← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 90

Sashe 82

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki cokalin ya cigaba da cin abincin, lemo na tsiyaya masa a cup na mika masa ya kar'ba ya kur'ba ajiye cup din yayi ya cigaba da cin abincin nace"Amma ba zan 'boye maka cewar naji ciwon abinda kayi ba.

Kallona yayi yana tauna abincin dake bakinsa a tsanake yace."Me nai miki."? nace" Sabida ka shirya tafiya da Lawisa america sai ka 'boye min kasan dai ni ban isa na hanaka abinda kayi ra'ayi ba."

Tissue ya dauka ya goge bakinsa yana kallona yace."Lawisa ta samu labarin kina dauke da ciki hankalinta ya tashi wanda har hakan yasa take zargina akan nafi bukatar haihuwa dake shiyasa bana baki kwayoyi na nuna mata cewa nima karfina kikafi ta'ki aminta da maganata har tana ikirarin kai maganar gurin Maimartaba wannan dalilin yasa na yanke hukuncin tafiya da ita domin na rarrasheta acan."

Girgiza kaina nayi nace"To menene na 'boye min ni shine abinda yafi komai bani haushi sai dazu da naje gaishe da Mamma take fada min a lokacin nuna mata nayi kawai na san maganar dan Allah ka daina irin haka babu dadi."

Yace."To shikkenan tunda kin dauki hakan da wata manufa Allah ya baki hakuri." nace"Ai dole na zargi wani abu tunda naga kamar kana 'boye min.

Hannu ya daga min da fadin"Maganar ta isa haka kin san dai ke baki isa naji tsoronki ba ko? kallonsa nayi ya cigaba da cewa'' Bana munafurci kamar yanda kika zato kawai Allah ne bai nufe ni da na fada miki da wuri ba tunda yanzu kin samu labari magana sai ta wuce."

Mi'kewa nayi na bar masa gurin dan na lura da cewar ba zai fuskanci abinda nake nufi ba idan kuma nace dole sai na ganar dashi shaid'an zai shiga tsakaninmu.

Har nayi bacci bai shigo dakin ba......sai can naji motsinsa na bude idona ina kallonsa ya kashe fitila yazo ya kwanta kusa dani, jin shuru bai ta'bani ba yasa nasha jinin jikina ina tunanin ko yayi zuciya dan nasan halinsa da saurin fushi! ajiyar zuciya na sauke jin ya janyoni jikinsa ya rungumeni sai nasa hannuwana duka biyun na ratsa jikinsa kesses din fuskata ya shigayi kafin ya had'a bakina da nasa ya shiga tsotsar harshena da le'bena had'in kai na bashi sosai muka shiga biyawa junanmu bukata.

Washe gari cikin walwala muka tashi ni dashi sai abin arziki muke tamkar bamu ta'ba samun sa'bani ba, har bakin kofa na rakashi ya kar'bi wayoyinsa dake hannuna cikin kulawa ya rungumeni jikinsa yace."Ki kula da kanki da babyna." murmushi nai nace"Idan kana kiran babynka sai na dinga jin wani irin dadi a raina wallahi har so nake naga na haihu kana kula dashi."

Murmushi yayi yace."Ni kuma kullum da fargaba nake kwana nake tashi ina jin tsoron ranar da naquda zata kamaki ai ina jin kwanciya zanyi sai an k'ara min ruwa."

Dariya na dinga yi ina kallonsa, yace."Sumayya ina jin tausayin masu haihuwa wallahi shiyasa gabadaya bata burgeni." nace"Ka bar wannan maganar dan Allah dik abinda kaga Allah yayi to yana da manufa wuya bata kisa idan kuma na mutu gurin haihuwa aljanna zan shiga dan haka ka daina damuwa."

Yace"To na daina zan cigaba da yi miki addua." Cikin murmushi nace"Nagode rabin rayuwata." girgiza kansa yayi yana kallona tare da kannare idonsa " 'Dan sake maimaitawa naji sunana." yafada yana min wani irin kallo.......Hannunsa na rike tare da fadin"Rabin rayuwar Sumayya." yasa dariya tare da girgiza kai yace." Wani lokacin idan kina wani abu har mamaki kike bani! duk wannan soyayyar da kike nuna min anjima ba zata hanaki kiyi min rashin kunya ba.

Nace" Allah ya tsarani na raina ka kaifa mijina ne wallahi duk wani abu daka ga inayi maka a kan gaskiya ne, gashi dai mun dade a tare amma ka kasa gane halina."

Agogon hannunsa ya duba yace."Ni zan fadawa kowa halinki sumayya kina da kirki sosai amma baki yarda da zalinci ba kina da amana uwa uba addini bakya wasa da ibadah ke d'in 'yar baiwa ce ina kuma alfahari da samunki a matsayin matar aurena."

Sosai naji dadin yanda yake yabona rungumeshi nayi nace"nagode rabin raina naji dadi daka fahimci wacece ni ina rokon Allah ya dawwamar mana da zaman lafiya a tsakaninmu Allah ya baka ikon adalci tsakanin matanka."

Ya amsa da ''ameen my love yau dai kinsa na makara dubi time." da sauri na duba agogon hannunsa takwas da rabi nace" Gaskiya nayi laifi nasan jama'a nacan na jiranka idan kaje kace su yafe min.'' yana kokarin fita yace." Gurin Lawisa zaki nemi afuwa dan kin cinye mata lokacinta a yanzu dai ba zan samu damar shiga gurinta ba sai na dawo." hannu na daga masa da fad'in "Allah ya tsareka a duk inda kake." ya amsa da ameen ya Allah." Ajiyar zuciya na sauke na zauna kan kujera ina jin wani irin farin ciki a cikin zuciyata, inama ba zamu sake samun matsala da juna ba.

"Aunty Lauratu bana so wani mummunan abu ya biyo baya akan abinda kuke kokarin aikatawa dan Allah kada kuyi mata lahani ku kyaleta ita da cikinta nima insha Allahu zan samu." Lawisa ce take wannan maganar.......Hajiya Karima tace"Wato Lawisa har kin saduda ko? yarinya tayi sanadiyar da aka rataye d'an uwanki ki dinga nuna tausayinki akanta meye amfanin wannan yarinyar idan bamu bi dare da rana mun kasheta ba."!!!

A tsorace! ta kalli Mahaifiyar tata za tayi magana Lauratu tace"Ke! dallah rufe mana baki mara wayo kawai! wato ke har kin amince da dadin bakin da yayi miki ko har kina magana akan mu tausayawa kishiyarki to bari kiji wannan yarinya Sumayya ba zata haife cikin jikinta lafiya ba sai munyi ajalinta."

"Aunty Lauratu dan Allah ku bar al'amarin kada ku janyowa kanku wata masifar kunga garin irin haka Muddibo ya rasa rayuwarsa wallahi ni yanzu duniyar gabadaya tsoro take bani kuyi hakuri da daukar fansar nan kada ku janyo mana tashin hankali."

Hajiya Karima tace"Kinga Lawisa tashi ki koma gurinki tunda ba zaki bamu hadin kai ba, kije kawai kafin ku dawo daga inda kuka nufa komai ya zama tarihi." Lawisa jiki a sanyaye ta mike ta bar musu gurun, koda ta koma sashenta kasa aikata komai tayi ta dinga tunanin yanda zata 'bullowa al'amarin tana jin tsoron mahaifiyarta da kanwarta su janyowa kansu wata masifar gashi Wali baya gari bare ta sheda masa idan ta kira wayarsa bata shiga abin duniya ya taru yayi mata yawa sam bata so suyi tafiyar nan wani mummunan abu ya faru.

Ranar talata ranar ce ta kama ranar tafiya ya shigo gurina cikin shiri sai dai babu walwala a tare dashi, ganin haka yasa na danne damuwata na shiga kwantar masa da hankali ya rungume ni tsam! a jikinsa yana bani hakuri nace"Dan Allah ka daina bani hakuri kana sanyawa gwiwata tana sanyi wallahi." fuskata ya sumbata yana kallona yace."Sumayya dole na baki hakuri tafiyar nan kamata yayi ace dake zanyi domun na kula dake da babyna amma Allah bai nufa ba insha Allahu Allah zai kula min dake."

Nace"Ka gama magana tunda kace Allah insha Allahu zai kare ni cikin kariyarsa, hannuna ya rike muka fita falo tare yace."Sati uku kamar yau ne insha Allah ki kwantar da hankali ki.'' nace"Allah ya kaiku lafiya ya kuma dawo daku lafiya cikin nasara." Ya amsa da ''Ameen ya Allah." Hannuna ya saki da sauri ya kama hanyar fita, naji zuciyata ta karye hawaye suka zubo min da sauri nayi gaggawar shigewa daki dan bana bukatar ya juyo yaga halin da nake ciki, kwanciya nayi kan gado na dinga share hawaye ina jin wani irin kewa da damuwa a cikin raina...

*Na kudi ne.*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar biya ga yanda abin yake...Vip gruop#600 normal gruop#300 account... 0542382124...Binta umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne saki kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
104
Tunda suka tafi na kasa sakewa a gurina haka kawai sai na dinga jin fargaba da tsoro na dinga ganin tamkar wani mummun abu zai faru dani, kawai sai na tsiri zuwa gurin Mamma na wuni a can sai yamma nake komawa gurina, yawan zuwan da nake gurinta yasa ta gane cewa ina da ciki sosai ta nuna farin cikinta a fili tayi ta mamakin al'amarin nidai kunya ta hanani nace mata komai kasa hakuri tayi sai da ta tambayeni watannin cikin na fad'a mata watansa biyar, tace"Amma saboda baku da kirki dake da babana aka rasa wanda zai fada min ga ciki yayi kwari ban san dashi ba haka kuma Maimartaba bai sani ba meye abin 'boyewa a ciki." shuru nayi ba wai dan bani da abin fada ba sabida nasan idan na fad'a mata irin abubuwan da suka dinga faruwa kafin samuwar cikin sai ranta ya 'baci shiyasa nayi shuru domin fada mata bashi da amfani. wayarta ta dauka ta shiga kiran yaron nata, ina daga inda nake ina jin muryarsa suna gaisawa, tace"Babana ashe ka iya munafurci dama."? Da sauri yace."Mamma me ya kawo wannan maganar kuma."? tace"Sumayya nada ciki amma saboda rashin kirki kwanaki dana tambayeka kace babu saboda kana so kayi wasa da hankalina ko." murmushi yayi yace."Afuwa Mammana ni kaina wallahi yarinyar 'boye min tayi sai daga baya na ganshi." tace"To daka tabbatar dashi me yasa baka zo ka fada min ba." Yace."Mamma ki gafarce ni wallahi ina jin kunyar nazo na fada miki cewar Sumayya nada ciki shiyasa nayi shuru da bakina idan ya fito nasan dole ki gani." Tace"Ni ban yarda da maganarka babana watakila dai akwai abinda kake 'boye min." Gabansa ne ya fad'i! yace.'' Haba Mamma me zan 'boye miki kina matsayin uwata dan Allah ki yarda da maganata." Ajiyar zuciya ta sauke tace"To na amince da maganarka amma Sumayya zata dawo gurina ta zauna har sai sanda kuka dawo tukkuna."
Chapter 82 · 0% Book details