← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 90

Sashe 48

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta jima kanta a kasa tana kaiwa Allah kukanta kafin ta d'ago kanta tana zubar da hawaye ta daga hannuwanta sama ta dinga addua tana 'kas'kantar da kanta a gurin mahallicinta, Mamma Fulani ta dade hannunta a sama tana neman sasaauci gurin Ubangiji kafin ta shafa a fuskarta a nutse ta juyo tana kallon mijin nata dake zaune akan kujera, tace"Ranka ya dad'e Har yanzu bai dawo ba kenan."? Maimartaba ya sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya yace."Bai shigo ba har yanzu gabad'ayan mu mun gaji da zaman fada kowa ya shige gurinsa.'' Kanta ta d'aga ta kalli agogon dake kafe a falon tara na dare, a sanyaye tace."Inasha Allahu, Allah zai dawo mana dashi lafiya." Maimartaba ya amsa da ameeen tare da mikewa tsaye! sallama yayi mata ya nufi gurin Uwargida Huwaila.......Tana zaune a bakin gado kunnanta makale da waya sai 'ba'bbaka dariya takeyi da alama tana cikin nishad'i, Tace."Ai al'amura gabad'aya sun dagule wannan karon mun samu nasara akansa dan har yanzu yana hannun 'yan sanda kuma gwamnati ta shigo cikin al'amarin asibitin da yake tutiya dashi gwamnati ta rufe shi, wannan dalilin yasa duk na kira wayarku na sheda muku cewa yau kuyi bacci harda munshari dan bukatarmu daf take da ta biya." Daga daya b'angaran aunty Safiyya ta dinga k'yakyata dariyar farin ciki tace"A gaskiya naji dadin wannan abu Wai!! ya muka ga idon mutsiyaci a cell a gwara yasha duka dan ya bamu wuya." Uwar gida tace"Ai be zama lallai su doke shi ba yanzu abinda nake so daku shine gobe da sassafe ku shigo cikin nuna alhini da damuwarku bana so ko kad'an a gane akwai sa hannunmu a cikin al'amarin." Aunt Safiyya tace."Kada ki damu Mama zamu shigo da wuri kuma ba zamu nuna farin cikin mu ba zamu nuna tsantsar damuwar mu dangane da faruwar al'amarin." Uwar gida tace"To shikkenan sai kun......shigowar Maimartaba dakin yasa ta kasa karasa maganar kashe wayar tayi ta ajiye kusa da ita tana masa barka da shigowa.

Guri ya samu ya zauna a nutse yace."Dawa kike waya da daddare haka."? Tace."Wallahi Safiyya ce ta kira ni yanzu take sheda min cewa na nema mata alfarma a gurinka wai tana so ta 'kara jari akan wanda take juyawa gashi tana jin kunyar Tambayarka kudi."

Murmushi yayi yace."Da alama basu san abinda yake faruwa ba a masarauta ba." Da sauri tace."Me yake faruwa ranka ya dad'e."? yanda ta nuna damuwarta sai ka rantse da Allah bata san komai ba.

Maimartaba cikin nutsuwa ya sheda mata dukkanin abinda yake faruwa, fashewa tayi da kuka ta ri'ke kanta tana fad'in "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'una! wannan yaro yana ganin tashin hankali wai shin me Aliyu yayi wa mutane ne suke nema suga bayansa."

Maimartaba tace."Wallahi ni kaina na rasa abinda yasa mutane suke nuna masa 'kiyayya al'amarin yana bani mamaki mutuka! ada ina zargin daga waje al'amarin ya fito sai da na zauna nayi tunani sosai na gane cewa a kwai saka hannun wasu daga cikin masaurata.".

Tana kuka da fyatar majina tace"Allah ya taimake ka shin kai wa kake zargi da aikata wannan aikin dukkaninku cibiyarku d'aya ashe akwai wanda zai iya neman ran d'an uwansa."

Maimartaba yayi murmushi mai ciwo yace."Hulaiwa baki san mulki ba har yanzu mutane na iya aikata komai akan mulki na lura da tun sanda na fara kiransa da Magajin sarki fuskokin wasu daga cikin makusanta na ya nuna b'acin rai ni ban kira Aliyu da Magajina ba wai dan ya gaji kujerata Ali sunan surikina ne wato mahaifin Fulani ke kin sani itama ta sani wannan dalilin yasa nake kiransa da wannan suna na Magajin sarki."!

Uwar gida girgiza kanta ta shagayi kafin ta sauke ajiyar zuciya tace"Babu shakka mutum daya ne zai iya aikata wannan rashin imanin ba kowa bane sai Waziri shine makusancin ka wanda kafi aminta dashi shine kuma zai cutar da kai da zuriar ka Waziri bai ta'ba haihuwa ba tsayin shekarunsa wannan dalilin zai sa ya aikata mugun abu akan 'ya'yan 'yan uwansa sabida yana ba'kin cikin shi Allah be bashi haihuwa ba......

Cikin wani irin yanayi Maimartaba yake kallonta yana mamakin maganarta akan d'an uwansa mafi kusanci dashi wato Waziri." Ganin ya nuna alamun alhini yasa tace"Nasan dole za kayi mamakin maganata ranka ya dade kada kayi mamaki halin dan adam wallahi ko shakka ba nayi Waziri zai iya kashe Yarima saboda wannan dalilin dana fad'a maka.".

Maimartaba girgiza kansa yayi cikin yanayi na damuwa yace."Huwaila kada ki sake wannan maganar zargi bashi da kyau Waziri yana da kyawun zuciya na yarda ba zai cutar dani da zuria ta ba idan da wa'inda ya kamata a d'ora zargi a kansu to Ciroma da Galadima ne domin sune suka fito da hassadar su a kaina kada fa ki manta gwagwarmayar da nasha dasu a lokacin da Allah ya bani mulki nasha wahalarsu kafin su rabu dani nayi mulki cikin nutsuwa, Waziri kuwa tunda muke dashi bai ta'ba nuna min hassadar sa ba yana kaunata yana kuma kaunar zuria ta wannan al'amarin da ya faru yafi kowa damuwa bana zargin akwai saka hannun Waziri dangane da faruwar al'marin."

Huwaila shuru tayi bata sake tofawa ba, ta dauka mijin nata zai dauki maganarta babban burinta ta raba zumuncin dake tsakaninsa da dan uwansa Waziri saboda ta fahimci cewa Wazirin kamar shi yake hana Maimartaba ya kula da 'ya'yansa tunda ta lura da irin kaunar da yake wa Magajin sarki gabadaya taji ta tsane shi dan ita duk wanda zai kaunaci Fulani da d'anta to bata kaunarsa.

Magajin Sarki tare da Acp Mahmud a station, cikin nutsuwa suka gaisa da juna Acp yace.''Ranka ya dade ya kuma ji da faruwar wannan al'amari."? Ajiyar zuciya ya sauke yace.'' Sai godiyar Allah.'' Acp yace."Ranka ya dad'e wannan al'amari daya faru yayi mutukar girgiza mu mun shiga alhini da damuwa dangane da faruwar al'amarin dalili kuwa shine wannan asibitin naka asibiti ne mai mutukar muhimmanci a gurin al'ummar dake cikin wannan jaha mai albarka duka-duka asibitin bai kai rabin shekara da kafuwa ba amma ya kawo mana cigaban da bamu ta'ba tsammani ba, sai dai mace-macen da ake samu a asibitin yasa dukkaninmu jikin mu yayi sanyi dayawa daga cikin mutanan dake kwad'ayin zuwa asibitin domin a duba lafiyarsu tabbas nasan zasu tsorata su janye jikinsu domin tsira da ransu, ranka ya dad'e muna so kayi mana cikakken bayani akan dalilin daya sa ake samun wannan matsala a cikin asibitin ka." Acp ya 'kare maganarsa yana kallonsa.

Dago kanshi yayi da niyyar magana, dan jaridar dake tsaye ya matsa kusa dashi yana gyara masa abin magana, shi kuma Acp ya gyara biron hannunsa....Yana fara maganar ya fara rubutawa a jikin takardar dake gabanshi............A nuste yace."Acp Mahmud wannan al'amarin da yake ta faruwa sai nace maka family issue ina nufin abinda ya shafi cikin gidanmu . wannan al'amarin tunda na diro duniya yake faruwa dani bazan 'boye maka ba kuma bazan 'boyewa media ba al'amarin nan daga cikin gidanmu na sarauta yake fitowa, Acp a rayuwa ta banta'ba nufin wani da sharri ba amma ni kullum cikin 'kokarin so a ga bayana ake abin na damuna mutuka gaya."

Acp ya girgiza kanshi a nutse yace."Ranka ya dad'e Allah ya kare ka daga sharrin abinqi.'' Ya amsa da ameen yana goge gumin dake goshinsa.....Acp yay rubutu jikin takardar ya d'ago a nutse yace."Ranka ya dad'e afuwa shin ya akayi kasan abincin ka na dauke da guba mai karfi ka bawa hadimanka suka ci muna so muji yanda akayi haka ta faru."

Murmushi yayi ya girgiza kansa yace."Acp kasan Allah ban san abincin nan na dauke da mugun abu ba, yanda al'amarin ya faru shine........Na sauko cikin shiri domin zuwa gurin aiki na samu Amintacciyar hadimata tana aikace-aikace muka gaisa da juna nan take sheda min cewa ta kammala breakfast lokacin na duba time naga idan na tsaya break zan 'bata lokaci dalili kuwa shine akwai marasa lafiyan da zan duba sai nace ta bari kawai bana bukata, ta biyo ni da magana akan na daure naci abinci saboda yanayin aikina....still na sake duba agogon hannuna na kalleta naga ta nuna yanayi na damuwa, nace ba zan tsaya ba amma ta had'a abincin ta bayar a kawo min ofis. da wannan na fita na barta a sashen nawa. ina zuwa ofis na samu coffee nasha na cigaba da gudanar da aikina misalin sha biyu shaura na rana sai ga Hadimi na Haruna marigayi ya shigo ofis d'ina da kayan abinci a hannunsa, muka gaisa yake sheda min abunda yake tafe dashi, time na duba naga idan naci abinci a lokacin zan samu matsala kai tsaye nace ya koma dashi bana bukata idan kuma yana so to ya samu wani ya taya shi ci." daga wannan magana sai na sallameshi na cigaba da aikina. to daf da zan tashi d'aya daga cikin masu kula da hospital din yaga gawarwarkin wad'annan bayin Allah a can gurin shukoki a guje yazo yana sheda mana abinda ke faruwa, Acp wannan shine cikakken bayanin da zan iya yi maka dangane da faruwar wannan al'amari.

Acp Mahmud girigza kanshi yay yayi rubuce rubuce a jikin takardar kafin ya d'ago kansa yana kallonsa Yace.'' Ranka ya d'ade tilas mu aika yanzu yanzu azo da wannan yarinyar domin alamu na nuna mana cewa akwai sa hannunta a cikin faruwar wannan al'amari."
Kallonsa yayi yana girgiza kansa yace."Acp ba wai zanyi maka katsalandan a cikin aikin ba amma kasan Allah yarinyar nan ta gari ce, ni zan bada shaida a kanta ba zata ta'ba yarda a had'a baki da ita a kashe ni ba, ni nasan ta ciki da waje nasan wacece ita Sumayya ba zata iya kashe kishayi ba ballanatana mutum mai rai."

Acp yayi murmushi yana kallonsa a nutse yace."Ranka ya dade kai da kanka kace itace ta girka abincin nan to amma me yasa kake 'kokarin kare ta."? Girgiza kansa yayi yay shuru yana kallon kasan gurun....Acp yace."Kayi hakuri ba zamu yi mata komai ba kawai zamu tsoratar da ita ta fad'a mana gaskiyar lamari."
Chapter 48 · 0% Book details