← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 90

Sashe 66

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shatima yace." Haba babu komai wallahi kada ku damu Hajiya uwa ce komai tana iya yi mana mu hakura." Murmushi tayi tace"Nagode sosai.'' Shatima ya kalleshi sai yaga ya k'urawa k'asan gurin ido, yace.''Bari nayi gaba na bar amarya da ango su tattauna." da sauri ya dago kansa yana harararsa, Dariya yayi ya bar gurin, kokarin tafiya yake ta rike hannunsa, ya juyo yana kallonta cikin wani irin yanayi yace." Kina bukatar wani abune."? murmushi tayi tace.'"Babu abinda nake bukata sai angona hakika yau ina cikin murna da farin ciki da Allah ya tabbatar mana da alkawarin mu.'' shuru yayi yana kallonta a sanyaye tace" naga kana kallona ko dai kwalliyata ba tayi kyau ba."? tafada tana duba jikinta

Girgixa kansa yayi yace."Kinyi kyau sosai dalilin daya sa ma kenan na kasa dauke idona a kanki ." wani farin ciki ya ziyarce ta hannunsa ta damqe da fadin"Lallai tunda kana son ado zan diga yi maka mai kayatarwa." shima murmushin yayi yace.''Nagode amaryata anjima zan kira ki kizo ki taya ni hira." dadi ya sake rufeta lallai malamin da yake musu aiki gwani ne yau ita da Yarima ne suke hirar soyayya babu fada, fari tayi da ido tace"To shikkenan angona." hannunsa ya cire daga cikin nata ya bar gurin, kallon so da kauna tabi shi dashi har sai daya 'bace daga gurin sannan ta koma ciki cike da murna da farin ciki, kasa boye farin cikinta tayi ta shedawa mahaifiyarta sauyin da'aka samu Hajiya Karima ta dinga murna tana kara kuranta aikin malaminta.

Samun Shatima yayi a tsaye a wani guri yana jiransa saboda haka yana karasowa suka nufi sashen Uwar gida Huwaila da jakadiyarta suna magana shigowarsu yasa ta washe baki kamar mutuniyar kirki ta dinga tsokanarsu su kuwa sai sunkuyar da kai suke suna murmushi jakadiya ta gaishesu da sauri ta fita daga falon, suka zauna a nutse suna gaisheta, ta amsa cikin sakin fuska tace"Tun dazu 'Yan uwanku suke zaman jiran shigowarku ku gaisa suyi muku Allah ya sanya alkairi ganin dare yayi sosai yasa nace ko wacce ta tafi dakinta daga baya sai su dawo ku gaisa sosai! ta fadi hakane domin ta karesu gabad'ayansu ana gama daurin aure kowacce ta shiga motarta ta tafi a cewarsu ba zasu tsaya zuciyarsu ta buga a banza da wofi ba sun tsani suga mahaifinsu na nuna kulawa akan dan uwansu ba kuma sa kaunar wani alkairi ya same shi hassada suke masa sosai suna ganin kamar mahaifin nasu yafi kaunarsa saboda yana namiji.

Magajin sarki yace."Allah sarki aunt's d'ina banji dadi ba wallahi amma babu komai in Allah ya yarda duk zamu bi gidajensu daya bayan daya muyi musu bangajiya." Tana dariyar yake tace"Haka yayi kyau Tabbas zasuji dadi idan kuka ziyarcesu yana da kyau ma idan zakuje kuje musu da amaran naku." Shatima yace."Insha Allah hakan za'ayi." sallama sukayi mata mikewa tayi tabi bayansu sai surutan banza take musu wai ita a ganinta tana musu nasiha akan zamantakewar aure! Suna fita Shatima yace."Wannan matar kana ganinta kaga mara gaskiya gabad'aya halayenta na munafukai ne."
Murmushi yayi yace."Shiyasa ai nake kallonta ita da yaran nata nasan dukkaninsu ba kaunata suke ba kome suke na ganin idone idan babu idona a gurin Allah ne kadai yasan sharrin da suke shirya mun."

Shatima yace."Addua zaka dage dayi ka kuma dinga azkar safe da dare insha Allah duk wanda ya nufe ka da sharri zai koma kansa." A hankali yace."Ina godiya dan uwa insha Allahu zan kula da shawarwarin ka."

Kai tsaye sashen mahaifiyarsa suka nufa, suka sameta ita da Maimartaba a falon suna tattauna abinda ya shafe su, cikin girmamawa suka gaishe su Maimartaba ya dinga kallonsu yana jin dadi da farin ciki a zuciyarsa, addua mai kyau yayi musu ya kuma yi musu nasiha mai ratsa jiki itama Fulani ta d'ora ta tace"Dukkaninku yanzu wani nauyi na mussaman ya hau kanku mussaman kai Babana ka kula sosai kayi adalci a tsakanin matanka Allah yayi muku albarka ya sanya alkairi a cikin zamantakewar auranku." Gabad'aya suka amsa da "ameeen." suna kokarin mikewa tace"Babana na manta ban fada maka ba Sumayya na can gurin iyayenta na tura ta suyi sallama da juna watakila ma a can zata kwana."
Jim yayi kafin yace."to shikkenan Mamma babu damuwa ai." Maimartaba yace."Gobe da safe sai kaje ku gaisa da iyayen nata daga nan sai ku tawo da ita." Yace."To ranka ya dad'e Allah ya kaimu lafiya." suka amsa da ameeen.'' sallama sukayi musu suka fita koda suka fita din basu jima a a tare ba sukayi sallama da junansu kowanne ya nufi sashensa, Magajin sarki zama yayi a falonsa yana jin takaicin abinda Sumayya ke masa tunda suka samu sa'bani kwanakin da suka gabata ya dauki fushi da ita bata ta'ba bashi hakuri ba, idan ta gaishe shi shikkenan sai ta fita sabgarsa ko kiransa a waya ba tayi kawai sabgar gabanta takeyi tana nuna tamkar bata damu dashi ba! abin yana bashi mamaki mutuka a ganinsa shine yake sama da ita koda shine bashi da gaskiya tunda itace a kasa dashi ita zata bashi hakuri amma saboda ta dauki kanta wata mai matsayi ta'ki kallonsa da mutunci dole ya nuna mata shi ba tsaranta bane tunda dai an riga an daura aure zata gane bata da wayo tsarinsa kuwa dole tabi ko tana so ko bata so.
Wanka yayi yasa kananun kaya ya sauko kasa da wayarsa a hannunsa Lawisa ya kira domin tazo ta d'ebe masa kewa aikuwa ko minti ashirin ba'ayi ba ta shigo cikin ado har yafi na dazu! kusa dashi ta zauna tana kwarkwasa kamshin turaranta ya kashe masa jiki hannunta ya rike yana mata wani irin kallo yace."Muje sama ko."? kanta ta daga masa ya mike tare da ita, kugunta ya rike ta sosai tare da manneta jikinsa suka nufi saman rungume da juna.

Bangaran Sumayya kuwa tana cikin farin ciki da annushuwa tana tare da iyayenta sai walwala sukeyi sai dai a duk sanda ta tuna da mutumin nata gabanta sai ya fadi! tana tunanin irin bahaguwar rayuwar da zasuyi ita dashi tunda dai ita tayi rantsuwa akan cewar ba zata amince da tsarinsa ba shi kuma ya tabbatar mata da cewa dole tana karkashinsa tayi masa biyayya mutukar tana bukatar zaman lafiya dashi inda ita kuma take ganin babu yanda za'ayi ya sata ta kauce hanya ba za tayi tsarin iyali ba sai dai shi yaje yayi tsarin iyalin amma ita ba zata cutar da kanta ba......Wannan dalilin yasa gabadaya ta kasa sakin jikinta dashi domun tana so ta nuna masa cewar har yanzu fa tana nan akan ra'ayin ta babu gudu babu ja da baya idan Lawisa tana iya yi taje tayi amma itakam bata da ra'ayi.

Magajin sarki da Lawisa soyayya sukayi sosai kafin kuma ya rabata da budurcinta sai da ya bata kwayoyi tasha tukkuna suka cigaba da gudanar da abinda suke a daran ya kar'bi sadakinsa alhamdullh kwalliya tabiya kudin sabulu dan yaji dadin kasancewarsa da ita bukatarsa ta biya ya dinga alfahari da ita shine yayi mata wanka ya gasa mata jikinta tsaf suka fito daga toilet din a tare, kayanta ta mayar a sanyaye take kallonsa yace."Kada ki damu nasan abinda kike tunani! sunkuyar da kanta tayi yace." Kinzo dakin ki kenan ba zaki koma ba kuma inaso na sheda miki cewa na sameki cikakkiyar mace ina alfahari dake." ajiyar zuciya ta sauke tana kallon bedshirt din daya 'baci da jini! tace."Wannan zanin gadon zaka sa a leda nasan da safe Hajiya zata aiko a kar'ba.'' yace."Lawisa wannan tsohuwar al'adace bana san tonan asiri wallahi." cikin alfahari tace"Ni dai gwara kowa ya gani ya sheda na kawo mutuncina." yace."To babu damuwa." bedshirt din ya cire yace'' kar'bi abinki kisa a leda ki daure." da sauri ta kar'ba! wardrobe dinsa ya nufa can kasa ya dauko sabon zanin gado ya fara kokarin shimfidawa, karba tayi suka shimfida a tare, kwanciya yayi yana kallonta gaskiya yaji dadinta sosai gata da ni'ima ta kowanne fanni tayi ta burgshi lumshe ido yayi yana tunanin irin ni'imar da zai kwasa gurin Sumayya.

Hajiya Karima sashe sashe ta dinga bi tana nuna zanin gadon amarcin Lawisa Jakadiyarta sai rangwada buda take tana fadin"Yarinyar arziki ta cika mace ta kai mutuncinta dakin mijinta! Hajiya Karima ta kalli Fulani cikin farin ciki tace"Fulani inaso ki ajiye wannan zanin gadon idan Maimartaba ya shigo sai ki nuna masa." Fulani na kokarin magana na shigo tare da sallama! gabadaya suka amsa min Hajiya Karima ta wani dauke kanta tana girgiza kafa, a nutse na zauna kusa da ita nace"Mamma barka da asubah." tace"Barka dai Sumayya ya kika baro iyayen naki."? nace"Suna nan lafiya lau sunce suna gaisheki da kyau." tana murmushi ta amsa, ta cigaba da cewa"Tare kuke da babana ne."? girgiza kaina nayi alamun A'a, tana kokarin magana Hajiya Karima ta katseta da fadin" In banda abinki Fulani ina za'a ga Magajin sarki yana can tare da yarinyar arziki aini nayi alfahari da faruwar wannan abu.''
Chapter 66 · 0% Book details