Sashe 22
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rai a 'bace! nace"Saboda ina kula lafiyarka kake min tsawa maganin nan fa kanka zaka shawa kake watsi dashi." Dirgowa yayi daga bed din ya durfafo ni yana huci! da sauri na bude kofar dakin na fita ina jin wani irin faduwar gaba, shin wai me yayi zafi ne? me mutumin yake so ya mayar dani! daga taimako sai sharri ya biyo baya.
Jikin kofar na jingina ina mayar da numfashin fargaba gabadaya gwiwata tayi sanyi nayi masifar tsorata da al'amarin, sai da na samu nutsuwa tukkuna na samu guri na zauna tare da rafka ta gumi.
Na kai minti talati a zaune kafin na yake shawarar sake shiga dakin...mikewa nayi a sanyaye da niyyar shiga dakin, Ya shigo gurin. sunkuyar da kaina nayi a nutse nace"Ranka ya dade barka da asubah."
"Barka dai." kawai yace yasa hannu a jikin kofar ya bude ya shiga tare da mayar da kofar ya rufe.
Shuru nayi ina tunanin waye a cikinsu sam bana gane su Shatima ne ko Muddibo kusan dai suna yanayin kama da junansu harshi Yarima tunda dukkaninsu farare ne masu tsayi.
Komawa nayi na zauna ina jiransa ya fito daga dakin na shiga, ko minti uku banyi da zama ba ya fito yana duba agogon dake daure a hannunsa, ganin ya fito yasa na mike da sauri "Ranka ya dade ka sauka lafiya." Tsayawa yay yana min wani kallo kafin yace."Meye ma sunanki."? Nace"Sunana Sumayya Lawi."
Yace."Okey na shiga na sameshi yana bacci idan ya tashi ki sheda masa zuwana akwai tufa (Apple) dana kawo masa inaso idan ya tashi a bacci ki bashi yaci kinji ko."
Da sauri nace"Insha Allahu zan bashi." Hanyar fita ya kama ba tare da ya sake magana ba, dakin na shiga da sauri. yana kwance ruf da ciki ya matse fillo a kirjinsa, girgixa kaina nayi cikin zuciyata nace aikin kenan rungume fillo gaskiya yana da tsananin bukata daga ganinsa, yana da kyau ya gaggauta aure domin shine mafita a gareshi.
A hankali na karasa shiga dakin,nasa hannu na dauki ledar tufar(apple) din kan kujera na zauna na shiga fito da ita guda shida ce manya manya ido na tsira mata ina nazari, gani nayi kaman huda a jikinta dan a yanda nasan apple bata da huje huje sumul take, a take na tsargu da ita nayi saurin mayar da ita ledarta na daure bakinta tamau! toilet na shiga na wanko hannuna na fito, maganin dake tarwatse a kasan dakin na kwashe tsaf na ajiyesu kan drowar dan tsayawa nayi ina kallonsa bacci yake sosai kuma daka gani yana jin dadinsa, ajiyar zuciya na sauke na dauki ledar apple din na bud'e dakin na fita.
Can inda aka tanada domin zubar da shara na nufa, na samu wata sanda mai tsayi na tona sharar ledar apple din nasa a ciki na mayar da sharar na rufe, gurin na bari da sauri.
Daf da zan shiga reception din na hango su Haruna gurin masu gadin asibitin suna hira cikin zuciyata nace"Wato dama nan suke zuwa su zauna girgiza kaina nayi na bar gurin
Ina shiga Dr na fitowa daga wani daki, murmushi naga yayi min wanda ya ban mamaki yace."Sumayya ina fatan Yarima yasha maganin nasa."? shuru nayi ina tunanin abinda zance masa." "Yake kyakkyawa Ina magana kinyi mun shuru ki bani amsa mana."
Maganarsa tasa na tsira masa ido ina mamaki! tunda nake babu wanda ta'ba kirana da kyakkyawa kowa muni na yake gani amma saboda cin mutunci na likita yake kirana da sunan mai kyau.........Dago kai nayi na kalleshi naga yana sakar min wani lafiyayyan murmushi, shan kunu nayi nace"Be sha maganin ba bacci mai nauyi ya dauke shi.
"Ayya keda nace kiyi kokari ki bashi kafin ya kwanta alright bari na shiga yanzu na tashe shi yasa magananin." Dakin ya nufa da sauri nima na rifa masa baya.
A zaune muka sameshi da waya a hannunsa, kallo guda yay mana ya watsar damu Dr na ya'ke ya karasa kusa dashi da fadin"Ranka ya dade garin ya yau ka kwanta ba kasha maganinka ba."
A dan ya tsine yace."Bacci ne yaci karfina amma ina ganin babu damuwa yanzu idan naci abincin zansha." Dr kallona yake cikin tuhuma yace."Haba baby me yasa kike wasa da aikin ne? wannan fa shi muke sa rai ya zama Sarkinmu amma kina wasa da lafiyarsa." Nace"Dr ba laifina bane shine yace sai yay bacci ya tashi zaici wani abu."
"Okey to tunda ya tashi yanzu dan Allah ki tsaya sosai ki tabbatar yaci ya koshi kin gane ko.''? da sauri nace" Eh na gane" Juyawa yay yana kallonsa yace."Yallabai ni zanje na duba marasa lafiya dan Allah ka daure kaci abinci sosai kasha magani."
Yace."Okey kada ka damu." Dr fita yay daga dakin shi kuma ya mi'ke tsaye. had'a ido mukayi nayi gaggawar yin kasa da nawa.
Yace."Wai baby sunan bai dace dake ba yarinya kinfi dacewa da *Gwamma* dubeta dan Allah da ba'ki kamar wani guri."!
Cikin tsantsar takaici da bakin ciki na kalleshi ya watsa min harara mai zafi! hanyar toilet ya nufa yana jan tsaki! bin bayansa nayi da kallo zuciyata nayi min wani irin zafi.....
*BINTA UMAR ABBALE*
*Littafin na kudi ne*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina so ki biya ga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300 account 0542382124...Binta umar gtbank idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta whasap da wannan number
*07084653262*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊ðŸ?)
41&42
Cikin wani irin yanayi wanda yake nuna tsantsan 'bacin ransa yace."Kina nufi auntyna zata sa min guba a abinci dan ta cutar dani, ashe har kin kai matsayin da zaki kalli tsabar idona ki fada min wannan maganar."!!! Hawaye ne ya wanke min fuska bakina na rawa nace"Kayi hakuri idan maganata ta bata maka rai ban yarda da nagartar abincin ba shiyasa nayi wannan maganar amma ni bana zargin auntynka da wani mugun abu, dukkanin abinda kaga nayi a kanka ina kokarin ganin na rike amanar da mahaifiyarka ta bani.
A lalace yace."Wato ke har kin kai matsayin da za'a dauki amana ta a baki me kika sani a rayuwa." ? Ido cikin ido nace"Ni nasan abinda baka sani na ranka ya dade dan Allah ka bani goyon baya akan dukkanin abinda za kaga nayi a kanka wallahi ba zan cutar da kai ba." "Rufe min baki." Yafada yana watsa min harara, ya cigaba da cewa'' Daga yau sai yau kada wani dan uwana ya kawo min abu ki dora zargi a kansa bani da kamar su a duniya banyi imanin da cewa zasu cutar dani ba saboda haka babu abinda ya shafe ki da tsakanina dasu." Sunkuyar da kaina kasa nayi tsabar takaici ya hanani cewa komai...."Kina ji ko bakya ji."? Ba tare dana dago ba nace "To." "Zuba min abincin naci." Yafad'a yana tsatstsare ni da idonsa.
'Kin zuba masa nayi na sake 'boye fulas din a bayana gabana sai faduwa yake ina jin tsoron ya turmushe ni ya dauki abincin yaci.......Gani nayi ya dafe kansa yana girgizawa da sauri nayi yunkurin tashi da fulas din a hannuna ya wani finciko ni na fad'a kansa fulas din abincin yay nasa guri duk rabi ya zube a gurin. da sauri na mike daga jikinsa gabana na bugawa, ya dinga hararata murya na rawa " nace kaga ka zubar ko." Tsaki yaja mai karfi ya mi'ke gani nayi ya nufi inda d'aya kwandon abincin yake ya dauko guri ya samu ya zauna yana kokarin zuba abincin. Nufarsa nayi dan na zuba masa "Idan kika zo nan sai ranki ya 'baci ki fita ki bani guri bana bukatar ganin ki.'' A sanyaye na tsaya ina kallonsa yana kokarin bude fulas din. juyawa nayi na fita raina a bace na dauko tsintsiya da abin kwashe shara gyara gurun daya 'baci nayi na goge gurin tsaf, ina kokarin fita Dr ya shigo, a nutse na gaishe shi nasa kai na fita daga dakin zuciyata gabadaya babu dadi.
Muna zaune a reception likita ya fito daga dakin cikinmu babu wanda yay gangancin shiga muna dai kallon yanda 'yan uwa da abokansu suke zuwa su shiga dakin domin dubashi.....goma da rabi jama'a sun tsagaita, Haruna ya kallemu da fadin" Yana da kyau muje mu dubashi idan akwai abinda yake bukata sai muyi masa muje mu kwanta."
Gabad'ayan mu muka miqe muka nufi dakin....Yana kwance kan bed da waya a hannunsa muka gaishe bai tare daya kallemu ba ya amsa, Haruna yace."Ranka ya dade akwai abunda kake bukata muyi maka.''? Girgiza kansa yay yace."Bana bukatar komai kuje ku kwanta sai da safe." Godiya muka mike muka juya da niyyar fita.
Nice ta karshen fita naji ya kira sunana. juyowa nayi ina kallonsa. "Zonan." yafada idonsa a kan wayarsa, a sanyaye na saki kofar ta rufe na koma na tsaya tare da sunkuyar da kaina, na kai minti goma a tsaye a kansa kafin yace."Ki matsa min kafafuna." Kallonsa nayi inaso nayi magana naga yasha kunu.
Kasa motsi nayi gabana na faduwa ni kam na rasa wane irin mutum ne wannan abinda Allah ya haramta sai yace sai nayi masa.
"Ko ba zakiyi bane."? Nace" Bai dace ba na ta'ba jikinka ba dan Allah kayi hakuri na kira maka Haruna yayi maka." Mikewa zaune yayi yana kallona yace."Kafafuna nace ki matsa min ba Al'aurata nace ki matsa ba." da sauri na kalleshi ina mamakin maganarsa, Al'aura lallai mutumin baida kunya. Ya cigaba da cewa! ni bazan ji wani feelings ba ballanatana kiyi tunanin wani abu zai faru a tsakaninmu dan kin matsa min kafafu babu abinda zai faru ki kwantar da hankalin ki."
Wannan maganar da yayi tasa naji kwarin gwiwa a jikina dama ina tsoron faruwar wani al'amarin ne. Ajiyar zuciya ya sauke ya ajiye wayar kan drowar ya koma ya kwanta yana kallon rufin dakin.