← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 90

Sashe 18

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na sake kallonsa zuciyata sai zafi take kamar na mayar masa da martani sai dai na daurewa zuciyata da sauri na bar gurin, kicin na nufa, koda na shiga kicin din kasa aikata komai nayi na tsaya jikin drowars ina sa'ke-sa'ke! yanzu dai koda nayi masa abincin baci zaiyi ba tunda ya fad'a min to ina ganin idan nayi abincin na ajiye tamkar nayi albazazzaranci ne. wata dubara ce ta fad'o min ina ganin itace mafita a gareni.
Zama nayi kan wata kujera ta mussaman wacce aka tanade ta domin hutawa, sai da na dauki kimanin mintuna ar'ba'in kana na mi'ke na dauko tire din da nake jera masa abincin sabbi fulas na jera a kai na fita daga kicin din hannuna rike da tiren kai tsaye gurin cin abincin na nufa, na jera tsaf tamkar da abincin a ciki.

Da sauri na baro gurin nesa dashi na tsuguna nace"Yallabai na kammala." ko kallona beyi ba ballanatana ya amsa min, miqewa nayi da fadin" A tashi lafiya'' da sauri na nufi kofar fita.

Kallo ya bita dashi yana sauke wata zazzafar ajiyar zuciya, akan idonsa ta fita daga falon, ya tsirawa fuskar wayarsa ido ta nayi masa gizonta a idonsa......Ya'ki yay da zuciyarsa ya miqe ya nufi danning din domin ganin abinda ta girka, dan yayi wa mahaifiyarsa al'kawari akan ya daina cin abincin waje sai na yarinyar tunda da ita ta amince masa, A kwanakin da suka gabata yana aika Haruna restaurant yay masa take a way da safe kuma ruwan tea kawai yake sha da biscuits...... Zama yay kan kujerar daning din a nutse ya fara kici-kicin bud'e fulas din, yana budewa yaga wayam babu komai. da sauri yasa hannunsa kan d'ayan tunkafin ya bud'e ya nuna masa da babu komai a ciki.......Cike da takaici ya daga fulas din yana duba cikinsa tamkar me neman wani abu. Lallai ashe yarinyar bata da mutunci ashe bata girka komai ba amma tazo ta jera fulas a daning sai kace wacce tayi abin arzi'ki! sosai ya shiga mamaki abunda tayi, kafin kuma al'amarin ya shiga bashi dariya.

Ya dinga dariya shi kad'ai ya mi'ke ya nufi 'kofa da niyyar fita Haruna zai kira yazo ya samo masa abinda zaici dan yunwa yake ji.

Moddibo ne ya shigo falon a lokacin da yake daf da fita, tsayawa yay yana murmushi, shima Muddibon murmushi yay masa ya bashi hannu suka gaisa da juna.

A nutse yace."Ina zuwa na ganka cikin manyan kaya ina Shatima yake.''? Muddibo yace." Shatima na gurin aiki ni kuma zanje gurin bikin birthday din wani friend d'ina shine na keso muje tare ko babu komai kaga gari na lura tunda ka dawo kullum kana gida baka san zuwa ko'ina.''

Sajensa ya shafa a nutse yace."Okey jira ni nayi wanka na kimtsa jikina dama yanzu yanzu nake tunanin kiran Haruna ya samo min abinda zanci babu damuwa yanzu idan mun fita sai mu tsaya a gurin cin abincin." Muddibo yace."Okey to babu damuwa muje ka kimtsa a nutse sai mu fita." Sai suka nufi saman a tare suna maganganun da suka shafe su......
*BINTA UMAR ABBALE*

*Please kuyi sharing👏🏻*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *[email protected]*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_

*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
37&38
Shigar 'kananun kaya yayi a jikinsa kasancewar ana d'an busa sanyi yasa ya d'ora jacket wacce ta sauko har gwiwarsa hular sanyi yasa ya sunkufe kanshi, ya sakaye idanunsa da bakin galishi, Moddibo sai tsokanarsa yake yana kiransa da bakin bature wai idan ba wanda yayi masa farin sani ba babu wanda zai ce ya had'a jinsi da bakar fata, murmushi kawai yake bai tanka masa ba, suka sauko a tare suna hira Moddibo farin ciki fal a zuciyarsa yana addua Allah yasa bukatarsa ta biya a kansa.

Su Haruna na ganin fitowarsu suka mike suna mika gaisuwa, ya tsaya yana magana dasu shi kuma Moddibo parking area ya nufa direba ya mike tsaye da sauri ya karaso gurin, Moddibo key ya kar'ba daga hannun Direban ya bashi umarnin tafiya....a nutse ya karaso gurin yana kallon Moddibon dake zaune a cikin motar yana sa mata key yace."Meye Amfanin direba za kayi draving da kanka.

Moddibo na murmushi yace."Yau d'aya naji ina sha'awar tuqa mota da kaina shigo kawai mu tafi." Jim yay na minti biyu ya kama murfin motar zai bud'e, da sauri Yakubu direba ya bude masa ya shiga ya mayar da murfin ya rufe da fadin"A sauka lafiya ranka ya dade." Hannu kawai ya daga masa Moddibo yaja motar suka bar gurin.

Hira suke sosai a tsakaninsu Yarima Ali ya saki jikinsa da Moddibo yana ganin dan uwansa ne dake kaunarsa ba zai ta'ba cutar dashi ba, yayin dashi kuma Muddibon ke Allah Allah su isa gurin birthday din ya cimma manufarsa a kansa, Yanayin Moddibo bai nuna cuta da zalinci ba sosai ya saki fuskarsa sai fara'a yake yana nunawa d'an uwan nashi kauna da kulawa, Magajin sarki ya sake sakin jikinsa dashi yana ganin ba zai ta'ba cutar dashi ba.

Gurin birthday din ya cika da samari da 'yan mata 'ya'yan manya masu kudi duk wanda ya hallaci gurin birthday diin
Nura promise to d'an gayu ne kuma ubanshi mai kudi ne kuma mai mu'kami ne

Guri na mussaman aka tanadar musu suka zaune a killace Magajin sarki sai sake tamke fuskarsa yake ganin yanda idanun 'yan mata yayi caaa a kansa, gaskiya yayi dakacan zuwa gurin a rayuwarsa ya tsani kallo mussaman daga gurin mace...........Cikin k'ayatarwa Nura ya yanka cake kafin a shiga rabon kayan ciye ciye. A nutse ta k'araso gurin da suke zaune hannunta dauke da tire da yake cike da kayan ci da sha, ajiyewa tayi kan tevur din dake gabansu ta zauna kusa da Moddibo suka gaisa tana satar kallon Yarima Ali wanda shi kuma tun zamanta a gurin yayi kici kici da fuska.

"Moddibo ganinku yayi wuya tun bayan kammala karatunmu kowa ya watse ko a waya bama gaisawa yanzu dai kafin taro ya watse inaso ka bani number wayarka.

Muddibo yace." Wallahi kam Latifa al'amura ne sukayi yawa ina fatan kina lafiya ya mutan gida." Da murmushi a fuskarta ta amsa kafin tace"Wannan d'an uwanka ne naga kuna yanayin kama da juna."

Muddibo murmushi yay ya kalli gefan da yake zaune yace."Kingdom kenan Magajin sarki kenan shi muke sa ran ya gaji sarautarmu."

Latifa zare ido tayi tana kallonsa tace"Ashe masu 'kasar ne a gabana Yallabai barka da wannan lokacin." tafad'a tana kallonsa, Ba tare da ya kalleta ba ya amsa ya mayar da hankalinsa gurin Moddibo da fadin"Yana da kyau mu tafi kamar yanda na fad'a maka inaso na samu abinda zanci..

Moddibo yace."Okey me zai hana kaci abincin gashi nan Latifa ta ajiye mana ina ganin ba sai munje restaurant ba.'' tevur din ya kalla ya dauke kansa daga gurin, yana da kyankyami ba kowane abincin yake iya ci ba.

Latifa ce ta shiga bud'e mishi ledar da aka rufe abincin tana fadin "bisimillah ranka ya dad'e." Ya sake kallon abincin a karo na biyu...Shinkafa ce akayi mata wata irin dahuwa sai kayi da gaske sannan zaka gane shinkafa ce taji kayan lambu da nama sai kamshi take daya plate din kuma gasheshshen nama ne da akayi mishi had'i da ganyayyaki sai manyan lemuka masu sanyi......A nutse yasa hannu kan cokalin ya d'ebo abincin yasa a bakinsa, yana taunawa yaji tes din abincin be masa ba daurewa yay yaci cokali uku ya ajiye tare da goge bakinsa da tissue.

Moddibo yace.''Ya naga ka ajiye cokalin." Girgiza kansa yay yana ya mutsa fuska "Alhamdullhi wannan da naci ya isa." Moddibo na dariya yace."Ashe ba yunwa kake ji ba dama." Ta'be bakinsa yayi yace."Ina jin yunwa sosai dan rabona da wani abincin kirki tun jiya da daddare kawai tes din abincin ne beyi min ba."
Muddibo murmushi yay a cikin zuciyarsa yace."Ai tunda dai kaci magana ta 'kare. A zahiri kuwa cewa yay ."Okey bari ni na gwada na gani ko zan iya ci." Shiru yay yana kallonsa. Moddibo a maimakon yaci na plate din dake gabansa sai ya janyo sabon plate ya bude ya fara ci a nutse....Lokacin Latifa ta jima da barin gurin..Moddibo abinci yake ci yana satar kallonsa ta kasan idonsa.

Yana zaune yaji kansa na juyawa amai na taso masa, daurewa ya dinga yi yana danne aman sabida jama'ar dake gurin, Moddibo ya kalleshi hade da fadin"Ya dai dan uwa naga sai ya mutsa fuska kake.'' Hannu yasa cikin Aljihu ya dauko hankici ya tsane gumin goshinsa a kasalance yace."Wallahi kaga ina zaune kawai nake jin jiri ga wani amai na taso min.

Cikin kulawa ya ajiye cokalin hannunsa da fadin"Subahanallahi kodai abincin da kaci ne ya janyo maka hakan." Cikin damuwa yace.Mybe shine amma nafi tunanin yunwar dana tara ce ta janyo hakan kai dai yi sauri ka gama mu tafi gida dan na soma ganin dishi dishi a cikin idanuwana.

Moddibo ya mike tsaye da sauri da fadin"Ina zan ga nutsuwar cin abinci bari na kira Nura yazo ku gaisa mu wuce kawai.'' yana gama maganarsa ya kusa cikin mutane domin kiran abokin nasa.

Tare suka dawo gurin da Nura, Magajin Sarki ya danne abinda ke damunsa suka gaisa da Nura yay masa fatan alkairi sosai kana ya mi'ke gaba yay ya barsu suna magana.

Cikin mota Muddibo ya sameshi yay gaggawar bude motar ya shiga ya zauna kunnar motar yay hankalinsa a kansa yace.''Kodai mu tsaya a hospital ne dan naga kana jin jiki sosai." Girgiza kansa yay yace."Muje gida kawai a yanzu babu abinda nake so sai kwanciya daga baya sai a kira Family doctor ya duba ni."
Moddibo yaja motar da fadin"To Allah ya sawwake.
Chapter 18 · 0% Book details