidan sannan ya nufi massalaci domin gabatar da sallar asubahi.

Tambaya rungume ni tayi ta dinga kuka da kyar na rarrasheta tayi shuru ta dinga duba jikina wai ko sun dake ni. nace"Tambaya ki kwantar da hankalin ki babu abunda akeyi min sai tambayoyi."

A jiyar zuciya ta sauke tace."Sumayya jiya na shiga tashin hankali da damuwa sakamakon zuwan 'yan sanda da tafiyarki na dinga addua ina rokon Allah akan kada ya basu dama su cutar dake ina jin tsoron kada wani mara imanin ya keta miki alfarmarki."

Girgiza kaina nayi nace"Tambaya Allah ya kare ni kuma zai cigaba da bani kariya albarkacin adduarku insha Allahu wani mummunan abu ba zai faru dani ba."
Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta cigaba da kallona kai kana ganinta zaka san tana cikin tashin hankali mai tsanani, sai da na tabbatar hankalinta ya kwanta tukkuna naje na dauro alwala, na dawo kuryar dakin na shiga nasa hijabi kana na tsaya kan dadduma a nutse na tayar da sallah.

Ganinsa a massalacin yasa jikin Ciroma da mu'karrabansa yayi sanyi ikon Allah yaushe ya dawo gidan? kai amma ba suji dadin ganinsa ba. Maimartaba da Waziri kuwa babu wanda ya kaisu farin cikin ganinsa ko bayan da'aka idar da sallar Liman ya dade yana addua akan abubuwan dake faruwa a masarautar Liman yayi zafafan adduoi akan Allah ya tuni asirin masu aikata mugun 'kulli a masaraura, Ciroma da galadima jikinsu ne yayi sanyi ganin yanda Liman ya dage yana addua jama'a na amsawa da ameeen ya Allah! duk sai suka tsargi kansu da kansu suna ganin kamar asirinsu na daf da tonowa.......Muddibo kuwa dama ana idarwa ba tare da kowa ya ankara ba ya silale daga massalacin, can sashen Uwargida ya nufa ya sheda mata abinda ke faruwa, Uwargida Huwaila ranta yayi mugun b'aci! jin cewa ai Yarima ya dawo gida su duk a tunaninsu hukuma zata ri'keshi akan abinda ya faru sai kuma suka ga sa'banin haka, jiki a sanyaye ta koma ta zauna kan kujera tana tunanin mafita.
Chapter 49 · 0% Book details