← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 90

Sashe 46

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya keda kika fita da littafin keda Allah idan kina so ki biya ga yanda abin yake Vip gruop#600 normal gruop#300 account... 0542382124...Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta whsap da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
78
Tun bayan tafiyar Haruna na tsinci kaina da fad'uwar gaba, guri na nema na zauna ina kiran innalillahi wa'ina ilahi raji'un domin na tabbata itace zata saukar min da nutsuwa, na dauki kimanin minti ashirin a zaune a guri daya kafin na dan samu sassauci a sanyaye na mike na nufi bandaki bokitin wanka na dauko naja ruwa a rijiya na cika bokitin da ruwa wanka zanyi ko naji sassauci dauka na shiga bandakin dashi............Ina fitowa na samu Tambaya ta shigo tana zaune a tsakar gida tana hutawa, nace"amma yau kun gama aikin da wuri." tace."Eh yau aikin yayi sauri nima nayi mamakin haka ai yau mutumin ki akayi." A sanyaye nace "Wake da shinkafa." Kanta ta d'aga min. na kalleta sosai sai naga kamar tana da damuwa! nace"Tambaya kamar akwai abinda ke damunki." Tace"Wallahi tun safe gabana yake faduwa." Shuru nayi ina kallonta tace."Allah yasa dai alkairi ne amma faduwar gabar ya tsananta!! ajiyar zuciya na sauke nace"Nima haka tun dazu gabana ke faduwa sai dai ki yawaita kiran innalillahi insha Allahu babu wani abu da zai faru."
Tace."Insha Allahu. daki na shiga ina addua a cikin zuciyata, na shirya jikina, dadduma na hau na tayar da sallar azuhur, bayan na idar fitowa nayi na sameta a kwance a rumfa bacci na nema ya dauketa, nace"Tambaya ai gwara ki tashi kiyi wanka kada kiyi bacci lokacin sallah yayi." Tace."Ai naji ba'ayi kiran sallah ba shiyasa na d'an kwanta na matse." nace"Yanzu za'a kira daya da rabi." Kiran sallar ne ya katseni nace"Kinji ko.'' mikewa tayi tana hamma, nace "ai zafi akeyi kawai kiyi da ruwan rijiya nima dashi nayi." tace."aikam dai waye zai sawa kansa ruwan zafi yanzu.
Mikewa tayi nayi sauri fita na zuba mata ruwan wankan kicin na shiga na d'ebo abinci a plate na zauna a tsakar gidan, loma uku kacal nayi naji gabad'aya abincin ya fita daga kaina, duk sona da wake da shinkafa naji bana sha'awa, guri guda na zubawa ido......"Sumayya." muryar babana naji a kaina. da sauri na dago ina kallonsa yace."Me yake damunki kika zabga tagumi." Da sauri nace"babu komai baba." zama yayi kusa dani yace."Sumayya akwai abinda ke damunki tun dazu nake tsaye ina miki magana kina can tunani kinsa abinci a gaba kin kasa ci."
Hawaye ne suka 'kwace min. Lawi jikinsa yayi sanyi ganin yanda take kuka.
A sanyaye yace."Ki fada min damuwarki."? hanci na shaqa nace."Baba wallahi tun dazu gabana ke fad'uwa sai nake ji a jikina kamar wani abu zai faru dani."

Lawi jikinsa yayi sanyi yace."Sumayya dukkan tsanani yana tare da sauki babu abunda zai faru sai alkairi ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa a duk lokacin da gabanki ya fadi ki dinga addua kinji ko." Hawaye nagoge yay murmushi cikin sigar so ya kwantar min da hankali yace."Bari na zauna na taya ki cin abincin." murmushi nayi nace."Aikuwa naji dadi baba ka zauna muci tare ina so na samu albarka." hannunsa yaje ya wanko yazo ya zauna kusa dani a nutse yace."To saka hannu muci. ina murmushi nasa hannuna a nutse muka fara cin abincin Tambaya ta fito daga bandaki ta same mu mirmushi tayi ta shiga daki domin kimtsa jikinta, koda muka cinye abincin cewa yayi na bari ya dawo daga masallaci sai mu 'kara wani nace "to." ruwa na zuba masa a buta ya daura alwala ya fita.

To wajejan biyar saura na yamma na isa sashen Yarima na dinga wulkita idona a harabar gurun ina neman Haruna banganshi ba, Sai Hamza na gani a zaune a rumfar masu gadi suna hira, kai tsaye rumfar na nufa a nutse muka gaisa dasu.

Nace."Hamza ina Haruna ne."? yace."Sumayya tun safe rabona da Haruna amma Mika'il yanzu yake fad'a min wai sunje kaiwa Yarima abinci ofis."

Na kalli Mika'il cikin faduwar gaba nace"Kana nufin har yanzu basu dawo ba."? Yace."Eh wallahi basu dawo ba watakila ko Yallabai din ne yace su zauna su jirashi." ajiyar zuciya na sauke nace"Eh haka zata iya kasancewa ai yanzu zaka gansu tunda biyar ta kusa." Suka ce hakane, nace"bari na shiga ciki." suka ce "To sai kin fito." wuce wa nayi ina sauke ajiyar zuciya da godewa Allah.

To har na gama dukkanin ayyukana a shashen babu alamun dawowarsu na shiga mamaki mai tsanani dan idan ba wani gagarimun abune ya faru ba to Yarima baya kaiwa karfe shida a asibiti biyar yake dawowa ko biyar da rabi yau gashi har shida ta wuce ana dab da kiran sallar isha'i bai dawowa, gabad'ayanmu ma'aikatansa mukayi jugum-jugum muna Jimami, Mika'il yace."Bari kawai naje asibitin naga abinda ke faruwa ni dai nafi tunanin aiki ne ya rikeshi." Nace."Idan aiki ya ri'ke Yarima su kuma su Haruna me zai ri'kesu."? Hamza yace."Nima dai abinda na gani kenan." Mika'il yace."Bari dai naje insha Allahu babu matsala." Muna kallo Mika'il ya shiga mota ya tafi gabad'ayan mu muka zauna zaman jiran tsammani.

'Daya daga cikin ma'aikatan dake tsabtace asibitin ne yake shawagi a sa'ko da loko na asibitin da tsintsiya da mazubin shara a a hannunsa duk inda yaga leda ko takarda sai ya dauke, tun daga nesa ya hangesu a kwance k'udaje sai binsu suke, gabansa na fad'uwa ya isa gurin, ganinsu a sheme ido a kafe yasa ya tsorata a guje ya yar da mazubin sharar ya ruga cikin asibitin........Yana haki! ya shiga reception din, jama'a suka bishi da kallo, kai tsaye ofis din Yarima ya nufa, masu gadin gurin suka mike tsaye, tare shi suke yana yun'kurin shiga daya daga cikinsu ne ya buga masa tsawa da fad'in "Kai kada ka karya mana doka mana ka nutsu kafad'a mana abinda ke faruwa." Yana haki! yace."Babu lafiya a cikin asibiti nan can wajejan shuke-shuke naga gawarwakin mutane biyu."" Gabadaya jama'ar dake gurin suka tsorata jin abinda ya fada, gurin ya kaure da hayaniyar da tayi sanadiyar fitowarsa, kafin ma ya tambayi ba'asi suka fara sheda masa abinda ke faruwa. kafin kice kwabo gumi ya jiqashi, hanyar futa ya kama wasu daga ciki suka rufa masa baya masu tsoro kuwa tuni suka silale daga asibitin.

Magajin sarki hankalinsa yayi masifar tashi ganin su Haruna a sheme idanunsu a tsaye suna kallon guri guda, kallo daya yayi musu ya fahimce cewa sun dade da rasuwa, jikinsa ya dinga kyarma ya dinga nanata kalmar innalillahi wa'ina ilahi raji'un! hankici ya dauko ya goge gumin goshinsa ya dago kansa yana kallon jama'ar da sukayi dafifi a kansa, tsaye ya mi'ke ya umarci mutum biyu daga cikinsu akan suje su sanyo safa a hannuwansu domin su harhad'a kwanakun abincin................Jami'an tsaro da 'yan jarida ne suka k'araso gurin, kallonsu yake yana mamakin wanda yaje ya fad'a musu, suna zuwa gurin suka fara aikinsu sai bayan da suka gama daukar gawarwakin a hoto suka dawo da hankalinsu kansa, yana tsaye kamar mutum mutumi k'wayoyin idanunsa sun kad'a sunyi jajawur....."Yallabai ya akayi wannan al'amarin ya faru a cikin asibitin ka wanda muke mutukar alfahari da samuwarsa a wannan jaha tamu." ? Tambayar da suka jefo masa kenan dukkaninsu sun rufeshi had'e da kara wayoyinsu a gurin bakinsa.

Girgiza kansa kawai yake yana kallon Kasan gurin yayinda masu daukar hoto suke ta aikin daukarshi a duk motsin da zaiyi.....ya kai kimanin minti biyar yana kallon kasan gurin kafin ya dago kansa a nutse yace."Ni akayi nufin a kashe sai tsautsayi ya ritsa da wa'innan bayin Allahn kamar yanda ya kwanakin baya d'aya daga cikin bayina ya rasu a sakamakon cin abincin daya kasance abincin cina."

"Ranka ya dad'e " A gaskiya wannan al'amarin yana bukatar kayiwa mutane cikakken bayani shin ya akayi suna hadiman ka suke cin abincin daya kasance naka abun tambaya anan shine a ina za suga abincinka suci? ranka ya dad'e muna so kayi mana cikakken bayani."

Murmushi yayi wanda kana ganinsa kasan na nadama ne yace."Ni nake basu da hannuna." gabad'aya mutanan gurin suka zuba masa ido suna mamakin maganarsa, 'Yan jaridar kuwa caaa! sukayi a kansa, Girgiza kansa kawai yayi ya kalli ma'aikatansa ya basu umarnin su d'aure gawarwakin su had'a guri guda susa a mota sukai masarauta..........Daya daga cikin jami'an tsaron yace.''Yallabai akwai bukatar muje da kai station mu tattauna da kai."
Ba tare da damuwa ba yace "babu damuwa........ Gaba yayi suka rufa masa baya yayinda jan jarida suka bi bayansu a guje suna daukar hotonansu har suka shiga mota, da hannu ya kira d'aya daga cikin ma'aikatansa yace." Lallai a ajiye masa ragowar abincin da mamatan suka ci zaiyi binkice a kansa." Jiki a sanyaye ya amsa ya matsa daga jikin motar, suna daf da fita Mika'il ya shigo da mota, ganin dandazon jamaa harda 'yan jarida da motar 'yan sanda yasa Mika'il gabansa ya tsananta faduwa, da sauri yayi parking ya fito yana tambayar abinda ke faruwa, wanda ya fara ganin abun ne yayi masa bayani, Mika'il a gigice! ya nufi inda yaga mutane na fitowa, tun daga nesa ya hango abunda ke faruwa, yana karasawa ya zube gaban gawarwarkin da'aka gama dauresu, ihu! yake kurmawa yana dukan kansa Wani bawan Allah ya dafa kafad'unsa yana rarrashinsa yace."Ba ihu za kayi ba innalilihi wa'ina ilaihi raji'un zaka dinga fad'a." Mika'il ya dinga fad'in Kalmar innalilihi wa'ina ilahi raji'una da karfin gaske!

Cikin tsantsar tashin hankali Shatima ya shiga masarautar kai tsaye sashen Fulani ya nufa ganinta cikin nutsuwa yasa ya fahimci bata san abinda ke faruwa ba, gaisawa sukayi tana nazarinsa tace"Shatima ina fata dai lafiya dan ba haka na saba ganinka a hargitse ba." ajiyar zuciya ya sauke yace."Mamma lafiya inaso naga Maimartaba ne." Tace."Yau ba anan yake ba yana gurin uwargida." sallama yayi mata ya nufi gurin uwargidan
Chapter 46 · 0% Book details