← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 90

Sashe 30

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa nayi ina jin kunya da nauyi na shiga daki, kayana na tube nayi shirin wanka.......Bayan nayi wanka naci abinci gurin karatu na nufa karfe biyar da rabi mun taso Lahira na bawa jakata nace ta kai min gurin mu kai tsaye sashen Yarima na nufa

A falo na same shi yana kallace-kallace a tv gaishe shi nayi ya'ki amsawa mikewa nayi na nufi kicin na shiga aikina............Tsaf na shirya mai abinci na jera komai kan tire mai fadi ina kokarin dauka ya fad'o kicin din.

Gabana ne ya fadi da sauri na risina ina gaishe shi, sama-sama ya amsa yace."Yawwa kin gama abincin ko."? kaina na daga masa gabana na bugawa.

Wata yar takarda ya ciro daga aljihunsa ya kwance cikin bada umarnin yace."Bude abincin.'' a sanyaye na bude fulas din, maganan ya zazzage a cikin miya yace ."Sa cokali ki juya sosai." da sauri nayi yanda yace."maza dauki muje." da sauri na rufe fulas din na dauki tire din hanya ya nuna min da hannunsa, na fito falon ina diri-diri!! cikin tsawa! yace."Wuce muje sama ki kai masa abincin yana can mutukar naji maganar nan ta fito sai na kashe ki."

Da sauri na shiga hawa benan har ina had'awa da biyu, shawarwari nake da zuciyata shawarar karshe na yanke da zuciyata, da gangan na gurde kafata na fadi a gurin sosai na bugu da karfen benan tire din abincin da abubuwan dake kai suka watse a gurin fallatsin miya har jikin rigarsa.

Cikin zafi nama ya mi'kar dani tsaye! wuyana ya matse yana tsuma yace."Kina sane kika zubar da abincin nan ko."? idanuwana sun gwalalo waje sabida wahalar sha'ka na girgiza kaina, alamun A'a, hannu ya fitar ya tsinka min mari wanda sai da hancina ya fashe na dinga jin dummm! a kunnena! dishi dishi nake kallonsa yana wani irin huci!! ya sake fitar da hannu zai mare ni, Yarima ya bude ya kofar dakinsa

Ganinta sha'ke a hannun Muddibo yasa da sauri ya k'arasa gurin kokarin cire hannunsa yake daga wuyana yana sake matse ni.....cikin b'acin rai yace."Muddibo wai me tayi maka ne ka matse mata wuya haka."? Yana huci yace."Ka duba jikina da kyau ka gani yarinyar bata san ta ratse a wani a gurin na wuce ba ta hada kafada da kafada dani har sai da ta samu nasarar 'bata min jiki da miya."

Kallon jikinsa yayi yaga duk jar miya a jikin rigarsa hakuri ya shiga bashi yana kokarin cire hannunsa dake d'amke da wuyana, da kyar Muddibo ya cika ni na zube a gurin ina tari makogwarona ya bushe sosai sai zare ido nakeyi ina kallonsu suka sauka k'asa a tare, sunkuyar da kaina nayi ina kiran sunan Allah a cikin zuciyata.

*Na kudi ne*
Kika karanta baki biya ba Allah ya isa! idan kina so ki biya ga yanda abin yake...Vip group #600 normal gruop#300 account....0542382124...Binta umar gtbank.....idan kati zaki turo #400 sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:26 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
57&58
Sai da na samu nutsuwa tukkuna na mike jikina a mace na sauka 'kasa sunkuyar da kaina nayi ban yarda na kalli inda suke ba na wuce kicin tamkar kazar 'kwai ya fashewa a ciki. gabadaya jikina ya mutu ina tunanin da Muddibo ya samu nasara kashe ni yayi niyyar yi, tsintsiya da abin kwasar shara na dauko ina fitowa muka hada ido dashi, ganin fuskarsa nayi tamkar hadarin dake daf da zubar da ruwan sama da sauri na janye idona cikin zuciyata nace''duk wani abu da nake akanka inayi ne domin mahaifiyarka daba dan daraja da mutuncinta ba wallahi da bazan zauna ina wahalar da kaina ba......gurin na gyara tsaf nayi mopping dinshi ina kokarin sauka kasan sai gashi, ratsewa nayi na bashi hanya yazo daidai dani yana hararata da fadin"Na dauka nima kafad'a da kafad'ar zakiyi dani."

Sunkuyar da kaina kasa nayi ina Allah-Allah ya wuce dan bana bukatar tashin hankali

"Kizo ina san ganinki." Da sauri na dago kaina naga ya wuce ni yana kokarin bude dakinsa, sai da ya shiga tukkuna na ajiye mopper hannuna bayansa nabi ina adduar rinjaye.

Samun sa nayi kan sofa yayi zaman kasaita na tsuguna dan nesa dashi babu walwala a fuskata nace"Gani." sai daya mula tukkuna yace."Ashe haushi kika ji dan na kore ki daga sashena shine kikaje kika hadani da mahaifiyata ko."?

Babu fara'a a tare dani nace"Banji haushi ba wallahi sai ma farin ciki da nayi naje na fad'awa mahaifiyarka ne domin yana da kyau ta san cewar ka kore ni tunda itace ta turo ni nayi maka hidima ni ban fada mata domin na shiga tsakaninku ba."

Tsaki yaja yana min kallon kaskanci yace.''Ke dai kika sani munafuka kawai tunda kin nace sai kinyi min aiki sai kizo na saki aikin kuma wallahi kikayi min gardama ranki sai ya 'baci.''

"Ranka ya dade ko wane irin aiki ka sanya ni zanyi maka mutukar bai sha'ba sharia ba."

Shuru yayi min yana duban k'asa nasan idan ya tsirawa kasa ido yana daukar lokaci yasa nima na dauke kaina ina jiran ya gama.

sai da ya dauki mintina goma tukkuna yace."Shiga toilet ki hada kananun kayana ki wanke." ba tare da nace komai ba na mike na nufi toilet din.....Bin bayanta yayi da kallo har sai da ta shige ya dauke idonsa shi dai ya rasa yanda zaiyi da rayuwarsa sha'awarta kullum karuwa take yayi yayi ya cireta daga ranshi abin ya fassakara ya rasa wace irin masifa ce Allah ya dora masa.

Duk kananun kayansa dake toilet din sai da na wanke tas na shanya inda aka tanada toilet din na gyara yayi tsaf tsaf dashi na fito na same shi zaune a inda yake ya kurawa tv ido.....nishin dake tashi a cikin tv yasa nai saurin kallon gurin mace da namiji ne suke sex sai nishi suke namijin yana kan macan ta daga kafafunta sama shi kuma sai bugunta yake tana nishi hade da sambatu.

Da sauri na dauke kaina ina fadin"Subahanallahi! kallonsa nayi naga idanuwansa sunyi jajawur! ya k'ura min ido yasa lips dinsa na kasa a baki yana tsotsa, tsorata nayi da yanayin sa nayi gaggawar kama hanya domin fita daga dakin wata zuciyar tace "Ki tsaya ki tunasar dashi abinda yake aikatawa bai dace ba.

Juyowa nayi still idonsa na tsaye a kaina, nace" Ranka ya dade kaji tsoron Allah kaji tsoron ranar haduwarka dashi, wallahi wannan abinda kakeyi sam bai dace da kai ba, yanzu meye amfanin ganin tsaraici Allah ya la'anci mutanan dake ganin tsaraicin wani wannan dan abun daka raina yana iya janyo maka fushin Ubangiji ranka ya dade a daidai wannan lokaci ya kamata ace kana massalaci kana salati kafin a kira sallar amma ka zauna kana kallon shed'anu kafurai wa'inda Allah ya la'ance su fisibilillahi meye fa'idar abinda kake aikatawa."
Har na kare maganata idanuwansa na tsaye a kaina. ganin bece min komai ba yasa na girgiza kaina na kama hanya zan fita.

A sanyaye naji ya kira ni "Sumayya." juyowa nayi a karo na biyu ina kallonsa, nadama nagani a fuskarsa, yace."Zo nan muyi magana." Zuwa nayi na durkusa gefansa ina addua Allah yasa ya dauki nasiha ta.

"Zoki zauna nan muyi magana." kusa dashi ya nuna min wai naje na zauna, gaskiya ba zanje ba dan ina tsoron abinda zai biyo baya.

"Ranka ya dade ba sai nazo kusa da kai ba zan fahimci abinda xaka fada kunnuwana naji duk abinda zakace." romot ya dauka ya kashe tv kana ya juyo yana kallona, ni kallon da yake min shine yake d'aga min hankali dan a tsorace nake a dakin.

Sai da ya gama kallona tukkuna yace."Naji nasihar ki nima kuma nasan abinda nake yi bashi da kyau na rasa yanda zanyi ne Sumayya a duk lokacin da kika gifta ta gabana sai naji sha'awarki a yanzu bani da muradin ko wace mace sai ke na roke ki ki bani kanki na rana guda na biya bukatata."

Ji nayi gumi na tsatstsafowa daga jikina kallonsa kurrum nake ina mamakin maganarsa, kallon da yake min shine ya tabbatar min da gaskiyar maganarsa duk ya koma kalar tausayi sai marairaice fuska yake yana kankantar da idanuwansa.......sunkuyar da kaina kasa nayi ina tunanin abinda zance masa, motsinsa naji a kusa dani da sauri na dago kaina ido muka hada yana gurfane a gabana ya wani zuba min idanuwansa kamar zai cinye ni.

Cikin wani irin yanayi na fargaba da tashin hankali nace"Ranka ya dad'e nasha fada maka baza ka samu abunda kake so ba, ni bana daya daga cikin irin matan dake sarayar da kima da mutucinsu inaso jikina da komai nawa ya zama mallakin mijina na sinna dan girman Allah da darajar Annabi kada ka sake yi min irin wannan maganar wallahi tallahi bazan ta'ba amincewa bukatarka ba kayi hakuri da maganata ranka ya dade kayi na farko kayi na biyu idan ka kuskura kayi na uku zan samu mahaifiyarka na fada mata abinda ke faruwa ka rabu dani da wannan maganar." Ido jawur nakare maganata inaso na tabbatar masa da cewa daf nake dana tona masa asiri.

a maimakon ya saduda sai ya sake kusanto ni ya matseni jikin kujera yana min wani shu'umin kallo gabadaya ya fita daga cikin hayyacinsa dan da alama ma bai ji barazana ta ba.

tureshi nayi ina kokarin mikewa ya rike hannuwana tsam na dinga kokarin kwacewa karfin ba daya bane hawayen fargaba ne suka soma zubo min.

Kirjina ya ban'kare min ya tsirawa nonuwana ido ajiyar zuciya ya sauke ya d'ora fuskarsa a kan kirjina yana wani irin abu, wani irin abu naji ya tokare min a wuya, hannuwa nayi yun'kurin kwacewa ya rike sosai ya cigaba da goga fuskarsa a kirjina sai nishi yake fitarwa.

Ya kai minti biyar yana iskancin da yake so kafin ya dago kansa, yawun bakina na tofa masa a fuska ina masa kallon banza nace"Yanzu me kaji da akayi hakan wato kai kai baka jin nasiha ko? kasan gaskiya kasan abinda kake aikatawa haramun ne shine ka ban'kare min kirji kana iskancin da kake so Allah ya isa."
Chapter 30 · 0% Book details