← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 90

Sashe 80

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace."Ai Banda nauyi kinfi ni nauyi baby." girgiza kaina nai nace" Ban yarda ba." 'yar dariya yayi yace."Sumayya bana san 'kiba shiyasa bana mayar da hankali gurin cin abinda zai janyo min ita, amma kuma ina sha'awar mace mai 'kiba da kumari irin ki.'' dan 'bata rai nayi nace"Wato kana k'arewa matan mutane kallo kenan."? girgiza kansa yayi yace."babu ruwana da matan kowa sai nawa na fada miki abinda ke raina ne."

Shuru nai ina kallonsa ya kashe min ido da fad'in muje ciki ko." dauke kaina nayi, ya mike tare da kama hannuna na mi'ke kai tsaye bedroom din muka nufa sai shashshafa jikina yake gabadaya ya gama rikita min jiki.

A daran ranar ya nuna kulawa mutuka dan ya saki jikinsa sosai ya gamsar dani tarin sha'awar dake damuna, a tare mukayi wanka na dinga addua a zuciyata akan Allah ya d'orar da zaman lafiya a tsakaninmu..........

Kwana biyu zamana dashi yayi kyau muna mu'amular arziki kuma idan na bashi abinci ko baya so sai ya zauna yaci duk dan ya faranta min rai har zuwa yayi ya duba babana na dinga murna ina sake godewa Allah daya kawo mana zaman lafiya da junanmu.

Satin mu uku da shiryawa ranar lahadi da safe na tashi da wani irin ciwon mara, na fito daga toilet na sameshi yana bacci, cikin faduwar gaba na zauna kusa dashi ina tashinsa, ya bude idonsa da fadin"Menene baby please ki bari na huta.'' nace" Ka tashi bani da lafiya.'' idonsa ya bud'e! yana kallona kafin yace." me yake damunki."? murya na rawa nace"cikina ne ke ciwo."? jim! yayi kafin ya cusa hannunsa cikin rigata 'kasan marata yasa hannunsa yana d'an dannawa! nai saurin dauke hannunsa ina ya mutse fuska! yace."baby bashi da lafiya." gabana ya fadi! hawaye na soma zuba nace"Dan Allah ka tashi ka bani magani." shuru yayi min yana kallona..... Cikin damuwa nace" ka zuba min ido kana kallona ka tashi ka bani magani nace."

'Dan 'bata fuska yayi yace." Ke! ni kikewa tsawa haka."? ganin yanda ya hasala ne yasa na shiga bashi hakuri ina hawaye.

Yace." Bani da magani a gida kuma tun jiya na fada miki cewa ba zan fita asibiti da wuri ba zan kwanta na huta a gida sai ki bari na tashi tukkuna."

Wani irin kallon takaici nake masa yaja bargo ya rufe jikinsa! fizgewa nayi ina kuka nace"Ashe dama munafurci ne."? ya kalleni nace" Wallahi kaji tsoron Allah akan abinda kake." mi'kewa zaune yayi rai a 'bace! yace'Tashi ki fita ki bani guri na huta." hannunsa na rike ina cigaba da zubar da hawaye nace"Dan Allah ka tausaya mana nida babyna."

Girgiza kansa yayi yace." Zan baki magani amma sai na gama bacci tukkuna." komawa yayi ya kwanta yana sake rufe jikinsa da bargo! a fusace! na fuzge bargon ai kafin na ankara ya kwada min mari!!! na dafe kuncinta ina kallonsa.......Cikin rashin mutumci yace." Wallahi zan tattakaki idan baki bani guri ba." mi'kewa nai a sanyaye na fita daga dakin, tsaki yaja mai karfi ya koma ya kwanta yana addua akan Allah yasa cikin ya zube ya huta.

Koda na fita falon kasa danne damuwata nayi kawai na zauna kan kujera ina kuka domin nasan shi kadai zanyi na samu sassauci a cikin zuciyata, abubuwan da mutumin yake min sunyi yawa akwai abunda nake dubawa shiyasa kwata-kwata bana so na shedawa mahaifiyarsa Mamma macace mai karamci da mutunci zaman da nayi da ita ya sa na fahimci nagartattun halayenta ta nuna min dukkanin kauna da kulawa wannan dalilin yasa kwata kwata bana so naje na tayar mata da hankali bayan haka kuma ina kokarin ganin na rufa asirin aurena sanin da nayi cewar fallasa sirrin aure bashi da amfani ga ma'aurata shiyasa nake hakuri da duk abubuwan da yake min amma yanzu ya zama dole na sheda mata irin halin da nake ciki domin na tsira da lafiya nida abinda ke ciki......hawaye na share na mike na shiga dakin na sameshi yana bacci cikin kwanciyar hankali, girgiza kaina nayi firji na bude na dauko goran ruwa da cup kadan na tsiyaya na zauna kan kujera Fala'ki da nasi kafa uku na tofa a cikin ruwan sannan na tofa ayatulkursiyu kafa daya bisimillah nayi nasha na rage kadan na shafe cikina dashi.....cup din na ajiye na kwanta kan kujera tare da tsirawa rufin dakin ido........cikin ikon Allah na samu sassaucin abinda nakeji Allah nagodewa na gyara kwanciyata bacci mai nauyi ya daukeni.

Sai wajejen uku na rana na tashi babu shi a dakin da alama bai jima da fita ba dan gabadaya dakin kamshin turaransa yake, wanka nayi na dauro alwala na fito nai sallah na shirya jikina na fita na sami abinci naci naji karfin jikina, su Mariya sukayi min rakiya can gurin mahaifana, alhamdulillahi naji dadin yanda naga jikin babana yayi sauki na zauna mukayi hira sosai sai daf da magariba na koma gurina.................. Sanin da nayi cewa ba a gurina yake ba yasa na rufe kofa dan ina tabbacin tinda mukayi haka dashi ba zai shigo yayi min bankwana ba, aikuwa har ya gama kwana biyunsa a gurin Lawisa bai shigo gurina ba kuma bai kira wayata ba, nima fushi nake sosai inaso na nuna masa cewar na gane abinda yake nufi dama ashe yaudarata yake yana nuna kamar ya hakura ashe domin ya samu biyan bukatarsa wannan dalilin yasa na dauki al'kawarin bijire masa tunda dai shi baya tsoron Allah.

Ko kunya daya dawo gurina ya dinga wani lalla'bani har tambayar jikina ya kawo wani magani wai na ciwon cikine duk sanda naji ciwo nasha zanji sassauci kar'ba kawai nayi na ajiye na bar masa dakin.

Falon ya fito wai na bashi abinci na hada masa komai na bar masa gurin, a falo na kwanta na kyaleshi a dakin, can dai da yaji shuru ban shiga dakin ba ya fito ya tsaya a kaina yana min magana! a fusace! na mike nace"Kai! na fa daina yarda da yaudararka na gane har yanzu kana kan bakanka baka kaunar cikina to Allah yana kaunarsa kuma insha Allahu sai na haifeshi lafiya."

"Sumayya ni kike d'agawa harshe?" nace"Ai kai ka janyo ni dai dan Allah ka matsa daga kaina bana bukatar dadin baki.''

"Okay naji kina iya tasowa kina bani hakkina ko kuwa."? wani banzan kallo nai masa nace" Ba kaji kunya ba!" shan kunu yayi yace."Kifa shiga hankalinki dani bani da sauki kin dai san halina ko."?

A fusace! nace"Ka jima ba kayi min mugun abuba dama ai ka saba nima na saba duk wani mugun sharrin da kuke bibiyata dashi zai koma kanku.'''

"Sumayya bayan ni ashe akwai masu binki da sharri.''? nace" Kwarai kuwa kaje kayi binkice." ajiyar zuciya ya sauke yace." Yanzu dai kiyi hakuri ki tashi muje." nace'' Kai komai abinka sai ka hakura ka kyaleni.''

Murmushi yayi yace."Kin san Allah bazan kyaleki ba ko kina so ko bakyaso sai na biya bukatata.'' kafin nayi yunkuri ya fara kokarin daukata, hannunsa na dinga bugewa ina matsawa, kawai sai ya turmusheni akan kujerar gabadaya ya sakar min nauyinsa! rashin karfi da kuzari yasa jikina ya mutu kyaleshi nayi ya biya bukatarsa saboda nasan idan nace zanyi buge buge ni zansha wuya amma ko kusa ban bashi had'in kai ba dan sandarewa nayi yayi kid'ansa yayi rawansa.

****
Abinda ya cigaba da faruwa kenan a tsakaninmu dik ranar da yake gurina da kokawa yake samun biyan bukatarsa ni a galabaice shi a galabaice gashi sabida tsabar fitina sai yayi sau biyu farkon dare da kuma asubahi.........

*Bayan wata biyu*
Cikina ya shiga wata na biyar sai jikina ya soma nauyi nayi wata irin qiba 'kuguna ya sake fad'i cikin gabadaya ya shanye gurin breast d'ina sai dai ya d'an fito tunda ya huda zani ana ganin tudunsa amma sai mai 'kurulla ne zai gane! bani da laulayi mai zafi sai dai nayi haske sosai mussaman kafafuna da hannuwana, 'Bangaran Magajin sarki kuwa kullum cikin 'kunci da takaici yake mutukar zai budi ido ya ganta da cikin sai yaji kamar ya sha'keta saboda haushi! shiyasa kullum cikin yi mata iskanci da wulakanci yake kuma idan dare yayi yazo ya mori albarkatun jikinta.

Ina zaune a falo tayi sallama ta shigo, cikin kwalliya, murmushi nai nace"Barka da zuwa." Mansura ta samu guri ta zauna nace" Ba kiyi zuciyaba." mirmushi tayi tace" Na dai kusa." nace"Kiyi hakuri insha Allahu ina nan zanzo musha hira.

Tace."Ai ke yanzu dole ayi miki uziri tunda kinyi nauyi.'' nace."Bangane nayi nauyi ba." dariya tayi tace" Ashe baki da hausa ina nufin d'an baba ya kusa zuwa." sai nasa dariya da fadin"Waye yace miki ina da ciki."? tace"Haba Sumayya gashinan har yayi kwari ai mu ba makafi bane."

Murmushi nayi ina girgiza kaina, ta mike da fadin"To ni zan koma amma kafin nan zan shiga gurin Lawisa itama mu gaisa da juna." nace"Gaskiya kin kyauta sosai kina da kokarin zumunci insha Allahu zamu zo." tace"Ai ita Lawisa zuwanta uku kece dai baki ta'ba zuwa ba." nace"Kada ki damu insha Allahu zanzo a kurkusa." tace" To shikkenan sai na ganki." har bakin kofa na rakata mukayi sallama cikin mutunci.

"Mansura kika ce Sumayya na dauke ciki."? Lawisa ce ke wannan maganar cikin tashin hankali!! Mansura ta girgiza kanta da fadin" Kwarai kuwa wallahi ciki ne da ita dan da alama ma ya kwana biyu tunda gashinan har ya fito.

Lawisa taji wasu zafafan hawaye na nema su kufce mata, murya na rawa tace"Mansura ya akayi haka ta faru? ya akayi Sumayya ta dauki ciki bayan Sai da ya tabbatar min da cewar itama yana bata kwayoyin hana haihuwa.''

Mansura tace"Lawisa bangane maganarki ba."? hawaye ta share ta shiga warware mata yanda sukayi, tun kafin a daura aura

Mansura tace"Amma gaskiya Lawisa kinyi ganganci waye ya fada miki ana haka? kawai sai ki dinga dibgar kwayoyi ba tare da kin tabbatar da cewar kina haihuwa ko bakya haihuwa ba, a gaskiya Lawisa na raina wayonki."

Hannu tasa ta goge hawaye tace"Wallahi Manusura na rasa yanda zanyi ne shiyasa na amince da bukatarsa sai gashi ya ha'ince ni." Mansura tace"Ai a zahiri ya fi sonta shiyasa yake so ya haihu da ita ke kuma yana baki kwayoyi idan zakiyi hankali kiyi idan ba hakaba to tabbas zai kaiki ya baro."
Chapter 80 · 0% Book details