← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 210

Sashe 94

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Washe gari kusan tare sukayi aikin gidan ita da mama,kasancewar qarfe shida da rabi su halima na fita makaranta sai goma na safen suke dawowa a irin wadan nan ranakun,a yanzu haka ma shirin tafiya musabaqa suke wanda suna daya daga cikin wadanda aka zaba,sunayi suna hira irin ta tsakanin da da uwa,zuciyoyinsu fes,sumayya na jin gata ga mamanta kamar kar ta sake tafiya,yayin da maman ke farincikin sauyawar diyar tata,tara da rabi suka kammala har karin kumallo,wanka sumayyan ta shiga tayi sannan ta shirya cikin atamfarta super wadda tayi mata kyau ainun,ta dan taba kwalliya kadan sannan ta sanya hijabinta ta nufi dakin malam.

     Karyawa take sanda ya shiga,ta gaidashi ya amsa mata yana fara'a
"Mutanen abuja yau anyi kwanan kano" kanta tai sunkuyar tana dariya
"Ai malam,duk wanda ya bar gida gida ya barshi" tace tana wasa da yatsunta
"Wannan kuma gaskiya ne" labari take bashi kadan kadan game da abinda ta fahima kan rayuwar garin har mama ta cimmasu a haka
"Qarfe sha daya ne daurin auren fa malam" maman ta tuna masa,a gogo ya duba sannan ya miqe
"Au,au,ai kuwa na manta,gashi sha daya saura kwata,hira ta dauken hankali,idan na dawo ma qarasa ko?"dariya tayi." To,a dawo lafiya"
"Allah yasa".

      Falon mama ta koma don ta karya itama,tana tsaka da hada tea abdallah ya tashi,dole ta bar karyawar ta yi masa wanka ta karbi kayansa wajen mama ta sanya masa
"masha Allah"ta fada tana dubansa tana murmushi ganin yadda yayi kyau,shima sai ya maimaita abinda tace din,dariya ya bata dai dai sanda mama ta shigo bayan ta sallami malam
"gaskiya mama bakin yaron nan ya kuma budewa"
"Ba dole ba,yaron dake zuwa makaranta me zai hana bakinsa budewa", su halima ne suka shigo hakan ya sanya ya qyaleta yayi wajensu can yana buga musu rigima,gefe ta koma ta soma karyawa tana jinsu tana dariya cikin ranta.

        Sallamar abdur rahman data jiyo ita ta sanya ta kusa qwarewa,da sauri ta dauki ruwa ta sha,tare da janyo mayafi ta yafa kafin a amsa iso,yana sallama cikin falon ta soma tattare kayan breakfast din ba tare data kammala karyawa ba ta maida kitchen,tunda ya shigo idanuwansa na kanta,don bai tsammaci tazo garin ba,bayan sun gama gaisawa da mama ta miqe ta fice,su halima ma suka gaidashi sannan suka fice don sauya unifoarm da kama aikin abincin rana na gidan.

       Idanu ya zuba mata har sai da taji nauyinsa ta kau da kai
"kin kyauta qwarai,tunda har baki iya gayamin cewa zaki zo kano,matsayin yaya ma da nake tunani an bani ashe ba haka abun yake ba na bar murna" murmushi ta saki tana kada kai
"Ba haka bane,afuwa,suprise naso baka"
"Da shi dai kike so ki fake,amma inda hakanne ai da a yau da safe zaki kirani ki gayan,ko kuma tun a jiyan ki sanarmin kina zuwa kano ko?"
"To nayi laifi babban yaya ayi haquri" ta fadi cikin raha,numfashi ya dan dauke kadan,kwata kwata baison sunan,wannan sunan bai masa ba,so yake yaji ta kirashi da wani suna dake qunshe ko yake nuni da zallar qauna,kai ya gyada kawai yana murmushi,sabida ya lura idan baiyi wasa ba wankin hula na neman kaishi dare
"Ina abdallah?" Sai ta dan ware idonta kamar tana nemansa
"Yanzun na masa wanka na bashi abinci,ina zaton ya fita"nashi idanun shima ya waro
" kan me zaki dinga barmin yaro yana fita waje?"dariya ta danyi
"To duka ma yaushe na dawo garin ni?,abdallah ya riga ya saba da fita tunda ya tashi gidan yara" halima ya kira yasa ta dauko masa abdallahn,ba dadewa ko ga dawo da shi,yayi budu budu da qasa da alama ya sha wasan qasansa ya qoshi,kicin kicin da fuska abdur rahman din yayi ya hau fada,tilas ta tashi ta sake gyarashi.

       Sai da ya tabbatar ta gyarashin sannan ya miqe yana dubanta
"Har zaka tafi?" Ta rigashi fadi
"Eh,dama ai zuwan ba naki bane,tunda ba'a gayan zuwan ba,amma zan dawo ko zuwa gobe,idan ba gobe ba jibi,akwai muhimmiyar magana da nake so mu tattauna" shiru ta danyi
"Allah ya nuna mana,ka gaida bahijja da hajiya don Allah"hararar wasa yayi mata
"bazan gaya mata ba,maruqar ba zaki je ki gaidata ba,ko kara ma sumayya fa baki da ita"dariya tayi a kunyace,ita kanta tasan bata kyauta ba
"Kayi haquri in sha Allah bazan koma ba sai naje na gaida hajiya" kafada ya daga yana fadin
"Da dai yafi" sallama ya musu ya danqawa abdallah kayan qwalama kamar yadda ya saba sannan ya wuce.

       Kwanakin ta a kano jinta take kamar wata sabuwar duniya,wuni suke hira,hakama anty dije idan ba wani gu zata ba tana gun mama,ranar da abdur rahman yace zaizo har yammaci taji shiru,hakan ya sanya ta shirya don zuwa tsohuwar unguwarsu kamar yadda tayi alqawari,halima da zainab ne 'yan rakiya,sai laila wadda a gidan ta kwana,sumayyan tayi kyau cikin wani leshi wanda daya ne daga cikin kayan sallarta da uncle farouq ya siya mata,mayafi ta yafa bisa matsantawar halima,duk da babba ne amma tayi kyau matuqa,talkalmi da jaka komai da tayi amfani da shi ya dace da kalolin jikin lace din,sai oga abdallah shima da tayi masa kwalliya cikin qananun kaya,da rufaffen takalmi irin na maza.

      Tana tsakar gida suna sallama da mama suka ji sallamarsa a soro kamar yadda ya saba bai shigowa har sai an masa izini,maganar da suke da mama ta katse tana duban soron,sai da maman ta sanya hijabin sannan aka masa iso,tunda ya shigo idanuwansa na kanta,tayi masa kyau fiye da duk lokutan da ya saba ganinta,yai yayi kamar yayi sallama da mama ya fito saidai ita tasan ba tafiya yayi ba,suna fitowa suka ganshi hakimce jikin mota,shi din ma yayi kyau cikin wani yadi mai taushi ruwan qwaiduwar qwai,gaban motar kawai ya bude mata tare da cewa
"Bismillah" kai ta rausaya ganin yadda ya tsareta da idanu kawai ta shige,su laila suka shiga baya sannan ya shiga ya tada motar.

        Sai da suka fice daga layin sannan yace
"Ina zuwa ranki ya dade?" Kanta ya sake rausayarwa tana murmushin sunan da ya laqaba mata
"Tsohuwar unguwar da muka zauna ni da ya mukhtar" wani kishi ne ya soki zuciyarsa,amma sai ya danne ba tare da ya nuna ba,kamar ta fahimci mekw tsinkulinshi sai tace
"Zanje mu gaisa da yara da iyayensu da muka zauna tare"
"Hakan nada kyau" ya bata amsa,da fari motar tayi shiru,sai daga bisani abdur rahman din ya sako hira,kadan kadan suke tabawa har suka isa unguwar.

      Unguwar na nan kamar yadda ta santa,saidai tsohon gidansu da suka zauna wanda mutanen da suka siyeshi suka masa kwaskwarima,gidan maman naana suka fara shiga,taso ta kasa gane sumayya sai da naana ta fito daga daki,da gudu ta nufi sumayyan tana ihun kiran sunanta,rungumeta tayi tana dariya itama tana kiran sunanta,daga nan maman naanan tayi mata iso zuwa falo
"Wallahi sam fuskarki taso bacemin sumayya saboda canzawar da kika yi,kin sake zama babbar mace?" Maman naanan ta sake fada cikin mamaki,murmushi kawai sumayya tayi sannan suka fara gaisawa,naana na gefe bakinta yaqi rufuwa,tashi tayi taje ta siyo wa sumayyan pure water mai sanyi da lemo,dubanta sumayyan tayi tana murmushi,ba zata manta ba wannan na daya daga cikin rainon da ta yiwa yaran na girmama baqo,ashe har yau basu manta ba,ita kanta nanan ta girma ta sauya,nan sumayyan ta dinga tsokanarta na ganin girman da tayi.

      Kafin ta bar gidan sai ga yaran na shigowa daya bayan daya,da alama nana ke shiga gida gida tana gaya musu zuwanta,dui wadda ta shigo rungume sumayyan take cikin jin dadi,itama mamakin girman yaran take,kusan awa daya da wani abu tayi a gidan sannan ta dinga shiga gida gida yaran na rakata,kowa mamakin sauyawarta yake inda ita kuma sam bata ganin sauyawar da tayi,duk gidan data shiga sai ta ajjiye musu dubu daya,cikin kudin da ya abbakar ya bata jiya a ribarta na kudinta da ake juya mata,sunyi murna kuwa sosai,sai magariba sannan suka bar unguwar duka abdur rahman na cikin mota yana jiransu.

        Sai wajen isha'i suka koma gida,don daga qofar gida da ya ajjiye motar masallaci ya tafi sallar isha'i,sai da ya dawo yayi kiranta a waya kan ta fito ya dawo,sanda ya kira din fitowarta kenan daga wanka,don ranar ta gaji da wuri take sonyin bacci.

        A sitting room dinsu ta sameshi wanda halima ta bude masa ta masa masauki a can,kamar kuwa tasan sumayyan bata son komawa cikin motar,kallonta yake sake yi,komai ta sanya kyau yake mata,rigar data sanya ba wata ta azo a gani bace amma ta mata kyau duk da hijabi ne a jikinta saidai qarami ne.

       "Sumayya,zuwa yanzu na gaji da zaman kare a karofi da nakeyi,lokaci yayi da zamu fukancu gaskiya baki dayanmu,ni na sani cewa bazai yiwu naci gaba da biye miki a yadda kike so ba,kamar yadda kema kika sani cewa indai da rai da lafiya malam bazai taba barinki babu aure ba" abdur rahman yayi shiru yana maida numfashi tare da nazartar yanayin da sumayyan ta shiga sannan ya dora
"Ko baki so sumayya dole a ce mukhtar ya koma ga Allah,kin sani na sani haka ma duniya ta shaida,don wani wanda kake so ya rasu ba shine zaisa kace kai kuma ka bar yim taka rayuwar ba,yin hakan dai dai yake da gayawa Allah bai maka dai dai ba kenan,tunda ya dauke wanda yaga dama ne ya kuma bar wanda yaga dama babu wanda ya isa ya tilastashi,gata daya zaki masa shi da yaronshi ki killata kanki a gidan aure,ki bani dama sumayya na cike miki gurbin farincikin da kika rasa"
"Sumayya!" Ya kira sunanta cikin kaurara murya
"Inason yau ki gayamin matsayina,mu bar wannan zaman qaryar,zaki iya aure na ki zauna da ni?" Shiru tayi maganganun abdur rahman na ratsata,babu shakka gaskiya ya fada mata,wanda shine ya fara gaya mata karo na farko tun bayan rashin mukhtar idan ka dauke malam da mama
"Idan har kin yarda ki barni na yiwa malam magana,tunda a yanzu yana tunanin na janye tunda har kin sake wani auren,ya taba gayan hakan cikin wasa,saidai ni sam cikin zuciyata ba haka bane,har yau sumayya sumayya ce bata sauya ba a idanuwa na"
Shiru ya sake yi don ya bata damar fadin ra'ayinta da abinda ke zuciyarta.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*
Chapter 94 · 0% Book details