← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 90

Sashe 24

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikina ne yayi sanyi jin furucinsa sai na tuno da nasihar mahaifina kullum sai ya umarce ni akan bin umarnin masarauta Yarima Ali ya nuna min cewa shi d'an sharri ne zai iya shirya min wani sharrin reshe ya juye da mujiya ni da iyayena mu muzanta a masarauta wannan tunanin da nayi yasa gabadaya naji gwiwata tayi sanyi da hukuncin da nayi aniyar dauka a kansa.

"Muje inda kika zubar min da apple ki dauko min kayata. maganarsa ce ta dawo dani tunanina, cikin rashin mafita nayi hanyar fita ya biyo bayana.

Sai dana isa gurin da kamar minti biyar ya karaso kwata-kwata yanayin tafiya ta da tashi ba daya bane ni ina da zafin nama yanayin girman jikina bai hanani kazar-kazar ba dalilin da yasa kenan da nasa hannu a aiki nake saurin gamawa

Karasowa yayi yana bin gurin da wani irin kallon k'yank'yami! sandar dana tona sharar dazu yanzu ma ita na dauka na fara yunkurin tona sharar domin dauka masa tsiyarsa......Hannu yasa ya kar'be sandar ya jefar da ita can nesa, babu fara'a a tare dashi yace." Hannu zaki sa ki dauko.'' Na dinga kallonsa ina jin takaicin abinda yake min.

kasa sa hannuna nayi dan nima k'yank'yami ne dani sai kawai na sunkuyar da kaina zuciyata kamar ta tsage saboda bakin ciki......"Ke! kin barni a tsaye rana na dukana ga kud'aje na bin jikina, kisa hannu ki dauko min apple dina ko kuma naci mutuncin ki anan gurin.

Cikin takaici nace"Ai da zan sa apple din ba hannuna nasa na tona sharar ba sanda nasa kuma ka jefar da ita." Babu ruwana da sanda kika sa yanzu hannu zaki sa ki dauki min." yafada yana kusantoni. ganin kada mu aikata abu irin na dazu yasa nayi shahadar sa hannuwana a cikin sharar ina tonawa, can na dauko ledar apple din har ta soma jikewa da ruwan k'azanta.....Mika masa nayi da fadin"Gashi.'' Ya kai minti biyu yana kallon ledar apple din ya tsine fuskarsa yayi kafin ya tsartar da yawu ya juya da sauri ya bar gurin.....kasa'ke nayi da ledar a hannuna ina tunanin abinda yake nufi da hakan da yayi.

Hawayen takaici da bakin ciki ne suka shararo min! nasa hannuna ina gogewa wasu na sake zubowa. gaskiya duk inda ake neman mara mutumci guy nan ya kai, ashe dan ya tozartani ya wulakanta ni yasa yace lallai sai nasa hannuna a cikin shara! kuka nake sosai abubuwa sun taro sunyi min yawa gabad'aya ni yanzu tsoro ma yake bani wallahi tunda ya nuna yana sha'awata nake jin fargaba da tsoron abinda zai biyo baya a tsakanimu, yanzu ta wace hanya zan kare kaina daga sharrinsa, shuru nayi ina tunanin karbar shawarar da zuciyata ke bani, zan shiga d'aure masa fuska daidai da 'kwayar zarra ya daina ganin sassauci a tare dani, duk sanda kuma ya sake yunk'urin kai hannunsa jikina to zanyi iyakacin kok'arina na 'kwaci kaina, da wannan tunanin na bar gurin, ina sake karfafawa kaina hukuncin dana yanke.

***
Tsakankanin kwana ki biyu aka kwance masa bandejin dake nannad'e a kansa alhamdullhi aiki yayi kyau dan goshin sa bai nuna wani mummunan tabo ba gurin da yayi rami ya ciko sosai sai abinda ba'a rasa ba, a ranar asibitin cika yay da 'yan uwansa suka kewaye shi kowa na nuna murna da farin cikinsa dangane da samun lafiyarsa, Lawisa na kusa dashi sai kula take dashi tana bashi abubuwan ci da suka kawo masa, gabadaya kasa nutsuwa nayi dan ina jin tsoro kada yaje yaci abinda zai cutar dashi, mikewa nayi a sanyaye na nufi d'akin, har nasa hannuna a jikin kofar sai kuma na cire tsoro nake ji na shiga dakin wani yaci min mutunci, a sanyaye na juya da niyyar komawa na zauna aka bud'e dakin da sauri na juya baya gabana na faduwa, Muddibo ne ya fito daga dakin fuskarsa babu walwala yace.......
*BINTA UMAR ABBALE*

*Na kudi ne*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal gruop#300 account 0542382124..Binta umar gtbank...idan katin zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta whasap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
49&50
Cikin nutsuwa na 'karasa na sameta inda take zaune, zama nayi kaina a kasa nace"Barka da wannan lokaci ranki ya dade jakadiya tace kina nema na."

A nutse ta gyara zamanta tana kallona cikin kulawa da kwantaccan murmushi a fuskarta tace"Barka kadai Sumayya ina fatan kun dawo gida lafiya." A nutse nace'Lafiya lau ranki ya dade." zamanta ta sake gyara tana kallonta tace." a gaskiya naji dad'in n ganin babana lafiya lau yayi ki'ba ya k'ara kwarjini idan ba'idona ne ke min gizo ba sai nake ganin kamar har haske ya k'ara, gaskiya Sumayya kin iya kiwo kin kula min da babana yanda nake so." Cikin farin ciki da jin dadin kalamanta kalleta nace"Godiya nake ranki ya dade.'' Tace"Ai ke zanyi wa godiya Sumayya dalilin da yasa ma kenan na kira ki domin na nuna miki jin dad'ina akan abinda kikayi min sannan na baki kyautar dana tanadar miki."

Murmushi nayi cikin nuna farin cikina da yabawar dana samu daga gurinta nace"Ranki ya dade sabida Allah nake kula da Yarima badan kyauta ko yawancin wani abu ba duk abinda nake masa saboda Allah nakeyi bayan nan kuma ai ya cancanta a kula dashi a hidimta masa.

Tana murmushi tace"Duk da haka dai Sumayya baki ji bahaushe yana cewa "yaba kyauta tukwici ba." Yar dariya nayi ina kara sunkuyar da kaina kasa....Tace"To kingani dole in nuna miki farin cikina a zahiri sannan nayi miki ihsani dan kiji dadi."

Nace"To godiya nake "Ranki ya dade." Wata madaidaiciyar akwati dake gefanta ta janyo tace"Ki dauki akwatin nan Sumayya duk abinda ke ciki naki ne na baki kiyi ado dashi a ranakun juma'a da sauran muhiman ranaku."

cike da murna da farin ciki na dubi akwatin sai kyalli take tana daukar ido nace"Kai masha Allah ranki ya dade hakika naji dadin wannan kyauta da kikayi min ina rokan Allah ya kare ki daga sharrin masu sharri ranki ya dade Allah yaja zamanin ki ya kara miki lafiya da nisan kwana." Da murmushi a fuskarta ta amsa da ameeen kafin ta d'ora da fadin" Kina iya zuwa ki aje akwatin a gurin ku kije sashen babana ki duba idan yayyunsa sun bar sashen ki fito da dukkanin abinda suka kai masa mutukar naci ne kada ki bar komai ki fito dashi a fitar dashi can waje a zubar."

Da sauri nace"Insha Allah yanzu zan cika umarninki ranki ya dade." Mikewa nayi da akwatin a hannuna nayi mata sallama.....sauri sauri nake tafiya da akwatin a hannuna har na isa sashen mu, ko zama banyi ba na aje akwatin Tambaya tace"Wannan akwatin fa ? kin shigo kina gaggawa ina fata dai lafiya."

Ina kokarin fita nace"Lafiya lau zanje sashen Yarima na dawo sai nazo mu bude akwatin dana ajiye." Ban jirayi amsar ta ba na fita da saurin gaske, gabadaya hankalina ya tashi da jin cewa tun dazu yayyunsa na sashensa, sai na dunga zargin mybe ma sun samu nasara a kansa watakila na shiga na tarar da gawar sa ko kuma na tarar dashi cikin mawuyacin hali, idanuwa na ne suka taru da ruwan hawaye nace"Insha Allah babu abunda ya sameshi." ........koda na shiga falon su Haruna na samu suna aikace aikace! ajiyar zuciya na sauke ina rarraba idanuna a falon, can na hango tarin warmas da kuloli a shirye akan kilishin da yake zama dan hutawa, ba tare da shawarar kowa ba na nufi gurin, ban yarda na zauna masa a kilishi ba gefe na tsuguna na soma binkicen abincin......Motsin saukowar sa yasa nayi gaggawar kallon benan gabana ya yanke ya fadi ganin yanda yasha kunu yana min kallon tuhuma, da sauri na mike daga gurun can gefe na matsa kaina a sunkuye nace barka da fitowa.

ko kallona beyi ba ya zauna a gurin, su Haruna suka karaso suka gaisheshi suka fita, kallona yayi a watse yace."Me kika tsuguna zakiyi min akan abinci ko zaki zuba min guba ne."

Idona na zuba masa ina mamakin maganarsa....Yace."kin tsareni da ido ko nayi 'karya ne."? girgiza kaina nayi ina danne 'bacin raina nace." "Zan duba ne domin na tabbatar da ingancin su." Ya 'kalle ni yana girgixa kai yace."Wato ke ba zaki daina saka kanki a kan abinda be shafeki ba ko."

Kaina a kasa nace"A gafarce ni ranka ya dade." tsaki yaja da fad'in" Ki bud'e ko wanne abinci ki zuba min cokali daya a plate yanda nayiwa kowacce al'kawarin cin abincinta to ba zan sa'ba ba."

Cikin bin umarninsa na tsuguna a nutse na fara budewa kular farko fatan doya ne wanda yaji kifi da da curry sai kamshi yake yi ido na tsira a cikin fatan sai naga kamar curry yay yawa da alama an zuba magani a ciki dan ban yarda dashi ba, kular na matsar gefe......tsawa! ya buga min da fadin"Meye haka zaki bude kuma ki matsar ko ba cewa nayi ki zuba min ba." Yanda ya tsattsare ni da ido yasa da sauri na de'bo fatan cikin cokali nasa a plate din.....Daya kular na bude.......Miyar hanta ce da taji kayan lambu itama sai kamshi take amma kuma ba tayi kyau a ido ba tayi b'aki kamar ba'a sa kayan miya a ciki ba.
Girgiza kaina nayi nace"Ranka ya dade kada ka hada abinci kala kala kaci cikin ka ya b'aci ina ganin kaci guda daya ya isa."

"Ina ruwanki ? cikin ki ko nawa."? abinda ya fada kenan yana tsatstsare ni da ido, cike da takaici na bude kular shinkafar na zuba a plata kana na zuba miyar hantar a gefe.
Kula ta uku na bude farfesun dankalin turawa ne da kifi a ciki sai daya kular dake dauke da supargetti (Taliya) plate na dauka na zuba a nutse na jere su a gabansa." kallonsa nayi ya wani hard'e kafafu nace"Na gama had'awa."
Warmars din ya duba da fadin"Kin bude wannan ne."?
Nace."Ka gama cin wa'innan." bece min komai ba ya gyara zamansa, barin gurun nayi ina jin faduwar gaba tsintar kaina nayi dayi masa adduar kariya daga Allah.
Chapter 24 · 0% Book details