Sashe 15
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Motsin tsayuwarsa naji a bakin kofa nayi saurin juyawa ina kallonsa, tsorata nayi sosai ganin yanda yake kallonsa da idanunsa da sukayi ja gashi sai lumshesu yake......Baki na rawa nace"Ranka ya dade kana bukatar wani abu ne."? Girgiza kansa yay alamun baya bukatar komai.
Jikina a sanyaye na juya domin cigaba da aikina amma inaa! tsabar yanda idonsa ke tasiri a kaina yasa na kasa ta'buka komai.
'Kasa - 'kasa naji yace.'' Idan kin gama kizo ki gyara min toilet d'ina." Na kalleshi inaso nayi magana sai naga ya juya ya tafi.
Tsayuwa nayi ina mamakin maganarsa na dauka ai gyaran gida dasu toilet duk nasu Haruna ne ni bani da hurumin hakan, to kodai yana da wata munufa ne? wani sashe na zuciya ta yake fada min haka.. shuru nayi ina nazari, to ko ma dai wace irin manufa yake da ita a kaina bana fatan ya samu galaba a kaina toilet zan shiga in gyara masa da tsarkakkiyar zuciya. saboda haka ina gama ayyukana na nufin dakin nasa domin aikata aikin daya umarceni.
Zaune na sameshi a kan sofa idanunsa tsaye a kofar shigowa hada ido mukayi nayi gaggawar sauke kaina kasa, cikin tsarguwa na k'arasa kofar toilet din zanin jikina sai hard'eni yake tsabar yanda ya 'kureni da idanunsa, toilet din na bude na shiga ba tare da nace masa komai ba gaskiya na fara gajiya da wannnan masifaffan kallon da yake min.........Girman toilet din da yanda aka 'kawata shi ya dinga bani mamaki bandaki gurin zubar da najasa an narka masa dukiya kamar baza'a mutu ba, girgiza kaina nayi na tattare zanina cikin sauri na soma aikina so nake nayi saurin gamawa kada magariba tayi.....Undis dinsa na tattara nasa cikin abin wanki ina kokarin kunna washing machine din ya shigo toilet din, ban yarda na kalleshi ba nace"Ranka ya dad'e za kayi wani uzirin ne."? Inda nake tsaye ya durfafo gabana ya tsananta fad'uwa adduar rinjaye na shigayi a cikin zuciyata.
Daf dani ya tsaya yana fesa min hucin numfashinsa, kasa kallonsa nayi sabida yanda naga ya koma wani iri gabadaya yanayin fuskarsa ya sauya kalar tausayi. babu zato naji ya riko hannuna ya d'ora saman short nickar din dake cikinsa, a zabure! na cire hannuna ina kallon gurin.....gabansa naga ya mike cikin wandon yana sake kokarin kamo hannuna yasa a gurun....bangajeshi nayi da karfin gaske! yayi taga-taga zai fad'i! cikin zafin nama na bude kofar toilet din na fita gabana na dukan uku uku anya kuwa zan iya cigaba da zama da wannan guy kuwa? gabadaya yanda na fahimce shi baya nufina da alkairi.
Bayan fitar ta daga toilet din goshinsa yasa a jikin bango (garu) yana furzar da wani irin huci mai zafi daga bakinsa, ya rasa wace irin masifa ce wannan gabad'aya ya rasa gane kansa da abinda ke damunsa burinsa bukatarsa ta biya da yarinyar ita kuma taki ta bashi had'in kai yarinyar gabadaya ba tsaransa bace har ya ajiye girma da muqamin sa yana biyayyarta tana wula'kantashi yana ganin dole ya nuna mata kuskuranta akan irin abinda take masa, da kyar yay wanka ya daura alwala ya fito fuskar nan babu fara'a ya kintsa jikinsa, k'asa ya sauka, lokacin na kammala komai na shirya gurin cin abincin ina zaune abin duniya ya isheni......tunda naga yanayin fuskarsa nasha jinin jikina, koda ya karaso inda nake sake risinar da kaina nayi da fadin"Barka da fitowa." Wuce ni yayi ya nufi hanyar fita ba tare da yace komai ba. bayansa nabi da kallo ina ayyana abubuwa da yawa a kansa.
Bayan fitarsa da minti goma nima na bar gurun.
Sai bayan daya gabatar da sallar isha'i ya shigo kai tsaye gurin cin abinci ya nufa ya zauna daya daga cikin kujerun gurin, wayarsa ya d'auko ya shiga ma'adanar hotuna tarin pictures ne na matan turawa da bakake fata wanda ba zasu irgu ba, yawanci kuma duk tsirara suke pictures din yake kallo wai ko zai samu sasaaucin abinda ke damunsa. Cikin wannan halin na fito na sameshi, kai tsaye inda yake na nufa.
Dan risinawa nayi murya k'asa nace''Ranka Ina iya zuba maka abincin." A watse ya kalleni yace."haka kawai zan zauna anan gurin babu dalili."? Da sauri nace"Afuwa ranka ya dade." Mikewa nayi cikin nutsuwa na bud'e fulas din dana sa tuwon a ciki na dauk'o leda biyu nasa akan plate na mayar da fulas din na rufe miyar na bud'e itama nasa ma a plate na bude daya fulas din dake dauke da jar miya waccan nasa mata naman rago itama nasa masa a plate kana na mayar na rufe ruwa da lemo na ajiye masa gabansa naja gefe na tsaya kaina a kasa nace"Ranka ya dad'e na had'a komai."
Dago kansa yayi yana bin abincin da wani irin kallo yana ya mutse fuska yace."Ke! wannan wane irin tuwo ne ba'ki sai kace ke."!! Naji ciwo cimin fuska da yayi, cikin dauriya nace"Ranka ya dade tuwon dawa ne.'' Tsaki yaja mai karfi ya mike a fusace ya d'aga k'yallen da abincin ke kai ya watso min a jikina.! cikin rashin mutunci yace."Waye zaici wannan ba'kin abun ko an fad'a miki kowa ma jaki ne kamar ki! dallah malama matsa ki bawa mutane guri."! Cikin hayaniya yake maganar har yana dukan daning d'in da hannunsa....
*BINTA UMAR ABBALE*
*Kuyi sharing pleaseðŸ‘ðŸ»*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALEðŸ’_ *[email protected]*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊ðŸ?)
31&32
Cikin wani irin yanayi na 'kunar zucci nake kallonsa kafin na kalli jikina gabad'aya gaban rigata ya 'baci da miya har wajejen wuyana da gefan fuskarta ya samu rabonsa, idona naji yana kawo ruwa wannan irin wulakanci ne dacin mutumci mutumin nan yake min, danne damuwa ta nayi na kalleshi yana zaune sai huci! yake kamar wanda akayiwa gagarimun laifi nace"Ranka ya dad'e kai ne ka bukaci da ayi maka tuwo ni kuma sai nayi tunanin tuqa maka na dawa saboda nasan abun marmari ne zai fi maka dadi akan sauran dan me zaka wulakanta ni ka wulakanta abinci babu kyau abinda ka'aikata domin akwai mutane da yawa da suke neman abinda zasu kai bakinsu kai ka samu kana watsar wa."
Cike da jarumta nake maganar.
Wani irin kallo naga yanayi min na k'askanci kafin ya tattaro yawun bakinsa ya tofa min a fuska cikin izigalanci yace."Ki 'bace min daga gurin nan na daine ganin wannan ba'kar fuskarta ki a idona."
Takaici kamar ya kasheni nasa hannu na goge yawun daya tofa min, baki na bude zanyi magana ya daga min hannu alamun baya bukatar yaji abinda zance, banyi shuru ba domin na riga na dauki aniya akansa, Nace''Kana yawan kushe hallitar Allah shin wai me bak'in mutum yayi wa mutane ne da suke 'kyamatarsa kada ka manta yadin da akayiwa d'akin Allah ado ba'ki ne,, da farin mutum da b'akin mutum duka Allah ne ya hallicesu kuma bai fifita wani akan wani ba duk daya suke a gurinsa wanda yafi kyautata masa shine mafi kusanci dashi, amma kun d'auki karan tsana kun d'orawa 'bakar hallita wannan yana nuni da cewar kuna nunawa Ubangiji cewar bai hallita ba."
Mi'kewa tsaye yayi ya nuna min kofar fita da hannunsa. Girgiza kaina nayi na bar gurin zuciyata na wani irin tafarfasa gabad'aya halayyar sa bata da kyau girman kai gami da izzah muna nan ayyuka ne wanda Allah baya so yana da ilimin addini daidai gwargwado yasan abubuwan da yake aikatawa basu da kyau amma saboda shed'an ya riga ya gama yi masa fitsari akansa kullum daukar kansa yake wata tsiya alhalin kuma a gurin Allah ba komai bane.
Koda na shiga gurin mu kai tsaye ruwa na zuba a bokiti na shiga band'aki domin wanke jikina nasan idan na shiga daki iyayena suka ga jikina a 'bace zasu tambayi dalili shiyasa nayi wannan dubarar, bayan nayi wanka zanin kamfalar na d'auro a kirjina na yafa dankwalin na fito, ina tsaka da d'aura alwala Tambaya ta fito daga daki, tace"haba ni tun dazu nake jin motsi ina daki nace bari dai na duba na gani ashe kece."tana kallon fuskata tafadi maganar, kokarin kawar da abinda ke damuna nayi nace"Ai ina shigowa bandaki na nufa nayi wanka ko jikina ya warware." Tace"Ai kam wannan uban wanki da kikayi ai dole jikin ki yayi miki tsami amma me yasa baki d'umama ruwan zafi ba? ina ganin da da ruwan zafi kikayi wankan sai kinfi jin dadi."
Nace"Nima sai da na fara wankan sannan nayi tunanin hakan." Tambaya kicin ta wuce domin ajiye kwanonin abinci dake hannunta ni kuma bayan na daura alwala dakin na shiga na samu babana zaune a kan dadduma yana lazimi sannu nayi masa na shige cikin kuryar dakin domin na kimtsa jikina.
Irin dai kayan nasa a jikina na fito da hijabin da nake sallah a wuyana, dadduma na hau na tayar da sallah..........Tambaya ta shigo dakin hannunta rike da silba mai murfi a kusa dani ta ajiye silbar tace"Idan kin idar ga abincin ki nan." kuryar dakin ta shiga domin gabatar da tata sallar, bayan na idar da sallar na jima hannuna a sama ina rokon Allah yasa naci jarabawar daya d'ora min na kuma tsananta addua ta akan ya kareni daga sharrin masu sharri. shafawa nayi a fuskarta na juya ina kokarin cire hijab din wuya na, sai naga babana na shafa fuskarsa da dukkanin hannuwansa hakan ya nuna min cewar adduata yake shafawa a fuskarsa.
Ina murmushi nace"Baba barkan ka da dare." Shima da murmushin a fuskarsa yace."Barka dai yarinyar arziki." silbar abincina na janyo a nutse nace"Naso na dawo da wuri muci abinci a tare domin samun tabarraki." da yalwatacciyar fara'a a fuskarsa yace."Na riga naci abinci Sumayya amma kawo na sa miki albarka."