← Book details Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 90

Sashe 61

Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A dakin taro kowa ya hallara iyaye da 'ya'ya da jikokin masarautar kowa yana gurin, Magajin sarki ya fito da wayarsa a nitse ya kunna rocoding din muryar Muddibo ta fito rad'au!! vollom ya karo yanda kowa zaiji da kyau!! kowa ya shiru yana sauraran Muddibo yana jawabi akan abubuwan da ya dinga shiryawa a masarautar........Famliy din Ciroma suka cika gurin da kuka Hajiya Karima kasa tsayawa tayi ta gama saurara tana kuka na tashin hankali ta bar gurin, da daya bayan daya 'ya'yanta suka bi bayanta, Ciroma yana zaune a gurin bai tashi ba har sai da recoding din ya 'kare! Magajin sarki ya kashe wayarsa ya ajiye kusa dashi, a nitse ya sheda musu cewa"Ranar litinin za'a shiga kuto dashi domin al'kali ya yanke masa hukuncin daya dace dashi dan haka dik wanda yaga yana da ra'ayin zuwa sai ya shirya yaje." babu wanda ya nuna sha'awar zuwa a cikinsu Iyalin Uwar gida Huwaila irinsu aunty Safiyya suka dinga zare ido a gurin gaskiya sunji dadi sosai da Muddibo ya rufa musu asiri suma sunyi nasu sai dai kuma bai ka nasa muni ba!! Maimartaba yace kowa ya tafi gurinsa tunda gaskiya tayi halinta sai a jira hukuncin da al'kali zai yanke a kansa, jiki a sanyaye kowa ya fita daga gurin taron..........Ciroma na daf da shiga sashen sa ya yanke jiki ya fad'i!! Hadiman dake aikace aikace a gurin suka rufu a kansa suna ihu!!!! kafin kice kwabo tawagar 'ya'yansa dake cikin gidan sun fito, mazan ne suka daukeshi suka shiga dashi ciki dakinsa suka shiga dashi su kwantar dashi a gado sun kewaye shi suna yi masa firfita! Ciroma bakinsa ya murgud'e sai zubar da yawu yake! magana yake so yayi amma ya kasa, Hankalin iyalinsa ya tashi, Wali shine me bin Muddibo da sauri yace."Bari naje na kira Magajin sarki yazo ya dubashi." Hajiya Karima cikin tsawa! Tace."Wali ka sake ka kira Magajin sarki ya shigo sashen nan sai na d'aga maka nono wallahi sai na tsine maka albarka."!!! Khalisat tace."To Yanzu hajiya muna ji muna gani zamu barshi ya mutu i duba da ki ga yanda yake haki! jininsa ne ya hau da karfi."
Cikin karaji!! Lawisa tace"Khalisat ba za'a kira Yarima ba ai bashi kad'ai ne likita a duniya ba! saboda haka kawai kai Wali ku daukeshi kusa a mota mu nufi babban asibiti a dubashi." Wali yace." me zai hana a kira Dr Sa'adu ya dubashi a gida."?
Hajiya karima tace"Aa shawarar Lawisa zamu dauka ku daukeshi kusa a mota muje babban asibiti." Manniru yayi saurin fita domin bada umarnin fito da mota...

*Na kudi ne!*
Kada ki karanta min littafi sai kin biya! keda kika futa da book din keda Allah! idan kina so ki biya ga yanda abin yake.....Vip group #600 normal group #300....account... 0542382124....Binta umar gtbank....idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
2/11/21, 2:28 PM - ???: *SADAUKAWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊�)
89
Sai bayan fitarsu daga gidan tukkuna Maimartaba ya samu labarin abinda ke faruwa ransa ya 'baci sosai da abinda iyalin d'an uwansa suka zartar ba tare da saninsa ba, ace akwai babban likita a gida amma su daukeshi su kaishi wani asibiti domin su nunawa duniya halin da suke ciki, sosai ya dinga jajanta al'amarin a cikin zuciyarsa, Waziri ganin yanda ya damu da a'lamarin yasa ya dinga tausar sa da kalamai masu sanyi Sarki ya dan samu sassauci a zuciyarsa sakamakon rarrashinsa da 'yan uwansa ke masa amma dai duk da haka zuciyarsa na can tunanin halin da Ciroma yake ciki dalilin da yasa kenan gari na waye wa suka shirya zuwa asibitin domin duba jikin nasa.

Yanda suka tarar dashi cikin halin ciwo ya firgitasu dan gabadaya komai na jikin Ciroma ya daina aiki yana kwance sai dai ayi masa komai, Likitan dake tsaye a kansa ya sheda musu ciwar jininsa ne ya hau sosai sanadiyar tashin hankalin daya shiga amma insha Allah zai cigaba da kwanciya a asibiti su kuma zasu cigaba da kula dashi har ya samu lafiya."

Maimartaba girgiza kansa kawai yayi yana mamakin kudirar ubangiji Tabbas ya yarda da cewa d'an adam ba'a bakin komai yake ba duba dai lafiya lau suka yini da Ciroma amma lokaci guda Allah ya sauya masa hallita, babu shakka idan suka rasa dan uwansu ta sanadiyar bacin ran Muddibo ba zasu yafe masa ba........Umartar Wali yayi akan ya kira Magajin sarki a waya ya sheda masa cewa ya turo motar asibitinsa tazo ta dauki Ciroman yana ganin kamar haka yafi mutunci.

Hajiya Karima ita da zuriar ta babu yanda suka iya suna ji suna gani Magajin sarki ya turo da mota a kasa Mara lafiyan a ciki a ka tafi dashi asibitin, Tsabar bacin rai yasa hajiya Karima buge zaninta ta koma gida tare da fadin"Ba zata zauna zaman jinya ba mutukar ba sanja wa mijinta asibiti ba.

Maimartaba yace kowa ya kyaleta! dama asibitin basa bukatar 'yan jinya akwai ma'aikatan da suka san aikinsu sai kawai ya basu umarnin tafiya gida bayan ya kwantar musu da hankali akan rashin lafiyar mahaifin nasu............Koda suka koma cikin tsananin damuwa suka samu mahaifiyar tasu sai zubar da hawaye take, Lawisa da khalisat suka zauna suna taya ta kukan. abun duniya ya taru yayi musu yawa Muddibo ya jefa su a cikin tsaka mai wuya ga rayuwar mahaifinsu na tangal tangal.....Hajiya karima hawayenta ta share ta kalli 'ya'yanta cikin rawar murya tace"Yanzu haka zaku zauna ku zuba min ido ina kuka kuna kuka ba zamu zauna mu nemawa kanmu mafita ba."

Wali yace."Hajiya wace irin mafita kike so mu nemawa kanmu? duk fa abinda kika ga ya faru to da sanin Allah saboda haka dan ki kada kice zaki dauki fansa saboda nasan halinki da ri'ko! Muddibo shine ya janyowa kansa masifa muma gashinan ya jefa mu a cikinta a yau da kwanan mahaifinmu ya kare da tuni sai dai labari."

A harkuqe! tace"Dallah malami rufe min baki mai matacciyar zuciya! ayiwa dan uwanka sharri amma ka dinga cewa shine ya janyowa kansa wato kana nufin kaima ka yarda da sharrin da'aka liqa masa."

Cike da mamaki! yake kallonta kafin yace."Hajiya dan Allah ki nutsu ki shiga hankali ki daina wannan abinda kikeyi mutane zasu dauka kin samu ta'bin hankali! wannan fa al'amarin da gaske ne Muddibo ne ya aikata ba sharri akeyi masa Kin saurari muryarsa a lokacin da yake shedawa hukuma gaskiyar lamari amma saboda san zuciya kina cewa sharri a kayi masa."

Lawisa na kuka tace"A gaskiya Yaya Wali ka bani mamaki wallahi wato kai ba zaka iya rufa asirin dan uwanka ba ko kenan yanzu ranar litinin din ba zakaje kuto ka bada sheda a kansa ba."

Dafe kansa yayi cikin tsantsar damuwa yace."Wace irin sheda zan bayar a kansa bayan da bakinsa ya fadi gaskiyar magana, dole zanje kuto domin jin irin hukuncin da sharia zata yanke a kansa."

Munniru yace."Ni wallahi na rasa ma abinda keyi min dadi a rayuwata nayi nadama nayi dana sani dana fito a cikin wannan masarauta gabad'aya bamu da power a masarautar nan komai mune a baya ai dole 'bacin rai yasa hawan jini ya kama babanmu.

Hajiya Karima ta share hawaye cikin takaici tace"Ai Munniru ba kuga komai ba a yanda babanku yake bani labarin yanda mahaifinsa yasha wuya a cikin masarautar nan sai kunyi mamaki mutuka! zuri'ar Abdullahi Adamu ta riga ta kwace sarauta ta kafa kanta ta hana kowa ya kar'ba daga hannunta ni wallahi har yanzu banga laifin Muddibo ba dan yayi yunk'urin kwatar hakkinsa, bari na fad'a muku abinda baku sani ba zuri'ar Abdullahi Adamu sune suka kashe kakanku da bakin ciki sai wayar gari akayi da gawarsa ya mutu da bakin ciki!

Munniru ya buga bango(garu) da hannunsa yana huci! yace."Tur! da zuria'r Abdullahi Adamu wallahi sun kasance azzalimai masu san kansu da yawa meye amfanin mu a masarautar nan da mu zauna muna ganin bacin rai a gwara mu tattara kayanmu mu fita daga cikinta..

Wali yace."Baka da hankali ko Munniru idan mun bar masarauta kana inda zakaje."? shuru yayi yana huci! Wali ya cigaba da cewa"Ka nutsu ka zauna kayi tunani malam komai kaga na faruwa to da yardar Allah idan Yayi nufin mulki ya cigaba da tabbata a hannun zuri'ar Abdullahi Adamu to babu yanda zamuyi idan kuma yayi niyyar k'wace mulkinsa ya kwace ya dawo dashi hannunmu kuma abunda nake so kuyi la'akari dashi anan shine Waziri da Galadima me yasa basa tayar da hankalinsu akan mu! kada ku manta suma fa suna da hakki amma sunyi shiru sun zubawa sarautar Allah ido ba wai dan basa sha'awar mulkin ba dukkaninsu suna so suna sha'awa sai dai babu yanda za suyi da abinda Allah ya hukunta saboda haka dan Allah kuma inaso ku hakura ku barwa Allah ikonsa kuma insha Allah idan baba ya samu sauki zan zauna na fahimtar dashi cewa shi mulki na Allah ne sai wanda ya za'ba yake bawa ba'a yiwa Allah dole akan ikonsa kowane irin hukunci ya zartar daidai ne."

Jikinsu ne yayi sanyi da nasihar da d'an uwan nasu, da alama dai duk cikinsu shine mai kyakkyawar zuciya tunda gashi nan ya zaunar dasu yana nuna musu abinda ya dace Ubangiji Allah yasa zasu dauki nasiharsa su hakura su barwa Allah ikon sa.
Chapter 61 · 0% Book details