Sashe 25
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bisimillah yayi ya fara da plate din fatan doya, ya cinye wanda na zuba masa ya janyo na gabanshi shinkafa ba ta dameshi ba shiyasa ko cokali daya beci ba miyar k'awai ya d"an sha ya ture plate din, na ukun ya janyo yana jin k'arnin kifin dake tashi a miyar zuciyarsa ta tashi, da sauri ya ture plate din, yana kallon gefan da nake, saurin sunkuyar da kaina nayi dan bana son ya gane kallonsa nake....."Zo ki janye kayan nan na gama." Da sauri na mike naje na kwashe plates din dake gabansa.
"Bude min warmars din." Ba tare da nace komai ba na tsuguna na shiga bud'e masa snacks ne duk a ciki suna ta kamshi...."Zuba min a plate." Ya umarce ni, zuba masa nayi na mika masa kusa dashi, gyara zama a nutse yasa hannu ya dauki cake guda daya yasa a bakinsa, yana taunawa yaji radad'i a bakinsa furzar dashi yay a gurin, da sauri nida shi muka bi gurin da kallo, babu komai a cikin cake d'in , na kalleshi da sauri sai naga alamun jini a bakinsa, cikin fad'uwar gaba nace"Ranka ya dad'e meye a bakin ka." ? Hannu yasa da sauri ya shafo jinin yana dubawa! kuka nasa ina kallonsa ina hawaye nace"Kaga abinda nake gudar maka ko.? ni dama nasan sai kaci baragurbin abu.....mikewa yay da sauri ya hau samansa, ina kuka ina dudduba cake din babu alamun komai a cikinsa shar dashi sai kamshi yake, na mike tsaye hankalina duk ya tashi! addua nake yi Allah yasa cake din be shiga cikinsa, dan daka gani guba mai karfi akasa a ciki.
Shawara na yanke a kan nabi bayansa domin ganin halin da yake ciki......Kofar dakin a bude na sameta ba tare da tunanin komai ba na shiga, kakarinsa naji a toilet a guje na shiga toilet din, na ganshi ya rike kirji yana ta kakari babu abinda ke fita, k'asan gurin na kalla naga jini d'is-d'is yana diga.
Hawayen nadama suka wanke min fuska Yanzu da wane ido zan kalli mahaifiyarsa data gama yabo na, me zan fad'a mata? bayan ta bani umarnin fitar da kayan abincin daga sashensa gashi na barshi yaci abinda ya cutar dashi, bani da bakin magana! dana sani da nadama suka baibaye ni, dana sani na bar shi ya dake ni ya mare ni nabi umarnin mahaifiyarsa na hana shi cin abincin......Sheshshakar kukanta ne ya ishe shi ido jawur ya dago yana kallonta sai yaga ta d'ora hannuwanta duk biyu a kanta tana zubar da hawaye.
Tausayi ta bashi! ya dafa bango(Garu) ya mike tsaye. da sauri na kalleshi nace"Sannu ina fatan babu inda ke maka ciwo ? bai kalle ni ba yazo zai wuce hanya na bashi ya fita nabi bayansa, samunsa nayi kasan kafet yana maida numfashi.
Gabansa na tsuguna ina kallonsa idanuwansa sunyi jaja wuyar, a sanyaye na sake yi masa sannu ina tambayarsa abinda ke damunsa.''' Kallona yay yace."Babu abinda ke damuna ki daina damunki kanki." Nace" To Alhamdullhi dama haka nake so naji dan Allah ranka ya dade ka dinga yarda da maganata dik abinda kaga inayi a kanka da umarnin mahaifiyarka nake yi ina fatan yanzu zaka gane gaskiyar maganata."
Hannu ya daga min da fad'in "Kije kawai bana san dogon surutu." A sanyaye na mike na kama hanyar fita daga dakin banji dadin gwasale ni da yayi ba..
Bayan fitar ta daga dakin mamaki sosai ya shiga yi akan abinda ya faru! to me hakan ke nufi? ashe dai duk tsayayyar da yarinyar nan takeyi da gaskiyarta 'Yan uwansa na jini zasu kasheshi!? wai shin ma snacks din da yaci na wacece a cikinsu.? bashi da mai bashi amsa, ajiyar zuciya ya sauke ya jingina bayanshi jikin gado har yanzu yana jin zafi a mak'ogwaron sa, yana jin kamar an tsatstsaga masa da reza, pridge ya bud'e ya d'auko ruwa mai sanyi wai ko ya samu sa'ida yana sa ruwan a bakinsa yaji radadi da zugi a mak'ogwaronsa da kyar ya iya had'iye ruwan ya ajiye goran ruwan a kusa dashi yana mamakin al'amarin.
Cikin sauri na fitar da kayan abincin na lodasu a cikin wani buhu mai zurfi dan har kulolin na hada ina ganin suma barinsu had'ari ne d'aure bakin buhun nayi na umarci Hamza da ya dauka ya fita buhun, oma nasa sosai na wanke hannuna kana na koma ciki.
Samunsa nayi tsakiyar falon yana safa da marwa, nace"Kana bukatar wani abune." ? "Kije ki kira min Haruna." yafada yayin da yake kokarin zama kan kujera da sauri nace to na juya na fita.
Tare muka shigo da Haruna yace."Ranka ya dade gani." Da kyar naga yayi maganar." Ungo jeka pharmacy (gurin seda magani) ka kar'bo min wannan maganin." Haruna ya 'karasa kusa dashi da sauri ya kar'bi takardar hannunsa da kudi.
Fita yay da sauri! nima na juya da niyyar fita......"Ke! juyawa nayi ina kallonsa, "Kada ki kuskura naji maganar nan a bakin kowa mahaifiyata ma ban amince ki fad'awa ba kinji ko."?
Da mamaki a tare dani nace" Ranka ya dade mai yasa baka so mahaifiyarka tasan abinda ke faruwa? wannan al'amarin fa bai kamata a 'boye ba, ya kamata ta sani domin ayiwa tufkar hanci da wuri."
"Ke baza a ta'ba fada miki magana kice to ba sai kin kawo hojjojin ki ko."? A sanyaye nace" Ranka ya dade ba haka bane duk abinda kaga na'ki aminta dashi kai tsaye to na duba naga ba mai kyau bane dan Allah ka bari a shedawa mahaifiyarka a'lamarin nan."
"Ke ki kula fa ni babu me shiga tsakanina da 'yan uwana kinji na fad'a miki ban yarda wani abu na cutarwa naci ba saboda haka na fada miki ki iya bakinki ban amince ki fadawa kowa wannan maganar ba.
Na dinga kallonsa ina jin wani irin takaici a cikin raina 'kiri-'kiri yana ganin gaskiya yana takewa sau biyu yana tsallake rijiya da baya amma wai fadi yake bai yarda yan uwansa zasu cutar dashi ba, girgixa kai nayi nace" To shikkenan tunda baka so kowa ya sani insha Allahu babu wanda zan fad'awa."
Kauda kansa yay daga kaina ya tsirawa kasan gurin ido." Nace"Ina iya tafiya."? hannu ya daga mun alamar na tafi, na juya da sauri na bude kofa na fice raina a 'bace! na isa sashen mu...
Na kudi ne..!
Koda zaki ganshi a gruopa na sata ne idan kina bukatar biyan kudi ga yanda abin yake.....Vip gruop#600 normal gruop#300...account... 0542382124...Binta umar gtbank....idan kati zaki turu #400 ne kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊ðŸ?)
47&48
"Ke ranar dana zo na kawo Apple din nan kin bashi yaci ko kuwa."? Cike da tuhuma yake min maganar sannan ya wani tsatstareni da idanunsa, cikin zuciyata nace"Ni dai na shiga uku kowa so yake yay amfani dani gurin cimma munufarsa, cikin ladabi nace" Ranka ya dade na bashi sai dai ban sani ba ko yaci ko kuma beci ba dan umartata yayi dana fita daga dakin.
Ajiyar zuciya naga ya sauke a fusace! ya bar gurin, zama nayi a sanyaye ina bin hanyar da yabi kallo nace "Insha Allahu Allah ba zai baku nasarar cutarsa ba." shuru nayi ina mamakin abinda sukeyi gabad'aya sunbi sun tayar da hankalinsu akan sa kowa so yake yaga bayansa sabida suna ba'kin cikin kada ya gaji mulki a hannun mahaifinsa, a gaskiya idan haka sha'anin sarauta yake da bita da k'ulli gami da ma'karkashiya to babu shakka akwai matsala da damuwa acikin al'amarin sha'anin sarautar dai ya zama sai gyaran Allah dan gabad'aya kowa babu Allah a cikin zuciyarsa.
Sai bayan la'asar Jama'a suka tsaigata, koda muka shiga dakin ragal muka sameshi a zaune yana ta abinda ya saba, latse latse a waya, a jiyar zuciya na sauke naji dadi sosai ganinsa lafiya lau, Haruna da 'yan uwansa suka shiga tsaftace dakin, ni kuma na kama hanya na fita daga dakin ganin ko kallon inda nake beyi ba.
Alwala nayi nai sallah na fito na sake zama ina saka wasikar jaki, muryar babana naji yana sallama da sauri na daga kaina sai na gansu shida Tambaya, wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyata dama kwana biyu dauriya kawai nake da tunaninsu nake kwana nake tashi, da sauri na mike naje na taresu ina dariya nace"Baba sannunku da zuwa naji dadin zuwanku." Tambaya tace"Muna ta sa ranar zuwa Allah bai nufa ba sai yau." Cikin kulawa babana yace."Ai izini na nema gurin Fulani amaryar Maimartaba shine tasa aka kawo mu."
Nace."Aikuwa naji dadi sosai da zuwanku kuzo muje nayi muku jagora." Hannunsa na rike muka nufi dakin..............Yana zaune a inda yake da alama ma baiyi sallah ba cikin zuciyata nace"Saboda rashin kula da addininsa komai aka nufe shi dashi na sharri yana iya kamashi, a zahiri kuwa cewa nayi "Ranka ya dad'e fatan ka wuni lafiya ga Iyayena sunzo domin su dubaka." Dago kansa yayi yana kallonsu, su kuma sun sunkuyar da kansu kasa cikin ladabi da tausasa harshe suke gaisheshi, sai naga shima ya sassauta muryarsa ya amsa cikin kulawa yana nuna musu gurin zama da hannunsa.
Yanda ya tar'bi iyayena da sakakkiyar fuska yasa naji dadi a raina, nace"Baba ku zauna ga guri nan." Zama sukayi kan kujera suna murmushi yanda na lura suma sunji dadin tar'bar da suka samu.
Shuru dakin yay na minti biyu nida iyayena tunani muke shi kuma hankalinsa gabadaya yana kan wayarsa, da alama yana duba abu mai muhimanci a wayar......Muryar babana naji yace."Kar'bi wannan Sumayya ki bashi kayan dubiya ne babu yawa, ranka ya d'ade gashinan babu yawa.'' Da sauri na kar'bi ledar da yake mi'ka min, na isa inda yake na bashi
A nutse yace."Ajiye kan drowar nagode sosai." Ajiyewa nayi da sauri na matsa daga gurin.....d'akin ne ya sake dau'kar shuru na tsayin minti goma kafin babana yace."Ranka ya dade zamu tafi Ubangiji Allah ya kare ya kiyaye gaba munayi maka fatan alkairi har karshen rayuwarka.