← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 90

Sashe 85

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabana ya fadi! jin abinda yace, nace"Ranka ya dade mai yayi zafi! kaida 'yar uwarka zaka saketa me tayi maka? haba kai kuwa ka barta taji da abu daya mana iyayenta babu lafiya kai kuma ka saketa ina ganin ko wane irin laifi tayi maka ai bata cancanci irin wannan hukuncin ba."

"Sumayya Lawisa ba matar rufin asiri bace " shuru nai ina sauraransa ya cigaba da cewa" A lokotan baya kafin na gane gaskiya na ta'ba cewa dake idan kika sake kika fitar da sirrina wani yaji zanyi miki mummunan hukunci ko."? Nace."Eh kwarai haka ya faru."

Yace."A lokacin da kinyi gangancin fad'awa mahaifiyata bana san haihuwa zan sake ne sai Allah yasa kika kasance mai hankali da hangen nesa mai kuma rufe sirrin mijinta wannan janyo miki kima da martaba a idona sannan kuma ba kiyi zuciya ba kika cigaba da nuna min gaskiya har Allah yasa na gane na dawo kan hanya madaidaiciya hakane ko ba haka bane."?

Da sauri nace"Eh hakane." Yace."Ita Lawisa saboda ta raina ni ta kuma raina maganata sai ta kira Mamma a waya ta fad'a mata duk abunda yake faruwa, wannan dalilin yasa na yanke igiyar aurena dake kanta."

Murya na rawa nace"Gaskiya wannan ba hukunci bane! me yasa ku maza daga zarar mace tayi muku laifi sai ku saketa ku dinga adalci mana laifinka shine a kan gaba akan nata me zai sanya ka yanke mata irin wannan hukuncin a kan gaskiyarta ni dai don Allah ka mayar da ita dakinta shine farin cikina."

Yace."Sumayya ba zan mayar da Lawisa ba dama can ni bana sonta wallahi ke nake so." Kuka nasa nace"Ni kam idan baka mayar da ita ba bazan ji dadi ba kuma idan kana so na tabbatar da maganar kana sona to ka mayar da ita dakinta shine farin cikina."

Da sauri yace." Bana so kina kuka bana kusa dake my lov akan me zaki dinga zubar da hawayenki akan Lawisa kiyi hakuri ki bar maganar nan ni ke kadai kin isheni rayuwa."

Nace"Ni dai bazan yi hakuri ba har sai ka mayar da ita zan daina zubar da hawaye kuma ko ka dawo ba zakaga walwalata ba." murmushi yayi yace."To shikkenan ki daina kuka zan duba maganarki."

Hawaye na share nace'' to zuwa dare ka yanke hukunci kuma kada naji sa'banin abinda nake tunani." murmushin dai ya kuma yi yace."Sumayya zuciyarki tana da kyau wallahi wace macace ce take son kishiya ai na dauka murna zakiyi dana saketa."

Murmushin takaici nayi nace"Haba sai kace ba mace ba zanyi murna dan ka saki matarka ciwon ya mace na 'ya mace ne kai da kanka kace dani na fitar maka da sirri sai ka sake ni to me zai sanya nayi farin ciki akan hakan nasan nima hakan na iya kasancewa dani."

Girgisa kansa yayi kamar tana gurin yace."No Sumayya ba zan iya rabuwa dake ba idan kuwa kaddara ta gifta a tsakaninmu nasan nida jin dadi har na qare rayuwata.''

Murmushi nayi nace"To na amince da maganarka yanzu sai naji labari mai dadi akan Lawisa." yace."Okey to inaso dan Allah ki cigaba da rarrashin Mammana kafin na dawo." nace"Kada ka damu insha Allahu zata yafe maka mutukar ka janye sakin da kayiwa Lawisa." Yace."Zanyi tunanin hakan." sallama mukayi da juna na kashe wayar tare da ajiyeta a kusa dani....

*Na kudi ne..*
Koda zaki ganshi a group na sata ne idan kina bukatar biyan kudin littafin ga yanda abin yake.....Vip gruop#600 normal gruop#300 account... 0543282124.....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
105
Cikin tsananin damuwa ya shiga kiran wayar mahaifiyar tashi, Mamma na ganin kiran wayar da sauri ta daga dan ta dauka Lawisan ce ta sake kira, jin muryarsa yasa da sauri ta datse kiran ta ajiye wayar gefanta, sake kiran wayar yayi ta dauka rai a 'bace tace"Me kuma za kace dani babana."? a sanyaye yace.''Mamma dan Allah kiyi hakuri kada al'amarin nan kada ya d'aga miki hankali Lawisa karya take duk abinda ta fada miki."

Girgiza kanta tayi tace"Babana in dan duk jikina kunne ne to bazan yarda da maganarka ba, Lawisa gaskiya ta fada min nasan halinka babana nasan abinda za kayi da wanda ba zaka aikataba wato zama da turawa yasa ka dauki d'abi'unsu kana gudun rahamar Allah har kana dibgawa iyalinka kwayoyi dan kar su dauki ciki ko."?

Murya na rawa yace."Mamma dan Allah ki tsaya ki fuskance ni kada ki dauki al'amarin nan da zafi ya janyo miki bacin ra......Katseshi tayi ta hanyar fad'in" Na fada maka fa duk abinda zaka fada min bazan yarda dakai ba, aini babu abinda zance da yarinyar nan Sumayya tayi namijin kokari data tsaya kai da fata taki daukar hud'ubar ka da tuni wannan cikin dake jikinta babu shi inda ta amince da tsarinka na rashin son haihuwa yanzu na gane dalilin da yasa kake 'boye min tana da ciki saboda ka samu damar zubar dashi cikin ruwan sanyi to insha Allahu bukatarku ba zata biya ba dakai da Lauratu kuma ka tabbatar da cewa sai Maimartaba yasan da wannan magana." Tana gama maganarta ta kashe wayar ta barshi da tasa a kunne, zamewa yayi yai zaman dirshan a inda yake, yana cikin tunanin mafita kira ya shigo wayarsa yana dubawa yaga Shatima ne hannu na rawa ya daga, Shatima yace."Wai ya akayi ne tun jiya ba'a samunka a waya.'' Jiki a mace yace."Matsalar network ne.'' Yace."Nima sai dana zargin hakan to ya mukaji da wannan abu da ya faru."?

Gumin goshinsa ya goge yace."Wai shin Shatima me yake faruwa ne yanzu muka gama waya da Mamma amma ban fahimci inda maganarta ta dosa ba."

Shatima ya sauke ajiyar zuciya da fadin"Dama yanda take cikin tashin hankali ai bai zama lallai tayi maka bayanin da zaka fahimta ba......... abinda ya faru shine..............Shatima ya warware masa dukkanin abinda ya faru. cikin tashin hankali da damuwa yace."Shatima ina fatan Yarinyar nan sumayya bata hadu da wani tsautsayi ba wallahi gabadaya jikina yayi sanyi jin yanda kace ta zubar da jini da yawa ina jin tsoron wani mummunan abu ya faru da lafiyarta.

Shatima yace."Ka kwantar da hankalinka ma'aikatanka sunyi kokari sosai akanta a daran suka tsaya a kanta sai da komai yayi daidai sannan hankalinsu ya kwanta yanxu haka. ita da abinda ke cikinta na cikin koshin lafiya."

Sanyi yaji a cikin ranshi yace."Shatima nagode kwarai da kulawarka yanzu ina Labarin Lauratu kasan Allah sai na daureta."

Shatima ya girgiza kansa cikin takaici yace." A daran nasa ayi binkice akanta ba'a ganta ba, sai da naje na turke Hajiya Karima tukkuna take sheda min cewa wai itama bata san inda take ba yanda take yi min bayani yasa nagane cewa bakinsu d'aya yanzu dai binkice ya nuna mana cewa Lauratu ta gudu dan babu irin neman da ba'ayi mata ba."

Cikin zafin zuciya Yace."Shatima tun kafin na dawo ku d'aure Hajiya Karima dan wallahi bazan saurara mata ba." A sanyaye Shatima yace." Kayi hakuri abi komai a hankali mana." murmushin takaici yayi yace."Shatima matar nan fa idan ba'a dauki tsatstsauran mataki akanta ba to ba zata fasa abinda take ba kasan Allah tasan inda Lauratu ta gudu idan taji matsa zata fadi gaskiya.''

Shatima yace."Wallahi ina jin nauyin yaron nan Wali bayan haka kuma ga Lawisa a matsayin matarka wannan dalilin yasa gabadaya na kasa wani abu akai shi kansa Maimartaba har yanzu bece komai ba nasan yana tunanin irin hukuncin da ya kamata a dauka a kanta."

"Shatima babu ruwana da wani dangantaka mutukar akan gaskiya ne me yarinyar nan tayi musu suke neman rayuwarta watannin da suka gabata Lauratu har cikin daki ta sameta da asid zata watsa mata Allah ya kareta yanzu kuma sun shiga da niyyar kasheta sai kuma kace akwai dangantaka to inaso na fada maka cewa a yanzu ni Lawisa ba matata bace na saketa.''

Shatima yace." Innalillahi wa'ina ilahi! raji'un! Magajin sarki me yake damunka ne? wane irin abu Lawisa tayi maka da har zaka saketa duka auranmu wata nawa ka yanke wannan d'anyan hukuncin.!!!! Jin yanda Shatiman ke magana a fusace! yasa ya sassauta miryarsa yace."Shatima wannan maganar mu barta dan Allah idan na dawo koma me zai faru sai da ya faru, babban burina a yanzu shine ka cigaba da kulawa da yarinyar nan Sumayya wallahi ita kadaice damuwata a yanzu saboda duk wani abu da zai faru da rayuwarta ta dalilina ne tayi min hallaci a rayuwata tilas nabi mata hakkinta akan dukkanin wanda yayi nufin cutar da ita."

Yace."In dai ta wannan ne kada ka damu Sumayya zata cigaba da samun kariya daga gurina insha Allahu zanyi iyakacin bakin kokarina a yanzu dai babban abinda ya d'aga miki hankali maganar sakin nan shine damuwa ta dan Allah inaso ka fada min abinda yarinyar nan tayi maka ka saketa.''

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Shatima yanzu ba zan iya yi maka bayani ba saboda bana cikin nutsuwa amma nayi maka al'kawari idan na dawo zaka san dalilin da yasa na saketa." Jiki a sanyaye yace."Okey to babu damuwa Allah ya dawo da kai lafiya." Sallama sukayi da juna kowanne ya kashe wayarsa cikin tsananin damuwa da fargaba.

"Mamma dan Allah ki yafe masa kada kiyi fushi dashi akan abinda ya aikata kiyi masa uziri insha Allahu Allah zai ganar dashi gaskiya.'' Da sauri ta juyo tana kallona nasan bata san da cewar na tashi a bacci ba shiyasa take mamakin maganata.

A hankali na mi'ke zaune ina kallonta tare da marairace fuskata

Karasowa tayi ta zauna a gefena hannuwanta ta ri'ke a sanyaye tace" Sumayya abunda Babana ya aikata ya zama dole a hukuntashi haba sai kace ba musulmi ba ya dinga abubuwa irin na kafurai sumayya meye abin gudu a haihuwa sabida tsabar butulci irin nasa Allah ya barshi da ransa da lafiyarsa ya bashi kyauta amma saboda butulci ya nuna baya so mutane nawa ubangiji ya jarraba da rashin haihuwa suna so suna nema ido rufe Allah bai basu ba amma ya za'be shi ya bashi rabo irin na haihuwa ya dinga kyamata dole sai na hukuntashi Sumayya saboda ina jin tsoron abinda zai faru anan gaba.
Chapter 85 · 0% Book details