← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 90

Sashe 58

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Na kudi ne*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya kudi...keda kika futa da littafin keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake....vip gruop#600 normal gruop#300 account... 0542382124...binta umar gtbank...idan kati zaki turo..#400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:27 PM - ???: *SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
87
Acp suna isa station yasa aka rufe Muddibo a cell ofis d'insa ya shiga ya zauna a kan kujera yana godewa Allah. Hakika samun nasarar dam'ke Muddibo babbar nasara ce a tare dasu, wayarsa ya dauka cikin nutsuwa ya nemi number Magajin sarki ya kirashi ya sheda masa cewa Muddibo na hannu a halin da ake ciki, a nasa 'bangaran ajiyar zuciya ya sauke yace."Alhmdullhi Acp gani nan zuwa insha Allah." Sallama sukayi ya kashe wayar yana kallon mahaifiyarsa, yace."Mamma ni zanje station domin ina bukatar naji komai a daga bakinsa, Tace."To babu damuwa babana Allah ya tsare.'' yunkurin mikewa yay ya kalleni da fadin"Idan kinci abincin rana kisha magani kinji ko." kaina na daga, cikin sauri ya fice daga falon, ajiyar zuciya na sauke ina kallon 'kasan gurin, gabadaya hankalina yana kan iyayena su kawai nake da bukatar gani...."Sumayya kina bukatar hutu saboda haka bari na kira jakadiya tayi miki jagora daki ki kwanta ki samu nutsuwa." Jin abinda tace yasa naji kamar na fad'a mata abinda ke damuna, shuru nayi ina jin nauyin fad'a mata, wayarta ta dauka ta kira Jakadiya, ta shigo da sauri tare da gurfana a gabanta, tace"Jakadiya kuje da Sumayya wancan dakin dake kusa da gurin cin abinci ki gyara dakin sosai idan da akwai abinda ake bukata sai kiyi min magana." Jakadiya tace"To ranki ya dade.'' Ta kalleni cikin kauna tace"Sumayya tashi kuje kinji ko kiyi wanka ki gasa jikin ki kafin ki kwanta ki huta." Yun'kurawa nayi domin tashi nace"Ranki ya dade godiya nake Allah ya kara girma." mirmushi kawai tayi min ta cigaba da kallona har muka shiga dakin.

Komai Jakadiya ta nuna min yanda zanyi amfani dashi a toilet din, ta fito ta barni ina wanka cikin sanyin jiki, har yanzu fargabar abinda zai faru a gaba nakeyi yanda naga mahaifiyar Muddibo na kuka yasa gabadaya jikina ya mutu.

Koda na fito daga toilet din samun kan gadon nayi da kayan sawa sabbi a d'inke cikin wata leda, atampopi da lesuka masu kyau da tsada sabbi kar dan kallo daya nayi musu na tabbatar da cewa ba wanda ya ta'ba amfani dasu, hannuna ne ya sauka kan wata leda, nayi saurin zazzageta sai naga wanduna dasu breziya na dudduba kayan sosai ina mamakin al'amarin! Jikina na shirya tsaf, na sauke ledojin kayan kasa, juyawa nayi ina kallon makeken gadon da yaji shimfid'u na alfarma, ko a mafarki banta'ba tunanin zan kwanta a irinsa ba, nasa hannu ina shafa lallausan zanin gadon da yake yad'e da bargo da wasu irin pillows masu ban sha'awa! lumshe idona nayi a hankali na kwanta rigingine a gadon ina tunanin halin rayuwa.

'Bangaran Magajin sarki kuwa yana fita mota ya shiga direba yaja kai tsaye station suka nufa amma kafin su isa sai da ya kira Shatima a waya yace."Idan bashi da aiki ya sameshi a bomfai wato headquarter 'yan sanda gabad'aya, Shatima cikin mamaki yace."Ina fata dai lafiya." ajiyar zuciya ya sauke yace."Kai dai kawai kazo idan baka da aiki za kayi mamakin abinda ke faruwa." Shatima yace."Okey to shikkenan bani da aiki da yawa a ofis insha Allah nan da minti ashirin zaka ganni." Yace."Okey to babu damuwa." Sallama sukayi da juna ya kashe wayarsa ya cigaba da kallon hanya.

Acp da magajin sarki suna ofis suna tattauna maganar Shatima ya iso kai tsaye Acp yace a bude masa kofa ya shigo, cikin nutsuwa ya shiga ya samesu a zaune kafin ya zauna sai da ya basu hannu suka gaisa tukkuna ya nemi kujera ya zauna yana kallonsu.

Acp waya ya dauka domin bada umarnin shigowa da Muddibo......Magajin sarki ya kalli Shatima cikin yanayin alhini da damuwa yace."Shatima ka jima kana kawo min 'korafi akan Muddibo ina gwasale ka, ashe kana da gaskiya kawai kana bari ne saboda a zauna lafiya, Shatima a yau Allah buwayi ya tonawa Muddibo asiri kowa ya gane cewa shine ke aikata 'barna mai muni a cikin masarautar mu.''

Shatima hularsa ya cire yasa hankici saman goshinsa ya goge gumi, girgiza kansa yayi yace."Dama ni nasan dole watarana asirinsa ya tonu Wallahi dukkanin wani abu da zanzo na fada maka akan Muddibo gaskiya ne ba wai dan na had'aka dashi bane, aa inaso ka kiyaye dashi, to sai dai kuma a duk sanda zanzo nace maka Kada ka yarda da Muddibo ta kowace siga kai kuma baka daukar maganar da muhimanci dan a wasu lokotan idan nayi maka maganarsa ka gwasale ni raina yakan 'baci ina daurewa ne kawai, amma yanzu alhamdullahi nagode Allah daya ganar da kai gaskiya, shi kuma Muddibo naji dadi sosai da Allah ya toni asirinsa, Acp kuyi binkice sosai a kansa na tabbatar da cewa yasan komai akan mace-macen da aka dingayi a masarauta."

Acp yace."Kada ka damu Shatima zamuyi binkice sosai akan wannan al'amari."

Dukkaninsu kofa suka tsirawa ido, jami'ai biyu suka shigo dashi ofis din, ganinsu a zaune yasa yaji wani iri a tare dashi 'boye razanarsa yayi ya tsaya hannu daure da ankwa......Acp ya zagayo hannunsa rike da key ya kwance masa hannun, kana ya nuna masa gurin zama, jami'an dake tsaye gaisuwa suka mika a gaggauce suka fita daga ofis d'in."

Magajin sarki da Shatima kallonsa kawai sukeyi suna mamakin sauyawarsa lokaci guda ya zabge yayi rama tsabar fargaba da rashin gaskiya, gashi dan tijara Acp yasa an cire masa tufafi daga shi sai Singlet da gajeran wando.

Acp ya koma gurin zamansa tare da tsira masa ido yace."Muddibo dani da 'yan uwanka guda biyu muna so ka gaya mana gaskiyar abunda yake faruwa, kada kayi mana gardama da jayayya zakasha wuya hukuma na bukatar kayi mata cikakken bayani akan yunkurin kashe Sumayya da kayi sannan kuma hukuma naso kayi mata cikakken bayani akan wane nau'in magani ne kace Sumayya ta zubawa Yarima a lemo kuma ka tabbatar mata da cewa idan ta sa'ba umarninka sai ka kasheta."!!!!!!!

Muddibo kallon acp yake bakinsa sai rawa yake yi yace."Wato Acp ba zaka daina yi min qazafi ba ko? yanzu ku dan Allah kun yarda da cewa zan iya kisa."!!! dukkaninsu suka kalleshi suna girgiza kai.

Ya cigaba da cewa"Shatima Yarima ni dan uwanku na jini amma kun bada goyon bayan aci zarafi na ashe ba zuwa kukayi ku tafi dani ba yanayin fuskokin ku ya nuna min da cewa kun yarda da wannan 'kazafin da akayi min."!

Magajin sarki ya girgiza kansa ko ka dan bai tausaya masa ba sai ma mugun haushinsa da ya tokare masa a kirji, yace."Muddibo ni dan uwanka ne amma kuma kullum cikin bibiyar rayuwata kake, a zahiri kana nuna min kauna a bad'ini kuma kai kadai kasan irin 'kiyayyar da kake min, wai shin dan Allah mai nayi maka ne."?

Cikin rawar mirya yace." Ya za'ayi na'ki ka Ali ka tuna fa tare muka taso in banda ka tafi america karatu babu abinda ke rabamu komai tare muke gabatarwa shak'uwar dake tsakanina da kai har tafi wacce ke tsakaninka da Shatima to kan wane dalili zan kashe ka me kayi min da zan dinga bibiyar ka."

Shatima yace."Dalilai suna dayawa Muddibo ni nasan waye kai tinda Ali tafiya yay ya barni tare da kai tsayin shekaru masu yawa, na sanka nasan kuma kan abinda yasa kake kokarin halakar da d'an uwanka, Muddibo ba zan za'bi Ali na barka ba dukkaninku d'aya kuke a gurina duk kuma wanda yayi kuskure sai nayi masa magana, a tun lokacin da naga kana da damun kanka akan sarauta da yanda kake zagin mai girma Maimartaba yasa gabadaya al'amarin ka ya fita daga raina saboda nasan mutukar akan mulki ne to babu abinda ba zaka aikataba kamar yanda ka fad'a cewa insha Allahu daka kan Maimartaba mulki sai ya dawo hannun zuriar ku, yasa na shiga kokwanto akanka saboda irin mugwaye kalaman da kakeyi akan zuriar sarki Abdul-aziz a wancan lokacin kayi furucin kisa ba d'aya ba biyu ba duk akan mulki Muddibo me yayi zafi? mecece duniyar kuma menene mulki da zaka d'aga hankalinka akai! har ka dinga d'aukar nauyin daya fi karfinka na tabbata kana da hannu a cikin wannan mace-macen da akeyi a masarauta! shiyasa gabadaya banyi mamaki ba dana ganka anan na tabbatar da cewa hakkin mutunan daka dauka ne yasa asirinka ya tonu."

Muddibo cikin wani irin yanayi na nadama yace."Shatima kaine da kanka kake fadar wannan maganganun akaina? hakan ya nuna min cewa kana da bukatar hukuma ta cigaba da binkice na akan abinda ban aikata ba! ashe zumunci yace haka? Magajin sarki kada ka yarda da wannan tatsuniyar Shatima dama tuntuni yake adawa da sha'kuwar da take tsakanina dai kai 'karya yake min ni ban kasance azzalimi ba ballantana na zalince ka, Ali kayi wa maganar kyak.............Acp ya buga tevur! din gabansa cikin tsawa! yace."Ka rufe mana baki a gurin nan bama bukatar wannan soki burotson naka sahihiyar magana muke bukatar kayi mana idan kuma ka tsaya gardama da 'karyata masu gaskiya yanzu zansa aje ya zane maka jikinka idan kaji a jikinka za kayi bayani."!!!

Muddobo bakinsa ne ya mutu murus! dan har yanzu bai manta da marin da yasha ba.....Acp ya mike daga gurin zamansa zagayowa yayi yaja kujera ya zauna yana fuskantarsa, fuska a murtuke yace."Kai nake saurare.''
Chapter 58 · 0% Book details