← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 90

Sashe 77

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nace"Ai ni na baku ku dauka wannan ya ishe ni." Hannu tasa ta dauki kwandon da fadin"Ranki ya dad'e mungode kwarai hakika muna jin dadin yanda kike mu'amula damu munji dadin kasancewarki a matsayin uwargiyarmu." Murmushi nayi nace"Mariya kenan nima ina alfahari daku kuna kulawa dani yanda ya kamata kada ku damu da dukkanin abinda zanyi muku." Cike da jin dadi sukayi min sallama suka fita, girgiza kaina nai ina mamakin al'amarin wai yau nice a wani matsayi mai girma wanda banta'ba tsammanin kasancewa cikinsa ba, koda yake Ubangiji Allah babu yanda baya tsara lamarinsa........Bayan na kammala cin abincin da kaina na gyara gurin, na dauki wayata daki na shiga na kwanta a gado, number shi na kamo na tura masa text kamar haka.

_Yallabai ina fatan kaje asibiti lafiya? sannan ina rokon Allah ya kula da kai kamar yanda kake kulawa da masu bukata."_

Ina tura masa text din na ajiye wayar kusa dani, lumshe idona nayi ina janyo bacci da kyar naji ana buga kofar dakin, da sauri na mike zaune ina mamakin irin bugun da ake! anya kuwa! saukowa nayi da sauri ina fadin "Waye ne."'" ?

"Ke d'iyar bayi wato har tambaya kike waye ki bude kofar mana sai kiga ko su waye."!! da sauri na bude kofar! Hajiya Karima ce tare da wata mata mai qiba da alama kanwarta ce dan naga suna kama da juna.

Cikin fargaba nace" Hajiya barkanku da zuwa ku zauna mana." Tsaki taja ta matsa gefe guda tana watsa min harara!!

Lauratu itace ta 'karaso inda nake ta kalleni sama da k'asa yawun bakinta ta tofa min a fuska! kafin nai wani yunkuri ta tsinke sar'kar gold din dake wuyana!! hannu nasa na dafe kirjina ina mamakin abinda tayi! karfi tasa ta bugi! kirjina nayi taga-taga zan fad'i! da sauri na rike 'kofa( 'kyaure) ina kallonta....... hajiya Karima tace"Aa Laure banda duka kici mutuncinta nace kada ki doketa."

Laure tace"Hajiya ki kyaleni nayi 'kuli-'kulin kubura da yarinyar nan jiya da takaicinta na kwanta bacci wallahi tunda Lawisa ta kira waya ta tana kuka take sheda min cin mutuncin da Ali ke mata akan wannan 'yar iskar yarinyar nake Allah- Allah gari ya waye nazo naci ubanta! kina 'Yar bayi sama da 'kasa har kina da wata power kwace miji wato ke ga gwana kin cancad'a ado da gold kina zaune lafiya kin dasawa wata ciwon zuciyata to yau sai kin gaya min waye ubanki."!!! tana dukan kirjina take wannan maganar.....Hajia Karima tazo taja hannunta suka matsa gefe tace"Lauratu kada ki doketa bata isa ki had'a jiki da ita ba kawai ki nuna mata matsayinta."

Nace"Hajiya wai duk me ya kawo wannan abun me nayi muku ko kuma akwai wacce nake aure a cikin k.......Gwa'be min baki tayi da fad'in "Rufe mana baki fanko bud'add'an gwangwani! har kina da bakin magana wacce ta rako mata duniya." !!! Hawaye suka wanke min fuska, Hannu tasa zata fizge yarin kunnena na rike hannun tare da yarfar dashi!! cike da mamaki suke kallona!

Sunkuyawa nayi domin daukar tsarkata dake tsinke a k'asan gurin, da sauri tasa kafarta mai dauki da takalmi mai tsayi ta danne min hannu! rintse idona nayi ina jin wani irin zugi!! ciki zafin nama! na tureta tai taga-taga zata fad'i! kafin tayi wani yun'kuri! na kwad'a mata mari a kunci! a gigice! suke kallona! sabida gudun abinda zai faru yasa da azama na banke kofar dakin, key na murza na barshi a jiki kan gado na zube na dinga rizgar kuka ina jiyyar yatsun hannuna data mutsike min da takalminta.

'Karar waya ta dake daf da kaina yasa nayi gaggawar mikewa zaune wayar na laluba na dauka ina dubawa, gabana ne ya buga ganin miss call dinsa hud'u! da sauri na daga wayar tare da daidata nutsuwata a sanyaye nace"Hello." Yanayin muryarta yasa ya dan ji wani iri........."Sumayya lafiya dai ko.''? da sauri nace"Eh.''' Yace."Okey to me ya hanaki daukar wayata na kira sau uku kin duba ko kuwa kina sane."?

"Kayi hakuri wallahi bana kusa da wayar na barta a daki shiyasa yanzu ma na shigo daukar abu sai naga kiran ka."

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Nifa yanayin muryarki yasa jikina mutuwa ina fata dai ba jikin bane." ? nace"Babu abinda ke damuna sai kasala ina fata kaga text d'ina."?

Murmushi yayi wanda har sai da naji sautinsa a kunnena yace."Naga text dinki kuma naji dadi sosai dalilin daya sa ma kenan dana samu sukuni na kira wayarki na ji lafiyarki."

Murmushi nai ina kokarin kawar da damuwata nace"Nagode sosai amma dai kasha tea din kamar yanda kace."

Girgiza kanshi yayi yace."Har yanzu ban samu nutsuwa ba tukkuna zan nemi coffee nasha d'azu nace miki zan dawo kiyi hakuri bana jin zan dawo gida da wuri inada marasa lafiya sosai."

A sanyaye nace"Allah sarki mijina gaskiya bama kyautawa da muke barinka kana fita da yunwa dan Allah ka bari a kawo maka abinci."

'Yar dariyar jin dadi yayi yace."My love bana son wahalar dake shiyasa nace kisha magani ki kwanta ki huta! kada ki damu zan kira Mamma a waya insha Allah zata sa a kai min abinci."

Ajiyar zuciya na sauke nace"Har naji dadi a raina wallahi sam bana son zama da yunwar da kake bashi da amfani." Murmushi yay yace."Naga sai wani lalla'bani kike me zan samu idan na dawo."?

'Yar dariya nayi nace"Zan baka duk abinda kake so.' " cikin wani irin voice yace."Kinyi alkawari dik abinda na bukata daga gurinki zaki bani."?

Nace"Eh nai al'kawari." ajiyar zuciya ya sauke yace."To nagode kwarai sai na dawo." Ina kokarin magana ya kashe wayar, ajiyar zuciya na sauke na ji sanyi a cikin zuciyata waya ta dashi yasa na samu sassaucin bakin cikin da nake ciki bazan damu da duk wani cin fuska da wulakancin da zan fuskanta tunda mijina yana sona iyayensa suna kaunata to komai mai sauki ne kuma bana jin zan fad'a masa abinda ya faru yanzu zan bari idan sun 'kara sai na samu Mamma na fad'a mata nasan dole za tayiwa tufkar hanci.

Sai bayan isha'i ya shigo gidan kai tsaye gurin Lawisa ya nufa dan tun jiya rabon daya taka inda take......Tana zaune tayi ado sosai amma kallo daya za kayi mata ka tabbatar da cewa tana cikin fargaba da tashin hankali, abinda Lauratu kanwar mahaifiyarta taje ta aikatawa Sumayya shike damunta bata ta'ba tsammanin mahaifiyarta zata bada goyon bayan a rugaza mata zaman auranta ba......Tunda ya shigo take kallon fuskarsa bata hango 'bacin ran daya tsallake tunaninta ba, sakin ranta tayi tai masa barka da zuwa ya amsa yana bin falon da kallo, kanta ta sunkuyar da fadin"Kayi hakuri akan abinda ya faru jiya."

Shuru yayi bai tanka mata ba! tace"Dan Allah kayi hakuri." Yace."Magana ta wuce ina fata ki gyara halinki sai ki zauna lafiya dani! ajiyar zuciya ta sauke tace"Insha Allah zan kiyaye.....Mikewa yayi yace."Ni zan tafi sai da safe kenan." ta mike tare da rakashi bakin kofa har da cewa ya gaishe mata da Sumayya." yace "Zataji insha Allahu." Yana fita kai tsaye sashen mahaifiyarsa ya nufa domin su gaisa, ya jima a tare da ita kafin suyi sallama da juna.

Ado da kwalliyar da sameta dashi ya 'kyatar dashi mutuka ya dinga murmushi yana satar kallonta wai lallai shi ba zata kamashi yana kallonta ba, sai kauda kai yake amma daga ya samu faraga zai ta kallonta daga yaga sun had'a ido zai kauda kansa.....Sumayya dariya kawai take masa tana mamakin halinsa, tun bai gane ba har ya fahimci dariya take masa ya 'bata rai tare da ajiye cokalin hannunsa" Yace." Wato Kin samu mahaukaci kinsa a gaba kina dariya ko."? da sauri na had'a hannuwa cikin sigar bada hakuri nace"Dan Allah kayi hakuri kaci abincin nan ni bakai nakewa dariya ba." Harararta yayi yana sake release akan kujera yace."Sai dai kici kayanki na koshi."

Kamar zata fashe da kuka tace"Haba rabin rayuwata dan Allah kada kayi min haka ka daure kaci abincin nan dan Allah kaji."!!! a marairaice ta karasa maganar......Yana dariya yace."Sai kin maimaita sunan da kika saka min.

Da sauri nace"Rabin rayuwar Sumayya." wani irin kallon kauna yayi mata yace."Da gaske kike."? kaina na daga nace"Eh wallahi idan babu kai babu Sumayya." ji yayi kanshi na kumbura! ya dinga jefa mata kallon so yace."Ashe kin iya irin wannan kalaman shine baki ta'ba yi min ba."

Mirmushi nayi nace"Akwai wasu ma na mussaman kai dai kaci abinci zan fada maka su." Kamar wani shashasha ya dauki spoon din ya ciko da abinci yasa a bakinsa yana taunawa yana kallonta, dariya ta kusa sub'ce mata daka gani abincin yay yawa a bakinsa, tissue ta dauka tana goge masa inda ya 'bata

Ya sake ciko spoon har yana zubewa ya tusa a bakinsa yana taunawa yana kallonta! dariya tasa tana gumtse bakinta da hannunta....'Kwarewa yayi da sauri ta mi'ka masa ruwa ya kar'ba yasha ya ajiye cup din spoon din ya dauka zai sake d'ebo abincin da sauri na kar'ba hannu yasa zai kar'ba na janye! tare da fad'in "Baka ci a nutse bari kawai na baka da kaina." cinyarsa ya nuna min wai na zauna! cikin jin nauyi na dauki plate din abincin na zauna a cinyarsa ya rikeni sosai na shiga bashi a baki yana ci yana yi min wani irin kallo wanda na kasa fassarashi.
Chapter 77 · 0% Book details