← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 210

Sashe 9

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta tsabtace ko ina har zuwa dakinta sannan ta shiga tayi wanka,tsab ta shirya cikim daya daga cikin ragowar sabbin dinkunanta,atamfa ce dinkin riga da skert da ta fidda shape din qugunta yayi das,bata sake yarda da kyawun dinkin ba sai da taga yadda yayi mata a jikinta,maman nana ce ta zabar mata shi.

Tsakar gidan ta dawo,kitchen ta shiga,sai yanzu taga jeran da aka ma fa'iza,za'a iya cewa ta fita duk wani kayan aiki na kitchen nesa ba kusa ba,bangaren ta ta nufa ta wanke tukunya ta tara ruwa ta dora ruwan tea wanda ya sha hadin kayan qamshi sannan ta koma gefe ta fara fere dankalin turawa,babu abinda mukhtar din bai siya ba na kayan abinci tun shekaran jiya.

Aikin take amma zuciyarta a cunkushe take,fuskarta kawau zaka kalla ta gaya maka hakan koda bata bude baki ta fada ba,ta gama firar ta wanke sannan ta juye shayin cikin wani sabon tea flask wanda yake seat ne da farantansa da kofuna.

Tana cikin suyar dankalin ta dinga juyo motsi a tsakar gidan,bata fasa abinda take ba kamar yadda bata damu tasan waye cikin su biyun ba,aikinta taci gaba da yi har lokacin da taji hancinta ya cika da qamshin turaren mukhtar,kamar ta waiwaya sai ta fasa,wani haushinsa ta dinga ji tana ji hakanan.

"Sannu da aiki uwar gida na" taji ya ambata yana takowa zuwa cikin kitchen din,ta dan waiwayo hannunta riqe da abun tsame dankalin yana tsaye a bayanta gab da ita,maimakon ta tarad da annuri da qyalli irin na ango sai ta tarad da sabanin hakan,fuskarsa tana nan kamar kullum
"Ina kwana" ta fada a taqaice fuskarta a daure ba tare da ta damu da yanayin fuskarsa ba,maimakon ya amsa sai taji ya sanya hannu ya karbe abun tsamewar ya matsa gefanta ya shiga kwashe dankalin wanda shi yayi saura cikin man
"Sumy,me yake faruwa?" Ya tambayeta yayin da take jingine da kantocin fa'iza hannunta harde a qirjinta
"Kamar me?" Ta tambayeshi tana debo qwan da zata soya tana zubawa cikin kwano,ya bata amsa sanda yake qwace bowl din ya fara fasa qwayayen
"Babu fara'ar nan a fuskarki yau ko kadan" shiru tayi masa bata da niyyar fankawa,ganin haka yasa shima ya ja bakinsa ya tsuke har ya kammala suyar.

Nata kayan karin ta diba ta kammale musu nasu a kitchen ta wuce dakinta,tana zaune kan kujera tana kallon mbc yayin da take zarar dankalin da dai dai da dai dai tana ci tamkar bata so mukhtar ya shigo dakin,yayi kyau cikin dinkin shadda ruwan qasa mai turuwa sai qamshi ke tashi
"A'aha,ya kike karyawa ke kadai ina namu break din"
"Yana kitchen" ta fadi tana ajjiye plate din hannunta,kai ya girgiza yana zama gefanta
"Ba haka na tsara ba,ki shirya mana a nan falon naki,gaba daya zamu karya,daga nan ki shiga ki kira fa'izan" bata ce komai ba ta miqe ta fita din ta dinga kwaso kayan tana jerawa har ta kammala.

A qofar dakin ta tsaya ta qwanqwasa mata,tunda tana ganin bai kyautu ta fada mata kai tsaye ba tunda ba falo gareta ba,sai data qwanqwasa kusan sau biyar sannan tace cikin alamun fusata
"Wai waye ne?"
"Sumayya ce", sai data bata kusan minti biyu sannan tace
" shigo"ciki ciki kamar wadda aka cusawa tsumma a baki.

Kan gado ta tarad da ita kwance,ta samu gefan kujera tadan dosana tana qoqarin dora murmushi saman fuskarta
"Sannu amarya" cikin shan qamshi da dauke kai tace
"Yauwa" ta danyi jim sannan tace
"Amm.....dama mukhtar ne yace ki fito mu karya" shiru tayi kamar bata ji ba sannan ta bude baki da qyar tace
"Bazan samu fitowa ba,kuna iya karyawa", bata sake cewa komai ba ta miqe ta fice ta isarwa da mukhtar saqon,kai ya kada sannan yace da ita
" zauna mu karya"gefan kujera ta zauna tana kada kai
"Nikam na qoshi"
"Ban son musu kinji ko,oya sauko" ya fada yana hada tea cup biyu,bata sake cewa komai din ba ta sauko ta karbi cup din tea din daga hannunsa ta fara kurba.

Duk yadda yaso janta da hira ta kasa sakin jikinta sama sama take amsa masa shima bai tsawwala ba har suka kammala ya miqe ya ajjiye mata kudin cefane ya fita.

Tattare kwanukan tayi da nufin fita da su ta dauraye,a bakin qofa taga fa'izan a tsaye mukhtar na bakin qofar yana sanya takalminsa,fuskarta a quntace da alama wani maganar take gaya masa
"Sai na dawo" ya fada bayan ya kammala sanya takalminsa,bata ce komai ba sai komawa dakinta da tayi rai bace,sumayya ta miqe daga durquson da tayi ta bi bayansa ta bude masa qofa kamar yadda ta saba
"A dawo lafiya Allah ya kiyaye ya bada sa'a"
"Amin my sumy" ya fada cikin jim dadi.

Bakin famfon ta dawo taci gaba da wanke wankenta,tana iya jiyo qunquni daga dakin fa'izan wanda batasan dawa take ko me take cewa ba.

Tana gab da gama wanke wanken taji ta turo qofar ta fito,qerere tayi a kan sumayyan
"Ke" ta fada cikin gadara,dago kanta tayi a hankali tana dubanta,sai yanzu ne zata iya gane kamannin fa'izan,baqa ce sosai mai matsakaicin jiki,bata da qiba bata da rama,tana da dogon hanci mai tsini sai qananun idanu,aqalla ta tasamma shekara a shirin da uku zuwa da hudu zata bata shekaru biyar ko shida kenan
"Yana kitchen" ta fada tana ci gaba da wanke wankenta zuciyarta na bugawa,addu'a take cikin zuciyarta kada Allah ya sanya fa'iza na daya daga cikin masifaffun kishiyoyi,indai ko haka ne bata san ta inda zata sanya kanta ba,bata san inda ta inda zata fara tarar wannan bala'in ba,mutum ce ita tun asali da bata son tashin hankali saboda sam bata iya ba,wani tsaki ta ja sannan ta juya zuwa cikin kitchen din.

Sai gata ta fito hannunya dauke da flask din data zuba mata dankalin don kada yayi sanyi,bude flaak din yayi ta sake tsayuwa a kanta cikin hayaniya tace
"Wai ke,kina nufin wannan abun zanci da ya sassanqame yayi sanyi?" Sai ta kuma dagowa tana dubanta
"Ina zaton kamar baiyi sanyin da zaki kasa ci ba,tunda cikin flask yake ko" tayi shiru tana jira taji ko zata tanka
"Shi yasa tun dazun ya mukhtar yace ko fito mu karya din gudun kada yayi sanyin"ta fada tana dan murmushi

Zaro ido tayi cikin masifa
"Iyeee,ashe abinda ake fada gaskiya ne lallai yarinya baki san wace fa'iza ba to banyi niyyar karyawar ba alokacin,ko dole ne?,gidan miji na ne fa,saboda haka babu wanda ya isa ya takurani sai abinda naga dama shi zanyi,saboda haka ki kiyayi shiga hurumina" ta juya fuuu ta shige kitchen din.

Ita dai binta kawai tayi da ido abun na bata mamaki,me tayi mata daga yin maganar da bata kai ta kawo ba?,tana tattare kayan zata maida kitchen din sai gata ta fito hannunta dauke sa dan matsakaicin kwandon tace taliya cike da dankali daya hannun wuqa da kujera 'yar tsuguno ta dawo bakin kitchen din ta zauna.

Bata ce mata komai ba ta rabe ta ta shiga kitchen din ta maida kayan wanke wanken muhallinsu ta jera ta sake goge gurin sannan ta fito.

Zamanta kenan taji muryar yaranta na sallama,murmushi tayi tana miqewa,ko banza ta samu anokan debe kewa,don ta lura fa'izar akwai matsala tattare da ita,haka take ko wani abun ke damunta oho Allah masani,miqewa tayi ta fito da tabarma hannunta,da yake wani lokaci idan bata so su bata mata gu a tsakar gida suke zamansu.

Tana shimfida tabarmar yaran na gaida fa'iza da dai dai da dai dai,ta amsa musu babu yabo babu fallasa,suka qaraso gun antyn tasu.

Tana tsakiyarsu tana biyewa surutunsu,fa'iza na kitchen tana fama da suyar uban dankali da qwai wanda a zahiri yafi qarfinta,so take tun daga yau ta fara nunawa sumayya ikonta cikin gidan kafin ta haifo yaran da zasu zama ajalin zamanta cikin gidan,kamar yadda yake cikin KUNDIN BURINSU ita da su yaya yahanasu.

har zuciyarta sumayya take jin dadin hirarta da yaran,duk wani bacin ranta ya gudu,ta miqe ta nufi kitchen don dauko dankalin da fa'izar taqi ci ta rarrabawa yaran don kada ayi asararsa,a nan taga uban dankalin da fa'izar ke soyawa daidai lokacin data kammala ta juye cikin babban bowl da tadauka ta fice,bata tanka ba tunda dazun ta fara mata da jan kunnem fita daga sabgarta.

'Yar carafke yaran keyi musu ya sarqe tsakaninsu kan rinton da aisha tayi musu,sumayya nata qoqarin sulhuntawa,tsawa suka ji wadda ta sanya su yin shiru baki dayansu suka waiwaya suna kallonta
"Dalla malamai kun cikawa mutane kunne,ina buqatar nayi ramuwar bacci kun hana mutane aikin banza aikim wofi,to wallahi bazan lamunci takura cikin gida na ba ku kintsa bakinku" ta banko qofar tata ta shige ciki.

Tsuru tsuru yaran sukayi saboda basu taba ganin an musu haka cikin gidan ba,sumayya ce tayi qarfin halin yin murmushi sannan ta miqe cikin son bagarar da abinda tayi musun
"Ku zo kuyimin cefane maza" nan suka miqe da hanzarinsu kuwa ta rararba musu aiken suka fice,yayin da ita kuma ta tattare tabarmar ta sake share gun kafin su dawo,sannan ta moma kitchen ta gyara duk inda fa'iza taci ubansa har bangaren fa'izar duka.

Bayan sun dawo ta gyara kayan miyar ta bada suka kai mata markade,suna dawowa ta rarraba musu alewa ta turasu gida ganin qarfe daya na rana tayi saboda zuwa islamiyya.

Shinkafa da miya da wake tayi niyyar dafawa a abincin rana,tunda mukhtar ya aiko da nama daga kasuwa,tana tsakar gida tana yankan salad ta juyo sallama da muryoyin mutane,ta daga kanta tana amsawa,baqi ne su kusan shida
"Sannunku da zuwa" ta fada fuskarta a sake,shigewarsu sukayi yayin da uku daga ciki suka juyo suka mata kallon banza kana suka wuce,sanyi sosai jikinta yayi,wai dama haka ake?,haka ake kishin ne wai?,ita kam sam bata sani ba ji take qwaqwalwarta ta kasa jan zaren ko wanne tunani.
Chapter 9 · 0% Book details