← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 90

Sashe 14

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
Lahira tace"Wai ya naga kin fito jikinki duk a sanyaye." Ajiyar zuciya na sauke nace"Lahira ina cikin tsaka mai wuya amma na roki Allah ya fitar dani cikin ruwan sanyi." Tace"me ya faru." A nutse na warware mata dukkanin abinda ke faruwa.
Lahira a jiyar zuciya ta sauke tace"Gaskiya dole ki shiga tashin hankali amma mungode Allah da ya sanya Maimartaba da amaryarsa masu fahimta ne, daba dan hakaba nasan da tuni kina fuskantar hukunci."
Nace"Hakane Lahira amma shi Yariman bai yarda da cewa 'yan uwansa zasu cutar dashi ba ban san abinda ke cikin zuciyarsa ba." Lahira shuru tayi tana tunani kafin tace"Dama ai bai za ma lallai ya yarda ba saboda ganin sun taso tare abu makamancin wannan bai ta'ba faruwa ba a tsakaninsu dole ya shiga ko kwanton cewa zasu iya cutar dashi." Nace"nima nayi kokwanto da farko daga bisani da nayi tunani sai na gane hakan zata iya faruwa tunda yanzu gabad'ayansu idanunsu ya rufe babu abinda suke so sai mulki na fahimci cewa suna masa hassada dan ganin kamar shi zai gaji mahaifinsa." Lahira tace"Dama abinda yake faruwa kenan yanzu duk wani abu da 'yan uwansa zasuyi masa a kan mulki ne saboda haka shawarar da zan baki itace ki zage damtse ki kula da amanar da kika d'auka kiyi iyakacin bakin kokarin ki gurin ganin kin kareshi daga sharrin masu sharri."
A sanyaye nace"Insha Allahu zan lura zanyi iyakacin bakin kokarina."
Da wannan maganar muka rabu da juna.

Sosai nayi farin cikin ganin babana a zaune yana cin abinci da kuzari a tattare dashi, cikin farin ciki na ajiye jakata na zauna kusa dashi ina murmushi nace"Baba nayi farin cikin ganinka a zaune kana cin abinci da hannunka hakika hankalina na tashi a duk sanda zanga Tambaya na baka abinci a baki yau naji dadi sosai dana ganka ka samu lafiya kana ciyar da kanka abinci da hannunka." Murmushi yayi a nutse ya kalleni yace."Ai tun bayan fitarku ke da mahaifiyarki naji kwari a jikina da kaina nayi wanka nayi dukk sallolin da ke kaina Sumayya hakika bamu da abinda zamuyi wa Yarima sai dai addua gami da fatan gamawa da duniya lafiya naji dad'in taimakon da yayi min Allah yayi nufin zan samu lafiya ta dalilinsa hakan yasa na yanke shawara kancewa bayan sallar isha'i zaki rakani nayi masa godiya kan alkairin da yayi min."

Ina murmushi nace"Gaskiya ne baba Yarima ya cancanci godiya daga gurinmu insha Allahu zanyi maka jagora zuwa gurinsa kamar yanda ka bukata." Yace."To masha Allah kema ki dauki abinci kici dan naga kamar da akwai yunwa a tare dake." Cike da walwala nace"Baba lokacin dana shigo ina dauke da yunwa mai tsanani amma ganinka a zaune kana cin abinci da kanka yasa naji cikina ya cika yanzu bana jin yunwa ko kadan." Yana dariya yace."Sumayya ban yarda ba dole kici abinci domin bana son ki zauna da yunwa. kwanukan dake gabansa na janyo
Cike da tsokana nace"To bari na fara cinye wanda ka rage saboda na samu albarka idan ban koshi ba sai na karo wani." Hannunsa na dama ya d'ora a saman kaina fuskarsa dauke da yalwataccen murmushi yace."Allah yayi miki albarka Sumayya." Ina kokarin kai abinci bakina Na amsa da ameeen baba."

Tsaf na gama cikin abincin na gyara gurin na gyara masa shimfid'arsa kana na shiga tattaro kayan wankin mu kwata kwata bana san zama da daud'a shiyasa kullum gurin mu zaka sameshi a tsaftace babu kazanta ko kad'an.
Wanki na fito dashi tsakar gida na ajiye a guri guda kana na koma cikin dakin, na sameshi yana duba littafin addini nace"Baba bari naje na duba dawakai bana so hankalina ya dauke gurin wanki na manta ban basu abinci ba."

Ya kalleni yana girgiza kansa nasan abinda yake ji a zuciyarsa game dani,sunkuyar da kaina kasa nayi yace."Ina alfahari da Allah ya bani ke a matsayin 'ya kin fiye min haihuwar maza goma Sumayya ina alfaharin samunki kuma ina mai tabbatar miki da cewa yanda kikayi mana biyayya kema da yardar Allah naki 'ya'yan zasuyi miki."
Murmushi nayi cikin jin dadin adduar da yayi min nace"Insha Allah baba kada ka damu zan cigaba da kula da aikin ka har sai sanda ka samu kwarin jikin ka." Murmushi yayi ya zuba mata ido har ta fita daga dakin, ajiyar zuciya ya sauke yana addua akan Allah ya bashi tsawan rai a duniya yaga auranta da abinda zata haifa...........
*BINTA UMAR ABBALE*

*Kuyi sharing👏🏻*
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALE🍒_ *[email protected]*

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_

*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
29&30
Tana zaune a kan kujera ya shigo ya sameta, zama yay a gabanta ya dafe kansa kana ganin fuskarsa kasan yana cikin damuwa....Kallon fuskarta nayi itama nan take na gane akwai abinda ke damunta, Uwargida Huwaila mai babban daki ina nufin uwargidan Maimartaba itace tare da Moddibo a zaune abin duniya ya ishe su, Kallonsa tayi cikin tsantsar bacin rai da takaici tace " Wai shin Moddibo ka tabbata duka maganin ka juye masa a abincin."? Ajiyar zuciya ya sauke a cizgune yace"Wallahi gabadaya na juye domin ki tabbatar da magana ta ma kinga muzubin maganin." Hannu ya zira a aljihu ya dauko wata madaidaiciyar kwalba.......Tace"Amma gaskiya abin ya bani mamaki wallahi, wannan maganin karfi ne dashi banyi tsammamin Yarima Ali zai shura a gurin ba." Yace."Ni kaina al'amarin ya bani mamaki wallahi a yanda nasan maganin nan da saurin kisa banta'ba tsammanin zaiyi rai ba." Ajiyar zuciya ta sauke tace"Shegen yaro karfin jini gareshi to tunda ya tsallake wannan zamu barshi ya huta idan an kwana biyu mu cigaba da bibiyarsa dan ba rabuwa Zamuyi dashi ba har sai munga baya motsi sannan zamu hakura." Muddibo tsaki mai karfi yaja yace."gaskiya naso ya ya she'ka barzahu amma babu komai kamar yanda kika fada cewa ba zamu rabu dashi ba har sai mun cimma munufarmu a kansa."
Tace"Ka manta kawai idan an kwana biyu zan sake kiranka mutattauna yanda za'ayi." Yace."Shikkenan sai naji daga gareki." Sallama sukayi da juna kowanne zuciyarsa cike da mugun nufi akan Bawan Allah.

Sai kusan biyar da Rabi na yamma na gama wanki lokacin Tambaya ta dad'e da dawowa ina jin tashin maganarsu a daki suna hira ita da babana na dinga jin wani irin farin ciki da nishadi a cikin zuciyata hakika ina matukar so na ga iyayena na walwala da farin ciki.

A gurguje nayi wanka na fito na kimtsa jikina da sauri na kallesu nace"Ni zanje sashen Yarima domin na dafa masa abinda zaici da daddare." Cike da nuna kulawa sukayi min fatan alkairi

Da sauri nake tafiya ina kallon rana wacce take 'kokarin fad'uwa hakan ya nuna min cewa yamma tayi sosai daf ake da kiran sallar magariba tunda safe ban kara komawa sashen ba sai yanzu, addua nake a cikin zuciyata akan kada Allah yasa ya tuhume ni da wata magana.

Su Haruna na samu a harabar gurin muka gaisa a gurguje na wuce su daya daga cikin masu tsaron kofar ne ya bude min na shiga falon........Can na hangoshi kwance kan doguwar kujera yayi filo da hannuwansa babu wata sutturar arziki a jikinsa vest ce mai duhu sai short nickar a jikinsa, kaina a kasa na 'karasa inda yake, tsugunawa nayi kamar koda yaushe nace"Ranka ya dade barka da yamma." Shuru yayi bai tanka min ba. satar kallonsa nayi ta kasan idona naga ya k'urawa rufin dakin ido, ganin yanda kwayoyin idanunsa suka kad'a yasa naji wani iri a jikina. gaishe shi na sakeyi yayi min banza.

Jikina ne yayi sanyi da halin ko'in kular da yake nuna min, a rayuwata na tsani nayi magana a shareni, muryata na rawa nace"Ranka ya dad'e zan shiga kicin yanzu inaso ka fada min abinda kake bukatar ci da daddare."

"Me ya hana ki shigowa da wuri."? a dakile yayi maganar, nace" Wallahi na tsaya nayi wanki ne shiyasa ban samu damar shigowa da wuri ba." Shuru yayi yana sake gyara kwanciyarsa, ta kasan idona nake kallonsa naga yana bin ilahirin jikina da kallo. sunkuyar da kaina kasa nayi ina adduar rinjaye.

"Kin iya tuwo."? Yafad'i maganar a kasalance. da sauri nace''Ranka ya dade kowane abinci kake bukata na zamani dana gargajiya na iya insha Allah baka da matsala."

Ji nayi ya sauke wata ajiyar zuciya kamar wanda yaci kuka ya koshi! saurin d'ago kaina nayi ina kallonsa har yanzu ni yake kallo koda muka hada ido bai dauke kansa ba, yace."Kiyi min tuwo amma bana san wannan abar mai wari a cikin miya. " na gane daddawa yake nufi nace"To insha Allah ba zan san daddawa ba." Mikewa nayi da sauri na nufi kicin din....Wani irin kallo ya bita dashi yana lumshe idonsa, a duk sanda zai kalli wani sashe na jikin yarinyar sai yaji kamar ana 'kara rura masa wutar sha'awarta a cikin jikinsa.
Kullum so yake ya yakice abin daga jikinsa abin yaci tura da yarinyar yake kwana da ita yake tashi, a zahiri da bad'ini yasan yarinyar ba kalarsa bace domin hausawa suna cewa *'Kwarya tabi 'kwarya* yana ganin ko iskanci zaiyi bai dace yayi da 'yar bayi ba wacce take ma'kaskanciya a 'kasan sa, dalilin daya sa kullum yake kokarin cire sha'awarta a cikin ransa abin nacin tura, sam rashin kyawunta da 'bakar fatar ta basa damunsa abubuwan dake da wahalar samu daya hango a jikinta yake kulafuci yana ganin zai huta sosai a jikin yarinyar, yaso ace tana daidai dashi ne to da babu abinda zai hanashi auranta kodan ya kawar da 'kulafuncinsa a kanta.

Mi'kewa zaune yayi ya rufe fuskarsa da tafukan hannayensa ya kai mintina goma a haka kafin ya mike yabi bayanta kicin din
Chapter 14 · 0% Book details