← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 90

Sashe 79

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kaina nayi na koma na kwanta ina addua a zuciyata akan Allah yasa ya saduda ya gane gaskiya ya hakura da hukuncin ubangiji.

Washe gari da safe daya shigo nake sheda masa rashin lafiyar mahaifina tare da neman izinin zuwa dubashi! ba tare da ya dauki maganata da muhimanci ba yace.'" Zaki iya zuwa ki dubashi amma ni kam banda lokacin amma ana iya kaishi asibiti kamar kowa."

Jikina ne yayi sanyi na bishi da ido har ya fita daga dakin, girgiza kaina nayi ina jin takaicin abinda yake nasan duk wulakancin da yake min sabida na'ki nabi umarninsa ne.

Yanayin yanda na samu babana a rikice yasa duk hankalina ya tashi, banyi zuciya ba na sake kiran wayarsa na sheda masa cewa yana cikin matsala dan akwance yake sabida galabaita......Cikin tsawa yace." To yanzu ya kike so ayi ko kina so na katse abinda nake nazo na dubashi? nace "Kisa a kawoshi asibiti."!! kashe wayarsa yay ba tare daya bari nace wani abuba.

Daure zuciyata nayi na cire duk wata damuwa a cikin raina na shedawa Tambaya yanda mukayi dashi, tace" To shikkenan sai a kaishi Asibitin. nace"Zan koma gurina yanzu zan turo direba da mutum biyu domin su kamashi." tace."To ubangiji Allah yayi miki albarka.'' na amsa da ameeen lokacin da nake kokarin fita.

To hankalina bai kwantaba sai dana ga dawowarsu lafiya ikon Allah babana da kafafunsa ya dawo Tambaya ke sheda min cewa 'karin ruwa akayi masa shine dalilin daya sa yaji kwarin jikinsa, ledar dake cike da magani ta nuna min.'' na zauna ina nuna mata yanda zata dinga bashi maganin akan 'ka'ida, ban tafi ba sai dana tabbatar da cewa yaci abinci yasha magani sannan nayi musu sallama na tafi, yanzu naji sassauci ta wannan bangaran.

Da har nayi nufin shiga gurina sai na fasa bangaran Mamma na nufa mun kwana biyu bamu gaisa da juna ba.

Tana zaune gurin da take hutawa Jakadiya ce a gefanta suna hira irin wacce suka saba, a nutse na karasa inda suke na zauna gabanta ina gaisheta, murmushin da takeyi yasa ni tunani wani abu. gaisuwata ta amsa tare da fad'in "Ya jikin naki.''?

" Da sauki" nace ina jin nauyin had'a ido da ita, bayan tashin jakadiya daga gurin ta gyara zamanta cikin nutsuwa tace"Sumayya tun kwanaki nake miki kallon mai juna biyu, sai yau dana turke babana da tambaya yake cewa dani baki da ciki, ni wallahi da naga kina laulayi yau da lafiya gobe babu na dauka ko na kusa samun jika ne".

Cikin kunya da jin nauyi nace" Eh hakane Mamma bani da ciki muna dai Addua Allah ya kawo masu albarka." da sauri ta amsa da ''ameeen 'yar albarka Ubangiji Allah ya amsa adduarki." shuru nayi ina murmushin ya'ke! tace"Yanzu babana da sassafe yake fita gashi baya dawowa da wuri ni kaina sai ya kwana biyu bai shigo mun gaisa ba, sai dai kullum muna waya dashi mussaman da safe yakan kirani yace nasa akai masa abinci ofis."

Nace"Eh hakane kam aiki ya hanashi sakewa da kowa abinci ma sai da kyar yake ci! Mamma kada kiga laifinmu wallahi muna iyakacin bakin kokarinmu gurin kula daci da shansa kawai dai yafi bukatar naki shiyasa muka rabu dashi.

Murmushi tayi tace"Haba Sumayya ai ni zanyi shedarki akan babana kin kula dashi babu aure a tsakaninku ballanatana yanzu da aure ya shiga tsakaninku na riga nasan halinsa da 'kiwar cin abinci shiyasa a duk sanda ya bukaci abinci ta gurina nake sawa a kai masa amma dai duk da haka zan zauna dashi nai masa fad'a ya dinga zama yana cin abinci tare daku."

Nace"To shikkenan Mamma mungode kwarai da gaske Allah ya 'kara girma." Ta amsa da "ameeen suma ameeen." Sallama nayi mata tace" Ya muna hira kuma zaki tafi." Murmushi nayi nace" Mamma naga magariba ta kusa ne." tace"Eh hakane to babu damuwa Sumayya Allah yayi miki albarka sai na sake ganinki ." nace "To Mammah a tashi lafiya nagode kwarai da karamci." Murmushi tayi tare da daga min hannunta, cikin nutsuwa nasa takalmana na fita daga falon

A daran ranar bai shigo ba shigo ba sai da safe ya shigo, kamar koda yaushe fuskarsa babu sassauci! muka gaisa nace"Nagode sosai da hidimarka akan mahaifina wallahi naji dadin ganin ya dawo lafiya da k'afafunsa." hararata yayi yace."Bana bukatar godiyarki ba sabida ki gode min na kula da lafiyarsa ba ina fata kin gane."

Murmushi nayi kawai na sunkuyar da kaina, yace."Ni zan fita." da sauri nace"To Allah ya taimaka." ba tare daya amsa ba ya kama hanya ya fita daga dakin, kwanciya nayi ina dan jin sassauci a zuciyata yau naji dadi sosai mun rabu cikin arziki.........Cikin baccin daya soma daukana naji mugun bugu! a furgice na bude idona ina kallon bakin kofa........... Yunkurin saukowa nake bugun kofar na sake tsananta, gabana na faduwa nace"Waye."?

"Ubanki Lawi ne."!!!! Jin muryar Lauratu yasa naji yawun bakina ya dauke Ubana take zagi akan wane dalili? fuskata a murtuke na bude kofar a shirye nake dana kare martabar iyayena........Ko kafin nayi wani yunkurin ta afko dakin! da sauri na bita da kallon mamaki! nace"Baiwar Allah waike dabba ce ne? haka kawai da sassafe zaki zo kina buga min kofa ko kuma kina bina bashi ne."?

Yanda take kallona yasa na fahimci cewa tana mamakin lafazai na a kanta, hanya na nuna mata da fad'in " Kizo ki fice min daga daki tun muna sheda juna dake."

Murmushi tayi tana durfafo inda nake na tsorata da yanayin kallon da take min amma dai na dake! sabida inaso na nuna mata tsageranci na, cikin zafin nama naga ta watso min abu a jikina! a gaggauce na matsa gefe guda kawai naga wani irin ruwa yana kumfa a 'kasan gurin ties din ya tsage! cike da d'umbin mamaki! nake kallonta tana huci!!! Ta bud'e kofar dakin ta futa a fusace! cikin karkarwar jiki na nemi guri na zauna ina jan kalmar innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! shin matar nan wane irin mugun abu tazo tayi min? " asid ne tayi nufin watsa miki a jiki domin ta 'kona ki." zuciyata ce ke fada min wannan magana, nai gaggawar kallon gurin ina mamakin yanda yayi 'baki ties din yayi duhu duk ya tsage! al'amarin ya shiga bani tsoro tare da mamaki! mai tsananin gaske..

*Na kudi ne!*
Koda zaki ganshi a group na sata ne idan kina bukatar biyan kudin littafin ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal group #300....account.. 0542382124....Binta umar gtbank idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
102
Na jima a zaune a dakin ina jimanta al'amarin kafin na mike jiki a mace na fita falo, nan na samesu a zaune ganin fitowata yasa duk suka mike tsaye, sunayi min barka da fitowa, zama nayi kan kujera babu walwala a fuskata nace "Ku zauna inaso nayi magana daku.'' zama sukayi tare da mayar da hankalinsu kaina, nace" Daga yau sai yau kada ku sake barin matar data fita yanzu ta sake shigowa kunji abinda nace ko." Gabad'aya suke ce "Eh ranki ya dade insha Allahu zamu kiyaye." Nace"Mariya ki shiga ki gyara min dakina." da sauri ta mike ta nufi dakin su kuma suka cigaba da aikace aikacen da suke..........

Da wuri ya dawo gida nai mamakin hakan amma ban nuna a fuskata ba barka da zuwa nai masa ya amsa a sake kamar bashi ba, ruwan wanka na hada masa na fito na tarar dashi yana kokarin cire kayan jikinsa, ido muka hada murmushi yayi min na bishi da kallo ina mamakin sanjawarsa jikin mirror na tsaya Nace."Na hada maka ruwan wankan.'' "Nagode." yafada a lokacin da yake kokarin ajiye agogonsa kan mirror wani irin kallo yayi min yace'"Ba zaki taya ni wankan ba."? Murmushi nai nace"Da alama yau kana cikin nishadi .'' yace."Saboda me kikace haka."? nace"Saboda ba haka kake mu'amula dani ba." Shuru yayi still da murmushi a fuskarsa ya nufi toilet din, girgiza kaina nayi na bude wardrobe na dauko masa jallabiya da gajeran wando na zauna gefan gado ina jiran fitowarsa

Ido muka hada a lokacin da ya fito daga toilet din da sauri na kauda kaina tsigar jikina duk ta mi'ke ni kaina nasan ina bukatarsa cikin zuciyata nace" Allah yasa dai yau muyi abin arziki da juna.

Zama yayi kusa dani yana goge jikinsa da towel nace"Ga kaya na dauko maka." "Nagode." yace na mike a nutse na dauko man da yake shafawa, a nutse na tsuguna kasan kafet na fara shafa masa a kafafunsa.

"Sumayya." cikin wani irin voice yayi maganar, kallonsa nayi naga idonsa yayi ja. amsawa nayi tare da cigaba da shafa masa man.

Yace."Ya jikin naki."? ba tare dana kalleshi ba nace da sauki.'' Yace." Allah ya rabaku lafiya." da sauri na kalleshi ina mamakin adduar da yayi. girgirsa ya daga min yana murmushi.

Ajiyar zuciya na sauke nace"Yanzu ka gane kenan." hannu na ya rike yace.''To ya zanyi tunda kinfi karfina." girgiza kaina nayi nace"Kada kayi sa'bo ba laifina bane Allah ne ya nuna maka ikonsa."

Yace."Na sani Sumayya na hakura na bar masa ikonsa." murmushi nayi nace"Nagode kwarai insha Allahu za kayi alfahari da dan da za'a haifar maka."

Yace." To shikkenan yanzu me zaki bani." nace"Zan cika maka ciki da abincina mai dadi da gamsarwa.''' da murmushi a fuskarsa yace."Bayan naci na koshi me zan samu." ?

Shuru nayi yace."Yau da soyayya nazo gurinki." kallonsa nayi ya kanne min ido......murmushi kawai nai ina mamakin shu'umancinsa dama ai ruwa baya tsami banza.

Hannuwana ya ri'ke yana murzawa yace."Baby kinyi shuru ko bazan samu ba." ? nace"Zaka samu mana." yace."To nagode muje ki bani abinci naji karfin jikina." mikewa nayi ya rike hannuna muka fita falo.

Da kyar ya iya cinye abincin dana zuba mishi nace"Wai dan Allah me yasa baka san cin abinci."? yace."Haka kawai tun ina yaro haka nake nafi mayar da hankali kan biscuits da sauransu kayan zaqi." nace"Shiyasa mana gakanan kullum jiya i yau ka'ki kumari." dariya yasa yace."Kina so nayi qiba kenan."? kai na daga ina murmushi yace."Idan na zama 'kato zan dinga turmusheki fa." dariya nayi nace"ai yanzu ma turmushenin kake.''
Chapter 79 · 0% Book details