← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 90

Sashe 13

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waziri ne yayi masa tsawa yayi shuru yana huci......Uwargida wato mai babban daki tace"Wato ba zaki fadi gaskiya ba kenan musu zakiyi akan binkicen da likita yayi akan farfesun da kika bashi yasha, to shikkenan tunda kina gardama ki dauki farfesun kisha mu gani."

Ina kuka nace"Ranki ya dade wallahi kiyashi ban ta'ba kashewa ballantana mutum, ni kuwa me Yarima yayi min da zan kasheshi dan Allah ku duba maganata kuyi binkice sosai akan al'amarin wallahi ban sa masa guba a acikin abinci ba."

Ciroma yace."Zaki rufe mana baki ko kuwa." Shuru nayi ina kallon qasan gurin nace"Ku gafarce ni na fada muku iya gaskiyata ne."

Dakin shuru yayi kowa yana jira yaji ta bakin Sarki, wanda yay shuru yana nazari tabbas al'amarin na bukatar bunkice kamar yanda yarinyar ta fada.

Itama Mamma tunanin da take kenan ba zai zama dole ace yarinyar ce ta zuba masa guba ba mybe akwai dai wata mak'arkashiyar shiyasa tayi shuru ba tace komai ba.

Sarki gyaran murya yay yace."Sumayya kin san girman Allah da Annabin Allah." Da sauri nace"Eh ranka ya dad'e." Yace."To magana ta k'are tunda har kinyi rantsuwa da Allah da annabi baki zubawa Yarima guba ba ki tashi ki tafi." Da sauri na kaskantar da kaina kasa nace"Godiya nake ranka ya dad'e.
Yunk'urawa nayi na miqe da fadi "Na barku lafiya." Babu wanda ya tanka min har na fita daga dakin.

Maimartaba ya kallesu a nutse yace."Ina ganin zamu tsananta binkice akan wannan al'amarin dan alamu sun nuna cewa yarinyar nan bata da alhaki akan wannan al'amarin saboda haka zamu bar maganar tunda Allah ya kiyaye gubar ba tayi tasiri a tare dashi ba ammafa hakan ba zai sa mu kasa d'aukar mataki akan duk wanda muka samu da alhakin faruwan wannan al'amarin ba." Waziri yace."Hakane ranka ya dad'e tabbas yanayin yarinyar ya nuna gaskiyarta sai a 'kara saka matakan tsaro a sashen nasa saboda gujewa faruwar wani abu makamancin wannan." Galadima da Ciroma shuru sukayi dan al'amarin gabad'aya bai musu dad'i ba sun so ace gubar ta kashe yaron kowa ya huta....... .

Ko kallonta banyi ba na nufi kofa da niyyar fita daga dakin. cikin tsawa tace"Ke! mai baqi kamar bakin tukunya tsaya anan gurin." kamar kada na tsaya sai dai na yanke shawarar tsayawa amma ban juyo ba.

Kamshin turaranta ne ya tabbatar min da cewa tazo inda nake na dago kaina ina kallonta tana yi min kallon kaskanci tace." Da izinin wa kike shige da fice a sashen Yarima." Wani kallo nai mata nace"Da izinin mahaifiyarsa." Girgiza kanta tayi tace"Itace ta baki guba kisa masa a abinci ko kuma wa." wani irin kallo nai mata nace'' Uwa ta haifi d'anta ta kashe shi anya kina da hankali kuwa."? Rai a bace ta kalleni tace"Ni kike fadawa wannan maganar."? Nace"To ai ji nayi maganar taki tayi kama data mahaukata."
Shuru tayi na minti biyu, kafin tace"Tunda kin zama mai kula dashi ta fannin abinci inaso nayi amfani dake domin cimma munufata."! Kallonta nayi babu walwala a tare dani nace"Wace irin manufa ce."?
Murmushi tayi tace"Kije zan neme ki gobe zamu tattauna." Girgiza kaina nayi na wuce daga gurin ina mamakin maganar ta

Gurinmu na koma a gurguje nayi wanka na sauya kaya kana na zauna domun karyawa hira muke da Tambaya amma koda wasa ban fada mata abinda ya faru ba, Tace"Sumayya babu abinda zamu cewa Yarima Ali kinga maganin nan da kika kawo jiya yana da kyau dan jiya gabad'aya babanki bai kwana da zazzabi ba kinga jikinsa ma gumi yake alamu na nuna lafiya ta samu." Nace"To Alhamdulilahi idan na koma sashen zanyi masa bayanin yanayin jikin nasa." Tace"Hakan yana da kyau ki 'karayi masa godiya." Nace "Insha Allah."
A gurguje na kammala karin kummalo na dauki jakar litattafaina sallama nayi mata na nufi gurin karatu.

'Karfe d'aya da rabi mun fito daga karatu hira muke da Lahira ina tunanin fada mata abinda ya faru, Lantana ta k'araso gurin. "Sumayya kije b'angaran Mamma Fulani tana son ganinki."
Gabana ya fadi ido na tsirawa Lantana ina so nayi magana amma bakina yayi nauyi ina kallo Lanatana ta bar gurin na garara cewa komai..........."Lahira dan Allah zoki rakani." A sanyaye nayi mata maganar. Tace"Muje Allah dai yasa ba laifi kikayi ba." Nace" Bana tsammanin hakan." Tafiya muke ni da ita kowa na sa'ke sa'ke a ransa. Lahira guri ta samu ta zauna a harabar gurin ni kuma na nufi kofar shiga falon masu gadin kofar ne suka bude min na shiga a nutse sallama nayi cikin nutsuwa na 'karasa inda suke zaune ita da yaron nata.
Gwiwa a kasa kaina a sunkuye nace"Ranki ya dade barkanku da wannan lokaci." Amsa min tayi a nutse tana gyara zamanta shi kuwa ko kallona baiye ba kanshi yana dukufe yana kallon kasan kafet kamar yanda ya saba.

"Sumayya." Sunana data kira yasa na dawo cikin hankalina. a nutse na amsa "Na'am ranki ya dad'e. " Inaso ki nutsu da kyau zamuyi magana dake." Ciki da tsantsar ladabi Nace"To ranki ya dade ina sauraranki."

"Sumayya kiji tsoron Allah kiji tsoron mahallicin ki ki fad'a min gaskiyar lamari shin waye ya saki zubawa Magajin sarki guba a cikin abinci? inaso ki fad'a min gaskiya akan al'amarin nan daya faru babu abinda za'ayi miki idan kin fad'i wanda yasa ki aikata wannan mugun aikin gaskiyar magana nake jira ta fito daga bakin ki.

Zuciyata ce ta karye hawaye na kokarin zubo min ina kokarin mayar dashi sai da ya zuba a raunane nace" Ranki ya dade wallahi tallahi Allah d'aya ne daga shi babu wani, babu wanda ya sani na zubawa Yarima guba a farfesu wallahi ban san yanda al'amarin nan ya faru ba." ina kuka na kare maganar.

Shuru falon yay na minti biyu kafin tace"Yi shuru ki daina kuka nayi miki wata tambaya." Hannu nasa na goge hawaye nace"Ranki ya dade ina sauraranki." tace"Bayan kin kammala aikin ki babu wanda ya shigo gurin."? Shuru nayi ina tunanin maganar.......
*BINTA UMAR ABBALE*

*Kuyi sharing👏🏻*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *[email protected]*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_

*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
27&28
"Anya Shatima da Moddibo zasu iya cutar da d'an uwansu? tunanin da nakeyi kenan a cikin zuciyata. ni dai nasan babu wani 'bako daya shigo sashen bayansu sai ni dasu Haruna bana tsammanin Abokanshi kuma shaqiqan 'yan uwansa zasu iya sa masa abunda zai kashe shi a cikin abinci. shuru nayi kaina a kasa ina tararrabin fad'ar maganar dake bakina.
"Sumayya ke nake saurare." Muryarta ce ta doki dodon kunnena.

A nutse nace"Ranki ya dade babu wani bako daya shigo sashen sai 'yan uwanshi wato Shatima da Maddibo sune suka shigo bayan na jera abincin a daning na hau sama domin in sheda masa lokacin dana sakko na samesu su biyu a falon." na karasa maganar ina sake sunkuyar da kaina......Fulani na shirin magana ya katseta da fad'in "Me kike nufi da wannan maganar kina nufin Maddibo ko Shatima wani na iya samin guba a abinci."? Shuru nayi gabana na fad'uwa sabida yanayin yanda yay maganar ya nuna min 'bacin ransa."

"Sumayya." naji ta kira sunana, amsawa nayi ina kallonta, tace"Tun ganina dake na farko naji kin kwanta min a raina sosai na yaba da nutsuwarki da hankalinki ina mutukar son mutum mai gaskiya da rikon Amana, inaso ki ri'ke amanar dana dam'ka miki hannu biyu kisa idonki sosai akan masu shige da fice a sashen babana, tunda ka kan 'yan uwanshi maza da mata da kuma sauran bayin dake cikin gidan nan inaso kisa idonki sosai akan shige da ficen su a sashen sannan ki dinga lura da abincinsa gami da abin shansa ruwa ko lemo ko makamancin haka Ina neman wannan alfarmar a gurin."

Cikin sanyin jiki nace"Insha Allahu zan kula da amanar da kika bani nayi al'kawarin bin umarninki." Murmushi tayi a nutse tace"Tashi kije Allah yayi miki albarka." na amsa da ameen ina jin sanyi a cikin raina. yun'kurawa nayi a nutse nace"A tashi lafiya ranki ya dade." Hannu ta daga min alamun naje da sauri na bar gurin zuciyata tas tabbas addua bata faduwa 'kasa banza.

A nutse ta kalleshi gami da fadin"Babana me ka fahimta a maganar yarinyar nan? ni ina ganin wannan al'amarin daya faru da akwai saka hannun 'yan uwanka ina nufin Shatima da Moddibo."

Kallonta yayi mamaki tattare a fuskarsa, tace"Ko shakka bana yi akwai saka hannunsa a ciki amma inaso kasa ido sosai a kansu sannan ka kula da kanka ba komai xaka ci a gabansu ba akwai mummunar manufa a zuciyarsu."

"Mamma bana tsammanin Shatima ko Moddibo wani zai iya cutar dani a cikinsu ni nafi tunanin wani abu yarinyar nan tayi amfani dashi gurin girkin wanda ya janyo hakan bana zargin kowa akan faruwar wannan al'amari.

Murmushi me ciwo tayi tace" Nima bana zargin kowa amma dai tunda nace maka kayi takatsantsan dasu to kayi domin hausawa na cewa makashinka na gindin ka nasan baka manta irin zaman marinar da akeyi a cikin gidan nan ba, kowa ka ganshi ka kalle shi kawai mafi akasarinsu babu kyakkyawar manufa acikin zuciyarsu."
Shuru yayi yana nazarin maganar mahaifiyar tasa.
Chapter 13 · 0% Book details