← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 90

Sashe 12

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan na idar da sallah na jima hannuna a sama ina rokon Allah ya kareni daga sharrinsa na shafa adduar na mike a nutse na fita falon na jima a tsaye ina sak'e sa'ke kafin na nufi kofar kicin domin shirya abin kari...........Tsaf na shirya kayan karin kummalo na fito dasu ina jerawa kan daning....Shine a gaba su Haruna na bayanshi, 'kasa nayi da kaina tare da risinawa nace" Ranka ya dade Barka da asubah." Banza yayi mun ya wuce benansa, a sanyaye na dago kaina muka hada ido da Haruna ya'ke nayi nace"Haruna kun tashi lafiya."? Yace."Lafiya lau Sumayya ina fata kema kin tashi lafiya."? na amsa da lafiya lau alhmdullhi." Har zai bar gurin sai kuma ya tsaya yace."Sumayya baki karanci damuwa a fuskar Yarima ba."?
Girgiza kaina nayi ba tare da na kalleshi ba nace"Banga komai ba ai ka san shi ba'a gane farin cikin sa da 'bacin ransa tunda kullum fuskarsa a murtuke take da rashin fara'a."
Yace."Hakane to amma yana da kyau mu had'u gabadayanmu muje mu sameshi mu tambayeshi ko munyi masa laifi sai mu bashi hakuri." Shuru nayi ba tare da nace komai ba na cigaba da ayyukana.
Yace."Kinyi shuru bakice komai ba." Nace"To hakan yayi muje." Haruna ya kalli Isa da Hamza yace."Shawarata tayi ko." ? duk sukace tayi muje mu sameshi mu tambayeshi ko munyi masa laifi sai mu bashi hakuri.
Jirana sukayi na gama gyara daning sannan muka hau saman nashi.

Yana kwance cikin bargo yace."Kowaye ya turo kofar, a bude take." Haruna ya bude kofar dakin muka shiga gabad'ayan mu kanmu a kasa muka ajiye gwiwowin mu a kasa gaishe shi muka farayi kafin mu fara neman afuwarsa duk da bamu san laifin da mukayi ba.

Shuru dakin yayi bayan mun gama magana uffan bece mana ba yana kwance cikin bargo fuskarsa na kallon rufin dakin.
Haruna yace"Ranka ya dade a gafarce mu."! Gyaran mirya yayi ya juyo yana fuskantar mu, sunkuyar da kaina kasa nayi ganin fuskarsa a hade gashi kwayoyin idanunsa sun sakeyin jawur! "Babu wani abu da kukayi bana jin dadi ne shiyasa kuka ganni haka da rashin kuzari."
Haruna dasu Isa suka shiga damuwa dajin furucinsa ni kuwa ko gezau banyi ba tunda nasan karya yake kawai ya fadi hakane domin kare kansa, sannu suke masa tamkar bakinsu yayi tsayi, nima sai nabi ayarinsu na dinga yi masa hannu ina rokon Allah ya bashi lafiya.

Gyaran murya yay a karo na biyu yace."Kuna iya tafiya." Haruna yace."Ranka ya dade sai zuwa anjima za kayi wanka ko kuma yanzu na hada maka ruwan wankan." ? girgiza kansa yay yace."Bari anjima ka shigo ka had'a min inaso nayi bacci yanzu." Yace."To godiya nake ranka ya dade a tashi lafiya." Mik'ewa sukayi da niyyar fita, nayi kasa da idanuna ba tare da na kalleshi ba nace"Ranka ya dad'e yana qarko na shirya danning ina nufin gurin cin abinci komai ya kammala idan baka bukatar zama a daning din sai kayi magana na kawo maka nan."
Shuru yayi min, jikina ya bani kallona yake, aikuwa ina dago kai muka had'a ido, a maimakon ya ji kunya na kamashi yana kallona sai ma ya sake k'ureni da jajayen idanunsa dake bani tsoro.
Yun'kurawa nayi zan tashi naji maganarsa a dashe "Ki kawo min nan." na risina da fadin"angama ranka ya dade." da sauri na juya domun fita daga dakin......kallo ya bita dashi yana jin yanda gabansa ke miqewa hannu yasa ya danne jijiyar tashi yana jan tsaki a fili yace."Sabida rashin adalci ki rasa a inda zaki nuna kwad'ayin ki sai a inda be dace ba mtwww! tsaki yaja mai k'arfi yana danneta ita kuma sai miqewa take.

Ina sauka qasa na samu 'Yan uwanshi Shatima da Maddibo har'kasa na durkusa na gaishe su, suka amsa min a sake mussaman Shatima sai murmushi yake min, wuce su nayi da sauri na nufi kicin na dauko wani tire na silver mai fad'i dainng din na nufa na shirya kayan break fast din akai na dauka a nutse na nufi saman da tire din a hannuna

Abin mamaki! samunsa nayi a zaune shida 'yan uwan nashi suna hira, a nutse na ajiye tire din a gabanshi, kai a sunkuye nace"Dan Allah ina neman alfarama."
"Wace irin alfarma." yafada ba tare da ya kalleta ni ba." naji dadi sosai da bai shareni ba nace"Zanje in duba dawakai kasancewar aikin babana kenan to tunda ya kwanta rashin lafiya na dawo da dawaniyyar hannuna bayan nan inaso zan zauna a gurin karatu."

Jim yayi na minti biyu yace."Kije." cikin jin dadi nace"Nagode ranka ya dade." yunkurawa nayi na mike tsaye da fadin"A tashi lafiya." babu wanda ya amsa min a cikinsu. da sauri na kama hanyar fita daga dakin.
Shatima ya kalli Moddibo da fad'in "Wannan yarinyar tana da dirin jiki mai kyau amma kuma bata da wani kyau gata 'baka."
Moddibo dariya yay yace."Kai ina ruwanka da muninta idan biyan bukata nake nema ni bana duba muni ina duba abinda zai gamsar dani." Dariya sukayi tare da tafawa a tsakaninsu, Haushin abinda suke yasa ya mike ya nufi toilet yana jin wani irin d'aci! a cikin ranshi, ashe dai bashi kadai ke ganin kyawun jikin yarinyar ba, har da sauran mutane yaji takaicin yanda Shatima ke kwarzanta kyawun dirin jikinta, brush yay ya fito da fuska a had'e.
kan kafet din ya zauna gami da tankwashe kafafunsa, a nutse ya tsiyaya bak'in tea a cup ya shiga kur'ba a hankali a hankali yana sauraran hirarrakin dasu Shatima keyi mafi akasari hiran ta 'yan mata ne, cup din tea ya ajiye a nutse ya bude wata silver farfesun zallan naman rago da dankali ne a ciki yayi kyau sosai sai 'kamshi yake Yaji yana sha'awar shan farfesun ya hada da bread a nutse ya zuba a plate ya kallesu da fadin"Bisimillah." Moddibo ya girgiza kanshi da fad'in" Ni dai Alhamdullhi ban san Shatima ba." Shatima dake duba wayarsa yace."Nima a koshe nake wallahi." Ba tare da yace komai ba ya fara shan farfesun yana had'ashi da bread....Modibbo ajiyar zuciya ya sauke ganin yana shan farfesun wani farin ciki ya cika masa zuciyarsa, dauke kansa yay suka cigaba da magana da Shatima.

Wani irin tari ne ya sarqe shi ya ajiye bread din hannunsa yana riqe kirjinsa tari yake sosai idanunsa sun cika da ruwa. Shatima ne yay saurin miqa masa ruwa ya kar'ba yana kokarin sawa a bakinsa ruwan na dawowa, sai kawai ya ajiye goran ruwan ya danne kirjinsa yana cigaba da tarin cikin galabaita ya mi'ke tsaye! sai suma suka miqe cikin tashin hankali suna rirri'keshi ya fadi a gurin, jini ne ya biyo bayan tarin da yake.......A gigice suka rufu a kansa suna k'okarin mikar dashi zaune.

Fitowa ta kenan daga gurin Dawakai Haruna ya karaso inda nake hankali a tashe yace."Sumayya Yarima Ali bashi da lafiya bayan fitarki daga sashen Tari ya sarqeshi ya dinga aman jini."

Kirjina na dafe cikin tashin hankali nace"Haruna wane irin aman jini kuma."? Yace."Aman jini dai da kika sani Sumayya yanzu haka sashen nasa a cike yake da 'yan uwa dan har maimartaba ma yana gurin ana bunkice akan abincin da yaci wallahi ke kadai nake tausayawa."

Kallonsa na shiga yi a tsorace nace"Haruna ni kuma meye laifina da kake tausaya min." Yana kokarin magana Hamza ya karaso gurin yace."Ke! Sumayya kizo ana neman ki a sashen Yarima." Naji gabana ya fad'i! Magana nake so nayi amma bakina yayi min nauyi, dakyar na iya furta kalmar innalillahi wa'ina ilaihi raji'un." nabi bayansu domin zuwa jin kiran da ake min......
*BINTA UMAR ABBALE*

*Kuyi sharing👏🏻*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *[email protected]*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_

*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
25&26
Cikin tararrabi gami da fargaba muka shiga falon, gimbiya Lawisa ce a zaune akan kujera muna shiga ta mike tsaye da sauri tana watsa min mugun kallo! sunkuyar da kaina qasa nayi nace"Ranki ya dade barka da safiya." Hannu ta daga min cikin tuhuma tace"Me kika zubawa Yarima acikin farfesu wanda ya janyo masa aman jini."?
Gabana na faduwa nace"Ban zuba masa komai ba ranki ya dade." Marina tayi tana huci! tace"Zaki fad'a ko sai kin fuskanci hukunci mai tsauri."! Hannu na dafe da kuncina nace"Iya gaskiyata na fada wallahi ban sa masa komai ba." Za tayi magana Haruna ya katseta da fadin"Sumayya ki hau sama Maimartaba na bukatar ganinki." naji jinin jikina ya tsinke gabad'aya neman yawu nayi na rasa a bakina, salo salo na nufi saman ina adduar akan Allah ya fitar dani.

Lokacin dana shiga dakin sai naji na sare da al'amarin dan ganin yanda dakin ke ciki da jama'a gabad'ayan su suna tsaye a kansa yana kwance a bed kansa a cinyar mahaifiyarsa bakinsa rufe da wani abu da ya nuna alamun an tare jini likita ne a tsaye a kansa.
Sunkuyar da kaina kasa nayi na zube gwiwata a kasa nace"Barkan ku da wannan lokaci." Gabad'aya suka juyo suna kallona.......muryar Moddibo naji cikin tsawa yace."K'araso ciki munufaka." Na yun'kura da sauri na karasa gabansu na tsuguna! Moddibo zai sake magana maimartaba ya katse shi.
Shuru dakin yayi kafin maimartaba ya fara magana kamar haka.
"Sumayya wace irin guba kika sakawa Yarima a cikin abincinsa inaso ki fada min wanda ya saki zuba masa guba a cikin masarautar nan."! hawaye suka k'wace min nace" Na rantse da wanda raina ke hannunsa ban zuba masa komai ba, lafiya lau na gama abinci na bashi kafin na tafi gurin mu."

" 'Karya kike munufuka akwai abinda kika zuba masa wato kina so ki kashe ki ko."? Moddibo ne ke wannan maganar kamar zai kai min duka
Chapter 12 · 0% Book details