← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 90

Sashe 16

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri na miqa masa silbar abincin ina murmushi, bisimillah yay yasa hannunsa ya d'ibi dafadukan shinkafar dake cikin silbar a bakinsa yasa yana taunawa yace."To gashinan nasa albarka."

Silbar na janye na gyara zamana ina murmushi nace"Godiya nake baba Allah ya kara maka lafiya." ya amsa da amin yana kallona da murmushi a fuskarsa.

D'akin ne yay shuru na minti biyu kafin na kalleshi a nutse nace"Yanzu idan na kammala cin abincin zamuje can sashen Yariman ko."? Yace"Af kinga na manta wallahi gwara da kika tuna min maza gama cin abincin muje."
"To nace" na mayar da hankalina gurin cin abincin...Tsaf na kammala na fita da kwanon ina shiga dakin na tarar dashi a tsaye kuryar dakin na leqa Tambaya na kan dadduma da carbi a hannunta nace"Zamuje sashen Yarima da Baba." Hannu ta daga min alamun sai mun dawo." Koda na juyo sai na tarar har ya rigani fita murmushi nayi nabi bayansa da sauri.

Lokacin da muka isa sashen shuru dan su Haruna ma a harabar gurin muka samesu nan yake sheda min ai Yalla'bai din ne yace su fita su bashi guri zuwa anjima sa dawo." hakan ya nuna mun cewa har yanzu yana cikin 'bacin ran abinda ya faru tsakani na dashi.....Babana na kalla a tsanake nace"Baba zauna bari na hau sama na sheda masa zuwanka.

Ya samu kujera ya zauna a nutse ni kuma na nufin saman domin sheda masa zuwansa.....Na jima ina nocking kafin naji yace."Waye."? A sanyaye nace."Nice." shuru na minti biyar naji alamun bud'e k'ofar matsawa gefe nayi kaina a kasa......Wani irin kallon banza ya watsa min da fad'in "Lafiya."? Kai a kasa nace" Babana nayiwa jagora zuwa gurinka yana so ku gaisa kana yay maka godiya kan alkairin da kayi masa sosai yaji dadin magungunan daka bashi yanzu haka yana 'kasa jiranka.''

Shuru bece komai ba na d'ago kaina a sace na kalleshi sai naga yana kallon 'kasan gurin, ajiyar zuciya na sauke cikin raina nace"Abin yazo kenan kallon k'asa kamar makaho." Mun kai minti biyar nida shi a tsaye a kafin naji yace." Ni Bana abun alkairi domin a gode min, ba ni na bawa babanki Lafiya ba Allah ne dan haka shi zaiyi wa godiya ba niba." Yana k'are maganarsa ya bugo min kof'a.

Na jima a tsaye a gurin ina kallon kofar kafin na sauke ajiyar zuciya a sanyaye na sau'ko 'kasa na sameshi a zaune a inda yake.

Cikin taushin murya na sheda masa abinda yace....bai nuna komai ba yace."To babu komai Sumayya dama mafi akasari masu taimako basa so a damesu da godiya tabbas hakane Allah ne ya bani lafiya amma kuma shine ya zama sanadi dan haka zan cigaba dayi masa addua har karshen rayuwata."
A sanyaye nace"Hakane baba Allah ne abin godiya a garemu addua kuma ba zamu daina yi masa ba tunda shi ya zama sanadi.'' To Har muka isa gurin mu muna tattauna maganar a tsakanin mu...........
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *[email protected]*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_

*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
33&34
Kwana biyu kyara da hantara ne a Tsakanina dashi komai nayi masa ba nayi masa gwaninta, magana kuwa sai nayi sau biyar bai bani amsa d'aya ba, haka dai na cigaba da hakuri da halinsa ina kokarin ganin na sauke nauyinsa dake kaina, a tsakanin kwanaki biyu zuwa hud'u duk abinda zan girka masa naci ko sha baya ko kallon daning din ballanatana ya zauna yaci, yanda na ajiye haka zan zo na dauke, ganin kamar 'barnar tayi yawa yasa na yanke shawarar samun sa muyi magana idan baya bukata sai na daina wahalar da kaina da asarar abinci........ samun sa nayi gurin da yake hutawa na tsuguna gwiwa a 'kasa kamar koda yaushe nace" Ranka ya dade Barka da yamma." Kamar da dutse nake magana, kallonsa nayi ina jin wani kunci a cikin zuciyata, a gaskiya na fara gajiya da wannan wulakancin, hankalinsa na kan wayarsa yana latse latse a kai......'bacin ran dake taso min na danne Nace"Dama inaso muyi magana da kai ta fahimta ne." Ta 'kasan ido naga yayi min wani kallo, na cigaba da cewa"Naga kamar baka 'bukatar abincin da nake hidimar girka maka safe da rana da dare me zai hana a daina a sarar abinci idan baka bukata sai na bari akan a dinga zubarwa."

Zamansa ya gyara yayi wani irin zama irin nasu na saurata hannunsa dake d'auke da zobunan azurfa ya d'ora saman gwiwarsa ya tsira min idanunsa.
Kasa kallonsa nayi a yanayin dan ganin yanda ya 'kara wani kwarjini da cika ido gashi zaman da yayi yay masa kyau ha'kika ya dace a kirashi da *Sarki!* ba Yarima ba dan komai nashi cikin mulki da muskilanci yake yi.

"Kece kika ajiye abincin gidan da kike wannan maganar."? Maganarsa ta bani mamaki sosai nace" A'a bani bace ba, ni a nufina 'barnar abincin da ake tayi yawa sabida na safe haka yake tarar dana rana sannan na dare ya tarar dana rana, wani zubin lalacewa yake sai dai na bawa dabbobi ko na zubar."

"Ki cigaba da aikin ki bana bukatar ki huta." Yafad'a tare da tsira mun ido gami da san ya tabbatar min da maganarsa, "Inaso ka fad'a min dalilin ka na yanke wannan hukuncin ya za'ayi kai ba cin abinci kake ba amma kasa a girka a zubar wannan ai izgilanci ne." Gaura min mari yay yana huci yace."Koda yaushe kina yawan fad'ar wannan maganar akai na sabida kin raina ni ko."? yana nuna ni da hannunsa yake maganar, d'auke kaina nayi daka fuskarsa nayi kasa dashi hannuna dafe da kuncina....."Wallahi duk sanda na sake jin kin jefe ni da kalmar izgilanci sai na baki mamaki na lura dake kwata-kwata bakya shakka fad'a min kowace kalma kodan kinga na nuna ina sha'awarki ne kike tunanin wani abu.'"

D'agowa nayi raina a 'bace Nace"Allah ya baka hakuri idan furucina ya 'bata maka rai ni inaso na tunasar da kai abinda ka sani ka manta ko kuma nace kake takewa saboda giyar mulki ranka ya dad'e kai mutum ne mai girman kai gami da Izigilanci a kan komai alhalin kai d'in ba komai bane a gurin Allah inaso na tunasar da kai cewa wannan d'abi'un da kake yi zasu nesan taka da rahamar Allah." Hawayen da nake maqalewa ne suka zubo.

"Tashi ki bani guri."! Kalmar da ya fad'a kenan cikin 'bacin rai! Mikewa nayi na sunkuya cikin tausasawa nace" A gafarce ni idan maganar da nayi ta 'bata maka rai." Ba tare da yace min komai ba ya sunkuyar da Kansa k'asa.
Gurin na bari da sauri na nufi sashen Mahaifiyarsa wato Fulani zuwa zanyi na sheda mata dukkanin abinda ke faruwa, domin kamar ita ta dauke ni aiki ta bani amana yana da kyau duk abinda ke faruwa tasa ni saboda kada wani mummunan abu makamancin wanda ya faru a baya ya faru a tuhume ni da wani abu, a tsakanin kwanaki biyar din da suka gabata bani da masaniyyar inda yake cin abinci na safe rana da dare idan ma a gurinta yake ci to yana da kyau na sani ko hankalina ya kwanta.

Ina gurfane a gabanta na sheda mata dukkanin abinda ke faruwa......a da tana kishingid'e a lokacin da nake maganar sai naga tayi saurin mi'kewa zaune gabad'aya ta mayar da hankalinta kaina tace"Sumayya kika ce yau kwana biyar babana baya cin abincin da kika girka."? Nace"K'warai kuwa ranki ya d'ade ganin kwanakin suna yawa ne yasa na yanke shawarar zuwa na sheda miki."

"A'ina babana yake cin abinci."? Tafad'a tana kallona, Nace" Ranki ya d'ad'e nima wallahi ban sani ba." Ajiyar zuciya ta sauke da sauri tace"Miko min wayata gata nan." Da sauri na dauka na mika mata.
Number shi ta kira inaji yana gaisheta bata amsa ba tace"Maza kazo sashena ina nemanka."
Kashe wayar tayi ta kalleni da fad'in "Sumayya kije ki cigaba da aikin ki kada ki fasa yi masa abinci a duk sanda kika kammala kika sheda masa idan bai ci ba kizo ki sheda min."

Nace"To insha Allah ranki ya dade zanbi umarninki."Tace."Tashi kije Allah yayi miki albarka." Cikin farin ciki na amsa da "ameen Ranki ya dade ina godiya."

Raina fari tas na bar sashen gurinmu na nufa domin nayi shirye shiryen shiga gurun karatu......Tsaf na fito cikin hijabi fari tas da jakar littafai a hannuna Babana na kwance a katifa bacci naso ya daukeshi nace"Baba kayi bacci ne."? Mi'kewa zaune yay yace." Yana dai so ya dauke ni dama ke nake jira ki shirya mu fita tare yau inaso na shiga gurin Dawakai na dubasu.''

Nace"Baba ka zauna ka sake samun 'kwari jikin ka dawakai na nan kalau babu abinda ya samesu." Yace."Sumayya zaman nan ya isheni wace lafiya kuma akeso na samu bayan wannan inaso na koma bakin aiki."Nace"To shikkenan baba nida naso ka k'ara watsakewa sosai kafin nan."

Mi'kewa yay yana dariya yace."Sumayya zaman gida sai mata idan kinga namiji ya zauna a gida to dole ce kamar dai ni da rashin lafiya ya hanani gudanar da harkokina." Murmushi nayi nace "Hakane baba, to tunda Tambaya na gurin aikinsu sai mu sawa kofar 'kwad'o." Yace."Eh hakane yi maza ki d'auko kwad'on insha Allahu kafin ta dawo nima na dawo."

'Kwadon (key) na dauko muka fito tare muna hira na kulle gidan na bashi key din yasa a aljihun rigar jikinsa, muka fara tafiya.......Daf da zamu rabu kowa yay inda ya nufa Lantana ta tari gabanmu, a duk sanda zanga Lantana sai gabana ya fad'i saboda duk sa'kon da zata fad'a bana alkairi bane.

"Sumayya kije can 'bangaran Maigirma Ciroma Gimbiya Lawisa ke san ganinki." Na kalleta da fad'in "Lantana kin dai ga shirin da nayi ko zan shiga gurin karatu ne sai dai idan na fito."
Chapter 16 · 0% Book details