Sashe 1
Kwarya Tabi Kwarya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
'Kwary tabi'kwarya complete
2/11/21, 8:19 AM - ???: *'KWARYA TABI 'KWARYA*
*NA*
_BINTA UMAR ABBALEðŸ’_ *[email protected]*
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📘🖊�*
_'Kungiyar Masu Nazari da Aiki da Ilimi_
_________________________
*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊ðŸ?)
1&2
Lokacin dana shiga masarautar sai da nasha jinin jikina dan ganin yanda tarin bayin dake karkashin masarautar suka nutsu gabas yamma kudu Arewa dukkaninsu suna tsaye sunja layi mazansu da matansu da 'ya'yansu suna sanye da uniform wanda ke dauke da tambarin masarautar gaba da baya, kowanne kansa a sunkuye 'kwakkwaran motsi babu wanda yake iya yi.......Can wata rumfa na hango iyayen masarautar zaune kan kujeru na alfarma sun jeru su uku wanda yake tsakiyarsu shine nafi tunanin shine shugaban masarautar wato (Sarki Maimartaba) abinda yasa nake tunanin shine Sarkin sabida ganin yanda wasu mutane gudu biyu masu dauke da jajayen kaya suke tsaye a gefe da gefensa suna masa firfita da wani irin mafici mai baza gwanin birgewa........Shiru masarautar babu hayaniyar mutane busar algaita gami da sarewa ne kawai take tashi a gurin.
Cikin nutsuwa wasu lafiyayyun motaci guda guda su shigo cikin masarautar, Maimartaba ya fara yun'kurin miqewa tsaye fuskarsa dauke da wani qayattacan mirmushi, Ganin zai miqe yasa fadawan dake gurfane a gabansa suka miqe da sauri suna baza manya manyan rigunan jikinsu......Waziri Galadima Ciroma suma suka miqe tsaye sabida ganin maimartabar ya miqe, dan ganin iyayen masarautar sun miqe ya sanya dukkanin wa'inda suke zaune suma suka miqe tsaye domin girmamawa.......masu busar sarewar suka rud'e tare da sanja salo....gabadayansu suka nufi inda motocin nan sukayi parking suna ta aikin busa algaita gami da sarewa, Wani bafadane yayi saurin bude motar ya fito da sauri ya bud'e daya hannun ya matsa gefe guda tare da dun'kule hannunsa alamun jinjina ga wanda ke cikin motar "Barkan ka da dawowa masarautar gado Aliyu Haidar namijin zaki Sarki mai jiran gado fari kake mai farar aniya Ali baka fito ba sai da ka shirya hakika masarauta da duk wanda ke karkashinta yana murna da dawowarka lafiya." Wannan kirarin daga bakin bafadan yake fitowa....shuru gurin yayi na minti biyar kafin ya zuro qafarsa d'aya kafar dake dauke da takalmin sarautar na tsirawa ido cikin socond guda na gane cewar mamalakin kafar mugun d'an izzah! ne a qalla ya kai minti biyar da zuro kafa daya ya gagara fito da dayar ko me yake a cikin motar oho! gabadaya idanun kowa a gurin yake mutane da dama sun 'kagauta suyi tozali dashi mussaman na qasa wa'inda basu sanshi ba sai dai labarin sa, cikinsu har da Sumayya wacce ta kasance d'aya daga cikin 'ya'yan bayin masarautar itama idonta kur! a gurin tana jira ya fito daga motar ta ganshi tun kafin ya fito ta gazgata abinda jama'ar masarautar ke fada a kansa wato shi d'in mugun d'an izzah! ne mugun d'an d'agawa ne! mugun d'an gadara ne! Mugun muskili ne wanda babu wanda yake gane al'kibularsa sai mutum d'aya itace mamanshi amma hatta da mahaifinsa maimartaba baya gane inda ya dosa.
Cikin nutsuwa ya rankwafo ya fito daga cikin motar tare da zura bak'in gilashin dake hannunsa dan saboda gujewa had'a ido da jama'ar da sukayi masa caaa! da idanunsu ya tsani kallo a rayuwarsa shiyasa sam baya sakarwa mutane fuska mussaman mata dan ya fahimci kamar kallo a jininsu yake be sai ba ko shi suka raina suke k'ure shi da kallon 'kurrula.
Wasu matasan samari ne wa'inda sukayi sa'anni dashi naga sun fito daga d'aya motar su biyu suna sanye da kayan sarauta a jikinsu amma shi uban gayyar suit ne a jikinsa Shatima da Moddibo sune suka tilasta masa d'aura alkyabba a jikinsa saboda da ita sukaje airport din suka kuma sheda masa cewar maimartaba ne yace lallai su bashi yasa ya shigo da ita cikin masarautar.
Da sauri naga wasu bayi su hudu sun shimfid'a wani farin abu mai tsayi a dadai kafafunsa sai da abin ya dangane har inda iyayen masarautar suke Cikin nutsuwa yasa kafarsa akan abin ya fara tafiya.
Tafiya yake abokansa kuma 'yan uwansa na gefe da gefensa, yayin da masu busa algaitu suka cigaba da aikinsu tare da rufa musu baya....Lokacin masu camera man vedio camera suka fara aikinsu suma 'yan Jarida ba'a barsu a baya ba aikin daukar hotonsa kawai sukeyi shi kuma yana d'agawa jama'ar dake gefe da gefan sa hannu ammafa babu walwala ko ta kwabo a fuskarsa wanda ya kamata ace ya saki fuskarsa ya tar'bi dubbanin mutanan dake murnar dawowarsa gida ko a jikinsa daga karshe ma daya ga yana damun kansa sauke hannunsa yayi sai kawai ya sunkuyar da kansa ya cigaba da tafiya babu um! babu umum!! Sukuwa jama'ar masarautar sai kirari suke masa gami dayi masa fatan alkairi a rayuwarsa amma gogan bai d'ago kansa ba ballantana yasan sunayi.........."Wani irin takaici ne ya rufe ni naja tsaki tare da kauda kaina daga kallonsa tabbas na gazagata maganganun da jama'a sukeyi a kansa na rashin kirkinsa yanzu ina laifi ga wanda ke murna da zuwanka gami dayi maka addua idan da mutunci yaci ace ya d'ago kansa ya nuna jin dadinsa amma saboda tsabar izzah! ya gagara kallon inuwar inda mutanan ke tsaitsaye.
Silalewa nayi daga cikin iyayena na kama hanya domin tafiya can shashenmu na bayi, zuwa zanyi na huta dan bazan iya jurar tsayuwa ba rana sai duka na take gashi wanda akeyi dominsa baya gani, mahaifina kawai nake tausayawa dan ba wata cikakkiyar lafiya gareshi ba amma saboda tsabar bin dokar masarauta yasa ya lalla'ba ya fito ya tsaya a matsayinsa..............
*BINTA UMAR ABBALE*
*Kuyi sharingðŸ‘ðŸ»*

*Littafin na kudi ne....!*
_#300.....0542382124...Binta Umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai ki same ni ta wannan numbers..08089965176 _07084653262 Zanyi miki bayanin yanda zaki turo katin.......... Ga masu bukatar VIP Group 600 ne_
_Mutanan Nijar zaku tura dala dari ta wannan numbers katin airtal ko orange VIP jakka d'aya 90899076_88137740_
*SADAUKARWA NE*
*GA*
*HAJIYA SHAFA'ATU S YARI*
(Kainuwa dashan Allah✊ðŸ?)
3&4
Yarima Aliyu a nutse ya 'karasa rumfar da iyayen nasa suke zazzaune ya cire rufaffun takalmansa a nutse yaje ya gurfana a gabansu tare da 'kaskantar da kansa sosai yace"Allah shi taimake ka ina fatan na same ku lafiya."? Maimartaba ya d'ora hannunsa a saman kansa cikin farin ciki yace."Lafiya lau alhamdullilahi Aliyu ina fatan ka dawo gida cike da samun nasarorin da muke bukata." Ali! Yayi murmushi tare da sake sunkuyar da kanshi qasa, Waziri ne ya karaso gurin a nutse yasa hannunsa ya d'agoshi ya miqe tsaye! wani qayataccen murmushi yayi wanda yay masifar yi masa kyau tabbas da yasan dariya nayi masa kyau to da ya mayar da hankali gurin yi.......Rungume 'Kanin mahaifin nasa yay a daidai kunnansa ya furta "Baba Waziri ina fatan duk na same ku lafiya." Waziri cike da walwala da farin ciki yace."Lafiya lau ka same mu Aliyu haki'ka muna farin cikin dawowarka masarauta lafiya." Idanunsa dake lumshe ya bud'e! still da ragowar murmushin a fuskarsa yana kokarin yin magana suka hada ido da Galadima shida Ciroma suna tsaitsaye a inda suke fuskarsu babu wata cikakkiyar walwala.
Gyara fuskarsa yayi dan saboda yasan halinsu da rainin hankali suna iya tsinkashi a gaban mutane a kullum burinsu suga sun 'bata masa rai tun yana yaro suke nuna masa qiyayya tamkar wani abokin gabarsu.
Inda suke ya nufa ya d'an risina cikin nutsuwa yace."Ina fatan na same ku lafiya."? Galadima ya gyara yanayin sa yana kokarin danne 'bacin ran dake ransa yace."Lafiya lau Alhamdullilahi ina fatan ka dawo gida tare da nasara."
"Alhamdulillahi." Shine a binda ya fada tare da yin kasa da kansa gami da goya hannuwansa a baya................Daf da zan shiga kofar mu d'aya daga cikin matsu tsaron 'kofa ya dakatar dani, tsayuwa nayi ina kallonsa har ya qaraso inda nake, Yace."Waye ya baki ikon barin gurin taro bayan ba'a tashi ba." Kai tsaye nace"Kaina ne yake ciwo sannan rana na takura min shiyasa na dawo gida.
Shar'be'biyar bulalar hannunsa ya labta min a qafafuna yace."Kina a matsayin baiwa maqasqanciya kike wannan maganar, baki san abinda kikayi ya sa'bawa dokokin masarauta ba to bari kiji har iyayenki sai an hukunta sabida abinda kika janyo musu." Wani irin gumi! nake ina kallonsa bakina sai rawa yake yi ga wani irin zafi da kafafuna sukeyi min.
Bulalar ya sake d'agawa zai shaud'a min nayi saurin riqe hannunsa hawaye suka 'kwace min nace"Bafa ni da lafiya na fad'a maka kaina ke ciwo sannan ga rana a gurin laifi ne dan na dawo gida na huta."!