Sashe 60
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hannu yasa ya dago fuskata ya tsira min ido lokaci guda ya karancin yanayin da take ciki.....cikin tausasawa yace." Me akayi miku kike kuka?
Kallonsa nayi ina kokarin bagarar da maganarsa nace"Wane irin kuka kuma yanayin bacci ne kawai a idona."
"Kada ki raina min hankali mana na shigo na sameki kina goge hawaye amma ki karyata maganata bana so kiyi zaman takura idan nan beyi miki ba zaki iya komawa sashena ki zauna mutukar hankalin ki zai kwanta."
Cike da mamaki nake kallonsa kafin nace"Na koma sashen ka na zauna akan wane dalili? wai kan dan Allah me yasa watarana baka tunani ne."?
'Bata rai yayi yace."Ni ne mara tunani."? girgiza kaina nayi nace"Allah ya baka hakuri ban fad'a maka maganar dan kaji haushi ba abinda ya dace nake so na nusasheka yanzu kawai ba'a daura mana aure ba sai na tare a sashenka me kake tunanin zai faru."?
Shuru yayi yana kallona, na dauke kaina tare da matsawa daga jikinsa, sake matsowa yayi ya matseni a jikin kujera, murya na rawa nace"Dan darajar Allah kayi hakuri ka matsa kada Mamma ta fito ta same mu a haka."
Ya matsa tare da fadin"Tunda kince Allah na matsa shikkenan ko .''? shuru nayi masa, yace."Kinci abincin dai."? kai na girgiza alamun aa. Yace."To tashi muje muci ko."
Mikewa nayi ya mike tare da kokarin rike kuguna da sauri na kauce na bashi guri, mirmushi yayi kawai yayi gaba nabi bayansa ina mamakin shu'umancinsa.
Muna zama gurin cin abincin ta fito daga dakinta jikinta nannad'e da lifaya da carbi madaidaici a hannunta, gani nayi ta saki fuskarta cikin wasa da dariya tace"Ango da amarya ne za suci abinci a tare." da sauri na sunkuyar da kaina kunya duk ta dabaibayeni.......tana kokarin zama gurin zamanta yace."Mamma na shigo na sameta ita kadai a zaune a falo tana share hawaye shine nake tambayarta dalili tace babu komai ni kuma na k'aryata tabbas nasan akwai abinda ke damunta take kuka.
Cikin kulawa tace"Sumayya menene."? kasa cewa komai nayi gabadaya kunyarta nake ji, tace"Ki gama cin abincin kizo ki sheda min abinda ke damunki ni ba surukar ki bace mahaifiyarki ce." Nace"Mamma babu komai wallahi kin san na yini ina bacci shine dalilin da yasa fuskata ta sauya.
Da sauri yace."Karya kike yi." shuru nayi tare da sunkuyar da kaina dan gabadaya bana san jayayya dashi.
Tace."Ki gama cin abincin Jakadiya ta rakaki gurun iyayenki ku gaisa." wani irin sanyi ne naji ya ratsa zuciyata, yace."Mamma ni zan rakata." Tace"To hakan ma yafi ma'ana sai ku gaisa sosai ka k'ara sheda musu abinda keda akwai duk da nasan maimartaba ya shedawa mahaifinta abinda yake faruwa a tsakaninku."
Yace."Babu damuwa insha Allahu zanyi musu bayani sosai wanda zai gamsar dasu nasan kuma zasuyi farin cikin da faruwar al'amarin."
Cikin farin ciki nake cin abincin na saki jikina sosai muna hira dashi, Mamma dake can falo tana jinmu idan ya kama tasa baki a hirar tamu tasa bakinta ayi da ita, cikin fahintar juna muka kammala cin abincin yace."To maza dauko maganinki a daki." da sauri na mike naje na dauko maganin, kar'ba yayi ya fito dasu ya dinga bani daya bayan daya, sai da ya tabbatar nasha kowanne sannan ya umarce ni dana mayar da ledar maganin daki, ina ajiyewa na fito na sameshi a tsaye suna magana da mahaifiyarsa magana ce dai akan abinda ya faru yana fada mata cewa Muddibon ya fadi gaskiyar lamari yayi rocoding din komai so yake Maimartaba ya shigo da daddare sai ya kunna musu su saurara."
Kaina a kasa nazo na wuce bakin kofa na nufa, ya biyo bayana, Mamma naji na fadin"Sumayya ki gaishe min da iyayen naki."
Da sauri na juyo cikin ladabi nace"Insha Allahu zasuji." Nice na fara fita kafinsa, gabad'aya naga ana bani girma yanda ake gaisheshi cikin mutunci da daraja nima hake ake gaisheni, na dinga takure jikina cikin hijabi ina mamakin ikon Allah!
Har muka isa gurinmu a takure nake saboda ganin yanda jamaa ke bin mu da kallo gami da girmamani!
Hayaniyar mata na dinga ji a cikin gidan namu. kallonsa nayi shima ya kalleni, nace"Ko zaka tsaya na shiga na sheda masu zuwanka."? yace."Duk yanda kika ce haka za'ayi ranki ya dade.''
Cike da mamaki nake kallonsa jin irin sunan daya kira ni dashi.
Yace."Meye kike kallona."? girgiza kaina nayi da mirmushi a fuskata na wuce cikin gidan, Tawagar mata na gani gurfane gaban Tambaya sai fadanci suke mata saboda abun al'karin daya sameta.....ina shiga Uwani ta mi'ke da sauri ta rangwad'a bud'a! da fad'in "Ga amaryar nan ma tazo." Gabad'ayansu suka mike tsaye Tambaya sai mirmushi take tana kallona! nima da murmushin a fuskata na shiga gaisawa dasu, suka dinga amsawa suna yi min fatan alkairi." Nace"Ku nutsu tare muke da Yarima yana waje a tsaye hayaniyar ku tasa ya tsaya." Gabad'ayansu suka shiga nutsuwarsu kowacce tasa takalminta domin tafiya.....Tambaya tace"Sumayya maza jeki shigo dashi, kin barshi a tsaye." nace"To." Tawagar matan dake gidan suka biyo bayana, ganinsa a tsaye yasa suka zube kowacce gwiwa a kasa take gaisheshi, na dinga mamakin yanda yake amsa musu a sake yace."Gabad'ayansu su tashi su tafi. da sauri suka mike suka wuce, sai da gurin ya samu nutsuwa tukkuna na kalleshi a sanyaye nace"Ka shigo amma Babana baya nan sai Tambaya kad'ai zanje na kira shi yanzu."
Girgiza kansa yayi yace."Ki bari kawai idan na gaisa da mamanki sai munje can gurin aikin baban mu gaisa." nace"Ka bari dai na kira maka shi." Dan 'bata fuska yayi yace."Haka zaki tafi babu sucurity kina so makiya su ritsa ki ko."?
'Babu abinda zai same ni sai ikon Allah." girgiza kansa yayi yace."Ban yarda ba tare zamuje kome zai faru ya same mu a tare.'' wani irin kallo nake masa shima yana yi min nasa da yake mutukar kassara ni. a sanyaye nace"To muje ku gaisa da Tambayan." da hannu ya nuna min hanya ma'ana nayi gaba, bayana ya biyo muka shiga.
Sosai nayi mamakin yanda ya zube gaban mahaifiyata yana gaisheta ita kanta Tambaya sai da abun ya bata mamaki ta dinga jin kunya da nauyi tana kauda kanta da barin kallonsa, addua kawai take mana tare da fatan alkairi a rayuwar auran da zamuyi, ya dinga amsawa cikin kulawa yana sake yi mata karin bayani akan al'amarin, ni dai shuru kawai nayi ina kallonsa ina mamakin sauyawarsa a kaina, lokaci guda na dinga jin wani irin masifaffan sonsa na ratsa ni yanda yake mutunta iyayena yafi komai dadi a gurina.
Lawi yana tsaka da hidima da dawakai muka shiga gurin, da sauri ya cire hular malafar dake kansa sabida girmamawa, yana kokarin zubewa a kasa kawai yaga Yariman ya zube masa, jiki a sanye yace."Ranka ya dade tashi dan Allah bancanci wannan gaisuwar ba."
Mirmushi yayi ya kalleshi da kulawa yace."Ka cancanci irinta tunda har ka haifa min matar rufin asiri." Lawi yaji hawaye na nema ya kufce masa! hannuwansa ya had'e guri guda yace "Godiya nake ranka ya dade."
Cikin kulawa yace."Baba babu kalmar godiya a tsakanina daku dan haka ku daina akan Sumayya babu irin abinda ba zanyi ba, wannan yarinya jigoce a rayuwata nagode kwarai da irin tarbiyar da kuka bata"
Lawi cikin farin ciki da alfahari ya d'ora hannunsa a saman kaina "Ubangiji Allah yayi miki albarka yarinyar arziki hakika haihuwarki babbar nasara ce a tare damu." hannuna na dora a kan nasa nace"Baba nima ina alfahari daku da kasantuwar ku a matsayin iyayena ko wane mataki na kai rayuwata kune sanadi kun kula dani kun tarbiyantar dani kun d'ora ni akan tur'ba mai kyau kun d'ora ni a kan hanya madaidaiciya babu abinda yake tsakanina daku a yanzu sai kyakkyawar addua ina rokon Allah yaja da ranku ya kuma kara muku lafiya mai amfani."
Ya amsa da ameeen suma ameeen Yarinyar arziki Allah yasa albarka a rayuwarki da rayuwar auranki." ya kalli Yarima dake tsaye yana kallonmu yace."Ranka ya dade naji dadi kuma nayi alfahari dacewar zaka auri jinina a gaskiya nayi farin ciki kuma nayi addua sosai ina rokon ubangiji Allah ya sanya muku alkairi a zamantakewar auranku Allah ya kade fitina yasa anyi kenan ya kareku ga dukkanin sharrin abin'ki."
Yarima cikin jin dadi ya dinga amsawa da ameeen ya Allah baba muna godiya sosai da sosai............Zuciyata tayi wasai! na dinga jin nutsuwa na ratsa jikina hakika yanzu na amince da cewa Yarima na sona tsakani da Allah yanda yake karrama iyayena yake mutuntasu yasa naji duk duniya bani da masoyi kamarsa ina mutukar kaunar iyayena shiyasa duk wanda ke mutuntasu nake ganin darajarsa Yanzu Yarima Ali ya samu kyakkyawan matsayi a cikin zuciyata Allah ne kad'ai yasan irin kaunar da nake masa.