← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 90

Sashe 50

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tare suka fito da Shatima daga massalaci, kai tsaye sashen fulani suka nufa suna tafiya suna tattauna al'amarin, karo suka ci da Muddibo ya fito daga sashen uwargida ganinsu a tare yasa gabansa faduwa amma da yake 'kwaro ne nan da nan ya dake! ya karasa inda suke a nutse ya basu hannu suka gaisa, yace."Yanzu nan nake tunanin zuwa sashen ka ashe ka dawo gida."? Yarima yace."Eh Allah ya takaita na dawo jiya misalin sha biyu na dare." Cikin alhini yace."To Ubangiji Allah ya kiyaye a gaba amma yana da kyau kasa ido sosai a sashen ka abubuwan dake faruwa da kai sunyi yawa." Yace."Insha Allah yau din nan zan zauna dasu saboda jiya bayan dawowata na samu abun hannun wani daga cikinsu hakan ya sake tabbatar min da cewa akwai sa hannunsu a cikin al'amarin."
Muddibo cikin faduwar gaba yace."Ka samu sheda kenan."? Yace."Kwarai kuwa." Muddibo girgiza kansa yayi yace."To babu damuwa Muje mu gaisa da Mamma sai mu zauna dasu din." tare suka shiga falon, tana zaune kan dadduma da carbi a hannunta, ganin gudan jininta lafiya lau yasa taji wani sanyi ya sauka a zuciyarta, lallai addua bata faduwa kasa banza, a nutse suka zauna gabanta suna gaisheta, ta dinga amasawa tana shafa kansu, tace''Ina rokon Allah yayi muku albarka ya kareku daga dukkanin sharrin abinqi dukkanin mai nufin ku da sharri ina rokon Allah ya mayar dashi kansa, babana hakika naji dadin ganinka cikin nutsuwa ina rokon Allah ya kiyaye gaba su kuma wad'annan bayin Allah da suka rigamu gidan gaskiya ina rokon Allah ya jikansu ya gafarta musu."
Suka amsa da ameeen suma ameeen."

Koda suka fito daga sashen mamma kai tsaye Sashen Waziri suka nufa, iyalin Waziri ganinsa lafiya lau yasa su farin ciki suka dinga yi masa adduar kariya daga dukkanin abinqi! lafiya lau suka fito daga sashen suka nufi na Galadima, babu yabo babu fallasa suka gaisa da juna har suka fito babu wanda yayi masa jajen abinda ya faru ballantana ya samu kyakkyawar addua, sosai al'amarin ya bashi mamaki! Shatima ma yaji takaicin abinda iyayensa sukayi 'karara suke nuna hassadarsu abin da iyayensa da sauran 'yan uwansa keyi sam bayayi masa dadi, hakuri ya shiga bashi, Magajin sarki ya dakatar dashi da fad'in "Kada ya sake bashi hakuri akan abinda akayi masa shi bai dauki abin da zafi ba yana ganin duk abinda sukayi a kansa daidai ne! Shatima ganin ransa ya baci yasa ya bar maganar, Suna daf da shiga sashin Ciroma Mudibbo yace." Su shiga kawai zai dauko wayoyinsa a gurinsa, ba tare da sunce wani abuba sukayi gaba, shi kuma kamar gaske ya nufi gurinsa, tsayawa yayi na minti biyar, ya leko kansa ganin sun 'bace daga gurin yasa da sauri ya fito, kai tsaye 'bangaran bayi ya nufa.

Babu yabo babu fallasa suka gaisa da iyalin Ciroma dukkaninsu suka cika falon kowa na fadin albarkacin bakinsa akan abunda ke faruwa, shi dai jinsu kawai yake dan ya kasa cewa komai saboda hayaniyar da tayi yawa a falon sai zagin Sumayya suke suna cewa ita za'a daure tunda itace ta girka abincin dole a tsaurara binkice akanta ta fadi wanda ya bata gubar.....Gimbiya Lawisa ta zage sai cin mutuncin Sumayya takeyi, 'yan uwanta suna taya ta, ga mahaifiyarta a zaune ta kasa tsawatar musu, takaici yasa ya mike Shatima ya mike sukayi musu sallama suka fito, rai a 'bace ya kalli Shatima yace." Gabad'aya naji na tsani Lawisa wallahi bata da tarbiya ko kadan." Yace."Kasan hausawa nacewa Tarbiya daga gida take farawa Hajiya Karima sam bata da tsawatarwa shiyasa 'ya'yanta suka lalace." Yace."Allah ya kyauta hakikanin gaskiya ina fargabar auran Lawisa ta haifi min lalatattun 'ya'ya." Yace."Haba ai ba 'anan take ba kaifa tsayayyan namiji ne kai zaka tsaya akan iyalinka sosai na tabbata zaka iya sanja mata hali idan kukayi aure." Girgiza kansa yayi yace."Hakika idan ta sake tazo min da mummunar d'abia to zata sha wuya a gurina dan na tsani mace mara nutsuwa wallahi." Shatima yace."Gaskiya mace mara kintsi bata da dad'in sha'ani kamar yanda na fad'a maka da farko hakane idan kukayi aure zaka iya canzata mutukar tana kaunar zama dakai dole tabi dokokinka." shuru yayi be sake magana ba har suka isa sashen nasa,

kafin su shiga ciki ya kira Mika'il yace dashi gabad'ayansu suzo yana san ganinsu.......Suna zama Muddibo ya shigo hannunsa rike da wayoyinsa kusa da Shatima ya zauna yana duba 'karamar wayarsa Shatima kallonsa kawai yake sam be yarda dashi ba, tuntuni yake zarginsa kawai dai yayi shuru ne yana kallonsa kuma yana rokon Allah ya tona masa asiri.......Su shida suka shigo suka samu guri guda suka jeru gabad'aya sunkunyar da kansu sukayi kasa suna jiran suji kiran da ake musu.

*Na kudi ne!*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya keda kika futa da book din keda Allah idan kina so ki biya ga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300...account... 0542382124....Binta umar gtbabk....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:27 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(kainuwa dashan Allah✊�)
81
"Idan ba shine yayi sanadiyar mutuwar Haruna ba to waye? ni daina nasan lafiya lau na gama abinci na shirya komai akan tire kafin na fito daga kicin din na sameshi yana kokarin fita! gabana ne ya fad'i! lokacin dana tuna kafin ya fita ya bani umarnin akan na gyara masa daki, tabbas a wannan lokacin wani zai iya shigowa ya aiwatar da kudirinsa" Anya kuwa ni nafi zarginsa akan shine keda hannu akan faruwar al'amarin watakila bayan haruna ya kai masa abincin ya zuba guba a ciki ya bashi." To in banda abinki Sumayya idan Yarima ya kashe Haruna akan wata manufa shi kuma direba mai yayi masa da zai had'a dashi ya kashe."? jikina ne yayi sanyi jin irin k'alabulanta ta da zuciyata takeyi akan zargin da nakeyi akan Yariman.

Gabad'aya jikina ne yayi sanyi na dinga tunanin waye yake da hannu a cikin wannan abu, ance zargi zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne to amma irin munanan kalaman da ya dinga yi akan haruna yasa nake zarginsa da kashe shi domin bukatarsa ta biya a kaina.

Na jima ina sa'kawa da kawancewa kafin naji motsin saukowarsa, kauda kaina nayi da barin kallonsa har ya karaso kusa dani ya zauna yana sanye da farar jallabiya mai karamin hannu da alama wanka yayi kafin ya sauko.

Ganin yanda ya naniqa dani yasa na janye jikina gami da sunkuyar da kaina kasa.

"Sumayya." Naji ya kira sunana! shuru nayi ban amsa ba.

Ya sake kiran sunana da fadin"Ina so ki kalle ni sosai zamuyi magana."

Kallonsa nayi, naga babu wasa a fuskarsa yace." Ni Ban kashe Haruna ba sai dai ajalinsa ya sauka ta dalilin cin abincin da ya kasance nawa, Allah yayi nufin Haruna da Atiku ne zasu mutu ta wannan hanyar saboda haka kada na sake jin kinyi furuci akan cewa ni na kashe su.

Bude baki nayi zanyi magana yasa hannu ya rufe min baki yana girgiza kai yace."Nasan abinda zaki ce! kina so ki kalubalance ni akan maganata ko."? shuru nayi ina kallonsa, ya cigaba da cewa." saboda kawai nayi wad'annan furucin nawa na baya kike so ki gazgata zargin ki a kaina wallahi Allah kenan ban kashe wad'annan bayin Allah ba."

Jin yanda yake rantsuwa da Allah! yasa jikina ya mutu, a sanyaye nace"To idan ba kai bane wanene ? ni dai nasan tsaf na kammala komai kafin naje na gyara maka dakinka kamar yanda ka umarce ni.

Girgiza kansa yayi yace." Wata'kila lokacin da kika tafi gyara min daki aka samu wani ya shigo yayi abinda zaiyi ya fita ba tare da kin sani ba, kin dai san yanda ni dake muke fama da masu farautata a kullum dama suke nema akaina su cutar dani , ki tsaya kiyi tunani sosai akan maganata, Sumayya duk 'kiyayyar da nakewa Haruna ba zan kashe shi a kan son duniya ba, naji ciwo sosai da abinda kikayi a station har kina fitar da hannu kina mari na! sannan har kina kiran mu azzalimai shin kin san irin masifar da zaki jefa kanki a sakamakon wannan haukan da kikeyi to bari kiji na tausayi miki ne saboda nasan kina cikin rud'ani inda naso a station d'in zan sa ayi miki rashin mutumci! bayan nan kuma na ku kulle ki har karshen rayuwarki!! ina da dama a hannuna wacce zan iya yi miki dukkanin abinda nake so amma na kyale ki kike cin kashi a kaina! ki sani idan ni na kashe Haruna wallahi ba zan 'boye ba, zan fada kuma na kwana lafiya babu wanda ya isa yace don me! ina da wannan ikon saboda dukkaninsu a k'arkashina suke, sai dai duk ikon da nake dashi na duniya ne idan naje Lahira nan zan ga sakamakona! Sumayya ki sani Haruna da Isa da Atiku sunyi mutuwar shahada wanda yayi sanadin mutuwarsu duk sun rataya a wuyansa Ubangiji ya wankesu tas saboda haka inaso ki nutsu sosai ki daina zargina akan wannan abu, idan Allah ya kaimu gobe Acp yazo ki nutsu kiyi masa cikakken baya ni amma kika sake wani mummunan furuci a kaina to zai cigaba da daukar ki a matsayin mahaukaciya."

Tun kafin ya gama maganarsa nake zubar da hawaye, ya kama dukkanin hannayena ya rike yana rarrashina, cikin sanyin murya nace"Yanzu to ta yaya za'a iya gane wanda yake aikata wannan mugun abu, idan ya kasance d'an sarauta ne shikkenan jininsu Haruna ya tafi a banza tunda kace shi mai mulki yana iya yin komai ba tare da an d'auki mataki a kansa ba."
Chapter 50 · 0% Book details