← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 90

Sashe 72

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa yayi tare da rike hannuna "Muje toilet kiyi min wanka." ban masa gardama ba na rike hannunsa muka nufi toilet din,

Abin mamaki zir yayi bai bar komai a jikinsa ba, na rintse idona da fadin"Dan Allah kasa wandonka." jawo ni yayi muka fada cikin kwamin wankan ya hau tu'be min tufafin jikina! na dinga hanashi ina kokarin fitowa yana mayar dani! gajiya nai na kyaleshi ya tu'bemin kayan jikina tas, murya na rawa nace"Dan Allah ka bari na fita a ruwan nan kaga da najasa a jikina kada na 'bata maka."

Girgiza kansa yayi yana cigaba da shashshafa jikina! "Ba zan iya bari ki fita ba kawai ki dauki soso da sabulu ki cud'ani! hannunsa na cire daga breast dina nace" Ka bari to nayi maka wankan."

Kwanciya yayi cikin kwamin wanka na dauko soso da sabulu na fara cud'ashi! kasa hakura yayi ya janyota tsam ya matse a jikinsa tare da sa bakinta a nasa.......haka muka lalace a toilet tsayin lokaci mai tsayi, kafin muyi wanka mu fito................A daran ranar na bashi kulawa sosai sai da na tabbatar da cewa ya samu biyan bukata sannan hankalina ya kwanta muka kwana cikin farin ciki da kaunar juna.......

*Na kudi ne*
Kada ki karanta mun littafi idan baki biya ba! keda kika futa da littafin keda Allah idan kina bukatar ki biya ga yanda abin yake....Vip group #600 normal gruop#300 account... 0542382124.....Binta umar gtbank idan kati zaki turo #400 sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
97
Kiran wayar Lawisa ne ya tayar damu daga bacci! wayar ta karaci ringing d'inta ta mutu bai daga ba, zaune na mike ina kokarin kare jikina da bargo wani kiran ya sake shigowa, a maimakon ya daga wayar sai naga ya mike daga shi sai karamin wando ya nufi toilet, wayar na dauka ina dubawa da mamakin wanda yake buga wannan kiran da sassafe! My Lawisa, sunan dana gani kenan yana yawo kan fuskar wayar, da sauri na ajiye inda take ina mamakin al'amarin, koda wayar ta katse bata sake kira ba, na tsirawa kofar toilet din ido ina fargabar shiga saboda nasan halin fitinarsa........'daure da towel ya fito da wani a hannunsa yana goge jikinsa, kai tsaye wardrobe ya nufa domin kintsa jikinsa, ina kokarin mikewa kira ya sake shigowa wayarsa, sai naga ko kallon wayar beyi ba yana ta kokarin fito da kayan sa, a sanyaye nace"Ranka ya dade ana kiran wayarka tun dazu."

Juyowa yayi ya kalleni babu walwala a tare dashi yace."Ina da kunne ai."! kallonsa nai ina mamakin yanda ya amsa min magana kamar wanda nayi wa laifi! jiya lafiya lau muka kwanta muna soyayya amma ya tashi da d'acin rai! girgiza kaina nayi na wuce toilet ina mamakin baud'ewar halinsa.

Tsaf na fito na sameshi ya shirya dakin sai kamshin turarukansa yake yana zaune a gefan gado yana daura igiyar takalminsa, na 'karasa gurin a sanyaye nace"Fita za kayi ne."? Shuru yayi min ya cigaba da abinda yake.........Zama nayi kusa dashi duk jikina ya mutu da abinda yake nace"Dan Allah ka fada min idan laifi nayi maka naga lafiya lau muka kwanta bacci amma ka wayi gari cikin 'kunci da 'bacin rai! gashi laifina yana nema ya shafi Wata.

Babu fara'a a fuskarsa yace." Sumayya baki min komai ba raina yana 'baci akan wannan jinin da kike dan wulakanci bai tashi zuwa ba sai a lokacina gashi daga yau ranar ki ta amarci ta 'kare."

A sanyaye nace"Ranar amarcina bata 'kare ba tunda baka kar'bi budurcina ba har yanzu ina da sauran ranaku masu muhimmanci ka kwantar da hankalinka insha Allahu zaka samu abinda kake so a tare dani."

Girgiza kansa yayi yace."Sumayya zanso kema jama'a su sheda cewa ke cikakkiya ce sai dai kash! lokaci ya shige miki yanzu koda na kar'bi budurcinki kin fitar da jini jama'a da yawa ba zasu yarda ba zasu ce 'karye ne idan na tuna hakan raina yana 'baci sosai wannan jinin naki yayi mana illah."

'Kwalla ce ta cika idona nace"Nima zanso masu kokwanto a kaina su tabbatar da cikar mutuncina to amma ina so ka sani hakan ba addini bane al'ada ce idan kai ka tabbatar ka amince da cewa ni d'in budurwa ce shikkenan dama haka ake bukata ka kwantar da hankalinka.

Girgiza kansa yayi yace."Ki kyale Lawisa ina so na koya mata hankali ne mahaifiyarta ce ke sheda mata cewa ke din fanko ce shine saboda bata da mutumci ta tunkareni da maganar."

Raina ne ya 'baci dajin maganarsa kawai dai na daure bance komai ba ina jinsa sai surutai yake akan Lawisan "Sumayya koda ke d'in fanko ce wallahi kin fiye min mata dubu ciki kuwa harda ita Lawisan wannan dalilin yasa na'ki daukar wayarta.

Murmushi nayi cikin zuciyata nace" Namiji kenan a gabana sai nuna min so yake, duk yanda yake aibata Lawisa a gabana gobe ina iya ganinsa yana rawar jiki akanta na riga nasan halinsa sam bashi da al'kibula amma dai na soma zargin yana sona tuna gashi yana jin haushinta akan ta kira ni fanko.

Mi'kewa yayi yana kallon agogo, a marairace nace"Yanzu ina ka nufa."?

"Zan shiga mu gaisa da Mamma na wuce asibiti." Nace"Dan Allah ka shiga ku gaisa da matarka ka duba lafiyarta meye dan ta kira ni fanko kake jin haushinta."

Tsaki! yaja yay gaba ya barni da baki a bud'e! bayansa nayi yunkurin bi sai na tuna da cewar babu suttura a jikina kuma watakila su Mariya na falon, saboda haka sai na juya da jiki a mace na nufi wardrobe domin kimtsa jikina.

Magajin sarki yana fita kai tsaye sashen mahaifiyarsa ya nufa nan ya samu Maimartaba suka gaisa Maimartaba cikin kulawa yace." Naga kayi shirin fita aiki baka dauki hutu bane."? Yace."Ranka ya dad'e hutun bashi da wani amfani gwara na cigaba aikina." Maimartaba yace."To babu laifin hakan Allah yayi maka jagora a cikin dukkanin al'amuranka.'' Ya amsa cikin nutsuwa, Fulani tace"Da alama dai bakayi break fast ba ko.'' yace."Mamma kamar kin sani kuwa ina bukatar tea a gurinki."

Tace."Ai nasan ka da 'kiwar cin abinci shiyasa nayi magana bari na kawo maka." Yace."To godiya nake Mammana." Maimartaba mikewa yayi da niyyar shiga fadarsa yace."Aliyu zaman fada a gurinka dai ya gagara aiki ya hanaka kazo ka koyi yanda ake mulki."

Murmushi yayi yace."Ranka ya dade mulki ai sai ku jajurtattu wallahi ni kwata-kwata bana sha'awar mulki ranka ya dad'e."

Maimartaba ya shiga jijjiga kansa yana murmushi yace."Ali kenan! kada ka bani kunya mana! nasan kasan da cewar duk inda mai suna Ali yake jajurtacce ne a fagen ya'ki da iya mulki mai yasa kai ka karaya kake ganin kamar mulki bai dace da kai ba.

Girgiza kansa yayi shima da murmushi a fuskarsa yace."Ranka ya dad'e ba wai na karaya bane! ina ganin yanda kake d'auki ba dad'i akan 'yan uwanka dukkaninsu sunsa ido suna ganin kamar mun kar'be mulki daga hannun kowa muna yanda muke so shiyasa nake ganin nan gaba ya kamata a sakar musu su kar'ba suyi ko sa kwantar da hankalinsu.

Maimartaba yayi murmushi yana kallonsa yace."Aliyu kenan! ai muma bamu ne muka tilasta lallai sai munyi mulki ba cancanta da nagarta gwamnati ta duba jama'ar gari sukayi mubaya har Allah ya tabbatar mana da mulki a hannun mu! bama hassada da 'bakin ciki idan Allah ya kar'ba daga hannun mu ya bawa wani dama shi mulki ga wani abin hallita baya dawwama Allah shine yake da mulki madawwami."

"Kwarai haka yake Allah shi kadai keda mulki babu wani Sarki ko governor ko shugaban kasar da zai dawwama akan kujerar mulki aro aka bashi komai tsayin shekaru sai ya sauka daga kujerarsa bayan nan kuma ya fuskanci kalubalan dake gabansa domin kuwa dole a ranar lahira Ubangiji ya tuhume shi, ranka ya dad'e ina rokon ubangiji Allah yasa sasaauta maka a ranar al'kiyama."

Cike da jin dadin adduar da yayi masa ya d'ora hannunsa a saman kansa yace."Allahumma ameeen Aliyu yaron arziki kwarai nagode da wannan adduar taka." Magajin sarki murmushi yayi yana me sunkuyar da kansa......cikin wannan halin ta fito daga kicin hannuna rike da tire na kayan tea. da sauri ya mike ya kar'bi tire din yana yi mata sannu! zama tayi gurin zamanta hankalinta akan mijinta Maimartaba yace." Kinyi tsammanin na fita ko."? tace."Hakane ranka ya dad'e." Yace."Na tsaya muna tattaunawa da Ali yau munyi hira mai tsayi irin wacce muka jima ba muyi irinta ba."

Murmushi tayi tace."Kai amma naji dadi sosai ina fatan kayi masa maganar zaman fada." Yace."Nayi masa magana yace shi baya sha'awar mulki." Fulani murmushi tayi tace"Idan kuma Allah ya bashi ya zaiyi." ? Maimartaba na 'yar dariya yace."Nima abinda na gama fahimtar dashi kenan." Kallonsa tayi yana d'an motsa tea tace"Babana idan Allah ya baka mulki ka kar'ba hannu biyu ka gode masa mu kuma zamu yi maka kyakkyawar addua." Yace."To shikkenan Mamma ina godiya da wannan karamcin." Maimartaba ya sauke ajiyar zuciya tare da fad'in "To ni zan shiga fada.'' Fulani mi'kewa tayi domin yi masa rakiya bakin kofa, Magajin sarki fatan alkairi yayi masa, ya cigaba da kur'bar tea din yana nazarin maganganunsu da mahaifinsa ya fahimci Mahaifinsa na so ya gaje shi a mulki shi kuma ko kadan al'amarin baya bashi sha'awa, amma dai zai cigaba da addua akan Allah ya za'bawa rayuwarsa abinda yafi alkairi.

To Sai kusa takwas da rabi na dare ya shigo gidan a jigace tarin yunwa da gajiya sun had'u sun dabaibayeshi, kai tsaye gurin Lawisa ya nufa saboda yasan ita dashi, Hadiman dake karakaina a gurin suka dinga zubewa suna gaishe shi, da kyar yake amsawa da ya gaji shuru yayi musu ya wuce su.
Chapter 72 · 0% Book details