← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 90

Sashe 39

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi nayi nace"Ranki ya dade ki daina hadani da Allah akan wannan al'amarin, wallahi kinfi karfin komai a gurina shiyasa duk sanda wani abu ya taso naga kina bani hakuri nake mamaki! kada ki damu insha Allah nayi miki al'kawarin cigaba da kula da amanarki har zuwa lokacin da kika fada ina rokon Allah ya bani ikon rike amanarki.

Murmushi jin dadi tayi tace"Sumayya dole nayi miki godiya domin kin cancanta ayi miki komai kina da hankali da nutsuwa gaki da iya lafazi kyawawan halayenki sune suka sanya naji kin kwanta min a raina har na yarda dake a matsayin mai kula da gudan jinina dan haka dan nayi miki godiya ba abin damuwa bane."

Murmushi nayi ina jin kaunar matar a cikin raina, hakika da Yarima ya gaji halinta da karamcinta da baiyi wasu abubuwan ba na rashin kyautawa cikin nuna farin ciki da yabawar da tayi min nace."Ranki ya dade nagode sosai da samun yabo daga gurunki."
Kaina ta dafa a nutse tace"Allah yayi miki albarka." na amsa da ameen ina mirmushi. tace"Kina iya tafiya gobe idan Allah ya kaimu sai ki cigaba da aikin ki." Risinar da kaina nayi nace"To shikkenan ranki ya dade a tashi lafiya." A nutse ta amsa tana murmushi, gefan da yake zaune na kalla nace"Ranka ya dade a tashi lafiya." Ciki ciki ya amsa min. na mi'ke a nutse na fita daga falon

Koda na koma gurinmu samun Iyayena nayi a zaune a tsakar gida suna magana shigowa ta yasa sukayi shuru dukkaninsu suka bini da kallo, murmushi nayi na zauna kusa da babana a nutse nace"Baba ina fatan baka ci abincin ba." Cike da kulawa yace."Ai ban jima da shigowa ba mahaifiyarki ke sheda min inda kike." Ganin yanayin damuwa a tare dasu yasa nace"Eh hakane dan Allah ku kwantar da hankalin ku ba wani abun bane aiki tasa ni shiyasa kuka ga na dad'e."
Ajiyar zuciya ya sauke yace."To Alhamdulillah maza jeki dauko mana abincin muci." Da sauri na mike na nufi kicin domin dauko abincin...Tambaya daki ta shiga ta shiga gyara mana gurin kwanciya, nida mahaifina abinci muke ci a nutse muna hira cikin fahimtar juna shakuwar dake tsakanina da babana ba takai wacce take tsakanina da Tambaya ba, babana mutum ne mai sauki hali yana da barkwanci kullum cikin wasa da dariya yake kuma dukkanin abinda za'ayi masa na 'ba tanci ba zaka ta'ba ganin bacin ransa ba mutum ne wanda duniya da dukkanin abinda ke cikinta be dameshi ba.

Washe gari da wurwuri na tashi domin ina so naje nayi duk aikin da zanyi na gama a kan lokaci na samu damar zama gurin karatu, tare muka fita da babana ya nufi b'angaran dawakai ni kuma kai tsaye sashen Yarima na nufa, duk wannan sammakon dana buga samunsa nayi a shirye cikin k'ananun kaya da cup a hannunsa ya shirya tsaf da alama daf yake da fita gurin aiki. jikina ne yayi sanyi na kalli agogon bango nan naga karfe bakwai da rabi, shaf na manta ya fara fita aiki dana sani ina idar da sallar asubahi na shigo nayi ayyukana na huta.

Babu walwala a tare dani nace"Ranka ya dade barka da safiya ina fata ka tashi lafiya."?
Cup din tea din ya ajiye kan tevur din dake gabansa babu yabo babu fallasa yace."Barka kadai." Kicin na nufa ba tare da na sake magana ba. Suwaiba na samu tana soya doya da kwai gaisawa mukayi na tsaya ina tunanin abunyi....kamshin turaransa ne ya tabbatar mana da shigowarsa kicin,
Kasa nayi da kaina dan har yanzu ina ganin bakinsa, a nutse yace."Ke Ki ajiye wannan aikin da kikeyi me shi ta dawo kije kawai na sallame ki kada ki kara zuwa kiyi min hidima." Suwaiba ta ajiye abin hannunta a nutse tace"Godiya nake ranka ya dad'e."
Hanya ya nuna mata da hannunsa alamar ta futa, kai a kasa ta fita daga kicin din.
Shiru na minti biyu kafin naji gyaran muryarsa, dago kaina nayi babu walwala a tare dani, yace."Me yasa baki zo akan kari ba? ko kin manta na fara fita aiki.'' Nace"Wallahi na manta amma ka gafarce ni naga Suwaiba ta gama hada komai bari kawai na fito maka dashi.....girgiza kansa yayi alamun baya bukata.
Juya yayi zai fita yace."Idan na dawo daga asibiti ina da muhimmiyar magana dake."
Bayansa nabi da kallo ina mamakin wace magana zamuyi, har ya fice daga kicin din ban dauke kaina daga hanyar daya bi ba, na jima sosai a kicin din ina tunani akan maganarsa, ajiyar Zuciya na sauke ina addua akan Allah yasa al'kairi ne ke tafe dashi, kicin din na gyara tsaf na juye soyayyar doyar da Suwaiba ta soya a cikin kula na dauka na fita da ita, can gurin su Haruna na nufa na dire musu kular a gabansu, Haruna yana murmushi yace."Ranki ya dade me muka samu ne."? Cikin kulawa nace"Soyayyar doya ce na kawo muku Suwaiba ta soyawa Yarima tayi mishi yawa shine na yanke shawarar kawo muku." Cike da farin ciki ya kalli su Isa da fadin "Ku taso ga abin arziki Sumayya ta kawo mana." Gurin suka iso suna min godiya na dinga mamakin godiyar da sukeyi min. nace"Haruna ni zan tafi gurin karatu sai yamma zan shigo." Yace."To babu damuwa Sumayya." gurin na bari da sauri naje na dauko jakar litattafaina na wuce gurin karatu.....ko zaman minti ashirin banyi ba hayaniya ta tashi wani malami ya shigo ajinmu da fadin"Ke Sumayya fito." gabana ya fadi jin ya kira sunana! fitowa nayi daga cikin 'yan uwana ya tasa ni a gaba tun kafin mu karasa gurin na hango Haruna da Isa ri'ke da kirji sai kakarin amai suke, a gigice na k'arasa inda suke ina tambayar abinda ke faruwa Usuman ne yace."Ki rufe mana baki anan gurin ba kece silar faruwar komai ba."
Murya na rawa nace"Usuman ban fahimce ka ba dan Allah kayi min bayani." Tsaki yaja kafin yace."Tun bayan da sukaci doya da 'kwai din da kika basu cikinsu ya hautsine sai amai suke suna zawo ko ba kiga yanda kudaje ke bin gurin ba.''
Da sauri na shiga binsu da kallo naga yanda kudaje ke binsu suna tashi sai kakari suke suna yunkuri idanunsu yayi jajawur! kuka na fashe dashi nace"Wallahi tallahi bani bace." Buba ya kawo min mari a fusace yace idan baki rufe bakin ki ba yanzu zaki sha duka anan gurin." Gum! nayi ina zazzare ido hade da kallonsu Haruna dake durkushe a gurun.......Jakadan maimartana ne ya iso gurin shida wasu fadawa suka saka su Haruna a mota suka nufi asibiti, hankalina ya tashi sosai na juya domin shiga gurinmu, Jakada yace."Kece Sumayya ko."? da sauri na daga kaina. Yace."Muje Maimartaba nasan ganinki." gabad'aya gwiwata tayi sanyi jin abinda yace bani da yanda zanyi dole nabi bayansa zuwa fadar Maimartaba nasan dai zai tuhume ni ne akan abinda ya faru dasu Haruna........

*Na kudi ne!*
Allah ya isa idan kika karanta! idan kina so ki biya ga yanda abin yake vip group #600 normal group #300 account.. 0542382124...Binta umar gtbank idan kati zaku turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
73&74
Da 'kyar na iya cin abinci na mik'e domin wanko hannuna dakin na dawo na same su suna magana shigowata yasa suka tsira min ido, a nutse nace"Zanje sashen Yarima koda abinda yake bukata nayi masa, cike da tausayi da kulawa sukace "To sai kin dawo." Fitowa nayi daga dakin nasa takalma na fita.

Koda na shiga falon shuru babu kowa da alama yana sama ko kuma be shigo ba, juyawa nayi da niyyar shiga kicin naji motsinsa, a hankali na juyo ina kallonsa yana sakkowa, kaina na sunkuyar har ya sauko ya zauna kan kujera gaishe shi nayi hade da fadin"Ko kana da bukatar wani abu.'' Kai ya girgiza kafin yace.''Bana bukatar komai kije ki huta." Tsira masa ido nayi......ganin inaso nayi magana yasa yay saurin katse ni da fadin"Sarkin zargi da rashin yarda nace kije ki huta naci abinci a gurin Mamma.

Sarkin zargi da rashin yarda maganar nayi ta nanatawa a cikin raina wato duk abinda nake nunawa a kansa bai dameshi ba tunga gashinan yayi min wata fassarar tunda nake kula dashi dayi masa hidima bai ta'ba yi min godiya ba ko kuma ya nuna min jin dadinsa kullum cikin fada min bakar magana yake, kaina na girgiza ba tare dana sake magana ba na juya da niyar fita daga dakin.

"Sumayya." a kasalance naji ya kira sunana, juyowa nayi muka hada ido dashi, yace."Idan hankali ya kwanta inaso muyi magana dake." ajiyar zuciya na sauke ina kallonsa ido da ido nace"Ko wace irin magana ce take bakin ka zaka iya fada min a yanzu ina sauraronka."

Girgiza kansa yayi yana lumshe ido yace.''Sai kin samu nutsuwa tukkuna dan na fahimci yanzu bakya cikin hayyacinki." Kaina na girgiza tare da fadin"Babu damuwa Allah yasa naji alkairi." Murmushi yay had'e da shafa sajensa yace ."Alkairi ne insha Allah.'' Ganin yana munafikin murmushi yasa na tsargu babu shakka har yanzu akwai mugun abu a cikin zuciyarsa, sallama nayi masa na kama hanya na fita ina mamakin al'amarin

Cikin kwanaki bakwai da rasuwar Isa al'amura sun d'anyi sauk'i masarautar ta samu nutsuwa kowa ya fawwalawa Allah ya cigaba da harkokinsa 'bangaran basawan masarautar kuwa kullum cikin shirya kitumurmura da ma'kar'kashiya sukeyi har yanzu sunqi saduda burinsa bai wuce ace sunga bayan Yarima Ali ba inda shi kuma nashi bangaran kullum zuciyarsa fes take a kansu baya ta'ba yarda da cewa sharrinsu da makircinsu zaiyi tasiri a kansa tunda ya riga ya kad'aita Allah yayi ya'kini da cewar babu abunda zai sameshi sai abinda Ya hukunta, ko a fuska bai ta'ba nunawa kowa ba duk bayan kwana biyu sai ya shiga kowane sashe na gidan sun gaisa inda su kuma suke nuna masa kauna a fili a bad'ini kuwa su kadai suka san irin 'kiyayyar da suke masa
Chapter 39 · 0% Book details