← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 90

Sashe 62

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan kwana biyu jikin Ciroma yayi sauki dan Magajin sarki ya tsaya a kansa sosai da sosai ya bashi dukkanin kulawar da ake bukata, alhamdullhi yanzu an samu yana iya sarrafa hannuwansa sai dai har yanzu idan yana magana ba'a fahimta sosai saboda yanda bakinsa ya karkace yana zubar da yawu....Ganin yanda hankali Maimartaba ya tashi akan hakan yasa ya zauna sosai ya kwantar masa da hankali yace."Insha Allah zai samu sauki ya dawo normal kamar yanda yake, jin haka yasa Maimartaba da 'yan uwansa hankalinsh ya kwanta, Suma su Lawisa suka kwantar da hankalinsu dan ganin yanda jikin mahaifin nasu yayi sauki sai dai har yayi kwana hudu a asibiti Hajiya Karima ba taje ba tana nan har yanzu da mugun nufi a cikin zuciyarta, cikin masarautar babu wanda bai je ya duba Ciroma ba amma ita da take a matsayin matarsa uwar 'ya'yansa ba taje ba tana zaune a gida tana sa'ka mugun abu a cikin zuciyarta.

*RANAR LITININ*
Kuto ta cika ma'kil da jama'a ana ta gabatar da shari'a yanda addinin musulunci ya tanada mai girma mai shari'a malam Umaru Musa ya d'auki takardar dake gabansa a nutse yake duba takardar yana girgiza kai! farin gilashin dake idonsa ya zare a nutse yace." Insha Allahu zamu kamanta adalci kuma zamu yankewa mai laifi hukuncin da addinin musulunci ya tanada muna rokon Allah yasa hakan ya zama izina ga masu hali irin na *Al'amin AbdulJabbar wanda akafi sani da Muddibo* Hukuncin da addinin musulunci ya tanadarwa dukkanin wani musulmin daya aikata kisa yana sane to shima akashe shi! Alhamdullahi wanda ake zargi da aikata laifin kashe masu rai guda uku ya amsa laifinsa ba tare daya wahalar da sharia ba saboda haka kuto tana bukatar ta saurari muryar wannan yaro a lokacin da yake wa hukuma bayanin yanda akayi yake aikata wannan 'barna kuto da jama'ar dake cikinta na bukatar su saurari jawabin da yayi domin kowa ya tabbatar da hukuncin da zamu yanke a kansa daidai yake da addinin musulunci."

Da sauri wani dan sanda dake tsaye a gefe ya dauko wayarsa a take ya kunna rocoding din da Acp yayi wa Muddibo a lokacin da yake jawabi a ofis dinsa......tun kafin rocoding din ya kare gurin ya kaure da haniya kowa na fadar albarkacin bakinsa, Muddibo dake tsaye gurin tsayuwar masu laifi ya sunkuyar da kansa zufa sai keto masa take hakika bai ta'ba nadamar rayuwa ba sai yau, jama'a sai zaginsa suke suna ala wadai dashi.......Wali da Muniru sai girgiza kai sukeyi suma tamkar su fashe da kuka su kad'ai ne suka iya halartar kuto Hajiya Karima dasu Lawisa suna gida suna kuka saboda jikinsu ya riga yayi sanyi da jin irin kotu'n da'aka kai Muddibon kotun musulunci ce tsantsa kowa yasan Malam Umaru Musa tsayayyan al'kali ne wanda yake yanke hukunci akan doron gaskiya Kudi ko mulki na mutum basu isa susa shi ya kauce hanya ba komai muqamin mutum mutukar yayi laifi baya d'aga 'kafa sai zartar da hukuncin da addinin musulunci ya tanada

Maigirma mai shari'a ya bada umarnin akan cewa kotu ta samu nutsuwa, nan take kowa ya nutsu gurin yayi tsit! A nutse ya cigaba da cewa''Saboda haka kuto zata yankewa Al'amin Abduljabbar hukuncin kisa kamar yanda ya kashe shima za'a kashe shi!! ta hanyar rataya."!! yana gama maganarsa ya buga tevur din gabansa da wani d'an katako! hukunci ya tabbata da izinin Allah! mikewa yayi gabad'aya jama'a suka mi'ke suna kiran sunan Allah.
"Allahu Akbar! Allahu Akbar! Allahu! akbar!! 'Yan sanda kusan hudu suka kewaye Muddibo a rirrike a ka fito dashi yana kuka yana d'agawa su Wali hannu aka fita dashi y'an jarida da jamaa suka bi bayansu.......Wali da Munniru rungume juna sukayi suna kuka Wali yace." Munniru kaga irin rayuwar da nake gudu ko ka duba ka gani yanda Muddibo zaiyi mutuwar wulakanci jama'a sai tsine masa suke saboda mugun abunda suka aikata, dan Allah Munniru komai rintsi ka rike gaskiya kada kabi san zuciyarka irin na Muddibo." Munniru hawaye kawai yake sharewa yana girgiza kansa tabbas duniya abar tsoro ce shikkenan yanzu sunyi bankwana da dan uwansu.
*Allah kasa mufi karfin zuk'atan mu amin.*

Hajiya Karima faduwa tayi ta suma lokacin da ta samu labarin hukuncin da ya sauka akan d'anta koda ta farfado ma sambatun surutai ta dinga yi tamkar wata mara hankali sai alwashi take ci akan wallahi ba zata yarda ba sai ta dauki fansa! Wali ya rungumeta a jikinsa yana mata addua yana share hawaye.........A ranar Maimartaba kasa zaman fada yayi saboda tashin hankali yaje ya kwanta a sashen Fulani yana tunanin rayuwa......Magajin Sarki da Shatima yini sukayi cikin alhini da damuwa amma daga baya da suka zauna sukayi tunani sai suka ga hukuncin da mai shari'a ya zartar akan Muddibo shine daidai hausawa na cewa da kunyar lahira gwara ta duniya watakila hakan na iya janyowa Allah ya gafarta masa zunubansa, saboda haka sai dukkaninsu suka kwantar da hankalinsu su tsananta addua akan Allah yasa haka shine yafi alkairi a rayuwar d'an uwan nasu....

*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba! keda kika futa da littafin keda Allah! idan kina bukatar biya ga yanda abin yake......Vip gruop#600 normal gruop#300 account number... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
90
Masarauta da jama'ar dake cikinta sun jima cikin alhini da damuwar abinda ya faru. mussaman 'bangarar Uwargida Huwaila ita da zuri'arta babu wanda ya kaisu shiga tashin hankali dan ganin irin hukuncin da ya sauka akan Muddibo duk sai suka tsorata kowacce ta shiga nutsuwarta dan saboda sun san koda sune suka aikata abu makamanci na Muddibo baza su tsira ba, sosai uwargida da iyalinta suke godiya ga Allah da bai nufi Muddibo ya kiran sunan d'aya daga cikinsu ba! wannan dalilin yasa kowacce ta nemi guri ta zauna a dakinta yanzu ba sosai ma suke zuwa masarautar ba saboda gudun kada asirinsu ya tonu..........Alhamdulillahi jikin Ciroma yayi sauki sosai dan yana iya komai da hannayensa sannan yana tafiya da kafafunsa sai dai rashin kuzari da bai dashi amma ya samu lafiya sosai Magajin sarki ya tabbatar musu da cewa zai warware idan an kwana biyu, Satin sa uku a asibiti ya dawo gida, duk irin kulawar da Magajin sarki keyi akan Ciroma baya burge Hajiya Karima kullum cikin zaginsa take tana kwashe masa albarka da fad'in "Yanda yayi sanadin mutuwar d'anta itama sai tayi sanadin mutuwarsa........duk sanda tayi wannan furucin sai Wali yayi mata nasiha harzuqa takeyi ta rufeshi da fad'a haka yake fita ya barta ransa a 'bace! bangaran Lawisa kuma ta dan samu sassauci kuma ta rage jin haushinsa tunda yayi sanadiyar samun lafiyar mahaifinta amma da itama ta k'ullaceshi a zuciyarta saboda yayi sanadin mutuwar dan uwanta! gabadaya idonsu ya rufe sam basa hango laifin Muddobo su dai suna nan akan bakansu na cewa sharri akayi masa, duk sanda zasuyi wannan furucin Wali hauka yake d'ora musu ya bar musu gurin dan takaici!! Ya lura Lawisa halinsu d'aya da mahaifiyarsu amma Munniru da Khalisat idan yayi musu magana suna ji kuma sun daina zagin Zuri'ar Maimartaba suna zaune lafiya da kowa a masarautar..............To Sati na uku a b'angaran Fulani gabad'aya na sanja fatar jikinta ta washe na 'kara qiba! su kansu sutturun da nake amfani dasu a jikina abin kallo da sha'awa ne duk wasu kayan kyale kyale da 'kawa na sarauta Mamma tasa an kawo min ina amfani dasu, kullum cikin ado da kwalliya nake na fito na zauna kusa da ita muyi ta hira Fulani wayayyiyar macace ta saki jikinta dani yanda na lura gabadaya bata suruktaka dani dan watarana ma idan nayi ado da irin kayan sarautar itace ke gyara min sai taga yayi daidai sannan hankalinta zai kwanta, a tsayin satikan da nayi a gurinta na koyi abubuwa da yawa na sarauta dana yau da gobe, sannan kuma sa'i da lokaci na kanje na gaisa da iyayena cikin walwala da farin ciki..............Cikin nutsuwa na fito daga daki na sameta a inda ta saba zama domin hutawa, kusa da ita na zaune a nutse nace"Mamma barka da hutawa." da murmushi a fuskarta tace"Barka kadai Sumayya yau kin wuni kina bacci baki fito da wuri." Murmushi nayi ina wasa da hannayena nace"Wallahi kuwa ni kaina nayi mamakin baccin da nayi sai da nayi tunanin ko maganin murar dana sha ne ya kashe min jiki."

Tace"Eh kwarai kuwa hakan zata iya kasancewa." Shuru nayi kaina a kasa kusan kullum idan inaso naje na duba mahaifana nakan ji kunyar fada mata, kwata-kwata bana so taga rashin kunyata.

Murmushi tayi tace"Sumayya kina so kije ku gaisa da iyayenki ko."? murmushi nayi tare dayin kasa da kaina. zamanta ta gyara tana murmushi tace"Ai duk sanda kike so kije gaishe da iyayenki ina ganewa na rasa me yasa kike jin kunyata Sumayya." 'Yar dariya nayi nace"Mamma kece Allah yayi miki kwarjini shiyasa nake kasa fada miki.'

Yar dariya tayi tace."Kwarjini har na kai ki sumayya."? da sauri na kalleta, ta daga min kanta tare da fadin"Gaskiya da rikon amanarki suna burgeki sumayya inaso ki sake dam'ke gaskiya hannu biyu duk rintsi kada ki kauce hanya ki tsaya akan gaskiyarki." Nace"Insha Allahu zan kula da maganarki.'

Tace."Babu damuwa kina iya zuwa ku gaisa amma kada ki tafi ke kadai kuje tare da mutum biyu." nace"To shikkenan." Ina kokarin mikewa ta shigo falon, kallo daya nayi mata naji gabana ya fadi, hajiya Karima ce! Mamma tace"Sannu da zuwa hajiya yau kece a gurina."

Cikin ya'ke tace"Fulani kenan ai kin san komai da dalili.'' guri ta nema ta zauna! na dan risina a nutse nace"Barka da yamma ranki ya dade." Wani banzan kallo tayi min kafin ta ta'be baki ciki-ciki ta amsa min. A sanyaye nace"Mamma sai na dawo." da sauri tace"To sumayya ki gaishe min dasu da kyau." Nace"Insha Allahu zasuji."
Hajiya Karima bin ta tayi da ido tana girgiza kanta, sauke ajiyar zuciya tayi bayan fitarta tace"Fulani gurinki nazo."

Mamma ta gyara zamanta sosai tana fuskantarta tace"Ai dama tunda na ganki nasan da akwai magana Hajiya Allah yasa alkairi ne yake tafe dake."
Chapter 62 · 0% Book details