Sashe 32
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aunty Safiyya tare da mahaifiyarta suna zaune suna sake tattauna maganar , tace"Nasan da wuya ya tashi dan lokacin dana fito daga sashen numfashinsa ya dauke jikinsa ya saki." Uwargida tace"Koda Allah yasa zai tashi to fatanmu ya tashi da nakasa so nake wani sashe na jikinsa ya lalace kafa ko hannu." Aunt Safiyya ajiyar zuciya ta sauke tace''Bari na koma sashen nasa domin ganin abinda ke faruwa.
Lokacin da ta shiga falon shuru taje ta tsaya a inda ya fadi tana mamakin ina yake, motsin saukowarsa taji tayi saurin daga kanta ganinsa tayi yana saukowa cikin kwalliya kamshin turaransa har inda take.
Gabanta ya dinga faduwa tana kallonsa yana saukowa sai murmushi yake mata, gwiwa a sanyaye tace"Kanina.'' yace."Na'am aunt Safiyya zauna mana kin tsaya." kujera ta nema ta zauna tana kallonsa ya zauna a kujerar dake fuskantarta, gaisheta yayi ta amsa jikinta sanyi kalau tace" Amma nayi mamakin ganin ka a haka dazu fa yanke jiki kayi ka fado daga sama, na fita a gigice domin naiman taimako abin mamaki kuma yanzu na ganka radau.
Yace."Nima a jikina naji abinda ya faru sai bayan na dawo daidai nake tambayar hadimata take sheda min abinda ya faru." Girgiza kanta ta shigayi kafin tace"Allah ya kiyaye gaba."
"Ameeen yace yana nazarinta ya soma hango rashin gaskiya a tattare da ita....gyaran murya yayi tayi saurin kallonsa yace." Aunt Safiyya na rasa abinda nayi wa mutane suke son suga bayana." Taji gabanta ya fadi jin abinda yace tace"Yarima ai dole mutane su nuna ganin kyashin su a kanka kai dai ka dage da addua.''
Murmushi yayi yace."Addua kullum cikin yinta nakeyi kuma a matsayinku na 'yan uwana ku tayani." tace"Kada ka damu dan uwana." Shuru falon yayi yace."Kin same aunt." girgiza kanta tayi yace."Na soma zargin wannan hadimar tawa domin dazu na ganta tana yayyafa wani abu akan stpes." yana maganar yana kallon reaction dinta
ta dinga kallonsa bakinta na rawa tace"To me take yayyafa wa ? kaji shegiya ko ta hada baki da wani a cikin gidan nan dan cutar da kai."?
Yace."Nima abinda nake zargi kenan." mikewa tayi zumbur ta nufin benan ta hau duddubawa! nan ta gane *kanwa* yarinyar ta zuba dan duk ga alamunta nan, lallai yarinyar nan bata da mutunci ta karya musu aiki, a sanyaye ta juyo suka hada ido dashi nan ya sake tabbatar da zarginsa gaskiya al'amarin ya bashi mamaki mutuka.
Zama tayi tana xage zage da fadin"Lallai sai ta tura an kira mata yarinyar ta turketa domin ta fada mata wanda ya turo ta ta zuba masa magani.
Yace."Aunt Safiyya ki barta kawai ni zan koya mata hankali daga yau ta bar aiki a sashena, tace."Eh dama hukuncin da zaka yanke mata kenan ni da kaina zan duba wacca ta cancanta ta kula da kai anjima zamu tare
Yace."To shikkenan godiya nake." Hira sukayi sama sama tayi masa sallama ta tafi, tana fita ya shiga mamakinta gabadaya yanayin data nuna ya tabbatar masa da rashin gaskiyarta, yana sane ya juya maganar kan Sumayya ya nuna ita yake zargi domin kawai yaga yanda zata nuna.
Shatima ne yay sallama ya shigo ya samu guri ya zauna yana kallonsa yace."Na ganka kamar kana da damuwa ina fatan ba aunty Safiyya bace dan naga fitar ta rai a bace.
Shuru yayi na minti uku kafin yace."Shatima al'amarin gidan nan yana bani mamaki mutuka ashe har yanzu ba zamu daina cin dunduniyar junanmu ba! ashe ba zamu kaunaci junanmu ba shin wai me muka mai da mulki ne? kowa babu alkairi a zuciyarsa kullum kudirinsa ya za'ayi ya cutar da jininsa ni aunty Safiyya ta shigowa guri da surkulle bansan me take nufi dani ba."
Shatima yace."Kayi min bayani yanda zan fahimta wane irin surkulle aunty Safiyyan ta shigo maka dashi."?
ajiyar zuciya ya sauke yace."Ina kwance a daki yarinyar nan Sumayya ta shiga take sheda min zuwanta lafiya lau na fito a dakina ina fara saukowa na fita daga hayyacina a yanzu zancan da nake maka jikina ciwo yake min.
Shatima mirmushin takaici yayi yace."Yarima kenan wato kai ka dauka zaka zauna lafiya a masarauta ko? to bari kaji na fada maka abinda ka tafi ka bari yana nan sai ma abinda ya k'aru Uwargida da 'ya'yanta suna nan suna shirya mugun abu Baba Ciroma da iyalinsa suma suna nan akan bakansu.....Baba Galadima shine mahaifina shima bazan rufe maka ba baya kaunarka dan saboda suna ganin kai zaka gaji sarauta dukkaninsu sunfi so saurauta ta dawo hannunsu saboda haka sai ka kula da kyau ni dai bana cikin tsarinsu dan mulki sam be dame ni ba shiyasa idan naga Muddibo na hauka yake bani mamaki Wallahi ni nafi bukatar kasuwanci na yafi min komai.
Yarima ajiyar zuciya ya sauke yace." Shatima su suka damu da mulki kasan Allah mulki baya gabana nafi bukatar na tsaya akan aikina na taimakon marasa lafiya nayi mamaki sosai da jin wannan magana, Muddibo duk yanda muke dashi ashe adawa yake dani."
Shatima yace."Ban fada maka wannan magana ba dan ka 'kullace su inaso dai ka kula sosai ka daina sakewa da duk mutanan dana lissafo maka wallahi basa kaunarka Waziri da iyalinsa ne kawai ke kaunar cigabanka." Yarima Ali shiru yayi yana mamakin al'amarin Shatima yace."Shiyasa fa sam banyi na'am da auranka da Lawisa ba nasan zasu Iya Shiryo wata ma'karkashiyar ta 'bangaranta."
Da sauri yace."Ni dama sam yarinyar ba tayi min ba wallahi tunda abun ya zama haka zan samu maimartaba akan maganar.
Shatima ya girgiza masa kai da fadin"Kada ka yanke wannan hukuncin tunda dai an riga an tsayar da magana sai kayi hakuri kasan ko kaje ka cewa maimartaba ka janye ba zai yarda ba sai anyi."
Shuru yayi yana tunanin maganar.
Washe gari da sassafe na tashi nayi mana Wanki nayi wanka na fito ina tsaka da shiryawa Tambaya ta shigo dakin ta same ni, tunda na ganta a sanyaye nasha jinin jikina tace"Sumayya jikina yayi sanyi jin Uwargida ta aiko kiran ki.
Gabana ya fadi jin abinda tace nace''Yaushe ta aiko." Tace"Yanzu yanzu. cikin tararrabi da faduwar gaba nace"Ki kwantar da hankali babu wani abu tunda dai nasan banyi mata komai ba ko naje ba zata tuhume ni ba."
Tace" To Allah yasa kiyi sauri kisa kayan ki kije. dankwalina na daura nace bari naje daga can zan wuce sashen Yarima tace."To Allah yasa muji Alkairi.
Koda na shiga falon sai da nasha jinin jikina ganinsu duk sun kewayeta fuskokinsu babu fara'a zubewa nayi ina gaishesu babu wacce ta amsa a cikinsu na sunkuyar da kaina cike da ladabi nace"Ranki ya dade gani."
Zama ta gyara tana kallona tace"Wama sunanki." da sauri nace"Sunana Sumayya Lawi." Tace"Ubanki wace irin bauta yake a cikin gidan nan."? nace"Yana bautawa Dawakai ne." Ta ya mutsa fuska tana wasa min kallon banza tace"Kece kika wargaza mana aikinmu na jiya ko."? mirya na rawa nace"Ranki ya dad'e wane irin aiki."? Wani bahagon mari aunty Safiyya ta kwada min tana huci! tace"Kada ki raina mana hankali dan ubanki tambaya ma kike."?
Ido jawur nace"Tuba nake ranki ya dade." Uwargida tace"Kalle ni da kyau."! na dago kaina ina kallonta, tace."Kinyi na farko kuma kinyi na karshe wallahi tallahi duk sanda mukaje muka gudanar da aikinmu kika karya sai na saubata miki rayuwarki sai kin rasa ruwan kur'ba a masarautar nan ki tsaya a matsayin ki na baiwa babu ruwanki da Yarima duk wani abu da zamuje sashen mu gudanar ido ne naki."
Nace"Ranki ya dade ku gafarce ni wallahi ban san wane aiki na lalata muku ba." Gabadaya zuba min ido sukayi, aunty Safiyya tace"Wato ba zaki daina wannan maganar ba ko. " shuru nayi tace"kinji abinda aka ce ko baki ji ba."? da sauri nace"Naji ranki ya dade....tace"Na tura hadima daga nan bangaran zata dinga saka mana ido akanki babu ruwanki akan dukkanin abinda zata gudanar aiki muka sata kiyi aikin ki tayi nata." nace insha Allah zan kiyaye." Aunty Bishira tace"Sumayya idan kika sake 'bata mana aiki a karo na biyu sai kin zubar sa hawaye wallahi tallahi mummunan mataki zamu dauka a kanki." Nace."Ranki ya dade zan kiyaye insha Allah."
"Tashi kije." uwargida ce tayi maganar, sunkuyawa nayi da fadin"Na barku lafiya." babu wacce ta kulani da sauri na fito gabana na bugawa, kai tsaye sashensa na nufa ina shiga na tarar da sabuwar hadimar da suka turo tana goge goge, harararta nayi na wuce, samansa na hau na tsaya bakin kofa ina bugawa
"Waye"? da sauri nace" Nice." "Kije babu abunda nake bukata an riga an gabatar min da komai." abinda yace min kenan ba tare da ya bude kofar ba, tsaye nayi ina mamakin maganarsa, an riga an gabatar masa da komai hakan na nuna min cewar dasa hannunsa gurin zuwan sabuwar Hadimar, na kai minti biyar a tsaye ina sa'kawa da kwancewa kafin na sauka kasa na sameta tana ta aiki.....hararar ta na sakeyi ina jin wani irin mugun haushinta, hanya na kama zan fita tace"Ke Sumayya wai me nayi miki ne tunda kika shigo kike hararata."
Juyowa nayi kamar zanyi magana sai kuma na fasa tsaki mai karfi naja na fice na barta taba bina da kallo
Koda na koma sashen mu kasa nutsuwa nayi na dinga tunane tunane marasa kyau ina idar da sallar magariba na koma sashen, babu kowa a falon shuru sai kamshi yake tsayawa nayi zuciyata sai sa'ke-sa'ke take min kai tsaya benan na nufa, hannu nasa na buga shuru beyi magana ba na sake bugawa gabana na faduwa gani nake Suwaiba na cikin dakin, can naji muryarsa a shaqe yana fadin"Waye."? da sauri nace"Nice ranka ya dade ka bude na gyara maka dakin." Still muryarsa a hard'e yace."Kije bana bukata." Gabana ne ya dinga faduwa kawai naji kwalla tana neman zubo min kasa barin gurin nayi sai kasa kunnena nake a jikin kofar dakin wai ko zanji wani abu shuru banji wata a alama ba na juya jiki a mace na sauka kasa, kicin na nufa nan na ganta a tsaye tana shirya abinci a tire ajiyar zuciya na sauke naji dadin ganinta a kicin din dan zuciyata babu irin sa'ke-sa'ke da ba tayi min ba.