← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 90

Sashe 54

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kusa da ita tace"Lami ki daina kuka haka dan Allah ku dauko mata igiyar akwai alamun gaskiya a maganar yarinyar nan watakila zarginta kawai muke saboda haka ki dauko mata igiyar."

Shuru lami tayi tana nazari kafin tace."Uwani wallahi ba zance miki ga inda igiyar nan take ba lokacin dai da'aka shigo da gawarsa na ganta a daure a hannunsa, sai dai ku duba gurin da'a kayi masa wanka ko zaku ganta."

Uwani tace"to bari na duba." Mikewa nayi da sauri nabi bayanta, sako da loko na gurin muka duba tsaf ba muga igiyar ba jikina yayi sanyi muka fito daga gurin, Uwani tace"Muje Shara mu duba mugani ko anshare.......Muka zazzage sharar a gurin duka muka tona babu igiya, Uwani tace"Kinga ni babu alamun igiyar nan a gurin, amma bari a kira wa'inda sukayi masa wankan."

Uwani da sauri ta fita ni kuma na jingina a jikin bango(garu) ina tunanin al'amarin, tare suka shigo su uku ita ta hud'u, had'a ido mukayi da Hamza na hango firgici a tare dashi, Uwani tace"Hamza kune kuka wanke gawar Haruna to binkice ne yazo ana bukatar igiyar hannunsa mahaifiyarsa ta tabbatar da cewa lokacin da'aka shigo da gawar akwai igiyar a hannunsa."

Labaran yace."Tabbas kuwa ni ne na kwance igiyar daga hannunsa, na ajiye a gurin." Salisu yace."Kwarai kuwa nima na ganta da idona wallahi." Hamza cikin dauriya yace."Nima naso naga lokacin da kake kwance ta sai dai yanayin tashin hankalin da nake ciki yasa shaf na manta ban dauketa ba." Nace"To gashi dik mun duba guraran da kuka zauna ba muganta ba." Cikin firgici Hamza yace." Ku muje mu sake dubawa." Dukkaninmu muka bi bayansa, ya dinga lalube a gurin baiga komai ba, yana sharce gumi ya dago muka hada ido sai yayi saurin dauke kansa yace."Amma al'amarin nan akwai ban mamaki gashi duk an duba ba'a ganta ba." shuru babu wanda yayi magana yace."Ku muje mu duba shara." Uwani tace"Wace shara kuma bayan duka mun duba." A sanyaye ya tsaya yana kallonmu, ajiyar zuciya na sauke ina wani tunani, anya kuwa babu sa hannun Hamza a gurin kashe abokinsa? nace"Uwani tunda ba'a ganta ba ni zan tafi Allah ubangiji ya tona asirin munafukai." Uwani ta amsa da ameeen ya Allah." gurin na bari na barsu suna sake tattauna maganar.

A ranar yini nayi cikin zullumi da tunanin yanayin furgicin da naga Hamza ya shiga na dinga tunanin anya kuwa be san wani abu daya shafi 'batan igiyar Hannun Haruna ba? tsabar damuwa da tunani ya janyo min ciwon kai mai tsanani idanuna sukayi jawur tamkar wacce taci kuka ta koshi nan kuwa tsabar fargaba da damuwa ce, Tambaya ganina haka yasa ta shiga damuwa ta dinga rarrashina da bani kulawa, ganin yanda duk ta tashi hankalinta yasa na sassautawa kaina tunani kawai na mika al'amarin ga Allah na cigaba da addua akan Allah yayi gaggawar tona asirin wa'ina suke shirya wannan mugun abun.

*Bayan sati hudu*
Al'amura sunyi sauk'i masarautar ta samu nutsuwa kowa ya kwantar da hankalinsa ya koma harkokinsa harshi Magajin sarkin ya koma aiki dama tunda gwamnati tayi dogon binkice ta gane daga inda badak'alar ke fitowa yasa ta bada umarnin bude asibitin tare da kira ga Jamaa cewa su cigaba da shige da fice a asibitin babu abinda zai sake faruwa da yardar Allah." Wannan kira da gwamnati tayi ga al'umma yasa kowa ya kwantar da hankalinsa, Asibitin *Zinariya* ya ci gaba da gudanar da aiki kan tsari da sanin ya kamata.........Al'amarin yayi masifar 'bata rayukan wa'inda suke adawa da samuwar asibitin dukkaninsu sai suka yanke shawarar karshe akan asibitin amma ba zasu aikata aikinsu ba sai ankwana biyu tukkuna sai kowa ya sakin jikinsa sai su kuma su gudanar da abinda suka shirya,

'Bangaran Yarima ya samu sabbin hadimai kamar yanda Acp ya bukata, kuma kamar yanda yayi alkawarin kawo jami'an tsaro guda biyu ya cika al'kawarinsa ya kawo jami'ai gudu uku tare da amincewar gwamnati, sosai gurin yayi lafiya kowa yana gudanar da aikinsa yanda ya kamata, jami'an tsaron sunsa ido sosai da sosai dan ba kowa suke bari ya shiga sashen kai tsaye ba sai sunyi binkice a kansa tukkuna suke bari ya shiga, mutukar kuwa Yarima baya nan to basa barin kowa ya shiga har sai ya dawo nima ina gama ayyukana nake fitowa.

'Karfe hudu da rabi na ranar talata na fito daga gurin karatu kai tsaye sashen Yarima na nufa domin gudanar da aikina, tun daga nesa na hangoshi a tsaye a bakin kofar shida jami'an tsaron, fuskarsa kadai na kalla na hango tsantsar bacin rai a tare dashi,

Koda na k'arasa gurin nan na fahimci akan abinda yake faruwa, wato yana so ya shiga sashen Su kuma sun hana shi sunce yayi hakuri mai gurin ya dawo daga aiki! Muddibo ya dinga huci yana sakar maganar da duk tazo bakinsa, Daya daga cikinsu yace."Ranka ya dade ba wannan muke nufi ba ai mun san kai ba zaka ta'ba cutar dashi ba muna so ka fahimci yanda tsarin namu yake Shugabanmu dashi kansa mai gurin yace kada mu bar kowa yana shiga sai da izininsa saboda haka kayi hakuri idan ya dawo ya bamu umarni sai mu barka ka shiga."

Muddibo ya dinga wani irin huci! yana zaginsu, gami da fad'in "Idan mai gurin ya dawo zai nuna musu muhimancinsa a gurinsa." a hankali nace"Ranka ya dade barka da yamma." ko kallona beyi ba ya bar gurin, Da sauri daya daga cikinsu ya bude min kofa da fadin"Maza shiga kiyi aikin ki ki rabu dashi." Da sauri na shige ina mamakin al'amarin, to me ya kawo Muddibo sashen Yarima bayan yasan baya nan? idan an bude masa ya shiga me zaiyi a ciki, ina ayyukana ina tunanin al'amarin, sai bayan magariba na gama aikina na fito lokacin sun fito daga gurin sallah bude min kofa sukayi na fita tare dayi musu bankwana,

Ganin gari yayi duhu yasa na kara sauri domin isa gurinmu kawai naji an tare ni!! gabana ya fadi ina dago kai muka hada ido dashi! ido jawur yake kallona cikin dauriya nace"Ranka ya dade kana bukatar wani abu ne."? Wawan mari! ya kwada min na fadi a gurin! tsaye na mike ina kallonsa hannuna dafe da kumatuna! wuya na ya shaqe na dinga kakari!! sai da ya galabaitar dani tukkuna ya sake ni! na sake faduwa a gurin! Ya tsuguna gabana yana kallona ina kallonsa makogwarona ya bushe kamas! Yace."Zan saki aiki a sashen Yarima wallahi tallahi idan kika kuskura kika ki aikatawa sai nabi dare da rana na kashe ki."!!!! Gabana ya dinga faduwa! ya cigaba da cewa'' Kin saba lalata mana aiki to wannan ce damarki ta karshe mutukar banga biyan bukatata ba to ki tabbata zakiyi kwanan barzahu! sai na kasheki.''!!! nace"Ranka ya dade babu mai kashewa sai Allah haka kuma babu me rayawa sai Allah! mutukar kaga na mutu to kwana nane ya k'are."

Hancina ya kaiwa duka! a take ya fashe! jini ya shiga shatata! ido jawur nake kallonsa, sai huci! yake! nace"Ranka ya dade wane irin aiki zanyi maka."? Murmushin mugunta yayi yace."Wato kinga uwar bari ko."? shuru nayi ina kallonsa hancina na cigaba da zubar da jini! Hannu yasa a aljihu ya d'auko wani abu a d'aure a takarda! " Wannan maganin nake so kisa masa a lemo." Kar'ba nayi ina kallonsa, yace."Kin gane ko."? kaina na daga masa! ya yunkura zai mike tsaye na kwance maganin na watsa masa a fuskarsa! da sauri na mike tsaye! zan gudu, ya tad'o kafata na fad'i a gurin! cikin fitar hayyaci na 'kwallara 'kara! wanda yayi daidai jin saukar wani irin bugu a kaina! idanu na na rintse na zube a gurin ina kiran sunan Allah! Muddibo na jin sawun mutane da sautin maga
na yasa da saurin gaske ya bar gurin..............

*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya keda kika futa da littafin keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake Vip gruop#600 normal gruop#300 account... 0542382124...Binta umar gtbank idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:27 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
85
Hayaniyar mutane na dinga ji sama-sama a kaina na mika hannu cikin mawuyacin hali nace"Ku taimake ni ku kira min iyayena mutuwa zanyi." Rumfa sukayi a kaina suna so su tantance abinda ke faruwa, cikin bushewar makogwaro na sake cewa"Uwani ku taimaka min ku kira min iyayena mutuwa zanyi." Uwani tasa salati tana fadin"Ai wannan Sumayya 'yar gidan Lawi ce." Da yake da karfi tayi maganar babu wanda beji ba, Tambaya turmutsawa tayi cikin mutane ta iske inda d'iyarta ke kwance cikin jini! dan dutsen da Muddibo ya buga mata yayi nasarar fasa mata kai.
Jiki na kyarma ta zube a gabanta hawaye na shatata a fuskatarta hannu tasa ta tattaro ta jikinta ta rungumeta tana kuka had'a kiran innalilihi wa'ina ilaihi raji'un.! Mika'il ne ya karaso gurin da toch a hannunsa yana haskawa dawowarsu kenan yaje ya dauko Yarima daga asibiti ya samu labarin abinda ke faruwa shine yazo ya ganewa idonsa, aikuwa ganin Sumayya cikin mawuyacin hali yasa a guje yaje ya shedawa Yallabai din halin da ake ciki.

Tare suka zo gurin da jama'i guda d'aya lokacin Sumayya ta suma dan bata san wanda yake kanta ba, Tambaya kuka kawai take tana jijjigata gami da kiran sunan Allah tana langwa'bewa! Jama'ar dake kewaye dasu suna ganinsa suka bashi hanya, ganinta cikin jini ya daga masa hankali, tsugunawa yayi yana kallon fuskarta, Tambaya ta fashe da kuka da fadin"Ranka ya dade ka taimaka mana kada mu rasa ta." Maganarta ce ta dawo dashi nutsuwarsa ya kalli Lawi dake gefe a tsugune ya had'a uban tagumi! yace."Me ya faru da ita."? Lawi yace."Wallahi ranka ya dade dukkaninmu bamu san abinda ya faru ba kawai dai munji ihunta ne koda muka zo gurin sai muka ganta kwance cikin jini."
Chapter 54 · 0% Book details