← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 90

Sashe 4

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

7&8
Tamkar mai tausayin taka k'asa haka yake cire qafa yana tafiya kanshi a 'kasa hannuwansa a goye a baya, Shatima da Moddibo suna gefe da gefansa sai hira sukeyi masa yana dai jinsu da kunne amma ya gagara cewa uffan sai dai idan sun fadi maganar da ta bashi dariya yayi murmushi had'e da girgiza kansa, Yarima Ali mugun miskili ne wanda magana ke masa wuya shiyasa mafi akasari mutane ke ganin kamar dan wulakanci ne 'Dabi'arsa ce ta rashin son magana da hayaniya gami da rashin fara'a 'yan uwansa da iyayensa sun san wannan halin nasa tun yana yaro dashi ya taso, tun kafin su qarasa bakin kofar masu tsaron gurin suka zube gwiwowinsu a kasa sunkuyar da kansu sukayi hade da d'unkule hannuwansu alamun gaisuwa.
Shatima da Moddibo ne kawai suka d'aga musu hannu shi kuwa gefan da suke ma bai kallaba ballantana yasan sunayi.......Shatima ne yasa hannu ya bude narkekiyar kofar da zata sada su da falon Fulani wato mahaifiyarsa, A nutse yasa kafarsa cikin falon tare da sauke ajiyar zuciya, lumshe idonsa yayi yana jin wani irin sanyi na ziyartar zuciyarsa yau dai Allah ya dawo dashi gida gaban iyayensa hakika babu wanda ya kaishi farin cikin wannan rana......Bude lumsassun idanunsa yayi ya sauke su a kanta tana gishingide kan kilishi jakadiyarta na gefanta a zaune tana mata firfita da wani irin mafice, Mama fulani kyataccan murmushi ne a fuskarta ta zuba masa ido tana jin wani irin farin ciki a cikin zuciyarta.

Da sassarfa ya k'arasa kusa da ita yayi zaman raquma a gabanta tare da sunkuyar da kansa yace."Mammah hakik'a yau ni dake ban san wanda yafi wani farin ciki ba nasan zuciyarki tana cike da farin cikin dawowata gida wannan dalilin ne ya sanya na kasa shiga sashena nace lallai sai nazo nayi tozali dake uwa tagari nayi farin ciki dana dawo gida na sameku cikin koshin lafiya keda maimartaba da duk wani makusancina."

Ajiyar zuciya ta sauke ta gyara zamanta hannu ta dora a saman kansa a nutse tace"Allah yayi maka albarka babana nayi mutukar farin cikin dawowarka masarauta lafiya tabbas farin cikin da nake ciki a yau ba zai yafi gaban a kwatanta shi zuciyata tas take da ganinka cikin koshin lafiya babana ka kara girma kayi lafiya ka kara nutsuwa ka cika mutum ta kowane 'bangare babu shakka dole nagodewa ubangiji a bisa wannan karamaci da yayi mana ina rokon Allah ya raya min kai ya albarkaci rayuwarka da zuriar da zaka samu."

Hannunta dake saman kansa ya r'iko yasa a bakinsa ya sumbuta lumshe idonsa yay yana murmushi yace."Mammah nagode sosai da adduarki akoda yaushe ina alfaharin kasantuwarki a matsayin mahaifiyata."

Murmushi tayi tare da girgiza kanta ta mayar da hankalinta kansu Shatima dake zaune a gefe da gefansa, murmushi ta sakeyi tana kokarin magana suka fara gaisheta, hannunta ta d'ora a saman kansu tace"Ubangiji Allah yayi muku albarka ya had'e kanku kuyi zumunci dan Allah tabbas nasan kuma yau kuna cikin farin cikin dawowar d'an uwanku lafiya." Shatima yace.''Hakane Mammah hakika muna cikin farin ciki mara mislatuwa muna yiwa Allah godiya daya dawo mana dashi gida lafiya.

Har yanzu da murmushi a fuskarta tace"Yana da kyau ku rakashi ko wane 'bangare na gidan nan ya gaisa da iyayensa kamar yanda yazo ya gaisa dani."
Moddibo yace."Insha Allahu Mammah." Kallonsa tayi har yanzu yana durkushe a gabanta tace"Babana zakuje sauran sashen iyayenka ku gaisa kafin ka shiga gurinka ka huta nasa hadimai sun shirya maka komai da komai." Hannunta ya sumbata cike da bin umarni yace."Mammah abinda kikace shi za'ayi insha Allah."! Miqewa yayi a nutse ya kalli 'yan uwan nasa da fad'in " ku Tashi muje." Shatima da Moddibo suka miqe kai a kasa suka ce "Mammah a tashi lafiya." Hannu ta d'aga musu fuskarta yalwace da fara'a idonta a tsaye a kansu har sai da suka fita daga falon ta girgixa kanta gami da sunkuyar da kanta kasa addua take a cikin zuciyarta kan Allah ya cigaba da had'a kawunansu suyi zumunci tsakani da Allah.

*Tushen Labari*
Maimartaba Sarki Adamu Abdullahi dattijon mutum ne wanda ya iya mulki gami da jagoranci akan komai maimartaba Adamu Abdullah mutum ne mai tsananin tausayi da jin'kai, baya ta'ba yarda talaka ya kaskanta kuma bai yarda da cuta gami da zalinci ba, al'ummar garin suna mutukar jin dadin mulkinsa gami da yanda yake gudanar da hukunci akan wanda yayi zalinci, Sarki Adamu yana da 'Ya'ya amma dukkaninsu matane d'aya ne Namiji a cikinsu, sai dai 'yan uwansa suna da yawan 'ya'ya maza shi kadai Allah yayiwa albarkar 'ya'ya mata sai ya bashi guda d'aya namiji wanda yake mutukar alfahari dashi kasancewarsa mai tsananin biyayya a gareshi.....Mahaifin Waziri da galadima ya rasu dama a hannunsa suka taso tare da 'ya'yansa tare kuma duk suka gudanar da harkokin karatunsu.........Sulaimanu Dan uwan Sarki Adamu ne ciki daya suka fito shine ya kasance mafi kusa dashi a fada sarki Adamo baya zartar da kowane irin hukunci sai yayi shawara da d'an uwansa wato Waziri Sulaimanu, duk da wannan karamcin da maimartaba keyi masa hakan bai sa ya janye muguwar kiyayyar da yake masa ba da shida zuriarsa kullum burin Waziri Sulaimanu yaga bayan d'an uwansa dan ya tsani ya wayi gari ya ganshi kan karagar mulki.......Shi a yanzu baya sha'awar mulkin tunda shekaru sunja masa yafi sha'awar d'ansa Ciroma ya hau kan kujarar badan komai ba sai dan kada bayan babu ransu a duniya mulki ya cigaba da tabbata a hannun zuriar dan uwan nasa wato Sarki Adamu, shiyasa kullum cikin damuwa yake gami da tunanin ya za'ayi ya ruguza karagar mulkin d'an uwan nasa, Kullum cikin shirya manakisa suke shida d'ansa Ciroma maimartaba sarki Adamu Allah na kareshi daga sharrinsu, Waziri Salmanu ganin ya kwanta ciwo sai jikinsa yay sanyi yana ganin kwanansa ya kare bukatarsa bata biya a kan dan uwansa ba, tabbas jikinsa na bashi mutuwa zaiyi sai kawai ya kira d'ansa ya zaunar dashi suka yanke shawarar karshe a tsakaninsu.......Ciroma mutum ne mara tsoron Allah da tunanin makomarsa, Kai tsaye ya shiga biye biyen malaman tsubbu bai bari ba har sai da bukatarsa ta biya ganin ya durkusar da maimartaba, mugwayen aljannu sun shafe jinsa da ganinsa kana sun kumbura masa jiki yana kwance sai sai komai ayi masa.....Wannan al'amari yayi wa Waziri Sulaimanu dadi mutuka yana kwance rai a hannun Allah amma 'kara tsarawa d'an nasa sharri yake yi.
Hankalin iyalan Mairataba ya tashi mutuka gaya jama'ar gari suka shiga tsananin tashin hankali da damuwar rashin lafiyar data samu shugaba nagari malamai suka dinga bada taimakonsu iyakacin bakin kokarinsu.......Waziri Sulaimanu ya tara su kaf a guri daya yace"Tunda al'amarin ya kasance a haka to shi a matsayinsa na mai zartar da hukunci da yawun d'an uwansa wato maimartaba Sarki Adamu ya wakilta AbdulJabbar wato Ciroma ya zauna kan karagar mulki kafin aga abinda Allah zai zartar.....Da yawa daga cikinsu babu wanda yay na'am da wannan hukuncin to amma saboda gudun tashin hankali da gutsiri tsoma yasa sukayi fatan alkairi ga hukuncin da ya yanke........ba'a wani ja dogon lokaci ba Ciroma ya soma zama a fada ya cigaba da gudanar da mulki cikin rashin iyawa gami da tsantsar mugunta da zalinci.........A take jama'ar gari suka gane inda ya dosa gabad'aya yafi bada muhimanci akan harkar zalinci ko sharia aka kawo gabansa baya iya yanke hukuncin da sharia ta tanadar shi a ganinsa duk abinda yake daidai ne, Jama'a suka dinga k'orafi gami da surutai har labari ya isa kunan gomnati, a lokacin ta shigo cikin al'amarin bata kuma ja wani dogon lokaci ba ta sauke Ciroma daga kan kujerar mulkin, sannan kafin gomnati ta d'ora wani a matsayin sabon sarki sai da ta duba cancanta tukkuna ta za'bi Abdul-aziz ya maye gurbin mahaifinsa tunda shi cuta ta kwantar dashi.......Komai na saurata gomnati ta damqawa Abdul-aziz jama'ar gari suka dinga farin cikin samun sa a matsayin shugaba.......Wannan al'amari yayi wa Waziri Sulaimanu da d'ansa ciwo dan Ciroma kulle kansa yayi a daki ya dinga bankar giya yana tam'bele shi kadai sai zage zage yake yana surutai...........Waziri Sulaimanu kuwa sai muce tsabar bacin rai ne yasa ya had'iyi zuciya ya mutu sai shiga akayi aka ga gawarsa.....Hankalin iyalansa yayi tsananin tashi suka dinga kuka suna tofin alatsine ga zuriar Adamu suna ganin kamar sune sukayi sanadiyar mutuwar mahaifinsu.......Tun daga mutuwar Waziri Sulaimanu gaba mai tsanani ta shiga tsakanin zuria guda biyu har yanzu kuma itace akeyi 'ya'ya da jikoki sai dai kowa na kokarin 'boye bakin cikinsa akan dan uwansa amma daidai da kwayar zarra babu mai kaunar d'an uwansa..........bayan rasuwar Waziri Sulaimanu da sati uku Ciroma yabi dare da rana yaje ya sanyawa Sarki Adamu fillo ya toshe masa hanci murus! ya kashe shi har lahira ya fito daga dakin ba tare da kowa ya ganshi ba.....Shima iyalinsa shiga sukayi suka ga gawarsa al'amarin da yayi masifar tashin hankalinsu, Mutuwar Sarki Adamu ta girgiza zukatan al'ummar gari dayawa yawansu suka dinga kokawa suna fad'ar kyawawan halayensa............
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *[email protected]*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
Chapter 4 · 0% Book details