← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 210

Sashe 13

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanu fa'iza ta dinga binsu da shi,to ko dai harshenta ne kadai ke gaya mata tuggunta yayi dai dai?,ganin sunyi uwar watsi da ita ya sanya ta kasa shiru sai da ta magantu
"Wai muntari bakaji uban gishirin dake cikin abincin nan ba ne?" Bai amsa maga ba sai da ya sake wata lomar
"Wanne abinci fa?"
"Na gabanku mana" ta fada tana nuna kwanon da yatsa tare da qanqance idanu
"Hala kina da matsalar dan dano ko?" Kafeshi tayi da idanu tana tantama,sai kawai ta miqa hannu ta kwaso miyar gabansa ta kai bakinta,tabbas iri daya ce haka ma dandanon iri daya ne,to tsabar iya asiri ne na sumayya yasa bai fahimta ba ko sun tasamma raina mata wayo ne,fa'iza macace da sam bata da siyasar zamantakewa,hakan ne ya sa ta kasa boye fushinta ta tashi ta fice fuuuu ta bar dakin cike da baqinciki,so tayi yau ya ciwa sumayya mutunci sannan ya janyeshi kuma ta kwana da shi yau ta cusa mata baqinciki.

Idanunta ta dora kan mukhtat fuskarta qunshe da tashin hankali,ta bude baki zatayi magana ya dora yatsansa kan lebansa
"Shshshshsh!,kada kice komai,ita ta zuba gishirin kan ido na bayan shigarki wanka,tana zaton bazanci ba,batasan ba maqaryacin so nake miki ba,zan iya cin wanda yafi haka ma,bare ma shekararmu nawa da sumayyaty na santa qwarai wajen iya sarrafa hatsi" yadda ya qare maganar ne ya bata dariya har sai da ta dara din,daga bisani ya wanke mata duk wani damuwa tata suka bige da hira,yace idan ba zata iyaci ba kada ta cuci kanta ta ajjiye ya sama mata wani abu shikam zai iya ci,tace sam tunda har ya iya ci itama sai ta ci,qarshe dai ramun muguntar gun fa'izar ya koma tunda ko banza ta tashi ciki babu komai.

Yau din da kanshi ya mata sai da safe,kishi ya kamata sosai ta dinga rayawa cikin ranta wato zashi yaje yayi abinda anty yahanasun ta umarceshi kenan dazu da safe,ta dinga juyi saman gado ita daya da qyar bacci ya saceta.

Bata jima da fara baccin ba ta dinga jin ihu sama sama cikin barcinta,a sannu ta bude idanunta tarwai,tabbas ba mafarki bane,ihu ne daga dakin fa'izan kuma muryarta ce cike da gunjin kuka,ta kasa kunne sosai ta dinga jin yadda take neman agaji da dauki,runtse idanunta tayi sai kuka ya subuce mata ta sanya hannunta ta toshe dukka kunnuwanta baccin da bata koma ba kenan.

Kiran sallar farko na asuba taji an bude falonta,ta kasa kunne sai kuma taji shuru har akayi kiran sallah na biyu,ta sauko daga san gadon da idanunta wadanda sukayi luhu luhu saboda kuka,ta zira hijabinta ta fito daga dakin jiri da dibarta.

A falon nata taga kamar mutum kwance,gabanta ya fadi da sauri ta koma da baya ta kunna makunni qwan lantarkin falon,haske ya qauraye ko ina,mukhtar ne kwance saman doguwar kujerarta tafin hannunsa dafe da goshinsa.

Dauke kanta tayi tamfar ma bata ganshi ba yayin da shi kuma ya bita da ido har ta fice,sai da ta daura alwala ta dawo sannan ya tashi ya fice,tana kan abun sallarta har gari ya soma haske,sallamarsa taji yana shigowa ta runtse idanunta har ya qaraso gabanta,ya fuskanci me take nufi domin yana da tabbacin mawuyaci ne idan baya jiyo qarajin fa'iza a jiya ba,saboda shi kadai yasan ta'asar da ga tafka mata da gayya.

Muryarsa a tausashe da irin salon dake kwantar da hankali da ratsa sassan jikinta yace
"Sumayya,kiyi haquri don Allah,wlh ban shiga dakin fa'iza a jiya don naci fuskarki ko na bata miki rai ba,kiyi haquri idan ranki ya baci,komai nayi nayi ne saboda koya mata saboda ta fice daga rayuwarmu....kiyi haqur....."
"Ya isa ya mukhtar" ta fada da sauri tana katseshi
"Ka daina bani haquri,matarka ce kamar yadda nake matarka,kuma adalcin kenan" ta fada duk da tana jin daci qasan zuciyarta amma hakan ba zaya hanata fadin gaskiya ba.

Hannunta ya sake kamawa sosai,kana ganin fuskarsa kasan cikin bacin rai tsantsa yake
"Duk da haka nayi da na sanin kasancewa ta tare da ita,fa'iza......." Hannunta ta dora saman bakinsa qwalla da digar mata
"Matarka ce bana son jin komai,don Allah ka tafi ya mukhtar kaji,ka tafi bacci nakeji" da gaske take fadin maganar saboda haka ya saketa ya miqe a sanyaye ya fice,tun tana kukan bilhaqqi har ta koma yi qasa qasa,da haka bacci ya sureta.

A firgice ta farka sakamakon hasken rana da ya dalle ta wanda ke alamta mata gari ya waye sarai,da sauri ta dubi agogo,har qarfe goma na safe,gabanta ya fadi data tuna cewa babu abinda yau tayi a gidan,a hankali ta miqe ta isa falo ta yaye labulen window dinta ta duba dakinsa,a kulle yake da muqulli tana jin mawuyaci ne idan fita kasuwa ba kenan,dawowa tayi uwar dakin ta tsaya gaban madubi don duba idanunta,bata so ta fita har fa'iza ga fuskanci tayi kuka ko ta fuskanci taji kishi ko ta gane abinda ya faru daren jiya cikin gidan har ta raina ta,hudubar anty dije ce boye duk wani abu da zai sa ta gane logonta,bare ta riqeshi ta dinga musguna mata da shi,fuskarta fayau haka ma idanun sun koma babu kumburin,saima haske da suka dada yi,hijabinta ta cire ta daura dankwali saman kanta ta fice tsakar gidan.

Sai da ta kammala aikinta tas tana bakin rijiya tana diban ruwan wanka sannan taga fitowar fa'izan,ta daga kai ta dubeta,da qyar take iya tafiya tamkar yaron da aka yiwa shayi yanzu yanzu,idanun nan sun kumbura sunji jazur,hatta da fuskarta a kumbure take,da alamu ba qaramar izaya mukhtar din ya ganawa rayuwarta ba a jiyan,har qasan ranta sai da sumayyan taji ta tausaya mata,amma da baqar zuciya irinta fa'izan sai data iya samun sararin wulla mata harara tare da fadin
"Baqar manufarki a kanki zata qare,anyi mai wuyar tunda yazo hannu ko,saiki saurari zuwan 'yan dagwai dagwai" ita kanta tasan ta fada ne kawai amma ita daya tasan halin da take ciki,dariya ta qyalqyale da shi sannan tace
"Wai.....a hakan,to bamusan gaibu ba" ta juya ta waiwayenta tare da sheqa dariya ta shige daki abinta don bata ga dacewar tsayawa cacar baki da fa'izan ba,ai kuwa ba qaramin qona mata rai dariyar tayi ba,sai ta dinga jin duk ta muzanta,ta dinga jin tamkar mukhtar ya kwashe duka cin kashin da yayi mata daren jiya ya gayawa sumayyar,ta dinga jin kamar ya gaya mata wace ce ita,jiki a sanyaye da jan qafa ta lallaba ta dibi ruwa ta shiga bandakin.

Bata fito ba balle ta biye mata suyi sai da ta kammala ta shiga daki sannan tayi nata wankan,tana daki tana shiryawa taji kamaf motsi cikin falon ta,bata leqo ba sai data kammala shiryawar,ta fito hannunta dauke da dan kwalinta tana daurawa,fa'iza ce tsaye a falon karo na farko tunda tazo gidan,gaba daya ta shagala da kallon yadda aka tsara falon,babu qarya babu fallasa amma yayi kyau matuqa,komai a tsaftace a killace,sosai baqinciki ya rufe ta na yadda dakin sumayya yafi nata kyau tsadar kaya tsafta da tsari bugu da qari ga yalwa dai dai gwargwado.

"Lafiya dai ko?" Sumayya ta fada bayan ta gama kallon yadda take qarewa dakin nata kallo,juyowa tayi cikin jin kunya da bori,ba tare da ta shirya ba abinda ke zuciyarta ta fito
"Hmmmm,lallai kam,kaga masu daki,kin tatsi muntari kin gyara kanki shi yasa kikewa kowa kallon banza ko?ayi mu gani naga ta yadda za'a mora" murmushi sumayyan tayi ba tare da nuna damuwa kan batunta ba
"Fadi meke tafe da ke nasan dai ba wannan ne ya kawoki ba"cikin qanqance ido fa'izan tace
" eh,ina abun karina?"ta tambaya cikin gadara,bata san cewa yau sumayyan jinta take dai dai da yadda tazo mata ba,dariyar nan ta rainin hankali tayi mata sannan ta zauna kan daya daga cikin kujerunta
"To idan banda abinki fa'iza amarya wanda yayi aika aikar ma ya tsallake ya tafi don me zaki dinga haushin kaza huce kan dami a kaina,ki roqeni kawai na taimaka ma baki abinda zaki sanyawa cikinki ko?".

Sosai ta hasala har ta fara huci,ba shakka da acw da qwarinta babu abinda zai hanata neman dambacewa da sumayyan,sanin cewa babu qarfin sai ta buge da nuna ta da yatsa
" ke baki isa ba wallahi qaramar mara kunya,dududu nawa kike da zan nemi alfarma gunki,na fuskanci kanki ya fara rawa ko bakisan wace fa'iza ba,wallahi sumayya ki kuka da kanki don ke abar tausayi ce nan gaba sai kin zama abarkwatancen wa wasu"
"Bakinki ya sari danyan kashi jeki ki duba kitchen ki dauki da'amin tunda duka don shi kike wannan dai ko?" Ta fada tana miqewa tayi komawarta uwar dakanta,nan ta barta tana hauka sannan daga bisani ta fice,abu goma da ashirin ga wani baqinciki da ta taras,dakin sumayyan ya kere nata da take taqama da shi,kuma tana da zaton cewa daga jikin mukhtar din ta yaga,tana jin dole ta dau mataki kafin zuwan yaran da zasu zama silar zamantowar gidan mallakinta.

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[27/12, 22:44] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

______________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*wa ufawwidu amri ilallah,innal laha basirun bil'ibaad*
__________________________

1⃣0⃣

Yau kam da ta dora girkinta zama tayi cikin kitchen din tana kallo cikin wayarta har takammala girkinta,duk da cewa yau din akwai sauqim zirga zirgar fa'izar tana daka tana jinya,yau daga ita har yaranta sun wataya abunsu.

Yau ma tare sukaci abincin dare,saidai babu fa'izan,don tun sumayyan bata jima da kammalawa ba ta fito ta kamfata ta fice,ita kam sumayyan mamakin shege cin abinci irin na fa'izan take.

Abin jiya akaso a maimaita ko kuma nace har ma ya wuce na jiyan,don kusan har da dambe ne yaso kaurewa tsakanin fa'izan da mukhtar din,ba wai don tana burgeshi ko abinta ya dada shi da qasa bane ya sanya shi dagewa kan sai yayi,ko kadan,yana so ne ta bambance tsakanin aya da tsakuwa,yana so ne ya dasa mata qin abun ta yadda ba zata sake marmari ko gigin nemansa ba.
Chapter 13 · 0% Book details