Sashe 52
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi idan baki biya ba, keda kika futar da book din keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake.....Vip gruop#600 normal group #300 account... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*0708465326*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:27 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊ðŸ?)
83
Cikin nutsuwa ya d'aga kansa yana kallonsu, "Ina Hamza yake."? yafad'a yana binsu da wani irin kallo. da sauri Mika'il yace." Yana can b'angaransu Haruna."
"Me yake yi a can."? Mika'il yace.''Yana taimakawa ne gurun had'a gawar." shuru yayi yana kallon k'asan kafet. Muddibo yace."Kai Mika'il maza jeka ce yazo yanzu yanzu." A nutse yace."Barshi kawai tunda akwai abinda yake yi, idan ya gama Mika'il kace ina nemansa." Mika'il yace."Insha Allahu zan sheda masa." Falon ya sake daukar shuru, Shatima ne ya mike fuska a daure ya karasa inda suke, daya bayan daya yake kallonsu kafin yace."Nasan kun san abunda yake faruwa ko."? gabadaya suka ce "Eh ranka ya dade mun sani muna rokon Allah ya kawo karshen Al'amarin." Ya amsa da ameeen kafin ya cigaba da cewa"Jiya misalin karfe bakwai zuwa takwas na safe waye ya shigo gurin nan wanda har ya samu nasarar zuba gubar data kashe wad'annan bayin Allah."?
Dukkaninsu suka shiga cikin wani irin yanayi na tashin hankali suka shiga tunanin waye ya shigo a daidai wannan lokacin." Shatima yace."Kunyi shuru idan fa baku fadi gaskiya ba dukkaninku d'aureku za'ayi muddun rai gwara ku fada mana gaskiya idan da akwai hadin bakin ku a cikin abinda yake faruwa."
Mika'il yace."Wallahi ranka ya dade ni dai banga wanda ya shigo gurin nan ba, iyakan mu ne kawai a gurin sai Sumayya da take shige da fice a gurin."
Magajin sarki mikewa yayi ya iso gurin, igiyar hannunsa ya fito da ita da fadin""Wannan ta wacece jiya na tsince ta a kicin." dukkaninsu suka tsirawa igiyar ido, kafin su fara duba hannuwansu! Shatima yace."Dukkaninku ku nuna min hannuwanku." suka fito da hannunsu kamar yanda aka bukata, abin mamaki kowanne da tasa a daure! al'amarin ya dauresu musu kai mutuka, Muddibo ya karaso gurin yasa hannu a kafadar Yarima da fadin"ammafa abun ya bani mamaki mutuka kodai Hamza nada hannu acikin al'amarin nan shiyasa ya tsaya a wani gurin."? Ya kalli Mika'il da fadin "Maza jeka idan sun gama kace ina nemansa, Mika'il ya kama hanya ya fita da sauri
Kujera ya samu ya zauna zufa na keto masa, Shatima ya zauna kusa dashi yana tausarsa, Muddibo kuwa kujararsa ya koma ya zauna yana cigaba da latsa wayarsa, Mika'il da Hamza suka shigo, da sauri ya mike tsaye, Hamza a tsorace yake kallonsa yace." Ranka ya dade a gafarce ni na tsaya ne gurin had'a gawar su Haruna." Yace."Babu damuwa, nuna min igiyar hannunaka irin wannan." Hamza da sauri ya mika masa igiyar hannunsa! Ya dinga bin hannun da kallo yana mamakin ashe zarginsa suke yi gashi kuma bashi ne ba tunda gashi yana daure da igiyarsa a hannu! Shatima yace." Wannan igiyar ta nuna mana cewa babu sa hannun d'ayanku a cikin wannan al'amari saboda haka zaku iya tafiya." Dukkaninsu sukayi godiya kafin su fita daya bayan d'aya.
Muddibo murmushi samun nasara yayi ya mike da fadin"Ni zan dan fita amma ba zan dade ba zan dawo." fatan alkairi sukayi masa, hanya ya kama ya fita cikin nishadi! Shatima yace."Kasan Allah ban yarda da Muddibo ba." Kallonsa yayi yace."Shatima me yasa kake da zargi ne?" Shatima murmushi yayi yace."Ba zargi bane halinsa na sani Muddibo baya kaunarka ko kadan duk wannan abin da yake yanayi ne kawai amma zuciyarsa babu alkairi." Ajiyar zuciya ya sauke yace."To idan yana nufi na da sharri Allah ya mayar dashi kansa, babban burina shine nasan wannan igiyar ta waye a cikin bayin dake cikin masarautar nan idan aka gane me wannan igiyar ina ganin 'karshen komai yazo dole ya fadi gaskiya.
Shatima yace."Binkice za'a tsaurara insha Allahu za'a gane mai ita." Yana kokarin magana, sallamarta ta katseshi, gabadaya idanu suka zubo min, a sanyaye na karasa tare da dan risinawa, gaishe su nayi, Shatima ne kawai ya amsa amma shi bina kawai yake da kallo, nace"Ranka ya dade me zan hada maka na break."
"Duk abinda kikayi ra'ayi." Ba tare da nace komai ba nabi hanyar kicin, akan idonsa ta shige ya sauke ajiyar zuciya yana girgiza kansa, Shatima yace."Sosai yarinyar nan take bani tausayi wallahi tana kokari akanka mutuka."
Yace."Nima nasan da haka Shatima yarinyar nan jajirtacciya ce mara tsoro naji dadi mutuka da Allah ya had'ani da ita wallahi daba dan tsayuwarta akaina ba da tuni na zama tarihi! duk wannan abubuwan dake faruwa suna faruwa ne a bisa kaddara shiyasa gabadaya naki bayar da goyan baya a station a d'aureta saboda nasan itama ba tasan yanda al'amarin ya faru ba, tunda tsaf ta kammala komai a lokacin na umarceta data gyara min daki, wannan damar aka samu aka shigo akayi abinda za'ayi aka fita tabbas Sumayya da tasan akwai abin cutarwa a cikin abinda ta dafa ba zata yarda 'kwaro yaci ba ballantana mutum mai rai." Shatima yace."Gaskiya nima na yarda ita duk rintsi ba zata taba yarda a hada baki da ita a cutar da wani ba, naji dadi sosai daka kareta a station din.'' ajiyar Zuciya ya sauke yace.''Yana da kyau muje mu samu jana'izar wad'annan bayin Allah." Shatima yace."Hakan nada kyau." Mikewa sukayi a tare suka fita, kai tsaye inda za'a sallaci gawarwakin suka nufa.
Koda na gama had'a masa abin karyawar kasa barin sashen nayi sabida ina jin tsoro na fita wani ya shigo, guri na nema na zauna ina sa'ke-sa'ke! shikkenan Haruna tashi ta'kare a duniya ya bar wannan duniyar mai cike da rud'ani, hawaye ne suka zubo min nasa hannu na goge ina girgiza kaina, hakika naso nayi rayuwar aure da Haruna saboda shine yake min sahihin so wanda babu algus a cikinsa, tabbas zanfi samun cikakkiyar nutsuwar da nake bukata mutukar na aureshi, ashe duk hasashe nakeyi rayuwar Haruna takaitacciya ce a duniya ya tafi ya barni da kaunarsa a cikin raina...........Hannuwana na daga sama na soma yi masa addua samun rahamar ubangiji ina kuka nace"Ya Allah ka tona asirin wanda yayi sanadiyar mutuwar bayin ka, ya Allah dukkanin wanda yake da hannu a cikin wannan al'amarin Allah ka nuna masa iyakarsa, Allah ka jikan Haruna da dukkanin musulmin da suka gabata bayansa........Adduar na shafa a fuskata, nayi saurin kallon bakin kofa, shine a tsaye yana kallona, ashe ya shigo lokacin hankalina ya dauke gurin addua, Mi'kewa tsaye nayi, ina kallonsa Acp ne ya shigo bakinsa dauke da sallama, sunkuyar da kaina kasa nayi na d'an matsa gefe guda, A nutse suka karaso cikin falon suka samu kujera suka zauna, "Barka da zuwa." nafada ina kallon Acp. kallon mamaki yake min, kafin ya amsa da "barka ka dai." dauke kaina nayi daga gurinsa nace. "Ranka ya dade na kammala komai." A nutse yace." Ki zauna Acp yana so yayi magana dake." a nutse na zauna kasan gurin......Acp ya jima yana kallona kafin yace."Ya sunanki! Nace"Sumayya Lawi." Rubuwata yayi a jikin wata 'yar takarda, Yace."Sumayya jiya da zaki shigo sashen nan suwa kika samu ina nufin mutane nawa kika gani."?
Shuru nayi ina nazari. Nace."Haruna ne da Hamza sai masu gadi da direbobi." Yace."Kin tabbata dukkaninsu kin gansu da idonki."? Nace"Eh na gansu." rubuce rubuce yayi jikin takardar, Ya cigaba da cewa! "bayan kin shiga falon baki samu kowa a gurin ba."? Nace" Eh gaskiya banga kowa ba dan har na gama aikina na fito wani be shigo ba."
Acp ya kalleshi cikin nutsuwa yace."Ranka ya dade jiya bayan fitar ka shin ka rufe kofar falo ko kuma a bude ka barta."? Jim! yayi kafin yace."Acp wallahi ba zan iya tunawa ba saboda a gaggauce na fita so na manta na rufe ko kuma ban rufe ba."
Acp yace."Okey daka fito wa ka samu a harabar gurin."? Yace."Ba zan iya tunawa ba tunda na fada maka a gaggauce na fito kuma ban tsaya amsawa gaisuwarsu ba kai tsaye mota na shiga direba ya jani ya fita dani."
Acp ya kalleni a nutse yace."Sumayya bayan kin hau sama domin gyare-gyare shin ko yaya bakiji motsin da zai nuna miki an shigo ba."
Murmushin takaici nayi nace."Banji motsin komai ba Yallabai ka duba nisan benan da kuma falon koda an shigo ba zanji motsin komai ba saboda akwai tazara mai tsayi."
Yace."Hakane shin da kika sauko ba kiga wata alama ba."? "Eh gaskiya banga wata alama ba dan yanda na bar komai haka na same shi, sai dai jiya da daddare mun tsinci igiyar hannu a kicin d'in." Yace."Eh Yallabai ya nuna min kuma kafin na shigo sai da nayi binkice a kanta." Da sauri nace"Ina fata an samu me ita."? girgiza kansa tayi yace."Ba'a samu me ita ba tunda duk wa'inda muke zargi suna da ita."
Jikina ne yayi sanyi na dinga kallon igiyar hannunsa ina tunani a kanta, Acp ya sauke ajiyar zuciya yana kallonsa yace."Ranka ya dade duk wani binkice da ya kamata ace munyi min gabatar dashi kuma mun rubuta komai insha Allahu zamu cigaba da binkice muna bibiyar lamarin a nutse da izinin Allah sai mun gano masu shirya wannan mugun abu, amma muna bukatar hadin kanka dake Sumayya keda kike kula da abincinsa da abinsha a duk lokacin da kika ga wani abu ko yaya ne to ki kira waya ki sanar damu halin da ake ciki insha Allahu mun shigo cikin al'amarin sai munga karshensa........Ranka ya dade shawara anan shine yana da kyau gabad'aya ka sauya hadiman ka tun daga kan masu gadi har i zuwa kan direbobi ga sanja sabbi tanan zamu gano bakin zare, sannan a cikin ma'aikatanmu zamu kawo mutum biyu domin su sa ido sosai akanka da dukkanin abinda ya shafeka ina ganin idan akayi haka za'a samu sassauci ta wani b'angaran."
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Acp din yace."Acp dukkanin abinda ka fad'a haka za'ayi insha Allahu zan duba shawararka yau da daddare zan zauna da mahaifiyata domin mu tattauna batun nagode sosai da kokarin ku akan wannan al'amarin ina rokon Allah ya saka muku da Alkairi."