← Book details Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 210

Sashe 194

Kundin Qaddarata Final Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Dukkanin maganganunsa ba damunta sukayi ba a yanzu,abu daya tak ke mata yawo cikin kwanya da qwaqwalwa,so qauna kulawa da tsantsar soyayya da ta gani zalla a qwayar idanunshi yana nunawa ga ciki dama wadda ke dauke da cikin,me yake shirin faruwa ne?,shine tambayar da take wa kanta,a hankali qwaqwalwarta ta soma mata tariyar wasu shekaru can baya da suka shude,shekarun da a cikinsu ta fidda mahaifarta,a sanda anty kubra ke zabga mata fada,a lokacin da take gaya mata tayi kuskure,take gaya mata zata iya dana sani a gaba,take shaida mata matakin kama almustapha a hannu da kyau shine ta ajjiye masa iri,ta hada jini da irin gidan baban,shine zata samu dukkan abinda take so,zata zama tasu ta har abada,jinta take kawai a sannan,gani take labarin qanzon kurege ne kawai,tunda bata ga wani damuwa ko alamu tattare da da almustaphan ba,saidai a yanzu jikinta ya soma sanyi,wutar kishi ta soma nuna mata akwai wani abu dake shirin faruwa,tattalin da take gani wajenshi a kanta ya zarce soyayyar da yake mata ita daya face harda ta abinda ke cikinta,indai ko haka ne itace mafi cancanta data samu wannan launin soyayya da qauna mai ratsa gangar jiki da zuciya,saidai zata sanya ido taga shin abinda take hasashen haka ne?.

*gobe ina da uziri,idan kuka jini shiru saidai kuyi haquri,duk da zanso ace na muku,so nake mu kammala littafin nan kusa in sha Allah,na gode*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣0⃣3⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa*

*kuyi guzuri,amma mafi alkhairin guziri shine TSORON ALLAH*
___________________________________

        Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali take renin cikinta,wanda bata taba sanin hakan kwanciyar hankali ke da dadi ba yayin rainon ciki sai yanzu,bata da wata matsala yanzu gaba daya a kafatanin rayuwarta,kullum kwanan duniya farinciki ke sake riskar rayuwarta,tako wanne bangare rayuwa na mata kyau fiye da yadda take so,gefe guda ga mai gidanta mai share kukanta yana tare da ita ako da yaushe,ba abinda ta nema cikin rayuwarta ta rasa,ko da yaushe suna waya da dukkan 'yan gida,halima tuni cikinta ya tsufa dab take da haihuwa,abdallah har yau na wajensu ya dawo wajenta baki daya,ya zama tamkar danta,kai idan ba gaya maka akayi ba bazaka taba cewa basu suka haifeshi ba su da abdur rahman,zainab ma ta samu wani cikin bayan barin da tayi,amira ana can ana fama da laulayi wanda ya sanyata tayi laqwas,ashe da wasa farin garki,nafisa qawarta matar auwal itama ana can ana fama,ko yaushe suna waya tare da yiwa juna fatan sauka lafiya.

       Sulaiman wato malam mahaifin sumayya tuni lamura sunyi nisa,ci gaba ake ci gaba da samu cikin gidajen gonakinsa,ya dauki ma'aikata sosai da zasu kula masa da gidajen gonar nashi dake gwambe kano da abuja,shike kula da na kano,na gwambe sun sake diban samarin dake cikin ainihin karkararsu,na abuja kuwa ya bar komai wajen baban tunda yafishin sanin ya yanayun garin yake,tuni malam din ya soma zama wani na musamman shima,gida ya gina musu yalwatacce wanda aka qawati shi da kayan alatu da more rayuwa,sashe biyu ne madaidaita hakan ya sanya yaya abubakar dauko meenat matarshi suka dawo daya sashen da yaransu guda uku,hakan ya yiwa mama dadi qwarai,don dama gidan ya zama sai ita kadai,gashi ya mata girman da bazata iya zama ita kadai din ha,amma dawowarsu amina da jikokin maman hakan sai yayi mata dai dai,zumuncin baba da malam din kuwa sai abinda yayi gaba,don basu cikakken wata basu ga juna ba,ko malam din yazo ko kuma baba yaje,da haka wani lokaci suke zuwa da matansu,wanda hakan ya haifar da sabo sosai tsakanin anty maamaa mama da kuma ummi.

       Ta gefan hajiya su'ad kuwa baki daya ta gama karance takun almustapha tsaf ta gane komai,son haihuwr yake kaman ya jawo randa yaron zai fito duniya,cikin qanqanin lokaci jikinta yayi sanyi ya mutu baki daya,a hankali ta soma tunanin me yasa bata fahimvi yana son yara ba?,me yasa bata gane ba?,tun daga sanda yace zaya bude gidan marayu da yanda yake nacin zuwa yaci ace ta karanci cewa shi din mutum me mai son yara da son mu'amala da su,kullum kwanan duniya ta kwanta tunaninta shine yadda zata gyara kurenta,ta yaya zata ganta da ciki?,ta yaya zata haihu?,har yau abinda ke sakadar zuciyarta kenan,batasan da wa zata yi shawara ba,anty kubra ce,saidai ta tabbatar cewa fada zata sha kafin daga bisani tace ita din ba ruwanta,da mamarta kawai zata shawarta,saidai maman sunyi tafiya da babanta basa samun zama,lokaci kawai take jira na dawowarta ta zauna susan yadda zasu gyara lamarin.

  ******  *******    ********

       A hankali take tako lallausan carfet dake dakin zuwa inda yake zaune shirye cikin jallabiya ta maza dark brown,ya dora hirami akanshi wanda ya dace da jallabiyar,hannunshi daure da baqin agogo,system ce gabanshi yana rage wasu ayyuka yayin da yake tsumayin fitowarta,zasu je siyayyan kayan baby ne,duk da cewa yana daga gida zai iya fadin duk abinda yake so a hado masa daga dukkan kamfanin da yakeso cikin fadin duniya,saidai yana so su fita su shiga kanti da kanta don sumayyan ta tattaka da qafafunta tayi zagaye saboda lafiyarta.

       Sanye take da abaya peach mai adon duwatsu masu qyalli,peach mai turuwa da mai haske,tayi rolling da wani wadataccen mayafi  dark peach,plate shoes ne a qafarta shima kalar rigar,sosai cikinta ya fito kai kace yau ko gobe ne haihuwar,wanda alokacin baki daya bai wuce wata bakwai da sati biyu ba,a jikinsa yaji fitowarta ya daga kai a hankali yana kallonta,baisan sanda murmushi ya subu ce masa ba,aduk sanda kake da buqatar ganin fara'a qarara kan fuskarshi to yayi tozali da sumayya tana takowa zuwa gareshi dauke da cikinsa,duk duniya shine abu na farko dake faranta masa rai a duk yanayi ko matakin da ya tsinci kanshi,sau tari yakan ayyana me zata haifa cikin ranshi,jikinsa na bashi cewa twince ne musamman idan yana mata awo,saidai bai taba sha'awar duba meye acikinta ba,yace koma meye yana marhaban da zuwanshi,miqeww yayi tsaye ha cimmata a inda take kafin ta qaraso,ya bude tafin hannunshi ya sanya nata yana murmushi
"Wai wannan cikin naki anya babe?"
"Mene?" Ta tambayeshi tana daga gira,tattausan murmushi ya sake mata yana kada kai
"Shikenan.....muga qafar taki,ina fata ba kumburi ko?" Silifa din ta zame tana tayashi duba qafar tare da cewa
"Eh yanzu kam babu,tun jiya bai sake yi ba" gabanta ya durqusa yana mammatsa qafar kafin ya miqe yana cewa
"Masha Allah,Allah ya raba lafiya" dariya ta qwace mata ta dubeshi yanayin yadda ya furta maganar kaman mace
"Amin abu abdallah"
"Ummu abdallah...da zarar kin haihu fa za'a sauyan suna,saboda na zama daddyn yara da yawa,zan koma ABUL AULAD ke kuma UMMUL AULAD" idanu ta lumshe tana jifanshi da wani kallo,sosai sunan yayi mata,tana mamaki idan taju yana larabci,duk da hakan bai rasa nasana da zamanshi cikinsu,kai take gyadawa cike da gamsuwa
"Hakan yayi,amma har yara nawa zamu haifa da suka zama AULAD?" idanunshi yadan zaro yana kallonta
"Ko dozen haka ai sunyi ko?" Dariya ta tuntsire da ita shina yana tayata
"Eh lallai kayi dariya mana,bakusan yadda ake ji ba,a haifa muku kawai" qugunta ya kama suka fara takawa yana bata amsa
"Da gaske wallahi Allah nake miki,ina son naga wannan ya dane min wuya,wannan ya zauna acinya,wancan ya kaman kunne,wannan yana jamim hanci,wannan yamin fitsari wancan yamin bayan gida" dariya sosai ta kamata yadda ya taqarqare yana zuba bayani,har sai sata dafe cikinta tare da dakatawa da tafiya tana dubanshi
"Kace nanny zaka koma kenan cikin gidan?" Giranshi ya dage mata
"Laifi ne?,bakisan ma'aiki yana taya matanshi ayyukan gida ba?,sunnah ne fa" murmushi taci gaba da yi,sai yayi bala'in burgeta ba kadan ba,haqiqa kyawawan halayensa basa rasa nasaba da iliminsa
"Haka ne,Allah yasa mu dace"
"Amin beauty" ya fada yana jan hancinta wanda ya bude ya sake girma,sai ta kwabe fuska tana dubanshi shi kuma yama boye dariyarsa
"Kawai kace mummuna mana ha'an?" Dariyar ta qwace masa baki daya,yasa hannu yana toshe bakinsa,sai ta soma kukan qarya tana buga qafa daya don babu damar yin rigima sosai,riqe hannayenta yayi sosai yana bata haquri kafin yace
"Ba wani yanayi da zaizo wanda zai sanya na kasa ganin kyanki,ko yaushe ke mai kyau ce a wajena,ko da kuwa duka duniya basa gani,bare ma ha wannan ba,matuqar dabi'unki na tattare da ke ko kece sarauniyar munana na duniya haka nakeson abata,kinsan me?" Sai ta kada kai tana sauraronshi
"Dabi'a furuci lafazi da mu'amala sune abu na farko dake tallata dan adam,sune abubuwa dake jefa soyayyar mutum cikin zukatan kowanne bil'adam,koda mutane basu shirya sonka ba,sai kyawawan dabi'unka su rinjayesu su soka,haka kika mamayeni babe,sonki ya cika qirjina" murmushi tayi ta sadda kai,shima fuskarsa dauke da murmushin ya saka hannunshi ya daga kanta
"Ita kunya daure take da imani,idan aka dauke daya dole daya ya tashi haka annabi S A W yace,kenan,duk wajen da kaga babu kunya to tabbas babu imani a wajen,haka wajen da babu imani to kunya tayi qaura,duka kin hada my summy,don haka kin cancanci duk wanu nau'in so da kulawa" yatsunshu uku ta riqe tana dubanshi
"Ummm ummmm,daina fasamin kai"
"Kin taba ji ko ganin na miki qarya" kai ta kada alamar a'a,don bai taba yi matan ba,koda gaskiyar da zai fada zata qona mata rai bai fasa fada din
"Na gode,ubangiji yaci gaba da shiga cikin lamarinmu" sai da yayi kissing goshinta sannan ya amsa da amin
"Muje ki kira su'ad mu wuce ko?"
"To....." Sautin bai gama fita ba suka ji anja tsaki,suka waiwaya suna dubanta sanda take daga labule tana ficewa,ranshi ya baci sosai,me ya kawota har cikin falon sumayyan?,bayan can ba shigowa take ba?,bama wannan ba,tunda suke tsaye tana wajen tana kallonsu,da wani abu suke kuma na daban fa?,ba sallama ba neman izini?,sumayya bata ce komai ba haka shima,sai yayi gaba ta tako a hankali ta biyo bayanshi,
"Shiga kice mata ta fito" ya fadi yana gyara agigon hannunsa
"To" ta fada tana takawa da irin tafiyar masu ciki,ya bita da kallo da idanunshi har ta shiga.
Chapter 194 · 0% Book details