Sashe 69
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Girgiza kaina nayi nace"Gaskiya kam nima na gazgata irin kaunar da kake min insha Allahu nayi maka alkawarin baka cikakkiyar kulawa." murmushi yayi yace."To nagode sosai yanzu sai da daddare zakiyi min irin na jiya ko."? rufe fuskata nayi da hannuna! kunyarsa ce ta rufe ni janyo ni yayi jikinsa ya rungume tsam! yana shafa gashin kaina! kwanciya nayi a jikinsa ina sauke numfashi, a hankali yace."Kince na bari kuma kinyi kwance a jikina wallahi duk kin tayar min da hankali.....mikewa nayi ina gyara towel din jikina nace"Ka bari sai da daddare zan kula da kai yanzu ka tashi ka kimtsa jikinka kaje ku gaisa da Mamma.".
Mikewa yayi yace."Ai tare zamuje kema ki gaisheta." cike da farin ciki nace"Gaskiya nayi farin ciki dama kwana biyu nayi kewarta." Yana kokarin fito da kaya daga wardrobe yace."Na manta ban fada miki ba jiya nida Shatima munje can bangaran mahaifanki munyi gaisuwar surukai." Murmushi nayi nace"Amma naji dadi sosai ina fata suna nan lafiya."? Yace."Lafiyarsu lau yana da kyau idan kin fito daga gurin Mamma kije ku gaisa ko."
Cikin farin ciki nace"Nagode.'' Tsaf! muka shirya muna fitowa falo muka ga mata a zaune!! gabana ne ya fad'i!! nayi saurin sunkuyar da kaina kasa ina mamakin abinda ya kawo ta.
A nutse muka zauna kan kujera muna gaisheta! ta amsa fuska a sake sai dariya take tana tsokanata ni dai gabadaya hankalina bai kwanta da ita ba..
A nutse yace."Ina fata baki dad'e a zaune zaman jiran mu ba." girgiza kanta tayi tace"Ban wani dade sosai ba nazo na samu hadimai na gyare-gyare sune suka tabbatar min da cewar kuna ciki baku fito ba shiyasa na zauna zaman jiran fitowarku.".
Ajiyar zuciya ya sauke yace."Ina fata dai lafiya." Cikin yar dariya tace"Lafiya lau! nazo ne domin na kar'bi zanin gadon da kuka kwanta a kai ana so ayi shela saboda kowa ya tabbatar da nagartar matar daka aura, alhamdullihi dai Lawisa ta fitar iyayenta kunya."
Tun kafin ta 'karasa maganar gabana ya dinga bugawa! wannan wace iriyar rayuwa ce ace da sassafe azo ace ka bada zanin gado, a gaskiya wannan al'adar bata da kyau! haramune fallasa sirrin aure.
Uwargida Huwaila tace"Ali ya naga kayi shuru ne ina fata dai wannan yarinya ba fanko bace."!!!! Kallonta yayi a cinkushe! yace."Wai don Allah hajia ba zaku watsar da wannan al'adar ba! meye amfanin ta"?
Cike da mamaki! tace"Al'ada mai tsohon tarihi da muhimanci kake cewa masarauta ta watsar! haba Aliyu! wannan magana sam bata dace ta fito daga bakin ka ba tunda dai kasan tun kafin a haifeka wannan al'ada take shin wai kodai baka sameta cikakkiyar mace bane."!!! A fusace! take maganar..
Yace.''Hajia wannan yarinyar bana kokwanto a kanta koda jini ko babu jini Sumayya kamila ce ba zata sarayar da budurcinta a hanyar banza ba, inaso na sheda miki cewa ni Ali ban taki Sumayya ba saboda tana cikin rashin tsarki koda mu'amula ta aure ta shiga tsakanina da ita to nayi al'kawarin babu me ganin sirrina."''
Cike da mamaki take kallonsa kafin tace"Wannan dai ba magana bace Ali idan kana so jama'a su dauki matarka da mutunci to ka dauko min zanin gadon da kuka kwana a kai a duba aga zahirin abinda ke faruwa dan gaskiya ni ban yarda da maganarka ba kawai kana kareta daga barin surutun mutane."!
Kuka ne yake kokarin kwace min da sauri na bar gurun ina shiga daki hawaye suka wanke min fuska zubewa nayi kan gado bakin cikin duniya ya sheni........ shikkenan kuma yanzu za'a sani a bakin duniya! tunda na ganta dama nasan ba alkairi ne ya kawota ba, kwanciya nayi ina tunanin abinda zai faru anan gaba.
Rai a b'ace! ya shigo dakin ya tsaya a kaina da fadin"Tashi muje." Girgiza kaina nayi tare mi'kewa zaune.
Yace."Bangane abinda kike nufi ba, nace ki tashi muje sashen Mamma kamar yanda mukayi niyya!
Ina magana hawaye na zuba nace"Kaje kawai ba zan iya zuwa ba." jikinsa ne yayi sanyi yace."Kiyi hakuri ki daina kuka koda mutanan duniyar nan za suga duhun ki akan wani abu ni nayi miki alkawarin baki kariya sai inda karfina ya 'kare! na riga nagane abinda suke nufi to koda nayi auratayya dake babu wanda zai ji ya gani wannan banzar al'adar ba dani ba."
A sanyaye nace"Ni dai gwara ka nuna musu domin su tabbatar ni budurwa ce bana so mutane suyi min wani kallo na daban.'' Tsaki yaja ba tare da yace min wani abu ya hau duba wayarsa.
Wayar ya kara a kunnansa yana gaisheta, jin muryarta yasa na nutsu ina jinta tana tambayata yace."Gata nan a kusa dani yanzu zan kawo miki ita ku gaisa." cikin jin dadi tace."To nagode Babana." Yace."Mamma yanzu nan Uwargida ta fita daga sashena wai tazo kar'bar zanin gadon da muka kwanta a kai."
Fulani tace"Ikon Allah yanzu da kanta taje a maimakon ta tura Jakadiyarta." Yace."Mamma nifa wannan tonan asirin ne bana so tazo tana wasu maganganun da basu dace ba! raina ya 'baci sosai da abinda tayi wannan dalil.......Katse shi tayi tace"Babana sai wata irin magana kakeyi shin wannan yarinya da budurci ka sameta ko kuwa."? kai tsaye yace."Nifa babu abinda ya shiga tsakanina da ita."
A d'an sanyaye tace"Saboda me Baba na."? yace."Sabida bata da tsarki shiyasa! Fulani shuru tayi tana nazarin maganarsa! tace"Babana sai dai kayi hakuri da wannan abu haka al'ada take tun zamanin iyaye da kakanni banji dadin faruwar wannan lamari ba to amma babu komai duk ranar da Sumayya tayi tsarki ka kwanta da ita inaso ka bada zanin gadon a duba sheda.
Cike da takaici yace."Mamma bana jin zan iya bayyana sirrina.''' cikin mamaki tace"Me yasa ka bayyana sirrinka da Lawisa babana yanda kake hanya-hanya yasa jikina yayi sanyi akan yarinyar nan! duk da bana kokwanto a kanta amma rashin amincewarka yasa ni zargin wani abu.
Jin abinda take fada yasa jikina ya mutu lallai ina cikin kalubale mutukar ba'a ga jinin amarcina ba! Yace." Mamma bana so na dinga jayayya dake akan maganar nan dan Allah ki cireta a ranki Wallahi ko haufi ba nayi zan samu budurci a tare da sumayya saboda haka dan Allah ki bar wannan magana.
Tace."To shikkenan na bari amma yanzu yanzu zanyiwa tufkar hanci sabida bana san surutai da qananun maganganu irin na mutane Zan kira Ita uwargidan mu zauna akan maganar......Yace."Yawwa haka shine yafi dacewa." Insha Allahu yanzu zamu shigo da Sumayya ." tace"To shikkenan sai mun shigo." Sallama sukayi da ita ya kashe wayar yana kallona.....wasa na shiga yi ya yatsuna, yace." Hankalinki ya kwanta ko."? kaina na daga masa, yace." To kije ki wanke fuskarki ki sake sabuwar kwalliya bana so muje gurin Mamma ta fahimci wani abu." mi'kewa a sanyaye na nufi toilet ina addua akan mak'iyana dake cikin masarautar..........
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKAWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊ðŸ?)
94
A nutse na fito jikina nad'e da lifaya, mirmushi yayi ya mike tsaye kallon da yake min yasa duk na tsargu, d'an harararsa nayi nace"Naga kana kallona ko da akwai matsala ne."? still da murmushi a fuskarsa yace."Baki da makusa my love kinyi kyau har na kasa tantance tsakanin keda Lawisa wace tafi iya ado da kwalliya." shuru nayi dan bana so muna magana yana kiran sunanta, hannuna ya rike muka fita, nan muka samu hadiman dake gurin suna ta aikace-aikace ganinsu besa yayi yunkurin sakin hannuna ba a haka muka dinga ratse su yana amsa gaisuwarsu dan ni kunya ce tasa na kasa dago da kaina na kallesu.
Tana hakimce akan kujera tayi ado sosai ni kaina dana ganta sai dana razana saurin daidaita nutsuwa ta nayi muka karasa inda take hannuwan mu a hade, sai da zamu zauna ne ya sake ni, kallonmu tayi babu yabo babu fallasa a tare da ita, a nutse nace"Ranki ya dade barka da safiya kin tashi lafiya."? babu walwala ta amsa. falon yayi shuru na kusan minti biyar kafin yayi gyaran mirya dukkaninmu muka kalleshi yace."To Alhamdulillahi nagodewa Allah daya nuna min wannan rana mai albarka a tare dani daku bakidaya ina rokon Allah ya tabbatar mana da alkairi yanda Allah ya had'amu zama a duniya ina rokon Allah ya hadamu zama a aljannar firdausi." Nice kawai na amsa da ameen, ya cigaba da cewa" Lawisa da Sumayya dukkanin ku na aureku ne da ra'ayin kaina saboda haka inaso na tabbatar muku da cewa babu wacce tafi wata a gurina sai wacce tafi kyautata min gami da bin umarnina! ina sonku ina kaunarku kuma ina bukatar ku zauna lafiya da juna, ke Lawisa kece babba yana da kyau ki kama girmanki bani da matsala da Sumayya domin nasan halinta zata girmamaki ta kuma mutuntaki! ki ajiye maganar sarauta a gefe bana so ki dinga nuna mata asalinki ki dinga daukar kanki daidai da ita Sumayya ba mutuniyar banza bace." Wani irin kallo Lawisa take masa ya za'ayi ma ta daidaita kanta da baiwa abinda ba zai t'aba yiwu bane."
Ya cigaba da cewa" Kowacce na zaune a gurinta ban amince ku dinga ziyartar junanku ba sai da k'wakkwaran dalili ina ganin hakan shine maslaha a gare mu baki daya. daga karshe nake mana adduar fatan alkairi tare da rokon Allah ya dawwamar mana da zaman lafiya a zamantakewar auranmu."
Cikin nutsuwa na amsa da "Ameen ya rabbi." Ajiyar zuciya ta sauke a cinkushe tace"Naji ni kayi min fada amma ita ba kace mata komai ba.''
Cikin kulawa yace."Bangane abinda kike nufi ba."? "Kace na dauki kaina daidai da ita na zauna lafiya da ita ka nuna min muhimancinta amma me yasa ita baka nuna mata cewa ina da muhimanci a tare da kai ba."
Shuru yayi yana kallon kasan kafet! ni kam mamaki ta bani na dinga kallonsa ta gefan ido ina jiran naji abinda zai ce, a nutse ya kalleni yace."Ke Sumayya Lawisa nada mahimanci ba sai na fada miki ba ki bata girma a matsayinta na uwargidanki."
Murmushi nayi nace"To insha Allah zan cigaba da bata girma da muhimanci, ranki ya dade kada ki damu ni ba zan raina ki ba Insha Allahu."
Murmushin dole tayi ta kauda kanta gefe, yace."Lawisa kin gama kwana biyun ki yau bangaran Sumayya zan tare nayi mata nata kwana biyun."