← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 210

Sashe 87

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Ramadan ya rage saura kwanaki uku,nan sumayya taga tsari,yadda anty dije ke tsara gidan nata tare da sauya abubuwa sabida shigar watan,baki ta sake tana mamaki don su duk basu irin wannan,dariya anty dije tayi
"Da kike mamakin nawa gyaran kice idan kika ga na gidan baaba prof saikin yada idonki?"ido ta qwalalo
"duk kyau da tsaruwar wannan gidan sai an sake masa wani tsarin?"
"Duk shekara iwar haka sai dukka gidan sun sake komai nasu,sai su rabar da tsofaffin ga 'yan aikinsu,wasunsu har kayan sawa da yayi shekarar nan ake canza wardrobe baki dayanta" baki sumayya ta sake tana duban anty dije kamar ita ce ke sanya su
"Gaskiya mutanen nan mabarnata ne,yanzu wannan gidan ba ya isheka har qarshen rayuwarka ba,wani ma idan yana wani gu baisan da wani ba,har meye ne zai tsufa a shekara a sauya shi?"dariya sosai anty dije tayi
" lallai har yau bakisan wannan familyn ba,kowa da irin matsayinsa fa,ita rayuwa kowa da inda Allah ya ajiyeahi,idan kaga rayuwar wasu kai a gunka barna ce da almubazzaranci,ko kaga tsabar warya ce ko bazata yiwu ba,amma kaima da Allah zai kaika irin wannan matsayin babu shakka sai kayi kamar ko fiye da abinda yakeyi,yanzu kamar ni din nan,da wasu zasu ga abinda nake cewa zasuyi nima almubazzaranci bane,amma ba haka bane,idan Allah ya wadataka kana da shi ka sauya to ka bawa na qasa da kai wancan su amfana suma,ba ka qanqame ba ka qanqame jama'a ba,amma.....zauna na gaya miki su waye wadan nan family din kinji"ba musu sumayyan ta zauna tana baza kunne,itama anty dijen zama tayi,kafin tace komai laila ta shigo tana sanar mata tayi baquwa tilas suka katse hirar ta fita wajensu,sumayya ta tashi ta kama mata aikin da ta tafi ta bari.

  *********  ******  ********

      Baki daya a yanzu rayuwar gidan bata yiwa karima dadi,bata da buri a yanzu da ya wuce taga yaranta da mijinta kusa da ita amma abu ya gagara,kowa tsoro da haushin zama kusa da ita yake,hatta da lukman din ma kwanciyar bacci kadai ke kawoshi bangaren,ya sauya mata irin sauyin da bata taba zata ba,bai shiga shirginta indai ba haqqinta na aure zai sauke mata ba,wanda shima yasan idan ya take mata sai Allah ya tuhumeshi,a nan takan so jan ra'ayinsa amma abu yaci tura,da ya gama yake wanka idan an kusa asuba ya zauna karatun qur'ani da addu'o'i har sai an kirayi asuba ya fita yayi sallah,idan ya dawo ya zarce wajen hajiya su hafu da yara suyi karatu sannan su shirya ya miqa su makaranta,idan ya dawo shine zai shigo mata yayi wanka ya fice ko sauraron abincinta baiyi gun hajiya shima yake ci,hakan shi ya sake taka muhimmiyar rawa wajen rugujewar duk wani aiki da zata masa,walau na abinci ko na jinnu,ya tsayawa addu'a abincinta kuwa baici bare ya dameshi,bata gane bata da wayo ba sai sanda taso ta gwada yi masa tawaye kan yadda yake maganar sumayya da daukar yaranta ya kaiwa mama su,ranar taga tijarar da tunda Allah ya hadata da shi bai taba yi mata ba,tayi kuka na fitar rai,a hankali kuma sai ta soma tunanin me yafi zaman lafiya dadi?,me zaisa ba zata haqura da komai ba ta kawo qarshen wannan zaman fagen yaqin da sukeyi,abinda bata sani ba tanqwara busashen itace abune mai wahala,ta riga da ra yiwa kanta mummunar lamba wajensa.

      Duk sanda yaje yakanyi yunqurin karbar adreas din sumayya wajen zainab ko halima,saidai duk sanda yaso yin hakan sai ya taras basa nan suna tahfiz,ita kuwa mama ba wani riqe adress din tayi ba,yaciji yatsa yaji ciwon abun da tun lokacin aurensu da tace zata gidan anty dijen lokacin da shima zaije abujan bai bita ba yaga gidan,da tuni yanzu bakinsa alekum sai ya kama hanya,wayarta kuwa idan ya kira sau biyar idan yaci sa'a zata daga sau daya su gaisa ta tambayi yara,daga haka zata katse kiran sai kuma wani lokacin.

******   ********   ********

       Ranar lahadi da daddare watan azumi ya bayyana,hakan ya sanya litinin daukacin al'umar musulmin duniya suka tashi da azumi a bakinsu,duk gidan kowa na azumi banda minal saboda shekarunta basu qarasa ba,ta fara gwadawa zuwa sha biyu anty dije ta bata abinci,kafin azahar su laila anyi laqwas saman kujera,khalipha an fara mutstsuka idanuwa,dariya sosai sumayya ta dinga sheqa musu yayin da anty dije tayi kicin kicin da fuska don kada ma wani yaga fuskar da zaice zai karya,hafiz ne kadai da qwarinsa da yake shine babba.

       Biyu da rabi bayan sumayya ta kammala sallar azahar tana tilawar qur'ani anty dije ta taddata da hijabi jikinta itama da alama bata jima da gama sallarta ba,gefe ta zauna hakan ya nunawa sumayya magana tazo yi da ita saboda haka tana kaiwa qarshen shafin ta rufe tayi addu'a ta shafa ta waiwayo ga anty dijen
"Ya ibada,ke kam azumi nasaj gwaninki ne,tunda kina na litinin da alhamis dama" murmushi tayi
"Wallahi kam anty"
"Allah ya kawo min sauqi wannan karon shi yasa nace bari nazo na sameki,kinsan duk watan azumi nike wa baabaa prof abinci har a kammala azumin,abban laila ne yasa a dinga yi saboda karamcin dattijon,yana son abinciccikan gargajiya duk da kasancewarsa dan boko,to su mutan gidan sun fishi boko,da azumi basa wani abincin azo a gani sai abinciccikan zamani,ummee ce ke masa lokaci lokaci don itama tana so,to wannan karon ummee sun tafi umra mazan ne kawai suka rage a gidan,duk da kowa na da mai aikinsa amma shima baabaan baison girkin ma'aikata shi danshi ya gado" ta fada tana dariya data tuno shi
"nasa gwanar girkin gargajiya ce ke,ni ki barni da girkin gida ki dinga na baabaa" murmushi tayi
"To ai zan iya ma anty duka,haba,sai kace ba mace ba"
"Nasan zaki iya,ai ranon mama ce,amma kya dai tayani na gidan"
"Tom anty" miqewa anty dijen tayi
"Naga yau garin kam masha Allah akwai hadari,ko yau zamu samu ruwan farko a ranar farko?"
"Allah yasa anty,dama tun muna kano naga irin garuruwan nan kunfi ko ina samun ruwa,ga damunarku itace qarshe wajen tafiya"
"Wallahi masha Allah,muna shan ruwa kam,saidai zafi"
"A hakan anty,duk wannan ac da kuke kwankwada"
"Saikin fita ai sumayya zakiji a jikinki"
"Saidai haka" ta miqe itama tana nannade abun sallahr ta don shiga kitchen saboda su kammala komai kan lokaci.

      Ana la'asar kuwa ruwan farko ya soma sauka zuwa qasa,tana kitchen din a lokacin,sai ta zuge glass tana kallon yadda ruwan ke juqa shukoki yana tayar da qamshin qasa,a rayuwarta tana son damina,murmushi ya subuce mata data tuna sanda suna tare da mukhtar,duk sanda baya gida takan fito ita da yaranta dake tayata zama susha wankansu a ruwan sama,kafin ya dawo ta share gidan ya sauya kayanta kamar bata shiga ruwa ba,amma kallon farko idan ya mata yake gane ta shiga ruwa,musamman gashinta dake saurin fallasata saboda cikarsa da tsahonsa bai bushewa da wuri,abinka da quruciya a lokacin yaron da bai saba qarya ba idan yayi ma sai an ganeshi,sai ta fitittike tace masa wankan tsarki tayi
"Wanne wankan tsarkin,me ya sameki bayan fitata da zakiyi wankan tsarki?" Narai narai take da ido tace itadai wankan tsarki tayi a tunaninta shi kadai ne mafitar da zai yadda ba wasan ruwa tayi ba tunda wankan tsarki ne kadai ake jiqa kai idan za'ayi,idan yaga ta dage sai kawai ya qyalqyale da dariya ita kuwa ta sake hade rai don kada ya gano,tilas yake sakin murmushi yace ya yadda,tana kawowa nan a tunaninta ta saki itama murmushin qwalla na bin kuncinta
"Allah ya gafarta maka ya mukhtar,ya kyauta makwancinka" tayi furucin tana goge hawayen da tafin hannunta,baki daya sai walwalarta ta tafi kamar yadda hakan ke faruwa yawancin lokuta idan ta tunashi,girkin take amma zuciyarta babu dadi,duk da haka hakan bai hanata hanzari ha,kafin kace me wannan ta gama girkin baabaa prof,dashishi ta masa da miyar ganye,wanda kallonta kadai ya isa ya tsinkar maka da yawu,tun ba yau ba tun tana qaramarta haka hannunta yake da iya sanwa,ballantana a shekaru takwas zuwa tara da tayi gidan aure ya sake maida ta gwana fagen iya girki.

      Ko da anty dije tazo tayi mamakin saurin girkinta,don tuni suma ta musu miya,miyar qwaice da alayyahu tayi shar tayi kyau sosao,gun any dijen ta koya amma sai take ganin kamar ta fita ma iyawa,kasancewar sumayya bai bala'in qwaqwalwa da saurin dauke abu,cewa tayi ta bar mata sauran ta qarasa tunda tayi kusan rabin aikin gidan bayan na baabaan.

      Daki ta shiga tayi wanka,saura kusan awa guda kafin a sha ruwa,ta fito ta shirya kanta cikin atamfa riga da zani,kanta ta daure da dan kwali ta dauki carbinta ta fito falo,dariya ta zo mata ganin yadda laila ta sake bajewa saman kujera,khalipha kuwa tuni bacci yayi awan gaba da shi,bata ce musu komai ba ta sauya tasha zuwa sunna t.v wanda suka sako tafsirij shehun malaminta sheik Ali ibrahim isah fantami,sosai take jin dadin tafsir din har zuwa wani lokaci data koma kitchen din ta tadda anty dije ta kammala komai,ita ta dinga kwaso kayan tana shiryawa saman dining anty dije kuma ta shiga wanka ganin saura mintuna akira sallah.

     Lokaci qalilan gidan ya kacame,kowa na kaiwa baki,daga nan uncle farouq ya kada kansu zuwa masallaci sukayi sallar magariba.

     Babu kowa gidan duka sun fita sallar asham tarawih,ta sanya hijabinta zata tada tata kenan cikin gidan anty dije ta shigo itama sanye da hijabi
"Sumayya,yanzu abban laila ya kirani,yace ki miqa abincin baabaa prof,ga driver nan yana waje zai amshi nashi abinci sai ya riqe miki wasu kwanukan" babu musu yau kam sai faduwar gaba jin an ambacin gidan tace to,dirvan nasu shi ya dauki kwandon ita kuma ta dauki flask daya da ya rage.
Chapter 87 · 0% Book details